Breaking News

Furar Danko 77

77


 

……..Yanda take kuma ya tadama Ammah hankali matuÆ™a, ta dawo kusa da ita da jawota jikinta ta rungume tana jin itama hawayen na cika mata idanu. Yanda Lulu ke kukan nan zai tabbatar maka al’amarin na matuÆ™ar taÉ“a mata zuciya, dan har Hawwah sai da tai hawaye. Sosai Ammah taji Æ™arin Æ™aunar Lulu a zuciyarta. Sai da tai shiru

sannan ta fara mata nasiha da bata addu’oi akan ta dage ta dingayi da yawaita karatun Alkur’ani hakan zai dinga rage mata nauyin zuciya, dan masu irin ayyukansu saboda yanda suke tara abubuwan É“acin rai da damuwar al’umma daga Æ™arshe sai kiga sun kamu da hawan jini dana ciwon zuciya. Sosai yanda Ammah ke jero addu’oi a bakinta taji ta sake birgeta da kwaÉ—ayin akan samun ilimin addini. A haka su Asma’u suka shigo Æ™arfe biyu. Da mamaki Ammah ke dubansu dan tasan dai sai biyar suke dawowa daga islamiyya duk ranar weekend. Hawwah ta ce, “Kukuma fa naga kun dawo?”. Kallon juna sukayi kafin Maryam tace, “Adda haddace bamu iya ba shine muka gudo, kin san dai malam Jabeer ba sauÆ™i wlhy”.

 

Ammah data tsira musu ido tace, “Duk karatun da kukai É—azun da asuba. Kudai faÉ—i wani ba wannan É—in ba. Wai Maryam yaushe ma kika fara Æ™arya?”.

 

Ƙasa Maryam tai da kanta tana shafa Æ™eya, Asma’u dake Æ™ara rakuÉ“ewa jikin kujera ta ce, “Ammah gaskiya da gaskiya dai saboda Aunty muka gudo, kinga fa yini zatayi amma mu banda mu. ALLAH muna son muma mu yini tare da ita shine mukai shiri tare da Adda Maryam idan akai salla muyima Malam Jabeer Æ™aryar zamu rakaki asibiti”.

 

Hawwah dake dariya tace, “ALLAH ya shiryeku Ammahn kukai ma sharrin ciwo kenan?”.

 

“A’a wlhy mu bamuce kowa ba, kawai dai munce zamu rakata asibiti”.

 

“Kuma ya yarda? Bayan nasan Malam Jabeer da shegen bin Æ™wanÆ™wanto”.

 

Dariya Asma’u tai tana kallon Maryam, ita kuma ta harareta alamar dai akwai wata a Æ™asa. “Munafukai mi kuke É“oyewa?”. Cewar Hawwah tana kallonsu cikin waro ido. Alamar zip Asma’u taima bakinta da faÉ—in “Ba ruwana ba’a bakina ba”. Lulu da ke murmushi ta ce, “Haba Auta bamu musha mana”.

 

“Aunty ba faÉ—ar bane matsalar, sai kun gudu gidajenku ta jibgan a É—aki ko Ammah bazata bari ta sani ba”. RanÆ™washi kuwa Maryam takai mata. Da gudu tabar wajen tana dariya. “Sonta yake ya kasa gaya mata, gashi kuma ya tsaya kallon ruwa kwaÉ—o yay masa Æ™afa. Dan ga wani tauraro mai babban haske ya faso kai da Æ™arfinsa”. Binta Maryan tayi suka shige É—aki da gudu. Kai kawai Ammah ta girgiza da faÉ—in, “ALLAH ya shiryeku”. Yayinda Hawwah da ke dariya ta ce, “A gama É“oye-É“oyen intai wari maji ai”. Lulu dai murmushi takeyi dan komansu burgeta yake yi. Bakomai ya jawo hakan ba kuwa sai yanayin rayuwar data tashi a ciki ita da nata Æ´an uwan. Bayan su Maryam sun cire Uniform suma falon suka dawo aka É—ora hira, anan sukaci abincin da aunty Amarya ta gama, bayan sallar la’asar Maryam tai zaman yima Lulu kitso. Dan nakan Hawwah ta gani ya burgeta ta tambaya duk da ba son kitso take ba. Jin Maryam ce tayi sai tace itama aimata ko kaÉ—an. Shine sukai zamanyi suna cigaba da hira harda Ammah. Nasreen da suka dawo daga makaranta tana zaune a cinyar Lulu suna shan chocolate dan itama shazumamun ce kamar Lulun. Sallamar Smart ta sakasu tsagaita dariyar da sukeyi dan Asma’u ce ke kwaikwayon Muryar malaminsu Jabeer dake son Maryam wai idan ya ganta har Æ™ara maÆ™ewa yake yi. Akan Lulu ya fara sauke idanunsa kafin yabi sauran da kallo, ya Æ™arasa takowa cikin falon yana kaiwa zaune da faÉ—in, “Miyay muku daÉ—i haka kuke kwasar dariya har tsakar gida kun cikama mutane kunne? Ammah duk sun zagayeki sun dameki”.

 

Cikin murmushi ta ce, “A’a basu damen ba Hydar, ai ko kurama da Æ´aÆ´anta take wasa a jeji. Sai yanzu muke ganin ka”.

 

“Wllhy ki bari dai Ammah. Da ga wani waje mai nisa muke fa, kin san Ahmad da shegen kutse-kutse can wani Æ™auye ya samo gona zai gyara yay gidan gona a wajen shine fa mukaje dubawa”.

 

“Kai masha ALLAH, ai haka mukeso mu kuyita shiga irin hakan dan nan gaba kaÉ—an kune manyan goben.”

 

Murmushi yay cikin jinjina kansa. Kafin ya maida hankali ga Æ™annensa da ke gaishesa. Idon Ammah ya sa Lulu faÉ—in, “Sannu da dawowa”. Sai da ya maimaita kalmomin guda uku a zuciyarsa yana mai É—an kafeta da kallo, sai kuma ya janye shima cikin basarwa ya ce, “Yauwa ya gidan”.

 

Abinci Asma’u taje ta kawo masa, sai cewa yay ta maida baya jin yunwa, garama in sunada fura dan yasan dai Ammah bata rabo da ita. Asma’u tace masa akwai, taje ta É—ibo masa a fridge ta kawo masa. Daga haka suka cigaba da hirarsu Lokaci-lokaci yana satar kallon Lulu da akema kitso masu Æ™yau. Wajen shida ya kalla agogo da faÉ—in, “Ku wannan kitson yaushe zaku gama shi har mu wuce? Gashi ina son mu biya ta wani wajen”.

 

“Ina? Ai ni nan zan kwana yi tafiyarka”. Cewar Lulu da iya gaskiyarta. Murmushi Ammah tayi, yayinda Smart dake mata kallon mamaki ya ce, “Kwana fa? Kin manta gobe Monday zakiyi resuming office?”.

 

“Ba damuwa jibi naje”.

 

Murna su Asma’u suka fara yi zata kwana. Ya hararesu duk sai suka nutsu. Ammah dai bata ce komai ba har sai bayan sallar magrib da ya shigo ya sameta a É—aki, lokacin su suna can É—akin suna tasu sallar. Zama yay kusa da Ammah, hakan yasata yin addu’a ta rufe Alkur’anin. “Ba dai tafiyarba ko?”.

 

“Da haka nake so dai ta shirya, da anyi isha’i sai mu wuce dan ina son mu biya ta gaida Kakanta É—azun Uncle Yousuf ke faÉ—amin baya jin daÉ—i ya dawo daga Legos É—azun, gashi kuma tana batun kwana anan”.

 

“Karka damu zan mata magana. Amma Aliyu sai nake ganin akwai wani É“oyayyen al’amari a rayuwar yarinyar nan dake damunta, na fahimci hakanne a É—an firarmu da ita ta É—azun. Sannan bata son kaÉ—aici, dan ta roÆ™eni na baku Asma’u ta koma can da zama. Danace mata Abbanku bazai yarda ba ina kula da ita sai da idonta ya cika da hawaye. Mizai hana a É—an samo mata ko tsohuwa haka da zasu zauna tare, sannan kai kuma ka Æ™ara Æ™aimi wajen janta a jiki dan ka fahimci minene damuwarta. Ko yaya ta sanar maka itama zataji nauyin ya ragu mata a zuciya. Ashe mahaifiyarta bata raye kuma?”.

 

“Ta rasu, tana haihuwarta. Inasha ALLAH zan yi iya Æ™oÆ™arina”.

 

“ALLAHU akbar. ALLAH ya gafarta mata. Wlhy duk sai yarinyar ta sake bani tausayi. Gata da sauÆ™in kai da sanin darajar mutane. Sai kuma yanda na fahimta akan aikin nan nata kamar zafinta akan al’amarin fyaÉ—e nada alaÆ™a da wani abu daya sosa ranta gaskiya. Ya kamata dai ka zama mai haÆ™uri da dinga Æ™arfafata”.

 

“Insha ALLAHU Ammah zan yi iya Æ™oÆ™arina. Batun Asma’u kuma haÆ™uri zakuyi ta koma can É—in tunda tana son hakan. Kodan ma tafiyar nan dake tunkarowa.”

 

“To bazance A’a ba, amma ka samu Abbanku da maganar kadai sanshi. In akan tafiyane kuwa bazai yiwu dama a barta ita É—aya ba. Ko ita da Asma’u kawai dole cikin samarin nan wani ya koma can ya dinga kwana da su”.

 

“Hakan ma yayi Ammah. Duk yanda kikace haka za’yin”.

 

Sun É—an Æ™ara tattaunawa akan abinda ya shafesu musamman akan Hawwah, kiran sallar isha’i ya sashi tashi ya fita. Bayan ya dawo sai da Ammah ta lallaÉ“a Lulu da wayo sannan ta yarda su tafi. Yanda take zubama Ammah É—in shagwaÉ“a sai Smart ya zama É—an kallo. Dan mamakin yanda tai bala’in sakin jiki da Ammahn yake yi har irin haka a Æ™anÆ™anin lokaci. Koda tajema su Umma sallama har yanzu akwai alamar takaicin Æ™yautukan data raba musu É—azun a tattare da ita. Dan kusan ma a tashin hankali ta yini, ga surukar jiya-jiya a gida daga zuwa tana neman fara haskawa, yarinya da baÆ™in wayo. Ai zama bai ganta ba, dan kuwa kamar ta kashe maciji ne bata dare kansa ba kasancewar Lulu matsayin surukar gidan nan na nufin disashe tauraron Æ´aÆ´anta da ake gani sama dana kowa. Oho Lulu ba damuwa da sabgar da ba’a sakata ba gareta, dan haka ita bata wani fahimci mi Umman ke ciki ba, dan ko kallon su Huwaila dake falon batai ba. Haka kawai jininta dana Umma baizo É—aya ba, da Æ™yar ma ta yarda ta biyo Smart É—in suka shigo da tace yaje ita zata je É—akin Aunty Amarya ya sameta ya nuna mata dole ta shiga ko’ina suyi musu sallama. Ganin babu wasa a tattare da shi yasata bin nasa badan taso ba. Daga wajen Umma sai É—akin Mama. Nan ma basu jimaba suka fito, nan ko Mama ta bata alawar madara da Hannatu keyi ta saidawa. Hakama aunty amarya ta bata farar data soya mata da rana har kwano biyu. Aiko taji daÉ—i tanata godiya. Abba ma sunyo masa sallama ya haÉ—a Lulu da tsarabar zuma da mazarÆ™waila kasancewar sa masoyinsu yana ajiyewa. Sai da zasu shiga napep Maryam ta ajiye mata ledar tsarabar Ammah. Duk sai Lulu taji Æ™aunar bayin ALLAHN nan na sake ratsata. Shi kansa Smart yaji daÉ—in wannan karamci da sukai mata. Kasancewar mai Napep É—in É—an anguwarsu ne zai kaisu har gida da inda ma zasuje kai tsaye ya nufi Nasarawa G.R.A dan Smart ya riga ya sanar masa tun kan Lulu ta fito. Ganin inda suka nufo ya sata jin farin ciki, a Napep É—in suka bar kayan suka shiga cikin gidan na Alhaji Sufi Ado Garko. Sun sami yaran gidan da jikoki da yawa, inda kowa yay musu ca aga yaya Lulun ta koma. Sai kuma suka ganta fes har wani Æ´ar Æ™iba kamar ta Æ™ara musu ma su a ido. Alhaji Garko dake kallonsu da murmushi ya nunama Aliyu kusa da shi. Maimakon hakan sai ya zauna a Æ™asa kusa da Æ™afafunsa ya gaidashi cikin girmamawa da tambayar yaya jiki. Da kulawa ya amsa masa da sanya albarka. Dada kam sama-sama ta amsa masa tana masa hararar Æ™asan ido Lulu na jikinta lafe. Ya gaisa da sauran wanda suke É—akin suma, daga haka yaja bakinsa yay shiru sai Baba ya takalesa da magana ko tsokana ne yake É—an murmushi koya bada amsa a taÆ™aice. Kusan awansu biyu sukai shirin wucewa, anan ne Dada ke cema Lulun “Ku bari sai anjima mana tunda dai mota ce kuma daga nan guda kukai”. Batare da Lulu ta kawo komai a ranta ba ta ce, “Dada a Napep muke fa, babu daÉ—i mun barsa a waje kusan awa biyu. Kuyi haÆ™uri zan dawo gobe in sha ALLAHU”.

 

A zafafe Dada ta ce, “Napep kuma? To ina motocin naki? Kodan shi baida motar hawan dan bakin ciki irin na talaka kema bazaki hau ba? Kamarki jikar Garko family a garin nan da hawa Napep…”

 

Yanda Dadan ke maganar a zafafe da É—aga murya kowa naji ya saka Lulu duban inda Smart yake, sai kuma ta dubi Dada zatayi magana cikin É“ata fuska amma ta dakatar da ita……..✍️

No comments