Tsutsar Nama Book 2 page 14
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_
.......Cak numfashina ya tsaya, illahirin jikina ya saki gaba ɗaya. Da ga ni har shi muka zubama juna ido. Yamutsawa kaina ya farayi saboda wani sinadari mai ƙarfi dake fitowa daga cikin cat ayes ɗinsa yana shiga cikin nawa. Wani irin kallo yake min mai kama da gargaɗi koma tsanace ban sani ba. Dan duk yanda naso dakewa hakan ya gagara. Tuni naji wani irin kwarjininsa ya gama mamayeni da cikani tamkar mu kaɗaine a wani matsatsen lungu. Hatta da iska ma ta fara min wuyar shaƙa neman komawa fisgar numfashi nake yi. Wani matsiyacin kallo daya dalla min tare da ƙoƙari janye jikinsa daga nawa ya sani tafiya gaba ɗayana baya zan faɗi. Bamma san na fasa ƙara ba da komawa gaba ɗaya jikin nashi na ƙanƙamesa tamkar zan huda shi na shige ciki...
Kusan kowa dake a wajen sai da ya sake waro idanu. Yayinda tuƙuƙin baƙin ciki da kishi mai tsanani ya gama mamaye zuciya da ruhin Azizat. A yanda take jin bawan ALLAHn nan a ranta ko macen sauro ta tsani ta taɓa mata shi, ai tuni idanunta sun sake rufewa. Batama san lokacin data isa gabansu ba. “Wlhy sai na kasheki ƴar iska. Bayan maita ma harda bin mazan mutane”. ta faɗa cikin ihu mai ƙaraji tana damƙo hannun Samraah da ƙoƙarin janta baya daga jikin Maash. Wani mugun kallo ya watsa mata. Sai kawai ta fashe da kuka tare da sakar min hannun tana ƙoƙarin kaimin mari. Nima tamkar wadda aka farkar a barci dai-dai nan na dawowa a hayyacina, Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na sakesa gaba ɗaya tare da turashi. Sai da me ko gezau, yana nan a tsayensa ƙyam saman ƙafafunsa tamkar dasashiyar bishiyar data kafu a muhallin daya dace da ita. Kallo ɗaya yay min da shegun idanun nan nasa kalar na maguna ya janye tamkar wanda ba'ai komai ba ma. Ga fuskar tsamm babu alamun rahama ko sassauci balle ma kai tunanin ya taɓa sanin mai kama dani a rayuwarsa. Duk yanda naso janye nawa idanun daga kansa na gagara hakan saboda tsabagen shiga ƙololuwar baƙin ciki, ruɗani da mamakin makirci da mugun halin mutumin nan, kenan da gaske shi MAASH ɗin ake nufi da sunan gidan nan?. Tayaya ma to hakan ta kasance?, farkon labarin a kano, cigabansa a Abuja, ƙarashensa a Lagos. Duka a ƙarƙashin ikonsa, kenan da gaske yayi winning kamar yanda yake iƙirari da cika bakin shi ba'a game da shi baiyi winning ba. Kai impossible...
Mugun zagin da Azizat ta lailayo min da sake yo kaina ya maidoni a hayyacina, raina a dugunzume na janye idanuna a kansa na dawo da shi gareta, dan wlhy tana sake taɓani duk haushi da takaicin mugun nan saina juyesu a kanta yanzun nan. Tana gab da kai hannunta jikina aka kira sunanta da ɗan faɗa-faɗa. “Azizat minene haka wai?!”. Mu dukanmu kalon Aunty Mama da tayi maganar mukayi, yayinda itama ta dakata tana hararata da famar huci sai kace wata kububuwa. Cikin sake bada umarni daga inda take tsaye ta dubi Mama Balki. “Kuje inda na turaku”.
“Godiya muke ranki ya daɗe, ALLAH ya ƙara girma”. Mama Balki ta faɗa tana risinawa tare da kama hannuna. Tamkar wadda aka zarema illahirin lakar jiki na shiga binta zuciyata na wata kalar suya da raɗaɗi mai zafi. Yayinda idanuna ya kasa daina kallonsa, nama rasa wana kalar tunani kuma ya dace nayi. Muna gab da fita muka haɗa ido, wani irin lumshe nasa yay da yamutse fuska ya motsa lips ɗinsa a hankali, (First Game) sai kuma ya cije gefen lips ɗin da wani salo ya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garemu.
Da ƙarfi na rumtse idanuna dake cikowa da ƙwalla. Cikin ɓacin rai na shiga ƙoƙarin son fisge hannuna daga na Mama Balki. Dan bazan iya haƙuri ba sai na maida masa murtani. Kai yau ma duk abinda za'ayi sai dai ayi wlhy. Sake damƙe min hannu Mama Balki tayi tare da jawoni gaba ɗaya daga cikin falon muka fito cikin main falo, sai da muka fito anan ma gaba ɗaya wajen compaund sannan. Cikin lallashi da ɗan faɗa ta furta, “Ya isa mana. Ki ƙyaleta. Banda abinki ina ke ina faɗa da ƴar masu gida. Kin san kuwa fitinar Azizat musamman akan bawan ALLAHn nan. Zuciya ba taki bace ba ɗiyata, anan a ƙarƙashinsu muke dole muyi haƙuri da koma mi zamu gani. Kima godema ALLAH Alhaji ƙarami yazo wajen da wlhy abinda zai faru ALLAH kaɗai ya sanshi. A hakan ma ALLAH ya taƙaita duk barci jama'ar gidan suke. Ita kuma Aunty Mama tana da sauƙi a cikinsu da ko gidan nan bazaki sake kwana ba. Kema dai na lura akwai ƙarfin hali, ki daure ki sauke wannan zuciyar taki kada ki sake kwatanta abinda kikayi yau”.
Zantukan Mama Balki sake ƙona min rai suke. Dan haka na sakar mata kuka kawai tare da faɗawa a jikinta na ƙanƙameta. Itama sai ta riƙeni hannu bibbiyu tana lallashi na.....
Su Samraah na gama ficewa a falon Azizat tayo kansa. “Yaya Please kace afitar mana da ita a gida. ALLAH yarinyar nan mayya ce. Tun jiya da aka shigo da ita gidan nan naji na tsaneta, jinake kamar ma na kashe banza. Dan bazan taɓa yafe mata rungumar da tayi maka b.....”
Ko kallon inda take baiyi ba, sai ma motsa lips ɗinsa da yay a hankali cikin silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Good Morning Aunt” yay wucewarsa. Wani irin tsayawa tayi cak jikinta na tsuma. Duk da ba yau ne farau ɗin hakan ba a tsakaninsu sai take jin na yau ɗin ya mata zafi. Da kallo ta bisa idanunta nayin narai-narai alamar gab take da sakin kuka. Murmushi Aunty Mama tayi da ɗan girgiza kanta tana binsa da kallo. Har sai da ya ɓacema ganinsu ta janye idanun, ganin Azizat ta zabura zata bisa ta sakko ta kama hannunta batare da tace komai ba ta jata suka koma saman dan tasan bin nasa bazai haifar da ɗa mai ido ba. Dama ga wata wutar dake neman tasowa akan matsalarsun....
★★★
Cike da nishaɗi Abba ya koma gida. Sai dai me, yana shiga ya samu Mom na jibgar Halime har Bibaa na tayata. Yayinda Baby ke kwance a kujera wanwar alamar tasha kayan nata. Tuni yay wata irin zabura batare daya sani ba ya hankaɗesu su duka. Sannan ya ɗauke fuskar Bibaa da mari. “Kinci gidanku Habiba. Dan uwarki wannan ɗin sa'arki ce?”.
Kafin Habiba dake kuka ta bada amsa Mom data sake shiga cikin matsanancin ɓacin rai ta hayayyaƙo masa. “Mitai maka zaka daketa. Akan ƴar aiki wulaƙantacciya da iyayenta ma suka sallama ma duniya saboda baƙin talauci”.
Wani irin ɓacin rai ne ya tasoma Abba. Cikin rufewar ido ya furta, “Jalilah! Halimatussa'adiyyar ce wulaƙantacciya?”.
“Kuturun ubancan! Imamu harma sunanta ka sani? Harda ƙara masa wani ƙaimi. To ko dai kana zagayowa ne ban sani ba ta zama karuwarka. No wander yanzu kullum sai ka dawo gida da rana. Idan ka zauna kuma kata waige-waige kenan...”
“You are vary stupid Jalilah! Ni kike dangantawa da fasiƙanci?”.
“Yo in ba fasiƙin ba minene kai? Taya akai kasan wannan tsinanniyar yariyar anan gidan ma? Bayan na mata gargaɗi kaima kuma nayi maka. To wlhy kuwa zaku mutu yau ku duka...” ta ƙare maganar da rarumo flower base tai kan Halime dake maƙure gefe tana kuka. Damƙota Abba yayi da masifar ƙarfi, aiko ta juyo gaba ɗayanta ta buga masa abin a kai. Lokaci ɗaya Bibaa da Halime da Baby da hayaniyarsu ta sakata buɗe ido suka ƙwalla wata irin masifaffiyar ƙara da duk maƙwaftansu sai da suka jiyo. Yayinda fuskar Abba ta gama wankewa da jini. A take ya faɗi wanwar ƙasa. Ai sai su Bibaa suka sake ƙwala wata ƙarar da tafi ta farko. Itama Mom ta yadda guntun flawer base ɗin daya rage a hannunta tayi wani uban tsalle gefe tana ware idanu. Halime kuwa tuni ta gigice tazura waje a guje.......
💦❤️💦❤️
Komai na daina ganewa. Komai ya tsaya min cak. Ba brain kawai ba, hatta zuciyata da gangar jikina komai dake taimaka musu ya tsaya cak. har muka baro inda Alajah ta sakamu zuwa anan cikin gidan bana iya gane komai. Bin kowa kawai nake da kallo tankar wadda ke a duniyar mafarki. Koda muka koma can sashen Mama Balki bata shiga ba. Tace na shige ciki ita zata koma kan aikinta. Shiru sashen babu kowa, hatta tv a kashe take. Ban zauna a falon ba na shige ciki, saman gadon dana kwana na kai zaune, cikin gushewar tunani na dafe kaina tare da fasa wata irin ƙara illahirin jikina na rawa har ta kaini da faɗowa ƙasa....
Da gudu Bahijja data shigo sashen domin shiga toilet ta ƙaraso ɗakin, dan da farko ma ita tsorata tayi, sai da tajiyo ihun kamar daga ɗakinsu ne sannan cikin ɗari-ɗari ta nufi can. Sosai ta waro idanu, sai kuma ta zabura kan Samraah tana faɗin, “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!. Kandala! Kandala! Miya farune haka?...”
Ƙanƙameta Samraah tayi sosai tana cigaba da kuka mai tsuma rai da zuciya. Sai kawai itama Bahijjar ta sanya kuka. Dan yanzu su Sumayya ke bata labarin abinda ya faru tsakanin Samraah ɗin da Azizat. Sun kai kusan mintuna biyu a haka kafin su sassauta kukan nasu. Cikin lallashi Bahijja dake rungume da ita ta fara faɗin, “Kiyi haƙuri Kandala kinji. Haka take sam bata da mutunci. Bata ɗauki ɗan adam komai ba sai abin wulaƙantawarta. Sai kace itama ba cin arziƙi tazo yi gidan ba. Tunda ba gidan ubanta bane ba. Ai wlhy naji daɗin abinda Uncle Boss yay mata, azzaluma. Nima kullum sai ta mareni ga bautar gyara mata ɗaki da nake kamar jaka, hatta da pants ɗinta nike wankewa. Amma sam bata gani, komai akai mata ba'a iya ba, bayan ita ɗin ma babu abinda ta iya sai barcin tsiya da gantali. In sha ALLAHU Uncle Boss bazai aureta ba zamu gani”.
A hankali na ɗago ina kallon Bahijja, haka kawai kalamanta sukai wani irin tasiri a zuciyata. Har ban san sanda na furta kamar ya ba ƴar nan gidan bace Bahijja?”.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 14"