Tsutsar Nama Book 2 page 32
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_
.......Uffan bance da ita ba na cigaba da sauka ƙasan. Tunkan na ƙarasa nake jiyo hargowa da ihun Hajiya Mammah. Nadai dake na cigaba da sauka ina kallon Mama Balki dake durƙushe gabanta kamar ma kuka take yi, sai matan nan guda uku suma durƙushe a gefenta, ai kafin ma na ƙarasa gabanta nima naji saukar mari. A take azaba ta sakani watsar da kayan hannuna suka tarwatse a wajen. Ban gama dawowa a hayyacina ba ta shaƙure min wuya da faɗin, “K wai wacece? Ƴar uban wacece a ƙasar nan dazan ce ga abinda zakiyi ki canja da naki tsarin?”.
Sam bana ma fahimtar mi take faɗa, sai kakari neman fitar rai kawai nake ga idanuna sun gama firfitowa waje. Wani marin ta sake yarfa min sannan ta hankaɗani baya. Buguwa nayi da kujera da Azizat dake ta wajen, sai itama kawai ta sake hankaɗoni na dawo. Na gama sallamawa sai na kai ƙasa, amma a mamakina sai na jini a jikin mutum babu zato...
Tun faɗowarta jikinsa a bazata ya tsaya cak tamkar bishiyar kuka. Bai kalleta ba, bai kuma motsa ba, bai kuma janyeta a jikinsa ba. Sai dai fuskar ta sake wani irin tsukewa mai tsanani dake sake fidda ɓacin ransa muraran ga duk wanda zai iya kallonsa. Duk da shi dama ba abin wasan kowa bane a gidan yanayin fuskar yasa ta sake saka kowa firgita. Hakan yasa numfashinsu ɗaukewa gaba ɗayansu a lokaci guda. Daga masu ɗora hannaye duka a saman kai, sai masu wage baki, sai masu waro idanu waje. Hatta da ita kanta Hajiya Mammah ɗin ta shiga shock da ganinsa dan babu wanda zaice ga sanda ya shigo falon. Amma da yake macece data goge a iya barikanci sai ta zaburo inda suke tana cigaba da masifa.
Har isowarta inda muke na gagara tashi a jikinsa. Saima ƙanƙamesa dana sake yi ganin takai hannu zata finciko ni. Jin bata fincikonin ba na buɗe idanuna dana rumtse. Sosai na warosu waje dan mamakin ganin shine ashe ya tare hannun nata da nasa. Ai zumbur na miƙe kan ƙafafuna na. Cikin ƙara zaburowa ta ce, “Barni Awwab naci uban yarinyar nan da bata da kunya da mutunci. Ni ban san a ina Auta ta kwaso mana ita ba. Baka san abinda tai ba da baka tare ni ba. Abinci na bada a kai sashen Hajiya Babba da magungunanta kafin naje na bata shine na tadda shegiyar yarinyar nan ta amsa a hannu masu kuka da ita tana floshing ɗin tables ɗin a cikin toilet saboda ita cikakkiyar ƴar iska ce. Kai dole ne ma musan miya kawota gidan nan yau”. Ta ƙara kai min duka. Kasa motsawa nayi a yanzu. Dan sumar tsaye nayi a wajen da jin kalaman makirci da sharrin da take min. A take idanuna suka ciko da hawaye. Na cije lips ɗina sannan na kallesa. Kansa a ƙasa yake bashi da alamar cewa komai. Sai da na share hawayen da suka ziraro min sannan na ce, “Wlhy ba haka ban...”
Bamm ta buge min baki da ƙarfi har sai da ya fashe. “Dan ubanki kina nufin ƙarya na miki ke nan. Lallai yau kam zanci ubanki a gidan nan. Anya kuwa yarinyar nan keba ƴar leƙen asirinmu bace ba ma? Ba wani ya turoki ba dan ki cutar da mu. Dan Ni ba'a taɓa fitsararriyar ƴar aiki tsagera mara kunya irinki ba anan gidan.”
Cikin tura baki gaba na ce, “To ni dai Mammah ai bamma kowa rashin kunya ba sai wanda ya shiga harkarta. Ni kuma bana son ana min sharri akan abinda banyi ba. Kuma manya idan suna ƙarya mutuncinsu zubewa yake yi”.
Ɗauu naji saukar wani marin mai azabar zafi da yafi na ɗazun a saman fuskata. Tsabar yanda ya shigeni har sai da jina ya ɗauke na wucin gadi. Ina ɗagowa ta sake ɗaga hannu zata ƙara min ya shiga tsakkiyar mu. Cikin silent voice ɗin nan tasa mai cike da ƙasaita ya furta, “Mammah it's enough.”
Babu wanda mamakin jin abinda ya fito a bakinsa bai bayyana a fuskarsa ba. Duk da mafi yawansu sun san ba sabon abun bane gatsa magana kai tsaye daga garesa musamman idan yana a ɓacin rai, sai dai dalilin yin ta yau ɗin ce ta Bama kowa mamaki. Irin wannan tsawa haka. Cike da azabar masifa itama Hajiya Mammah ta daka masa tsawa. “Awwab!! Kana fa jin abinda shegiyar yarinyar nan ke faɗa har kake iya cemin ya isa. Ka barni na dawo da ita a hankalinta idan bata san matsayina a gidan nan ba ta sani da ga yau!”.
Maimakon bata amsa ko barinta dani ɗin sai jinai kawai ya kama hannuna ya fara tafiya. Bani da zaɓin daya wuce bin bayansa. Tsitt falon babu wanda ya sake yin koda tari har muka shige ta hanyar nan data nuna min ranar na kai masa shayi....
⭐💞⭐💞⭐
Rashin wucewar Gwaggo ya ɓata shirinsu Mom. Duk da dai ita dama Ummanta ce ke tausarta. Saboda tafi ganewa ta fito ayima duk wacce za'ayi amma Umman tace a'a subi komai a sannu suma fara sanin wacece yarinyar tukunna. Gefe kuma rashin jin daɗin jikinta ya hanata iya komai. Dan da gaske jinin nata ya hau ga ciwon kai da ƙirji mai tsanani dake damunta...
A ɓangaren Halime amarya sai da aunty Zakiyya ta sakata gyara jikinta tsaff ta kuma ƙara tsaftace mata sashenta sannan ta wuce. Dan haka daga ita har sashen nata banda bulbula ƙamshi babu abinda sukeyi. Tayi fes da ita ƙyawunta da rashin kula ya ɓoye ya sake fitowa sosai. Duk wanda ya kalleta yasan tana cikin farin ciki da walwalar sabuwar rayuwar data tsinta kanta a ciki. Sai dai ta wani sashen zuciyarta rashin ganin Abba tunda aka kawota gidan na ɗan sosa ranta. Dan tun jiyan da suka iso bata sake ganinsa ba. Sai da safen nan da taji muryarsa yana gaida iyayenta dake falo. Tayi zaton zai nemeta amma sai taji shiru. Lokacin da ƴan uwan nata ma zasu wuce taji muryarsa a tsakar gida, sai dai kukan da take yasa batai yunƙurin kallon sashen da yake ba. Tunda kuma suka wuce bata sake jin motsinsa a cikin gidan ba. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke a hankali, sai kuma ta taɓe bakinta dan tasan zama ta iya ganin fiye da hakan kodan matar nan tasa a zababbiya. Jifa yanda aketa cin uwar sabada a gidan tun isowarsu jiya, a hakan ma tasan dan bata san itace matar da aka auro ɗin ba ma...
Yanda take ta faman yamutse fuska da taɓe baki ya saka Abba dake tsaye a kanta tun ɗazun kasa daurewa ya saki murmushi. Sai kuma a hankali ya kai zaune kusa da ita yana mai kai hannu ya shafi fiskarta. Tsorata tayi, dan harga ALLAH bataji koda ƙamshin turarensa ba balle motsinsa. Dan haka ta miƙe a firgice zata ƙwala ihu. Da sauri shima ya riƙota yana mai ɗora hannunsa saman bakin nata tare da jawota gaba ɗayanta cikin jikinsa yana faɗin, “Calm dawn Halimatussa'adiyya please calm down ni ne”.
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da numfashi a jajjere. Sai kuma taji duk kunya ta baibayeta. Ƙoƙarin zamewa tayi daga jikin nasa ya hana hakan ta hanyar sake matseta da ƙyau a cikin jikin nasa. A cikin kunnenta ya shiga raɗa mata, “Amin afuwa na tsorata amarya ko.”
Halime babu bakin magana dan gaba ɗaya a kunyace take. Sai ma mutsu-mutsu da takeyi na son tashi shiko yaƙi barinta. Dole ta haƙura ta nutsu ganin bafa barin nata zaiyi ɗin ba dai. Sun kai tsahon mintuna goma a haka sannan Abban ya sassauta mata yana sauke tagwayen ajiyar zuciya tare da mannama goshinta da kan hancinta kisses. Ina ma ƙasa ta tsage Halime ta shige ciki dan kunya. Sai dai babu damar hakan dole ta haƙura tana faman cikuykuye kanta a jikinsa.
Yanda take yi ɗin yay matuƙar saka Abba dariya. Dan haka ya shiga tsokanarta da raɗa mata wasu kalamai a cikin kunne da suka sake birkita mata lissafi...
💦★💦★💦
Muna shiga ya sakar min hannu. Ganin yana neman raɓani ya wuce nasha gabansa wani irin kuka mai ƙarfi na suɓuce min. Ƙin kallona yayi, ya sake raɓawa zai wuce ta side ɗin dama ta. Nan ma taresa nayi hannayena duka riƙe da ƙuguna. Tuni na cire duk wani tsoronsa da shakkarsa cike da tsiwa na ce, “Malam wai mi kake nufi da ni ne? Ka maidani gaban iyayena daka ɗakkoni bazan iya rayuwa a wannan gidan da ba'a san darajar ɗan adam ba”.
Tamkar bazai kallan ba sai kuma ya yamutse fuska tare da sake tsuketa. Cikin gadara ya furta, “Ki gayama wanda ya kawoki. Sannan bana son rashin kunya”. Daga haka yay wucewarsa. Wani irin takaici da bakin ciki ne suka sake turniƙe ni. Tuni na shiga kokawar maida hawayen dake neman zubomin. Dole ne fa ayita yau ta ƙare dan bazan iya wannan zaman ƙasƙancin ba saboda ni ba jaka bace ba. Bazan taɓa zama a maidani yanda aka maida mahaifiyarsa ba. Kaina tsaye na nufi hanyar da yabi dan idanuna sun gama rufewa da masifa. Babu ko gezau a tare dani na bankaɗa ƙofar farko dana gani a wajen. Sai da zuciyata ta jijjiga saboda karo da abinda banyi zato ba. Da sauri na juya masa baya ina mai rumtsewa da ƙarfi, jikina har rawa yake dan tunda nasan kaina ban taɓa ganin namiji babba a yanda yake yanzu ba. Su Yaya Musaddiq ko da boxer da singlet basa zama a gida. Balle kuma ace daga su sai pant kamar yanda yake. Gashi a tsaye ƙyam da suffar ƙarfi dogo masha ALLAH. Bazan iya kallon wannan abin kunya ba, dan haka na fara laluben hanyar komawa inda na fito cikin sassarfa, amma sai hakan ya gagara. Maimakon kama handle ɗin ƙofa da nake lalube sai na damƙi lallausar fata mai santsin tsiya. Da sauri na cire hannun nawa tare da daka tsalle baya ina buɗe rumtsatstsun idanun nawa. Idanu huɗu mukai da shi, tsabar rashin kunya kuma yana a yanda na gansan. Sake juya baya nayi da sauri jikina na rawa. (Wannan wane irin fitsararren mutum ne haka wai) na faɗa a zuciyata ina ƙoƙarin riƙe numfashina da tsumar da jikina keyi........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 32"