Breaking News

Zaman Dadiro 2


 ˙˚ʚ _*ZAMAN DADIRO*_ ɞ˚˙



Na... 

Oum Aphnan

09065990265


Littafin Kudi ne, zaki biya ta asusun bank dina 

9065990265

Mohammed Hassana

Opay

Regular 500₦

VIP 1000₦


Bismillahir rahmnir rahim

*002*

_______

_Littafin nan is Horny🍌, Don Allah in mijinki bayi kusa karma ki karanta, 'Yan mata na Hutassheku karku karanta kuma Allah ya aurar daku🥰_


______

"Ke Bani balance din mana"

Wani mugun Harara Zainab ta banka ma Abubakar 

"Yaya meye haka daga dawowa na ko hutawa banyi ba wai in baka balance, to sai dare "

"Innalillahi, zainabu ke wata irin mace ce? Ina rike da keke napep dina salin alin kin hanani tukawa kin ce ke zaki ringa jan keken in anga keken mace ce anfi ciniki, kuma gayinan naga kudi cunkus a hannunki, yanzu nace ki Bani kudi in samu inci abinci kin ce balance sai da daddare wannan ba mugunta bane? "

"Yaya Habu ni ka daina mun ihu, wannan kudin da ka gani fetur zan zuba , ku daga zaran kunga mutum ya dawo gida ya huta yaci abinci sai tambayan kudi, to bazan bayar ba faƙat!" Ta ƙare magana tana cire buturan gaban polo shirt dinta da yaji baƙin mai, ta zura duk kuɗin a brazier.


"Au anan wajen kika saka don kinsan bazan iya amsa ba? To wallahi danneki zan yi in ciro bari ki gani" 

Ya yunkura da gudu yabi ta, aikuwa da gudu ta falfala "Na rantse in na baka lazza ta cini"

**

Wanene Zainabu? 

Zainabu ƴar asalin ƙauyen Dakace dake hanyar Zaria Yarinya ce budurwa ƴar kimanin shekaru 21 , Baban Zainab Allah yayi masa rasuwa tun Zainab nada shekaru biyu a duniya, A don haka mahaifiyar Zainab bayan ta gama takaba ta sauya sabon aure a wani ƙauyen dake gaba da garinsu Zainaba, taso tafiya da dije amma  yayar babanta yace fafur ƴan gidansu bazasuyi agolanci ba. Babu yanda Uwar zatayi illah ta dangana tana binta da addu'a a duk inda take. 

Girman Zainaba cike yake da tarin kalubale, kasantuwar tarbiyya ba tsakanin uwa da uba ba, tayi makarantar allonta har sauka, tayi primary dinta a  LEA Dakace, tana gamawa ta zarce GSS Dakace ta cigaba da karatun gaba da firamare dinta , Zainab yarinya ce mai zuciyar neman na kanta amma fa ƴar bala'i ce masifaffa, bata taba zuwa makaranta ba kayan sana'a ba, In firifet suka kwace in an tashi makaranta ayi dambe, duk yawancin sa'oin Zainaba sunyi aure amma Zainaba kamar me aljanu da maza sun zo zata kore su, don yaron da yazo sonta na karshe malaminsu ne kwafa, Ashe dan iska ne suna zance a filin dannin karan gidansu zai tafi sai cewa yayi Zainaba ko ɗan Kiss din nan ki ɗanyi mun na masoya mana, aikuwa tace jirani, sai gata ta dawo da shirgegen icce ta bishi karce, da kyar ya sha, ana kuwa tambayar ta me ya haɗa su nan ta feshe ma mutan tsakar gida jawabi. 

Daga wannan lokacin zuwa makaranta ya gagari Zainaba saboda malamin ya sa mata tsama a makarantar dukda tana SS3 ne first term amma dole ta jingine makaranta a gefe ta koma soya dankali da awara me Sos. 

Ayuba yaron me gari yazo ya danni awara na 300₦ ya gudu bai bata kudi ba, ta wanke kafa tas ta je tayi ma mai gari tijarah, sanann ta Daura da masa gargadin duk inda sukayi ido hudu da ayuba sai ta zubar masa da jini, saita barshi a kwance sai an kashe masa kudi a asibiti ninkin ba ninkin kudinta,. 

Don haka ko a biya ta kudinta ko aga rashin mutuncinta.... 


Hankalin mai gari ya baci, a gefe guda ta sallaɗa masa tsoron ta nan ya fara fuffuka yana kumfar baki

"Ki kashe shi kinji ko? Ke zaki ƙaraci rayuwar ki a gidan ƙiri² (Prison) Kuma dai ina mune dattawan garin nan ko? To maga Anzo neman shaidan auren ki, saidai ki yi ta zama a haka... Fitsararriya"

(Bare with me lovelies💖ƴan Niger sunce in rage sa Turanci, Hausa dandaɓas😆)

Ana tsaka da wannan lamarin ne Yaya Habu ya dawo  garin wanda yake kwazin din ZainabaZainaba. 

Habu Driver ne yana jan wata Madam ce a garin Kaduna zuwa office in ta tashi aiki yaje ya dauko ta, sannan a gidan da yake haya yana da keke napep dinsa in ya dawo aiki zai tafi tukin keke napep ya samo ƴan canjin sa. 

Akwai mutunci da shakuwa tsakanin Zainaba da Habu, don haka Habu yayi nufin daukan ta su koma Kaduna da zama sai ya sa ta makaranta a can in ta samu miji tayi aure an huta da yawan masifa tunda garin Dakace dai yayi ma Zainaba zafi tayi fada da kowa kowa hantaarar ta yake.... 


Wannan shine mafarin zaman Zainaba a wajen Habu, amma kuma daga bisani ta fara ɗanɗana masa baƙin halinta..... 

Riga da wando take sawa kamar namiji da p_cap ta shiga tashan kawo ana damben neman fasinja da ita, kowa ya ganta mace ana son hawa keken ta, gashi  Zainaba bata daukan kazami a keken ta bata daukan mata masu goyo, in ta dauke ka iya fesfes Dinka iya tsadar kudinka, daga Kano road zuwa cikin gari zata iya mirje ido tace dubu biyu, maza saidai suyi dariya su bata kudin, in kuwa ta kannafa ma mata ƴan Kasu tsada suka nema turzawa sai ta kashe keken tace su fito a daku in ta ji wuya ta rage  masu, tsira suke da mutuncinsu su bata kudin su shige makaranta. 

Wannan Kenan. 



_Cigaban Labari_




TALLA***

https://chat.whatsapp.com/Kkd4eh70znQJdiYQdZVaJ0



Kinaso ki kasance mace ta musamman a gurin mijinki?? Kinaso ki zama abun alfahati agun mijinki, kinaso kisan ma'anar mallaka ta gaskiya ta hanyar soyayya da gyaran jiki babu boka babu malam ??ki naso kisan dadinda isashiyar mace takeji?? Hmm mi shiga wannan group domin samun sirruka da hanyoyin janyo ra'ayin miji babu boka babu malan



Domin neman shawara ko qarin bayani ki kira 

090 3484 6526 

08035848755

No comments