Breaking News

Soldiers Family 23-24

Page 23&24

 

__”cikin tashin hankali yake duban mama da,akayi can sama da ita kowa ya sadaƙar kawai tata tak’are Amma Banda Jalaludeen daya shiga wani tunanin daban…kamar


aljana hakan ta fad’o k’asa tsaye da kafafunta ko russunawa batayi balle ba,asin fad’uwa gashin kanta daya watse ga baki d’aya ya zubu ya rufe fuskarta….wannan karon dukkansu tsit sukayi suna kallonta duk da cewa sun Dan razana Amma Basu nunaba kasan cewarsu maza Kuma sojoji.

 

Wani irin d’agowa mama tayi dakanta atake gashinta ya koma baya fuskarta ta bayyana Amma wannan karon sunyi bala,in razana ganin yadda kamanninta suka sauya lokaci d’aya kamun Kuma tadawo normal mamarta tana kallon mutanen wurin idonta ne ya fad’a kan abbe cikin sauri tace, “abbana” tafad’a dak’arfi tare shigowa aguje wurinshi har abbe ya bud’e Mata hannu Yana sauke ajiyar zuciya sekuma yaga ta tsaya tsab kamar ankafeta…Kuma ita d’in daice ba wata ba fuska ta kwab’e kamar zatayi kuka tace, “way’annan dodannin bazasu bari nashigaba Abba…”da mmki abbe yace, “suwaye zaran Abba? Gasu anan yafad’a Yana nuna gurinsu Zaid da Ameer se Sulaiman dake gefensu… murmushi Abba yayi kamun yace yayunkine zaraan Abba bazasu hanaki shigaba kinjiko…Abba bafa way’annan ba gawasunan sune suke tareni….wannan karon ba Zaid kad’aiba hadda su Fahad seda sukayi tsaki abunkaga soja dasaurin zuciya gani sukeyi duk renin hankaline take yi musu…Abba dake tsaye tind’azu Yana kallonsu bece komaiba shine yazo yarik’a hannunta Yana fad’ar shigo abunki kinji Yar Habeeb rabu dasu..ai kamun Abba yarufe Baki aka sake fisgeta ahannunshi akayi wulgida ita saboda kawai takowar datayi…arane tace ahhhhhh bibiboonaaa zasu kasheenii…ai tinkamun tak’arasa wata irin guguwa takarad’e wurin kamar za,ayak’in duniya kowa dake wurin seda yasamu abunda yarik’e kafun su,iya tsayawada kafafunsu…wannan bubuwar tad’au kusan minti 15 tana kad’a wurin kamun talafa.

 

Koda duk suka bud’e idonsu arazane kowa yaja baya suna Kara zare idon hadda Alyasat da fitowarshi kenan saboda wannan guguwar.

 

Wani shirgegen maciji ne suka gani ya kanannad’e mama sosai Wanda suka kasa ganin k’arshensa Amma be matseta ba se huchi yakeyi me masifar zafi…itako mama sewani kwab’e fuska takeyi irin ya nagaban uwarta d’innan.

 

Innalillahi wa innailaihhiraji un mizan gani Dan Allah kutemaketa karya lahantata amanace aguna….””Kar Wanda yak’araso Nan sukaji wata murya me masifar amo da firgici…gabaki d’aya mutanen dake wurin sunshiga tashin hankali marar misaltuwa yayin da wasu sukaje suman wuccin gadi…Amma Jalaludeen kallo kawai yakeyi ba tare da wani mamaki ba Kuma ya gano wannan macijin bibibo ne.

 

“Dukkanku Muna buk’atar kunemi gida d’aya kushiga kab mutanen dake cikin stet d’innan ikuma ba hakaba mutun ze iya rasa ranshi….akasake fad’a cikin k’araji.

 

Shiru duk sukayi kowa yakasa magana suna tunanin wannan abun kamar daga sama sukaji muryar Alyasat Yana fad’ar, “akan wanne dalilin za,ayi hakan?” “Waye ke wannan maganar Idan ba tsoro ba ka bayyana kanka Mana…” Ido duk suka zaro shiko ko a jikinshi tsakanin gaskiya da gaskiya yake maganar cikin kunar zuciya.

 

Aiko Basu Kama tunanin ba gimbiya halila ta bayyana tare da Maheerah Amma wannan bayyanar da tayi fuskarta ba alamun rahama sai dai kallo d’aya abbe da Jalaludeen suka Mata suka gano ko wacece basu ce musu komai ba ila cewa da tayi Maheerrrrr ta fad’a cikin hasala…jiyowa majinnan yayi Yana kallonta kamun tacigabada fad’in kabayyana wamijin uwar gijiyarka domin yadena d’aga Mana murya anan domin ba,anshi kana ka danka mashi matarshi domin awannan lokacin shine kawar garkuwanta..shiru tayi nad’an wani lokacin kafintazo gun abbe tace Habibullah kayi hak’uri yazama wajibi zaraah tashiga wannan gidan kodan ceton rayuwar wadda ke ciki Amma hakan baze samuba seda gadin mujinta ahalinzu wannan dasuka hanata shiga bazasu tab’a Bari tashigaba ta azziki abunda maheerah tagaya muku hakanne dolene sekun keb’e kanku mu Halli d’aya na Yan wasu mintuna tahakanne kawai zamu samu damar Baku kariya.

 

Ayanzu Kuma dolene Alyasat ya kaɗaice da matarsa domin sai sunzama Abu d’aya zamu samu damar karya wannan mummunan sihirin Ina fatar kagane.

 

 

“”Nagane gimbiya kumana fahimta insha Allah za,ayadda kikace…”Wai miyake faruwa ne mikuke Shirin cewane suwaye wan..ya,Isa yusif ku,ajiye tambayoyinku zuwa wani Dan lokaci zaku samu dukkanin amsoshinsu… abud’e part d’in habibbty duk kowayashiga cikin…cikin sauri bibibo da kansa yakomana mutane yace Banda wannan kunemi wani…to shikenan kuyu part d’in dady suka fad’a a tare kana bibibo yayi wani girgiza segaya yadawo sak mutin Amma fa fuskarshi kamar besan minene dariyaba rik’e yake da hannun mama har K’arasa wurin alyasat kana yarik’o nashi hannnun yasa nata..

 

D’agowa sukayi atare suna kallon juna sabida wani mugun shock dasukaji lokaci d’aya tareda bugawar zuciya…kallan abbe alyasat yayi da,alamar mi hakan kenufi…girgiza Kai kawai abbe yayi alamar karyayi magana…shiyasa yayi shiru kowa awurin yanufi pert d’in dady seda sukayi nisa kana gimbiya halila tace habibullah…abbe yajiyo tace karka manta Muna buk’atar su Nan da lokaci kalilan alyasat da zaraah abunda zasuyi dolene sesun kasance Abu d’aya Kar su B’ata Mana aiki Dan Allah….insha Allah gimbiya za,ayi yadda kikace…shikenan kuyu sauru kuje tafad’a tareda juyawa suma duka suka K’arasa pert d’in na dady seda zasu shiga k’ofar perlon kana suka jiyo saboda Jin wata muguwar gumza da,akayi kamar stet d’in zata tsage wayam sukagani ba kowa dukkansu basuga su gimbiya ba kamun sugama tinanin Ina sukaje suka jiyo ana fad’ar kushiga manaaaaa…aicikin sauri suka fad’a pert d’in kowanne da addu,ar dake fita bakinshi…!

 

 

 

 

*SOLDIERS FAMILY* na kud’i ne nera 500₦ kacal 👌 ga duk me buk’atar complete kuma 700₦ ne Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub’ar wannan number 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number 👉 08107819124

 

 

 

 

 

Autar Alheri ✍️

 

*S F*

 

No comments