Breaking News

Soldiers Family 37-38

Page 37&38

 

__””yace Kai miya hargitsama Kaya hakan kamar Wanda akayi yak’i akansa? Ko


kallanshi Alyasat beyiba yarab’a tagefe yabar perlon.. dariya sukayi atare lateep nafad’ar kaga Dan,iska daga shiga bedroom harya kwaso dad’i Kai doline gaskiya muma mushiga dagaciki ko Adena Mana kwalele…dariya yusif yak’arayi yace tofa 🤔 harkadamu kenan? “Eh mana ai doline indamu kodan wannan Dan iskan yazo yawani shanyamu anan kamar bajiranshi mukeba duk kiranda kayimishi awaya bawanda yad’aga seyanzu zewani fito ayamutse..”Kai bro wlh akwaikada fitina wayagayama wani abunne yasakashi hargitsewa kafasan waye alyasat Wanda ko kallo mace Bata isheshiba shine zakayi wannan tinanin akanshi sedai wani abun Daban sabida ko abunda yayi awancan ranar ai abbe ne yasakashi..yusif yafad’a Yana dariya..bud’ar bakin lateep secewa yayi eh hakane tabbas tinda shid’in dutsene ba yadda za,ayakula mace..kamun yusif yayi magana alyasat yadawo perlon dawasu kayan domin harya canja hanyar bedroom d’in yanufa duk suka bishida kallo Yana zuwa yasamu mom na d’akin tana fitar matada Kaya..muje yafad’a adak’ile

 

Basusanda zuwanshiba kawai muryarshi sukaji..jeki abunka baranakaita cewar mom…D’an B’ata Rai yayi kamun yace mom tafiyafa zanyi natsa harnakaita kufito muje tare Mana…aa base anje asibitiba zata samu lpy insha Alla…bebari tak’arasa ba yace mom karyazan taraunatafa awurin yafad’a Yana Dan waro idonshi sam Shi badawata manufar yayi zancenba Kuma beyi tinanin yayi rashin kunyaba…itako mom cewa tayi tofa 🤔 gayamun kajimata ciwo son yoshe kazama Marar kunya? Tafad’a tana kafeshida Ido

 

Shisema yanzu yaji kunyar abunda yafad’a cikin sauri yabar d’akin Yana fitowa perlon yace muje..da kallo duk suka rakashi bayan yafita lateep yace D’an renin hankali kana sukabi bayanshi a perkin space suka sameshi Yana waya suna zuwa aka bud’e musu motocinsu sukabar gidan.

 

 

*Gimbiya halila*

 

 

Tindasu maheer sukabar stet d’innan suka koma gunta temako sosai suka duk’ufa bawa Y’ar uwarsu domin tajigata sosai Amma cikin ikon Allah da buwayarsa tasamu lpy a Yan kwanakinnan..Kuma duk wannan abun dake faruwa mahaifinsu besaniba Kuma basuda niyyar gaya masa..yanzu alhmdllh takoma kamar bawani abun da yasameta hakan bakaramin kwantarwada Y’an uwanta hankali yayiba.

 

 

Abbe ne zaune shida ammy suna firar yoshe gamo lbr yake Bata sosai akan mama domin yanzu beda firarda tawuce tata  Allah yasaka mishi k’aunar yarinyar sosai

 

Alhassan ne yashigo da sallama d’auke abakinshi yak’arasa cikin perlon Yana gaisarda iyayenshi cikin farin ciki domin yanzu har d’auki yakeyi yashigo yasanesu hakan…suma cikin farin ciki suka amsa kana ammy tace alhassan kakira Yan uwanka muje pert d’in habibbty kosunje?

 

“Aa ammy nade baro zasuje…to shikenan badamuwa yau Idan anfito masallaci inaso kayanka Mana ticket zamuje India zuwa jibi insha Allah…to shikenan Allah yakaimu ammy.. ameen ta amsa kana alhassan yafita…dubanta abbe yayi yace kinaga yanzu bawata matsalar Idan mukaje nifa banasan ciwonnan dakikeyi aduk lokacinda mukaje India…. murmushi tayi kamun tace insha Allah bakomai karka damu kaga munjima bamujeba..to shikenan Allah yakaimu…ameen ta,amsa.

 

 

Acan pert d’in habibbty kuwa cike yake tab kamar yadda suka Saba akowacce Friday..Mom ce tayi shigowar karshe itada mama suka shigo suna firarsu Dan tuni mama tawarke sabida kyakkyawar kulawarda take samu agun hajiya suhaima….sallama sukayi suka shigo perlon inda yaran sukayi chaaa suna gaisarda mom d’in tasu seda duk suka gaisa Kana itama taje gun appey da habibbty tagaidasu..itako mama gun abbe taje dasauri tana fad’ar abbana I miss you domin ita Sam Bata kallonshi amatsayin suriki sabida sabonda tayidashi…shima murmushi dayakeyine ya fad’ad’a yace Miss you too my angel kintashi lpy? Ashagwabe tace lpy qalau abbana..kana takalli ammy tace momma inakwana…lpy qalau zaraah kintashi lpy? Lpy qalau tafad’a kanta ak’asa kamun tad’ago tana k’arewa mutanen perlon kallo dasukayi tsit Suna sauraron sweet voice d’inta..can ta hango Wanda take nema suna had’a Ido yasakar Mata murmushi,,,itama maida Masa tayi kana tace yayana inakwana tafad’a yadda zeji…cikin far,a jalaludeen yace lpy qalau k’anwata y kikaji Kasar tamu da dad’i? D’an murmushi tayi kamun tace eh Yaya..to masha Allah taso kiga yafad’a shima Yana mik’ewa

 

Ba musuko tataso biyoni yace yanayi gaba…gun habibbty yace da,ita yace wannan granny d’inmu ce Muna kiranta habibbty wannan Kuma tsohon mijintane Amma yanzu nine angon shiko Muna kiranshi appey….dariya kowa dake wurin yayi hadda tsofaffin..kana appey yace aibakomai nabar maka domin nima nasamu sabuwar mata..mudai bamu gantaba cewar najeeb..ahankali mama tagaidasu kanta ak’asa..cikin barkwanci appey yace yawwa amaryata k’araso Nan yanzu ai gata kunganiko yafad’a Yana kallon najeeb din..Aiko duk aka sake saka dariya inda Al,Hussain yace tab aikwa akwai aiki jaa agabanka Idan zaka iya yiwa alyasat kwace..to wannan dai tawace sedai yanemi wata.. dukkansu dariya sukayi kana jalaludeen yajata zuwa gun abba yanuna matashi tareda gaya nata yadda suke kiranshi..tagaidashi

 

Hakan yakaita gun kowa iyayen nasu da k’annen  tareda gaya Mata sunansu dakuma matsayinsa agunsu daga karshe yakuma gunsu abbe kana yace wannan da abbe muke kiranshi please kidaure kema kirik’a fad’ar hakan Kar wata Rana kisakamu rud’ani kice Abba mud’auka abban kike nufi please wannan Kuma ammy muke kiranta kinji k’anwata…murmushi tayi kamun tace shikenan yayana insha Allah zanyi hakan..yawwa Lovely sis zo kuzauna ga antynki muhibbat wannan Kuma nusaiba..murmushi kawai tayi tazauna yayinda najeeb da Fahad suka bitada mayen kallo…sulaiman dai tuni yamaida kwadayinshi tinda yaji matar kanenshi ce Kuma gashi an aura Masa wadda yakeso muhibbat.

 

 

Ahakan aka fara zubawa kowa abunci inda nusaiba se janta takeyi da fira domin mama na burgeta sosai..muhibbat kuwa se tsaki takeyi tana hararar mama ahakan har akagama cinbabunci aka kwashe kayanda aka b’ata kana kowa yakoma yazauna kamun suheil yatashi yajona computer dasuke ganawada Y’an uwansu duk Friday d’in

 

 

Vedio call yashiga tareda Kira Zaid aka fara Kira domin shima yakoma gun aikinshi bugu d’aya yad’aga cikin rashin walwalarshe yashiga gaisarda mutanen perlon shima k’annenshi suka gaidashi daganan aka Kira yusif dagashi Kuma se lateep hakan sukayita barkwanci da lateep kamun akashe aka Kira alyasat seda takusa tsikewa yad’aga dafadin assalamualaikum…ai dasauri mama ta d’ago tana duban computer domin tin ranarda sukazo pert d’in mom yayimata wannan abun Basu Kara had’uwa ba ko awaya.

 

Amsawa Abba yayi kana akashiga gaisawa dashi kamun sutambayeshi aikinshi duk ya,amsa musu kallon gefen abbe yayi Aiko idonshi suka sark’e cikin nata atare zukatansu suka buga Kuma kowa yakasa janye idonshi daga kallon Dan uwanshi kowanne da abunda yake kallo a idon d’ayan wasu irin abubuwane kefita daga idon kowannesu suna aikawa juna kallon so da k’aunar juna Wanda dukkansu Basu fahimci hakanba…magana dady ketayiwa alyasat Amma Sam bejishiba yanacan yalula duniyar love

 

Kallon juna akayi tsakanin sadam da suhaif sekawai suka saki murmushi najeeb kuwa kamar yakurma ihu tsabar aushi hakama muhibbat datakeji kamar takashe mama…ganin kallon yaki k’arewane yasa jalaludeen cewa””bro wannan kallo haka please karka cinyemun k’anwa.. dukkansu suka saka dariya..se alokacin alyasat yafargada abunda yayi cikin sauri yakashe wayar..aikuwa suka sake kecewada dariya…cikin bak’in ciki darashin kunya muhibbat tace karya ciyeta kokarta cinyeshi wannan masifar dame tayi Kama yarinya Ido abud’e bakunya balle tsoron Allah ranarma hakan kikayi sex dashi acikin mutane ko kunya sabida tsabar karuwanci yanzu Kuma kinzo kina wani tsareshida Ido aikin banza karuwa gayyar aljan…tass tass tasss saukar marukan dataji har ukku alokaci d’aya yasata hadiye sauran maganarta..kowa dake wurin kallon mama suke wadda basusan lokacinda ta,Isa gaban muhibbat ba Amma dukkansu sunji abunda muhibbat kefad’a Kuma gabaki d’aya samarin jiran sukeyi takai karshe kowa da abunda yake Shirin yimata sekawai sukaji saukar wannan marukan.

 

 

Cikin fishida tafasar zuciya mama tanunatada yatsa tace “”bara kiji ingaya Miki bariganin Ina cikin gidanku bagata narasaba balle kitozartani dakike zancen rashin kunya Kuma kece marar kunya baniba domin kominayiwa yayanki mijinane Kuma halalina bawai acikin mutaneba ko,agaban waye yazomun zankarb’eshi hannun buyu tareda bashi abunda yake muradi ataredani kallo Kuma dakike magana nakai yakallenine shiyasa yake kallona idonki Basu nunamiki dedeba domin shine yake kallona Niko nayi accept d’inshi ne kisani macenda ta,Isa takai ita namuji ke kalla Koda saurayine kuwa balle mujin aure asheko Kinga na d’aga tuta tinda har yakalleni batareda lurada cewa bani kad’ai bace awurin..sekuma abuna karshe tafad’a tanadan zagayawa tadawo dabanta sosai suna kallon juna Ido cikin Ido kana tace

 

“”Zancen aljanu danaji abakinki narantseda izmul,a,azamu narantseda sarkinda kebusa numfashi nakarajin kalimar zancensu bibibona abakinki Sena gutsure Miki harshe..!

 

 

 

 

*SOLDIERS FAMILY* na kud’i ne nera 500 kacal 👌 ga duk me buk’atar complete kuma 700 ne Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub’ar wannan nomber 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan nomber 👉 08107819124

 

 

 

 

 

 

 

Autar alheri ✍️

 

 

*S F*

 

No comments