Breaking News

Soldiers Family 29-30

Page 29&30

 

__”tana fad’ar appey appey Imran na shiga ukku Ina appey d’inku yake? me ya sameshi?sekawai ta fashe da kuka!

 


Dukkansu y’ay’an Bata mik’ewa sukayi suma suna fad’ar innalillahi-wa-inna-ilaihi-raju’un to Miyake Shirin faruwa da sune? Ina mahaifin nasu? Sun dai san Yana raye bai rasu ba amma sun wofantar da lamarinshi hasalima sunmanta dashi gabaki d’aya arayuwarsu Kuma dukkansu ba wanda ya tab’a tunanin Ina mahaifin nasu ya shiga.

 

Allah humma ajirni fimuseebati wa,ahaleeqni khairan minhaa..shine kawai abunda suke nanatawa abakinsu..anrasa Wandama zai tunkari habibbty balle ya rarrasheta itako sai kuka takeyi domin ita kanta ta manta da mijin bata tsawon shekaru bama zata iya cewa ga iya marabarta dashi ba wannan wacce irin masiface…cikin k’arfin hali Lateep ya,Isa gunta yace””habibbty kiyi hak’uri zamu bincika duk inda appey yake afad’in duniya indai yana raye zamu kawoshi gareki Dan Allah kidena kuka komai tsanani yana tare da sauk’i Allah yakawo mana d’auki Dan Alfarman sayidina rasulillah (s.a.w) da Ameen suka amsa dukkansu domin Babu magwarinyin wani motsin sai dai sunsan tabbas akwai lauje cikin nad’i acikin wannan Al,amarin ruwa baya tsami banza tabbas akwai wata ak’asa duba da yadda Habibullah ya b’ata lokaci d’aya akazo ma,Isha Takoma kamar gawa kamin wannan lokacin Kuma duk Babu appey kana dukkansu ita da yaranta da jikokinta sun manta dashi acikin babin rayuwarsu.. k’wallar idonta ta share tana me rokon Allah yakawo musu d’auki acikin wannan mird’ad’d’in k’ullin..

 

 

Acan part d’in habibbty kuwa maheerah ce tayi kansu da sauri shigowarta kenan taga sunzube awurin””kiransu tafarayi tana girgizasu Amma ba Wanda ya motsa daga Alyasat har mama cikin sauri ta mik’e tana Kama gimbiya Halila ta mik’e tsaye daƙyar kana tadubi maheer dariko wannan abun dake cikin show glass d’in Yana k’ok’arin bud’eshi””kitemaka masa maheerah kufitar dasu daga wurinnan kucece rayuwarsu shine kawai abunda gimbiya Halila ke fad’a cikin galabaita domin itama ta raunata…Aiko dasauri tad’auki Alyasat da mama duka tab’ace dasu daga wurin kamun tadawo Maheer ya gama bud’e abunda ke rufe abun mmki wani kyakkyawan tsohone duka sumar jikinshi tayi farin ko,Ina na jikinshi se karkarwa yakeyj kamar mejin sanyi..ahakan maheer ta d’aukeshi shima kana gimbiya Halila tabar wurin bayan sun kaisu wani bedroom sun kwantar da sune sukabi bayan yayarsu sai da suka Rakata har cikin masarautarsu ta shiga turakarta kana suka dawo dan temakonsu Alyasat.

 

Sunjima sosai akansu kamun susamu sudawo hayyacinsu sedai sulula dogon bacci

 

hakanma wannan tsohon ya dena karkarwa da yakeyi sosai shima baccin wahala yayi awun gaba dasu..sai a lokacin suka sauke numfashi kana suka fito perlon inda su abbe…duka kowa juyawa yayi ana kallansu Dan basu ga lokacin da suka shigoba har suka shiga cikin bedroom fitowarsu yanzu kawai suka gani…suko duk da cewa sunsan kallon da suke masu hakan besa suka basu damar yin wata magana ba.

 

“Kuzo muje kuga Amma karkuyi hayaniya kawai munaso ku ganine da idonku sannan muyimaku bayani munaso mutafi domin yayarmu ma taraunata tana da buk’atar taimakon mu atare da ita…Ido Jalaludeen da abbe suka zaro dumin sunsan gimbiya halila suke nufi….sedai kamun suyi magana maheerah tece karku damu tinda munyi nasara akan abunda mukeso ai ba wani abunda zaifaru insha Allah saboda hakan kuzo kawai tak’arasa zancen tana juyawa.

 

Dukkansu bayanta sukabi har bedroom d’inda suka kwantardasu Alyasat da mama akan bed d’aya wannan tsohon Kuma akan doguwar kujera…duk Wanda yashiga yagani seya firgita musamman appey ganinsu hakan sedai badamar magana doli ahakan zaka fito kabawa wani wuri shima yashigo….ahakan akayi sai da kowa yagama shigowa kab kana suka koma perlon da tambayoyi fal a zukatansu.

 

Sai da kowa ya samu wuri ya zauna kana Maheer ya fara magana kamar haka, “da fari dai nasan dukkanku nan baku san mu ba to ba muda lokacin yi muku bayani akan mu suwaye? sai dai nasan kunsan cewa mu ba mutane bane kamarku Kuma bamad a nufin cutarwa agareku. shiru ya ɗanyi Yana kallon maheerah kamun ya cigaba da fad’in akwai abunda kefaruwa acikin ahalinku sai dai ba musan daga Ina abun ke zuwa ba abunda mukasani shine koma waye kebibiyarku ya bada matuk’ar ahad’ari saboda iya abunda yafaru a yanzu ya,isa yanuna hakan..Nan ya shiga basu labarin duk abunda ya faru tun daga shigowarsu stet d’in har hanawa mama shiga part ɗin ammy da masu tsaron wurin sukayi har kawo yanzuda suka fito da appey.

 

Kowa awurin ya shiga tashin hankali in banda tasbihi ga ubangiji Babu abunda mutanen wurin keyi gabaki d’aya sunshiga tashin hankali.

 

Ganin hakan yasa maheerah fad’ar karku tana da hankalinku insha Allah Babu abunda zaifaru muddin muna Raye bazamu Bari ahalin zaraah su to zartaba domin yanzu kunzamo ahali agareta….wannan tsohon Idan ya farka na,ajiye ruwan addu,a daza,abashi yasha saboda shekaru dayayi amatsayin sak’aho kamar Wanda baya duniya Kuma manta daku shine akayi ta yadda bazaku tab’a tunawa da shiba balle kuyi yunk’urin nemansa.

 

 

Alyasat da zaraah dolene su zauna acikin inuwa d’aya domin da temakon auren da ketsakanin sune muka karya wannan tsafin domin muddin suna tare baza,ataba cin galaba akansuba nasan yanzu mama zasu Hara itada mujinta sabida sune suka karya alkadarinsu Amma muddin suna tare hakan bazebasu nasara akansuba sabida hakan kukiyaye kurika addu,a danneman tsari agun Allah..suna gama fad’ar hakan du suka bace batt domin zancenne kawai sukeyi hankalinsu nakan yayarsu.

 

Shiru perlon yad’auka kamar ruwa ya cisu ko wada abunda ke ranshi sunrasa mai zasuyi farin ciki ko akasin hakan..sunjima awurin ba tare da kowa ya tab’ukawa kansa komaiba seda akayi Kiran sallar magarib kana duk mazan suka fita masallacin sake cikin stet d’in yayinda matan sukayi sallarsu anan cikin perlon

 

Mazan Basu dawo gidanba har akayi Isha,I seda sukayi sallar kana suka shigo Kuma har wannan lokacin su mama basu farka ba…ahakan suke zaune anan perlon har 10:00pm kana abbe da Abba suka nufi bedroom d’inda suke ciki…sukayi sa,a kuwa tashin Alyasat kenan Wanda mitsinshi ya tada mama sannu suka musu kana sukace sutashi suyi sallah

 

Seda sukayi sallar suka gama zasu fita kenan appey ya farka cikin sauri suka K’arasa gunshi suna mishi sannu…amsawa yayi Yana tambayar lafiya  me sukeyi anan? Domin Shi gani yakeyi kamar baccine yayi ya farka… murmushi kawai sukayi tare da cemai ba komai Sam basu nunamai akwai wani abunba…ahakan suka rankaya zuwa perlon kowa yaji dad’in ganin sutashi cikin koshin lpyr su sedai bawanda ya nuna alamar komai sema cewa da Abba yayi kowa yajeya kwanta dasafe akwai meeting insha Allah zasu K’arasa Wanda sukeyi abbe yadawo kana zasuso suji yadda mama takasance matar alyasat…da hakan kowa yanufi part d’inshi inda mama abbe Alyasat Yusuf Lateep Alhassan da alhusain da ammy suka nufi pert d’in ammy…suko appey da habibbty se su sulaiman da najeeb Fahad suka nufi pert d’in habibbty kowada burin yaga wayewar garin gobe domin Jin abunda yashige musu duhu…!

 

Nima dai sai goben nan domin alkalamina yace atsaya yahuta gobe naji yadda wannan abun ya kasance☺️

 

 

 

 

*SOLDIERS FAMILY* na kud’i ne nera 500₦ kacal 👌 ga duk me buk’atar complete kuma 700₦ ne Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub’ar wannan number 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number 👉 08107819124

 

 

 

 

 

Autar Alheri ✍️

 

 

*S F*

No comments