Breaking News

Tsutsar nama 47

 *_Typing📲_*

   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_






_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_

______________


_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_



https://chat.whatsapp.com/Cce1etNkvVKCBlgSqXa4Ek


___________


........Tun daga shigowar ƴan sanda har fitarsu a gidan Mum ta sani, amma batako leƙo ba. Sun tafi ma babu jimawa sai ga Mamanta da ƙanwarta dake aure a Bauchi. Acewarta tazo ne bikin Samraah domin yima Mom Kara. Bata bari sun zauna a falo ba ta shige dasu bedroom ɗinta. Da kanta kuma ta fito ta haɗa musu abinci takai musu. Ko kunya babu yanda ƙanwarta ta cire mayafi ta fara lodar abinci haka itama Maman tayi. Kai bakace a gidan suruki take ba. Bayani ta sake ma ƙanwar tata akan duk yanda aka samo Samraah, dan ita Mamansu tasan komai. Ƴar uwar tata kai ta jinjina. Sai kuma tai ɗan jimm alamar tunani,  kafin ta sake ɗagowa tana kallonsu bayan ta gama ƙulla abinda take ganin zai fanshi yarinyar nan tsakaninta da ALLAH. Dan magana ta gaskiya ita su Samraah sun jima suna bata tausayi, sai dai bazata iya fitowa ta faɗa ba dan tana shakkar Yayar tata da Mamansu saboda masifaffu ne na bugawa a jarida. Amma tana ji a ranta a wannan gaɓar bazata bari a cutama marainiyar ALLAH ba. Sai dai dole tai komai cikin siyasa. “Niko inada shawara”. Ta faɗa kanta tsaye.duk sake maida hankali sukai a kanta. Cike da zumuɗi Mum tace, “Miye shawarar Ikili, dan ALLAH faɗi muji”.

       Numfashi Ikilima ta sauke tare da ajiye cokalin hannunta ta sake fuskantarsu. “Ban sani ba shawarar ko zata gamsar daku, amma dai a yanayin da nake gani kamar guri ya ƙure mana a yanzu zata iya zama mafita. Mizai hana mubar yarinyar nan tai aurenta kawai. Bayan bikin mu duƙufa samowa Baby mijin aure na garari da yafi shi wannan yaron. Bayan itama ansha nata bikin mun nunama musu koda goma ta lalace tafi biyar albarka, sannan mu fara shiri akan komai ma da muke ganin ya dace akan auren nata. Dalilina na kawo wannan shawarar shine idan fa muka hana auren nan kamar mun gogama gidan nan wani baƙin fenti ne. Kun san dai halin mutane ai, hakan kuma na nufin kammu muka cutar tunda namu yaran ne dai basuyi aure ba a bayanta, dan ita wani zai iya jin tausayinta yazo ya aureta, sannan mu za'aita zagi da zargin mun hana ko muna mata baƙin ciki. Amma idan muka bari akayi hankali kwance babu mai aibanta mu balle idan mutanen kirki sun zo neman auren su Bibaa wani shege ya sokemu. Kunga mun samu nasara biyu kenan, mun kuɓutar da yaranmu, sannan mun sama musu abinda muke fata. Yo har miye wani Mansoor yake ma komi ALLAH na tuba. Shi da dukiyar ba tasa bace ta babansa ce.  Mu ɗan gaske zamu samo mai dukiyar kansa da kansa. Dama ba akwai mutumin nan daya haukace akan baby na anguwarmu ba amma tanata masa wulaƙanci ita bazata zauna da kishiya ba. To wlhy yanzu yazo nan Kano yayi wani mahaukacin gida a hotoro g.r.a ina gaya muku kuma aure yake son yi ruwa a jallo ya saka matar anan, su kuma waɗan can zasu cigaba da zamansu can Bauchin saboda ya musu tayi sunce su bazasu iya barin mahaifarsu da ƴan uwansu ba. Amma yaya kuka gani?”.

     Cike da zumuɗi Maman ta ce, “Ni dai wannan shawara tamun wlhy Ikilima, amma ke Jalilah yaya kika gani?”.

        Shiru Mun tai kamar bazatace komai ba, sai kuma ta sauke numfashi mai nauyi da faɗin, “Nima shawarar ta ɗan mun, sai dai ina tsoron tsutsun Baby wlhy, Dan nasan yanda ta tsani kishiya...”

     “Yo biye mata zamuyi, tuni zamu shiga mu fita a dasa mata sonshi a zuciya sanda ma zata soshin fawa tai shawara. Mufa muka haifeta ba itace ta haifemu ba. Kishiyoyi kuwa ai dasu da babu duk ɗaya ne tunda ba'a waje guda zasu zauna ba”.

     “Yo Mama ko waje guna ne Baby bata da matsala. Dan matansa wlhy a hakan ma kowa rayuwarsa yake babu wadda ta damu da wata tunda kowa da gidanta kuma kowacce kuɗi take juyawa na hauka. Yi kishin ma fa dama matan malam shehune sukafi zaman yin na haukannan aita damben tsiya da hayaniya. Amma mata masu aji da kuɗin nan zakiga kishin ma na ƴan boko akeyi, itama kuma dai tanada iliminta babu abinda za'a nuna mata. Kuma tana shiga zai bata maƙudan kuɗi ta fara kasuwanci kamar sauran dan haka yake yi”

      “Hakane wlhy Ikilima. Ni kubar komai a hannuna kawai zanyi maganinta, yanzun kam hidimar biki duk mu ware aitayinta damu. Ai kwantan mage zamu musu a yayin kama ɓera, tuni sai suzo hannunmu batare da sun farga ba”....



      (😂ALLAH ya rabamu da son zuciya to).




💦🌟💦🌟💦🌟💦


     Zaune yake a office yana ƴan ayyukansa sakatariyarsa ta shigo ta sanar masa d.c.o yazo yana son ganinsa. Karo na farko da MD yaji ransa ya fara ɓaci da bibbinin da d.c.o ɗin ke masa. Idan yace da yana da dalili yanzu kam shi baiga dalilin ba. Samraah dai ce ta kuma dawo sai me kuma, shi ma yaje dubata tare da staffs nasu har asibiti. To minene kuma na zuwa masa office yau. Rashin amsa ya sashi jan sirrin tsaki, tare da bama sakatariya umarnin ta barsa ya shigo.

    Fitarta bai fi da mintuna uku ba ko sai ga d.c.o ɗin ya shigo, sun gaisa cike da girmama juna. Kafin MD ya ce, “Yallaɓai akwai wata matsala ne?”.

    “No babu matsalar komai MD. Waccan dai matsalar ce akan staff ɗinku Samraah Abdul-wahab Gwarzo. Dan kasan koda ta bayyana ya kamata mu cigaba da bibiyar case ɗin domin gano da kama wanda sukai kidnapping ɗinta kodan musan dalilinsu”.

           “Hakan nada ƙyau yallaɓai. Domin muma zamu so ace an kama sun. Sai dai muna ƙarama ALLAH godiya da kuɓutar tata cikin ƙoshin lafiya. Yanzu mike tafe da kai?”.

      “Uhm kamar dai yanda aka saba zamu sake gayyatarka office ɗin mu idan babu damuwa. Kana kuma da damar muje ka samemu a can, ko mu tafi tare”.

     Murmushi MD yayi mai ƙayatarwa. Sai kuma cikin rashin damuwa ya ce, “Babu matsala muje ɗin kawai, dan bawani aiki nake da shi ba sosai yanzun. Zuwa anjima kuma aikin zai iya shamin kai, kaga kuma bai ƙyautu ace ban amsa gayyatar ba”

            “To Masha ALLAH, hakane kam mun gode sosai”.

    Murmushi kawai MD ya sake masa yana miƙewa. A jere suka fice suna ƴar hirarsu tamkar wasu abokai. Dan haka sauran staffs basu fahimci komai ba face tunanin akan dai case ɗin Samraah ɗin ne. Kuma babu wani damuwa a cikin ganin MD da ƴan sandan dake bincike akan case ɗin tunda ba yau ne mafari ba. Suma kansu dai duk sai da suka sha tambayoyi a kwanakin baya....



       💢🌟💢🌟💢🌟💢


  Kwanaki na biyu kenan da dawowa gida. Kwanaki biyu kuma kacal ya rage ɗaurin aurena. Dan zuwa yau har baƙin kusa sun fara isowa musamman dangi na jiki sosai. Ga Aunty Zakiyya ta duƙufa min gyaran jiki da ɗuramin abubuwa. Niko dana faki idonta sai na zubar dan bana sha sosai. Abinda zai baku mamaki duk da haramin biki da gida ya fara ɗauka ga masu gidan babu wani alamar motsi irin na biki a tattare da su. Dan hatta da abinci da aka girkama baƙin dake a gidan yau Yaya Musaddiq ne ya kawosa. Suko su Gwaggo suka girka batare da sun bi takan Mum daketa faman ɗacin rai ba. Shi dai Abba saboda su Gwaggo Gudidi yana ɗan nuna alamar damuwa da shirye-shirye. Sai dai fa bana aljihu ba na gayyatar mutanensa kawai, sai kuma takurama Yaya Musaddiq da yake ta bayan fage akan kuɗin kayan ɗakina da wanda za'ai hidimar abincin biki. Shiko Yaya Musaddiq nata masa zame-zame. Sai a yau ya fito fili ya shaida masa karya damu shi ya riga da ya kammala komai. Dan hatta da kayan kitchen ɗina ma a tanade suke tuni. Hakama kayan gado kafintan ya jima da kammalasu duk da Mansoor yace kar ayi shi baibi ta nasa ba. Wannan zance ya ƙona zuciyar Abba matuƙa. Amma ya gagara magana kodan mutane dake cike a gidan, yasan fitowar zancen babban abin kunya ne a garesa musamman a wajen danginsu dana ɓangaren mahaifinmu.

          Ban gayyaci wasu ƙawaye ba dan banda su, amma a ranar da yamma sai ga su Ruƙayya ƴan Office dinmu da gayyar ƴan ajinmu na islamiyya. Naji daɗin ganinsu sosai, dan ko kusa banyi zato ba. A bakinsu na fara jin ƙananun maganganu akan rashin kawo kayan da zanyi amfani dasu na biki da Mansoor ya ce sai daga baya dan ba'a saka ɗinkakken kaya ko ɗaya a lefen ba, kuma kowa na saka ran yau ne za'a kawo ɗin saboda kamu da ake shirin yi gashi babu kayan dazan saka. Amma har yamma shiru kake ji. Gashi yanzu banda waya a hannuna ko ɗaya. Rabona da Mansoor kuma tun jiya da dare. Koda yake nice nace yau kar yazo, kai daga jiya ma bazan sake yarda mu haɗu ba sai a gidansa. Shiko ya yarda da hakan acewarsa zai gwada yaga ko zai iya. Nayi tunanin kiranshi amma zuciyata ya ƙwaɓeni game da hakan, dan haka bance da su komai ba na haɗiye zancen a raina har sai bayan sallar isha'i da nasan Yaya Musaddiq ya dawo gida sannan na lallaɓa ɗakinsa na samesa, a wajen kamu kuwa Aunty Zakiyya ta samo kayan dana saka kawai........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments