Breaking News

Yanci da Rayuwa 37


Arewabooks;hafsatrano
Page 37

***Wuce Mummy AJI yayi ya tura kofar dakin da Asim yake ciki ya samu Abdullahi a tsaya gaban gadon sa yana masa sannu. Shigowar AJIn yasa shi saurin ja baya ya matsa yana gaishe shi.

“Abdullahi aje a samo masa abinci yazo yaci ya mike.”

Sai ya juya wajen Asim din

“Bana son shirme da sokonta idan zakayi ma kanka horon yunwa a banza zaka wahalar da kanka, dan babu wanda ya isa ya chanja kaddarar sa.”

“Sannan idan ka biye wa hudubar uwarka kai zata kai ta baro, son kanta ya hanata hango gaba burin ta kawai ta samu abinda take so, gashi nan zata kaika ta baro idan kuwa kace haka zakayi, ba zamu shirya ba.”

“Amma me yasa Rafeeq zai yi min haka? Bayan duk duniyar nan babu wanda na yarda dashi kamar shi, ya kuma san komai amma ya rufe idon sa.”

Dariya AJI ya saka yana kallon Asim din,

“Ashe abinda ta karanta maka kenan, toh uwarka duk ita ta shirya wannan abun, ba kare shi nake ba dan be isa na kare shi ba ka sani,amma bashi da hannu a wannan shirin, sannan abinda baka sani ba, shine ya fara son matar sa ba kai ba, tun tana yar kuciciyar ta har ta kai girman da ka ganta,kuma ko bayan nan da ya gano be yi yinkurin komai ba, ya karbi hakan a matsayin kaddarsa saboda yana ganin zai iya sacrificing komai akan ka, bansan yaushe zaka gane waye Rafeeq ba idan har yanzu baka gane ba, anyways kana da zabin zabar abinda yayi maka. Abu daya zan sake jaddada maka, bana son shiririta ka karbi abinci kaci ka roki Allah ya shirya maka mahaifiyar ka kuma, sannan ka koma bakin aiki. A hakan kake so ka karbi ragamar kasuwancin namu da raguwar zuciya? Lallai da sauran ka.”

Sai ya mike yana dogara sandar sa, ya fice daga dakin. Be ga mummy a wajen ba, sai kawai yayi tafiyar sa bayan ya sake jaddadawa Dr drip din na karewa a sallame shi gida.

***Aiki sosai ranar Rafeeq yayi, yana yi yana duba wayarsa ya sake dialing number ta amma switch off, sai a karshe ya sameta shine ya sanar da ita ta shirya zasu fita.
Karfe biyu ya tattara aikin ya rufe, suka fara sallar azahar sannan yace su biya asibitin. Asim din ya mike yana zaune ma yana danna wayarsa Mummy na gefen sa tana ta masa magana amma yaki ya bata cikakkiyar amsa. A gajarce kawai yake amsawa yana cigaba da danna wayar maganganun AJIn na ta masa yawo akai. Knocking Rafeeq ya fara yi kafin ya turo kofar a tunanin Asim din ne ma shi kadai. Shigowa yayi ya maida kofar ya rufe ya karaso ciki yana kin kallon side din da Mummyn take da take binsa da wani kallo da yasa shi zama uncomfortable. Hannu ya mikawa Asim din duk da baya tunanin sai karba amma ga mamakin sa sai yaga ya bashi hannun sun gaisa .

“How are you feeling now?”

“Alhamdullillah, yanzu zamu wuce gida ma.”

“Masha Allah, Allah ya kara sauki.”

“Amin.” Yace yana kallon kujerar dake gefen gado

“Ka zauna mana.” Asim din yace ganin yayi tsaye kawai

“No, tafiya zan. Idan ka dawo gidan zamuyi magana.”

“Rafeeq baka ganni bane ba? Ko wulakancin ne ya motsa?”

“Mummy please!” Asim yace yana bata fuska

“Will you shut up. Baka ga rashin kirkin da yayi min ba, ai ko kashi ya shigo ya gani a zaune da kai ya gaishe shi bare ni, nafi karfin wulakanci wallahi.”

“Ayi hakuri, na dauka mun gaisa dazu.”

“Idan uwarka ce ai ba zaka ce haka ba.”

Kallon ta yayi jin yadda ta ambaci uwarsa haka, ba dan Asim ba da ya bata amsa daidai da ita, amma duk tsiya mahaifiyar sa ce, dole ya yi hakuri saboda shi amma kam yau tabbas da ta yi dana sani. Murmushi yayi kamar abun be dame shi ba ganin yadda ran Asim din ya baci, yayi masa sallama ya fito ya barsu yana juyo sautin fadan ta.

***Kai tsaye gidansa ya wuce da burin ganin sanyin idanun sa, ko da yaji ransa na neman baci yana tuno ta da moments din da sukayi having tare sai yaji damuwar ta tafi gaba daya, sallama sukayi da Saddam yau ma yace masa shikenan dan shima kwana biyu shirye shiryen auren sa yake da ya taso gadangadan shiyasa rage din yake daga masa kafa. A gate ya sauka ma ya shigo da kafa hakan yasa bata ji karar bude gate ba bare ta san ya dawo har ya shigo falon yana shakar daddadan kamshin da falon ke fitarwa. Zama yayi ya mike sosai bayan ya zare takalmin kafarsa yana jin tarin gajiya da kasala na saukar masa lokaci daya.
Ta gama shiryawa ta dauko wayarta ta fito daga dakin kawai taga mutum a kwance. Da farko sai da ta tsorota kafin ta gane shine. A shanye yake kallonta da sexy eyes dinsa har ta karaso gaban sa tazo ta durkusa kasa ta gaishe shi cike da ladabi sannan tace

“Sannu da zuwa.”

Sosai ta bashi mamaki yadda tayin har ya kasa bude baki yayi magana sai hannun sa da ya mika mata ta kama ya jawota yana mata masauki a jikinsa.

“I’m damn tired, ganin ki kuma ya kara saka min kasala gaba daya, anya zan iya fita kuwa?”

“Kayi wanka, zaka ji gajiyar ta tafi.”

“Zakiyi min?”

“Na’am?”

“Umm, ki taimaka ma bawan Allah, kinga na gaji inata aiki kar AJI yace ya koreni gida nazo na rasa na maggi.”

“Ba zai koreka ba.” Tasa dariya

“Da gaske, toh muje kiyi min kinji?”

“Ni wallahi ba zan iya ba.”

Yadda ta fada tsakanin ta da Allah har da rantsuwa ya bashi dariya, ya cikata yana kyalkyalawa kamar zai fadi. Dariyar take itama tana kallon shi sam bata ga abinda zai saka shi dariya haka ba, iya gaskiyar ta, ta fada masa wallahi ba zata iya ba.

“You are funny wallahi, babu yar karar nan harda rantsuwa ko?”

“Umm.”

“Toh naji, help me ki hada min ruwan toh.”

“Ok toh.”

Tace ba tare da tunanin komai ba, ta tashi ta nufi dakin sa. Mikewa yayi yana dariyar rashin wayon ta, yabi bayanta yana zare kayan jikinsa gaba daya. Cirewa yayi ya dauka towel ya bi bayanta toilet din, tana gaban tap din tana kokarin daidaita ruwan ya shigo sai jin mutum tayi a bayanta, kafin tayi wani yinkuri ya ja ta zuwa cikin tub din tana ihu tana komai ya matse ta, kayan jikinta gaba daya suka jik’e haka tana ji tana gani ya gurje ta son ranshi, kafin ya kyaleta.
Kukan shagwaba ta dinga zuba masa yana bata hakuri, da kansa ya dauko mata wasu kayan ya taimaka mata tasa hade da wata yar ubansun laffaya golden. Sai da suka fara yin lunch sukayi sallar la’asar sannan ya taimaka mata, suka daura laffayar da taimakon tutorial da suka samo a YouTube. Ya dade yana admiring shigar shiyasa ma ya kwaso mata su ranar aikuwa tayi bala’i kyau a ciki, handbag ta dauka me kalar ta da flat shoe suka fito. Duk sanda zasu fita yafi son yin driving da kansa hakan na bashi nishadi sosai shiyasa yau ma su kadai suka fita.
Be fada mata in da zasu je ba,ta dai yi tunanin wajen Baba zasu tunda yace zai kaita. Wani estate taga sun shiga a area11, yayi parking a kofar wani block sannan ya kashe motar yana kallon ta

“Ina ne nan?”

“Siyar da ke zan.”

“Ai ba zanyi tsada ba.”

“Waya fada miki? Bari ki gani.”

Daukar wayar sa yayi ya kira Suraj yace masa ya bude kofa. Suna zaune cikin motar ya fito, ya gaida Rafeeq din sannan suka fito daga motar zuwa cikin gidan. Baba na zaune a falon yana shan fruit be san da zuwan su ba sai ganin su yayi kawai. Itace a gaba bayan Suraj din.

“Babaaaa.” Sai ta tafi da sauri ta fada jikinsa tana rungume shi. Kunya ce ta kamashi, ya tureta yana dariya

“Yaushe zaki girma?”

“Sannun ku da zuwa.”

“Yawwa sannu Baba.” Rafeeq yace a kunyace yana kokarin zama a kasan carpet. Da sauri Baban ya tare shi

“Karka zauna a kasa dan Allah, haba haba.”

“Nan ma yayi Baba, babu komai.” Ya zauna yana tankwashe kafar sa. Kasan Baban ya sakko shima suka gaisa sannan ya tambaye shi kafa

“Kafa yar gata, gata nan tayi lafiya Alhamdullillah.”

“Kuna fita ku zazzagaya surah?”

“Eh muna fita.”

“Muna zagaya wa ai, alhamdullillah.”

“Toh Masha Allah.”

“Baba baka kulani ba.” Tace tana turo baki gaba.

“Me zan ce miki toh uwata?”

“Ka daina sona yanzu Baba.”

Sai ta tashi tayi hanyar wata kofa,

“Toilet ne.” Baba yace yana dariya, juyawa tayi ta chanja hanya zuwa bedroom din Baban, ta shiga ta zauna a gefen gadon sa tana admiring dakin da gidan gaba daya. Kwalla ce ta zubo mata, kwallar farin cikin yadda rayuwa ta sauya musu a dan kankanin lokaci. Biyo ta dakin Baban yayi dan ya gane so take suyi magana su kadai, yana shigowa ta rike hannun sa tana dariya da hawaye shabe shabe.

“Kinga yadda Allah ke ikon sa ko? Ki rike mijinki dan Allah, kiyi masa biyayya ki so duk abinda yake so kiki wanda baya so, kinyi sa’ar miji na gari, me son ki da kaunar ki.”..

“In sha Allah.”

“Babu wata matsala ko?”

“Babu komai Baba, kawai dama tambaya zanyi, su waye suka zo tambaya?”

“Hajiya Maryam ce tazo min da maganar dai, daga baya suka zo tare da ita mahaifiyar tashi mutuniyar kirki, ita ta nema masa auren kafin maza su zo daga baya.”

“Ok.”

“Akwai matsala ne?”

“Babu komai baba.”

“Toh shikenan, bari na koma wajen sa, ki fito zanyi magana daku akan zuwa Mambila.”

“Mambila Baba?”

“Eh in sha Allahu, zamu je su ganki ki gansu saboda halin rayuwa, kwanan nan zaki fara tara iyali, yana da kyau ki je kiga asalin ki.”

“Da ma kar muje baba, tunda basa son mu.”

“Nine basa so, amma ke suna sonki.”

“Nima bana son su tunda basa son Babana.”

“Kayya, muje dai falon.”

Shi ya fara fita ya zauna suka dan cigaba da hira kafin ta fito tazo ta zauna a chan baya dan ba zata iya zama tare waje daya dashi da Baban ba. Nasiha Baba yayi musu me shiga rai musamman ita yafi bada karfin akanta, sannan ya bijiro masa da maganar zuwa garin nasu.
Daf da magriba sukayi wa Baban sallama suka tafi, Noor kamar tace ya barta amma babu hali, tasan Baba ma ba zai barta ba shiyasa ma bata ce din ba, a mota magriba ta same su, suka tsaya Annur suka yi sallah sannan suka wuce gida.

No comments