Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 51


[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: Da sauri ya kalli Akeeth ya ce “Boss binsan zaka yi? zuwa can Saudiyya É—in?” Akeeth ya dinga kallon yaron nasa mai suna Ziyad, ganin baiyi magana ba ya sanya Ziyad cewa “Idan babu damuwa kuma ba zan shiga rayuwarka ba, yau É—aya ina son ka bani dama na baka shawara a matsayina na musulmi kuma É—an uwanka, wanda yake ci a Æ™asan ka” Akeeth ya É—an yi gyaran murya hakan yasa driver ya ja suka nufi asibiti, Ziyad ya sake cewa “Ka bani dama please” “Ina jinka Ziyad, amma a cikin shawarar da zaka bani banda rabuwa da Malama Majeederh ok”
Da sauri Ziyad ya ce “Dole a kanta ne, ka saurare ni a karo na farko, ba zaka taÉ“a nadama a cikin shawarar da zan baka ba” A hankali Akeeth ya ce “Ina ji” Ziyad ya ce
“Kai babba ne, kuma mai hankali kasan menene ya dace da wanda bai dace ba Boss, yanzu menene ribarka idan ka auri wacce bata son ka?” Akeeth ya yi shiru, Ziyad ya É—ora da “Kai ne da matarka harda yara kuna rayuwa ta farin ciki, kwanciyar hankali da jin daÉ—i sai rana tsaka wani ya kawo kai da nufin rusa wannan farin cikin, da nufin rabaku rabuwa ta har abada bayan kuma duk duniya banda iyayenka ba wanda kake so sama da matarka don Allah ya zaka ji?” Akeeth ya rufe ido yana dafe kansa dake juya masa, a zaune yake amma jinsa yake kamar zai kifa, a hankali ya girgiza kansa ya ce “Ba zan barshi ba”
“Good, kuma tayaya kake tunanin Khalil zai barka ka raba su da Malama Majeederh? Idan da wanda zai fara bada shaidar soyayyar da sukewa junansu tun kafin su kasance miji da mata bai shige kai ba, zata kawo shi gidan marayunka, ya yi sati zuwa wata da Æ™yar suke rabuwa, balle yanzu da yake ganin cewa ita É—in matarsa ce? Kasan waye Khalil? Idan ransa ya É“aci shi da mahaukaci bashi da banbanci, ina tunanin kamar ka shiga cikin hurumin Ubangiji ta hanyar nuna maitarka ta son matar aure, matar wani, kuma ba Æ™iyayya tsakanin su balle ka ce” Akeeth kallon Ziyad kawai yake, sosai ya fahimta amma zuciyarsa ta kasa fahimta ko gane abubuwan da Ziyad É—in ke faÉ—a masa a nutse ya ce “Amma na riga shi son ta, tun a lokacin da take kawo shi gidan marayun nake son ta, i don’t know what comes over me dana kasa fuskantar ta da soyayya wallahi”
“Hakan yana nufin ita É—in ba alheri bace gareka, ita ba kowa bace face Æ™addararka (Your destiny)” A hankali ya ce “Destiny? Fate? Ƙaddara kuma?” Ziyad ya jinjina kai ya ce “Ko shakka babu, Majeederh is your destiny ita ce Æ™addararka, duk abinda Ubangiji zai jarabci bawa da shi har yake wahalar da shi to tabbas abun nan shi ne Æ™addarar shi, kuma kar ka bari hakan ya yi tasiri a zuciyarka akwai mata da yawa a duniya masu ilimi, aji, kyau, da duk wasu Qualities da kake buÆ™ata” A taÆ™aice Akeeth ya ce “Qualities É—in Malama Majeederh da ban yake, she’s different from others, daban take da sauran matan, kawai na yi sake ban taÉ“a zaton Abraham zai girma ya ce yana son Majeederh ba, ban taÉ“a zaton zata iya auren shi ba, na É—auka za ta yi tunanin yarintar shi ta dubi Æ™anÆ™antar shi” “Me zaka nuna masa a yanzu Boss? Dame zaka fi Khalil É—in? Da shekaru ne dai kawai, su kuma shekaru are just a number” Akeeth ya kalli Ziyad kamar yana son gasgatawa, Ziyad ya girgiza kai ya ce “Kuma shi namiji a duk inda yake namiji baya Æ™anÆ™anta, zanen sunan shi na namiji zai ta kasancewa cike da iko, kamar yadda Ubangiji ya faÉ—a a cikin Alkur’ani, suratul Nisa’i, maza gaba suke da mata zasu iya jagorantar su a komai, don Allah Boss karka raunata zuciyar Khalil yana tsananin so da Æ™aunar matarsa, yadda ya shaÆ™u da matarsa ko da iyayensa bai shaÆ™u ba, ni nake bibiyar shi nake ganin komai, yana da É“oyayyen sirri fitar shi kawai ake gani, amma yana da wani irin Qualities wanda ba ko wanne namiji ke dasu ba, yana yin abu don Allah shi ya sa bai damu daya faÉ—awa jama’a waye shi ba, yadda ba a haifeka mahaifa É—aya da Majeederh ba, haka ba zaka taÉ“a mutuwa saboda baka sameta ba, believe me” Akeeth ya ce “Abraham bashi da hankali, yana da zuciya bai cancanta da zama Mijin Malama ba, ina tsoran watarana ya yi mata illa nafi kowa sanin waye shi wallahi, Ziyad kar kaga laifina ko ban auri Majeederh ba, kawai ta samu wanda zai dace da ita but Majeederh ba tayi deserving auren mutum kamar Abraham ba, duk wahalar nan data sha” Ziyad couldn’t speak, ya kasa magana gabaÉ—aya sai kawai ya ja bakinshi ya yi shiru, hospital suka nufa aka bawa Ziyad gado saboda karayar hannunsa yana buÆ™atar resting bed.

Idanunsa rufe ya shigo cikin haÉ—aÉ—É—en parlourn gidan nasu, ya yi tsaye, magidanciyar matar dake zaune saman kujera da counter a hannunta ta kalli Akeeth a hankali ta ce “Baka sameta ba?” Ta faÉ—a a taushashe Akeeth ya yi saurin cillar da wayar hannunsa ya Æ™arasa gaban Nenne ya zauna yana É—ora kansa a cinyarta ta shiga shafa kansa tana jin yana sauke ajiyar zuciya “Zaka haÆ™ura yanzu dai ko? Ka tabbatar ba rabo tsakaninku?” Akeeth ya É—ago kai ya kalli mahaifiyarsa ya ce “Tayaya zan iya haÆ™ura da ita Nene? Nida ita kamar É“arin gyaÉ—a ne how can you imagine zan rayu without her eh?”
“Me kake so yanzu Akeeth?” A hankali ya ce “Your help, your support, and your prayer” Ta riÆ™e hannunsa ta ce “Addu’ata kullum tana zagaye da kai, ina yi ba ranar fashi”
Da sauri ya ce “Call Majeederh and ask her to love me, please Nene” Nene ta ce “Karka zama mai tsananin son kanka a cikin al’amarin rayuwa Akeeth, babu rabo tsakaninku tunda har bata kasance matarka ba, ka yarda cewa ba kai ne MIJIN MALAMA ba, Idan Rabo ya rantse ko babu ciwo dole a tafi, haka Idan Rabo ya rantse duk wahala duk Æ™iyayya dole ta kasance matarka ka nutsu ka kwantar da hankalinka”. A hankali idanunsa na cika da wasu hawaye masu zafi sosai ya ce “Nene!”
“Ka yi haÆ™uri” Ya damÆ™e hannunta sosai yana kifa kansa a cinyarta ya ce “Nene, zuciyata ba daÉ—i na yi kuskure” A hankali itama idanunta na cika da hawaye ta ce
“Babban kuskuren shi ne amfani da sunan Mr no name, da Akeeth ka sanya maybe da tasan da zamanka, kayiwa kanka uzuri kayiwa Majeederh uzuri idan da wacce ta cutar da rayuwarku bai huce Latifa Omar ba, ka yi addu’a ka manta” Ya yi shiru kawai, Nene ta shiga damuwa Akeeth kawai ta mallaka a duniya shi É—in maraya ne ubansa ya mutu ya barshi da arziÆ™i kamar ba zasu Æ™are ba, bashi da aiki sai na bata labarin Majeederh, ranar da aka ce Majeederh tayi cikin shege a sume suka nufi asibiti da shi, kuma shi ne wanda ya yi rubutu a media domin kare hak’Æ™inta, tana ganin al’amarin shi kamar zaucewa irin na masu fama da shigar sabuwar Soyayya. Ta ce “Akeeth ga Æ´ar uwarka? Ga Rusul?” Ya girgiza kai kawai ya ce “ALLAH YANA GANI Idan har ban auri Majeederh ba to na haÆ™ura da aure” Ta zare ido ta ce “Idan baka yi aure ba sai me? Ka rufa mini asiri kada Aljana ta aureka (ALLAH YANA GANI)”. Bai furta komai ba ya miÆ™e ya nufi part É—insa idanunsa rufe yana jin wani irin zazzafan zazzaÉ“i na rufe masa jiki.

A can Ikot Ekpene Prisons Mr President ne zaune shi da Latifa Omar bayan ya samu kaÉ—aicewa da ita, ta hanyar wani Gandiroba mai bala’in son kuÉ—i ta kalle shi ta ce “Amma Sir Khalil ya tsaneka” Ya girgiza kai ya ce “I knew my son more than anything, nasan waye shi yana so na, nasan kalar son da yake mini I just need your help” A hankali ta ce “Name?”
“Ya yafe mini, na yi regretting komai bani da tabbacin zan bar gidan nan ko a’a, idan har na bari to tabbas zan dawo ga iyalina idan ban bari ba to zan zauna a nan har zuwa mutuwata” Latifa ta ce “Sir kun yarda zaku mutu kenan?” Ya kalleta da mamaki a fuskarsa sosai sai kuma ya ce “Mun sani, a littafinmu ai mun san mutuwa gaskiya ce duk wani wanda ki kaga yana aikata abu wanda yake ba daidai ba ya sani, son kuÉ—i ta rufe idona na banbanta kuÉ—i da iyalina, wanda a yanzu ba kuÉ—in kuma iyalin nawa nake buÆ™ata su nake son gani, amma bani da confidence na zuwa inda suke bani da confidence na neman yafiyar su” Ya É—an saurara sai kuma ya ce “Ina son Gimbiya so mai yawa, komai nata birgeni yake amma rashin kishi da masifar son kuÉ—i nake son sadaukar da ita ga wani? Wanne irin miji ne ni?” Ya runtse idanunsa a hankali hawaye masu zafi suka shiga gangaro masa kafin ya ce “I am ashamed, I have failed as a father” A hankali ya lumshe idanunsa tears running down his cheeks”I made a mistake and I regret doing all the things I did in the past, dama lokaci ya bani dama na tariyo bayana domin gyara goben da bani da tabbacin kyanta, duk da ban kasance musulmi ba, amma nasan abubuwa masu kyau wanda littafinmu ya zo da shi” A hankali Latifa Omar ta ce “Kana cikin lokacin ka Sir, zaka iya amsar shahada, idan ka yi believing da addininmu” Ya girgiza kai ya ce “Da alama bani da rabo, ban ji son hakan a raina ba, Musulunci bai cancanta dani ba”
“A’a Sir!” Latifa ta faÉ—a a É—an gaggauce ta ce “Addinin Musulunci mai sauÆ™i ne, ga ma’abota soyayyar shi, baya da wariya wajen bambance wanda zai shige shi, kyakkyawar niyyar da tsarkakkiyar zuciya kawai ake buÆ™ata, abu mafi wahalar shi ne da wacce kalar zuciya kake son musulunta? A nan kuma sai ka saurari zuciyarka abinda duk kayi imani da shi, to shi ne daidai kayi amfani da damarka domin baka da tabbacin kawai anjima ko gobe” Da sauri ya ce
“Ina son musulunta Æ´ata, tsoro ne kawai ya hanani ina ganin kamar addinin ba zai amshe ni” Murmushin jin daÉ—i Latifa tayi, ya yi alwala a wajen aka bashi kalmar shahada yana faÉ—a idanunsa na cika da hawaye duk duniya yanzu iyalansa yake buÆ™ata, Gimbiya, Khalil, Clara, Zizi, Badi, da kuma Kiristi ko mutuwa ce ta É—auke shi a cikin su, Latifa Omar ma kukan take sosai zuciyarta babu daÉ—i, envelope din daya bata ta É—auka ta nufi part É—insu na mata a asirrince ba tare da ankarewar kowa ba. Cikin dare zuciyar Mr President ta buga ko motsawa bai ba Ubangiji ya zare ran shi a ranar daya karÉ“i shahada, daman haka ne idan kakan aikata aikin Æ´an wuta, idan Ubangiji ya soka da rahama kana dab da mutuwa ka koma aikin Æ´an aljanna, idan na Æ´an aljanna kake kaso taÉ“ewa sai ka koma na wuta, su Latifa na kwance aka dinga tashin su ana fita ta wata Æ™ofa har suka fice daga cikin prison aka sanya su a wata Æ™atuwar mota tare da É—aukan hanya da su.

“Sister ina za a kaimu?”
Latifa ta tambaya a tsorace, wacce ta tambaya É—in ta ce “Haka ake mana duk sati ko duk wata, sunan an kawo mu nan da niyyar gyaran hali ko yanke mana hukuncin zaman gidan kaso gabaÉ—aya har mutuwa ko mu yi shekaru mu fita, amma an mayar damu saniyar tatsa” Latifa ta ce “Pardon! Ban fahimta ba” Ta ce “Ina nufin yanzu haka kaimu wajen wasu manyan gari za a yi su kwanta damu, bamu da wani option wanda ya a shige obey, yanzu hatta Æ™wayoyin maye da ake karÉ“ewa wajen mutane sune suke amsa, to da irin haka taya rayuwa zata gyaru? Wani ma laifinsa bai kai matsayin da za a kaisa prison har haka ba…,” Ta kasa ci-gaba da maganar saboda kukan daya Æ™wace mata… Saukar yamma duk Khalil sukai Majeederh tunda jirgi ya tashi ba taga Khalil ba sai yanzu da suka sakko, ya kasa haÉ—a Idanu da ita, kunyarta yake ji sosai bai san mene ya sanya ya kasa controlling kansa a lokacin ba, ya kama su twins Yaa K na tare da Majeederh daman already ta faÉ—awa Zaytoon zuwan nasu sai dai bata shaida mata da Khalil bane, motocin Palace a jere wajen biyar, a nutse Gimbiya ta fito daga motar tana sanye da wata milk É—in alkyabba wacce ta amshi jikinta sosai, fuskarta a kame kamar kullum, sai Clara wacce take tsaye a gefenta ta saka baÆ™ar abaya tare da zagaye fuskarta da veil, sai Rohaan, É—aya motar Zainab da Badriyya ne suka fito gabaÉ—aya cikin abaya iri É—aya, Zizi da Badi. A kusan lokaci É—aya cikin daÆ™iÆ™a guda idanun Gimbiya dana Clara wacce itama ta musulunta ta koma Fatymerh ya sauka akan Khalil duk yadda Gimbiya ta kai ga jan ajinta da riÆ™e kanta kasawa tayi, ta saka hannu ta murje idanunta still Khalil take gani tsaye yana mata murmushi ga yaransa da matarsa zagaye dashi, Jee ta nuna kamar babu komai, Gimbiya komai nata ya tsaya ta kasa yarda ko gasgata abinda take gani da É—an sauri cike da nutsuwa Khalil ya nufeta yana zuwa ya rungumeta, suka sauke ajiyar zuciya “Ummie” Ya furta a taushashe tana jin muryarsa mai cike da kamala ta rungumesa a jikinta tare da sakin wani irin raunataccen kuka tana cewa “Khalil? My son…..
[

No comments