Tsutsar Nama Book 2 page 11
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_
__________
_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
___________
......Wajen zama Mama Bilki da naji sun ambata da Mama ta nuna min, babu musu na zauna. Ta nuna wata dake gab da inda nake tana faɗin, “Sayyada kawo ma baƙuwarmu ruwa da abinci ko”. Cike da fara'a wadda aka kira Sayyada ta amsa tana miƙewa. Wata ƙofa dake a falon can inda ƙaton dining table yake na katako ta nufa, mintina ƙalilan kuwa sai gata da tire madaidaici a hannunta. A gabana ta dire tana murmushi da faɗin, “Sister ga abinci ko.”
“Nagode”.
Na faɗa a hankali nima ina murmushin yaƙe. Wajen zamanta ta koma ta zauna. Yayinda ni kuma na zuba ma abincin ido nai shiru har sai da Mama Balki ta zungureni sannan na kawo numfashi. Abincin ta nuna min alamar naci, na ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin tausasa murya nace, “Mama dan ALLAH zan fara salla tukunna”.
Cike da fara'a tace min, “Lah ai babu komai ɗiyata. Kinga A'i tashi ki rakata ɗakinku sai tayi a can kunga kun samu abokiya kuma kun zama ku uku kamar kowa. Ɗan tsuke fuska wadda aka kira da A'i tayi, sai dai kuma batace komai ba ta miƙe. Nima miƙewar nayi nabi bayanta ɗan lungun da naga ta nufa. Dogon corridor ne mai ɗauke da ƙofifin ɗakuna kusan goma. Hannun dama biyar haggu ma biyar. Babu yabo babu fallasa bayan mun shiga ɗaki na biyu a hannun dama ta nuna min ƙofar bayi. “Ki shiga nan”. Daga haka ta juya ta fita. Komai bance da ita ba nima, face cikowa da idona yayi da ƙwalla. Ji nake komai ya ƙwace min, gaba ɗaya nama gagara hasashe balle tunanin komai akan wannan rayuwa dana jefa kaina. Dan a yanzu kaina nake zargi ba kowa ba. Ina ma kaina kaico akan bin hajiyar nan da nayi, sai naji inama tashar na nufa koda roƙo na samu kuɗin motar zuwa Kano. To amma bakin alƙalami ya riga ya bushe. Ni bama wannan ne tashin hankalina ba. Son sanin wanene mai wannan gidan shine tashin hankalina. Karfa ya zamto ANYI GUDUN GARA ne AN FAƊA GIDAN ZAGO. Kai amma da nayima kaina kaico. In sha ALLAHU ma bazai kasance hakan ba.
Bayan na idar da salla na jima zaune a wajen shiru, dan har sai da A'i ya biyo bayana sannan na miƙe na bita. Kamar yanda na barsu haka na samesu. Sai dai an sake samun ƙarin mutum uku suma duk manyan mata dan da kaɗan Mama Balki zata iya girmarsu. Gaishesu nayi a ladabce, duk suka amsa min babu yabo babu fallasa. Na ɗan ji jikina yay sanyi, sai dai ban bari al'amarin nasu yayi tasiri a raina ba na fara cin abincina. Ka ɗan na tsakura nace na ƙoshi, Mama Balki tai murmushi da faɗin, “Ƴar nan baƙunta zakiyi mana?”.
Murmushi kawai nayi kaina a ƙasa batare da nace komai ba. Itama sai tayi ƴar dariya da cigaba da faɗin, “To ai shikenan. Bara nayi wani karanbani duk da Aunty Mama bata sanar min ke wacece ba ko matsayinki. Amma dai duk wanda aka kawo nan mun san namu ne ai. Minene sunanki?“.
Shiru nayi jimmm kamar bazance komai ba. Sai kuma na sauke ajiyar zuciya a hankali na furta Kandala”.
Su dukansu sai da naga alamar shock a fuskokinsu game da jin sunan nawa. Amma ganin yanda na fiske abuna ya sasu basarwa. Wasu a cikinsu suka furta Masha ALLAH. Yayinda wasu suke taɓe bakuna a yamutse. Mama Balki ce ta katse yanayin da nuna kanta. “Ni sunana Balkisu, amma suna kirana da Mama Balki kamar yanda kika ji. Ni ce shugabar duk wani ma'aikacin wannan gida musamman mata. Mijina kuma shugaban ma'aikata maza. Wannan kuma ta kusa dake Sayyada, sai Afrah, sai Sumayya, sai A'i, sai Asiya, sai Bintu, sai Mansura, sai Kairat, sai Bahijja, sai Sadiya suna kiranta Aunty Sadiy, itama tana da miji. Ta nuna ɗaya daga cikin manyan matan nan uku da suka shigo daga baya. Sai Aunty Kubrah itama tana da miji, sai aunty Falilah. Dukanmu muna aiki ne a wannan gida. Kowa kuma da fannin sa. Wasu gyara, wasu wanke-wanke. Kowa kuma da sashen da yakema aiki dan komai a ƙa'idarsa yake. Idan har kema tamuce zamuji fannin da aka kawoki ki kasance”.
Sosai ƙirjina ke wani kalar luguden daka tunda ta fara. Sai dai inata dauriyar danne yanayin nawa. A rain kuwa komai ya dagule min, babu abinda nake ambato sai kalmar (Na shiga uku. Yanzu kuma boyi-boyi na koma kenan? Mike shirin faruwa dani ne haka?). Bani da mai bani amsa, dan haka na maida hankalina ga Mama Balki dake cigaba da min bayani. Sai dai sam bana fahimta har tayi ta gama. Mun cigaba da zama har akai kiran sallar la'asar. Sai a sannan dukanmu muka miƙe. Ɗakin dai ɗazun naje tare da wadda ta rakani A'i sai abokiyar kwananta Bahijja. Bahijjar akwai fara'a, dan sai jana take jikinta cike da kulawa. Muna idar da salla ta kwashe tarkacen kaya da suka jibge a ɗayan gadon ɗakin dan uku ne ta ce, “Nan shine gadonki Kandala”. Yanda tayi maganar da murmushi ya sani nima mayar mata da murtani ina jinjina kai, kafin na ɗora da mata godiya. A'i dai na jinmu amma tai kamar bata ɗakin. Bahijja dake ƙoƙarin saka uniform ta sake kallona da faɗin, “Kiyi kwanciyarki ki huta mu zamu je can sashen yin aikin yamma. Idan kuma zakiyi kallone to muje falo”.
Da sauri na girgiza mata kaina. Sai kuma na murmusa da faɗin, “A'a bari na kwanta ɗin, ai bazaku jimaba ko?”.
Tsaki akaja kafin ta bamu amsa, atare muka kalla A'i dake ƙoƙarin ficewa alamar itace tayi tsakin. Murmushi Bahijja tayi da maido idonta gareni. “Karki damu da ita haka take kamar mai aljanu. Nima farkon zuwana haka ta dinga min kamar mai jin haushin mutane. Amma bari kiga nan da kwana biyu zata fara kulaki. A'in ce kamar mai aljanu wlhy”.
Murmushi nayi yayinda ita kuma ta ƙare maganar da sakin ƙaramar dariya. Daga haka ta cigaba da faɗin, “Ya danganta da yanayin aikin da zamu tarar. Musamman ma ni, dan iyayen gidan nawa mutuncinsu ragaggene bare ma idan akace miki Aunty Azizat. Tana abu kamar mai jin warin mutane. Bari naje dan in nayi latti zan sha maruka gashi ƙa'idarta ne iyanzu take wankan yamma”.
Kasa cewa komai nayi, sai kaina dana ɗaga mata kawai sunan wadda ta kira na min kai-kawo a rai batare dana san dalili ba. Bayan ficewarta na saki nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma na miƙe cikin kasalar jiki zuwa gadon da tace nawa dake a farkon shigowa. Na can ƙarshen bango na A'i, na tsakkiya nata. Sai ni a bangon ƙarshe na farkon shigowa.....
❤️★★★❤️
Tsakanin Halime da Dady dai tun wannan ranar ba'a sake haɗawa ba. Dan washe gari uban aiki taci kamar kurar wasa. Dan kaf girke-girken da aka tanadama Alhaji Rufa'i itace tayi su. Tayi kuma gyaran gidan musamman falon tarar baƙi da Mom ta sakata ƙalƙalewa kamar za'a canja bangonsa. Ita dai bata san dalilin uban aikin da taci ba sai da yammaci take ji a bakin auta wai Baby ce tayi baƙo. An kuma ce ta saka hijjab da niƙab takai masa abinci falon baƙi. Bata da yanda zatai dole tabi umarnin Mom tayi shigar da akace taje takai komai. Da ɗunbin mamaki ta fito mara misali. Yayinda taketa jarumtar danne dariyar dake cinta har sai da ta shiga ɗakinta. Bata tsaya a tsakar ɗakin ba ta shiga toilet ta rufe kanta duk dan kar a jita sannan ta fara kwasar dariya harda hawaye. “Kambu taƙashin nan. Yanzu ni Halime ina Baby ta samo wannan tulun giyar, wlhy cikinsa kamar an kifa masakin Baba Lauren gidanmu na Daudawa. Gashi sanƙameme kamar samudawan da suka zo mana a labari. Tab ɗi jan, daga dai ganin wannan kasan sai dai a so shi dan kuɗi duk da dai ƙyaƙyƙyawa ne a fuska.” kiran da Mom ke ƙwala mata ya sata fita a guje dan tasan idan tai na uku sai ta sha maruka a wajenta.
Gab da magrib taji ihun Bibaa da Abbas ya cika gidan. Ta kitchen ta kasa kunne sai ta jiyo ihun nasu wai duk murna ne akan Alhajin nan ya bama Baby makulin mota, tare da alƙawarin kujerar maka gareta da Mom da Dad da kuma Abbas, su kuma su Bibaa da Auta da Nabil yay musu ƙyautar wayoyi iphones. Hakan dai na nufin su duka banda Yaya Musaddiq bawan ALLAH kowa ya samu alkairi daga Alhaji Rufa'i. Baki ta yaɓe ta cigaba da aikinta. Daga haka bata sake bi takansu ba sai washe gari da kakarsu tazo take jin har ƙyautar kuɗi yay ma yaran gidanta itama wai naira miliyan ɗaya. Itama kuma kakar tasu harda ita a zuwa saudia, da yaje gidanta kuma ya bata waya mai ƙyau ƴar dubu ɗari biyu harma ta sayar da ita yau. Sosai Halime ta jinjina kwaɗayin wannan mutane da mamakin maganganun da taji suna tattaunawa. Dan sai da Mom ta farga da ita sannan tasha maruka aka korata waje, daga haka bata san mi suka ƙarasa tattaunawa ba.
WASHE GARI kuwa bata ma san lokacin da Mom ta fita a gidan ba tare da Baby. Sai Bibaa da Auta da suka wuce makaranta. Shi dama Abbas ba'a sakashi a lissafin gidan. Yaya Musaddiq kuma ta lura jiya kamar bai kwana a gida ba. Tana a falo tana shara da raira waƙarta cikin zazzaƙar muryar nan tata taji kamar ana kallonta. Ɗan jim tayi cikin nuna tsarguwa. Sai kuma ta cigaba da shararta amma ta daina waƙar da take rerawar ta (kwanana ya kusa ƙarewa a gidanmu zan tafi ɗakina. A gidan mijina zan rayu zaman kaɗaici ya kusa yankewa).
Cikin sauke ajiyar zuciya da rashin jin daɗin daina raira waƙar tata Abba ya ƙarasa fitowa daga jikin ƙofar ɗakin barcinsa da yake maƙale.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 11"