Breaking News

Bamagujiya 6

Page 6*

★★★~~~★★★~~~★★★

Tashi yayi daga tsugunnon da yayi yana sauke wata ajiyar zuciya me ƙarfi ya juya ya nufi hanyar da zata sadashi da masaukinsu, Saida yayi nisa sannan ya juyo yaga ta miƙe tsaye tana me binsa da kallo,



Juyowa yayi ya dawo ya tsaya a gabanta ya zubanta idanu tare da numfasawa ya kira sunanta da wata irin murya da tasa Æ™irjinta bugawa da Æ™arfi ta É—ago idanunta da suke tsiyayar da hawaye yasa hannu ya kama fuskarta yana goge mata idanun ya buÉ—e bakinsa da yayi masa nauyi yace “zaki auren…..” Janyewa tayi dukan Æ™irjinta na Æ™aruwa tace “Aure….” Matsowa yayi gabanta ya damÆ™i hannunta yace “Yeah Beebah Aure zaki aureni koda danginki duka basu amince ba koda nima nawa bazasu amince ba kiji a ranki ke matata ce soon”
Sakin hannun nata yayi ya juya da sauri yabarta da sakakkiyar gwiwa data kasa turata ta kaita ko ƙofar gdansu saima guri data samu ta zauna ta zabga uban tagumi hannu biyu tanaci gaba da sharar hawayenta.

 

Ji tayi an daka mata tsawa ta zabura ta miÆ™e da sauri jikinta ya dauki rawa ganin Baba Uda tsaye a kanta taja baya da sauri ya kuwa tusota yana surfa mata ashar yana cewa “wato ke kunnen Æ™ashi ke gareki bakijin mgn ko to muje gdan uban naki naji daga inda kika samu É—aurin gindin kula wannan É—an iskan yaron me siffar munafukai”
Da gudu ta shiga gdan kamar an jefota Jumme da Jimo dukkansu suka miÆ™e ganin Baba Uda yasa Jumme shigewa É—aki yaci gaba da sababinsa yanata kundume² ashariya.

 

Cikin girmamawa Jima ya É—ago ya dubesa yace “Nifa yaya ban fahimci abinda kake nufi ba” “Eh ai dama bazaka gane ba nasani bazaka gane ba Jimo ka saki yarinyar nan sasakai abinda taga dama shine takeyi kaÆ™i matsa mata ta fitar da miji bare batun aure yanzu gashi garin sakacinka taje ta janyo mana abinda zai kashem” da bayannaniyar rashin fahimta Jimo yace “menene Yaya ka sanar dani” numfasawa yayi yace “wai har gida akaje akace min yarinyar nan Bibo anganta ita da É—aya cikin bakin nan da dagaci yasa akayi shelar zuwansu Æ™auyen nan haÆ™ar ma’adanai….”
Tafa hannuwa Baba Jimo ya shigayi yana girgiza kai kawai sai yayi wuf ya cafko Habibah ya rufe ta da duka ta saki ihun daya janyo hankalin mutanen da suke wuccewa gidan ya cika da mutane daÆ™yar aka kwaceta hannun Baba Jimo yana haki yace “Ni zaki tozarta Habibatu kwana huÉ—un can nayi Miki kashedi akan wannan yaron da labari yazo min yana binki gona shine ya sake canza salon yaudararsa to na rantse da abar dogaro kasheki zanyi Habibah yankaki zanyi da wuÆ™a na jefaki a rijiyar jeji domin bazaki zamemin haihuwar asara ba….”

 

Kuka takeyi tana matsawa daga inda take tsaye tana shirin fita Baba Uda ya cafko ta ta rushe da kuka tace “kada ku kasheni bansan meye yasa bana iya bijire masa ba yana kalaminsa da hankali kalaminsa na nutsuwa ne komansa a nutse yake bashi da hayaniya ku fahimceshi da gaske ba irin Jami….” Zubewa tayi Æ™asa hancinta da bakinta suna zubar da jini tsallaketa sukayi suka bar gurin dukkansu da bayyananniyar damuwa a fuskarsu kai tsaye gdan dagaci suka nufa idan ka gansu zaka zata korarru ne.
A Æ™ofar gida sukaga dagaci tare da baÆ™i suka tsaya a nesa dashi suna tattaunawa bayan dagaci ya gama sallamar baÆ™insa ya Æ™arasa garesu suka gaisa yayi musu iso zuwa fadarsa ya dubesu yace “yanayi ya nuna kuna cikin damuwa meye yake tafe daku?”
Numfasawa Uda yayi yace “damuwa babba ma kuwa ranka shi daÉ—e wato tun farko Saida mukace bamasan sauke baÆ™i a garin nan aka nuna mana bamu isa ba saboda baku abin yake shafa ba yanzu ga abinda hakan yake neman haifar wa wani a cikinsu yana neman lalata mana tarbiyyar Æ´ar wajen É—an’uwana Bibo nasan dai kasan Bibo….”

 

Nan suka kwashe duk abinda aka faÉ—a musu Æ™arya da gaskiya suka zayyane masa ya jinjina abin yayi shiru yana tunanin mafita can ya É—ago ya dubesu yace “yanzu dai zamu kira yaron gobe da safe jimo Uda kuje gda zamu nemeku”
Miƙewa sukayi sukayi bankwana suka tafi ranar kwana sukayi suna saƙa irin matakin da zasu ɗauka akan Habeeb.
Kwana tayi jikinta yana ciwo tana kuka Jumme nayi mata faÉ—an dalilin da yasa bataji kashedin da iyayen nata sukayi mata ba, cikin kukan tace “Nifa bani nace yazo ba kuma bani nake kulashi ba shine yake kulani sannan Jumme kece kike cemin babu kyau wulakanta mutum bare sh…..” Katseta tayi da cewa “naji banason ji nidai na faÉ—a Miki indai kinason naci gaba da sanya Miki albarka to ki fita daga harkar wannan É—an birni ba sonki yakeba cutar ki zaiyi ina me tabbatar Miki duk dariyar da É—an birni zaiyiwa na Æ™auye cutarsa zaiyi saboda haka ki kula da kanki”

 

******

Washegari da safe a fada Baba Uda ya miÆ™e ya zabgawa Habeeb Mari Najeeb ya miÆ™e da sauri yayo kansa Habeeb ya riÆ™e shi da sauri, nunashi Baba Uda yayi yace “Ƙarya kakeyi yaro baka isaba kayi kaÉ—an ka koma gurin munafukan da suka turoka ka faÉ—a musu kaidai baka isa mu baka aure ba kai bakai ba wani ma da yafika kama da galihu muddin daga birni ya fito bai isa mu É—auki jininmu mu bashi ba haba! haba!! Yaro aikai tawayar ma tayi maka yawa gaka musulmi kuma a zuri’ar mu kaje ka nema dai a wani gurin Habeeba tafi Æ™arfinka”
ÆŠagowa Habeeb yayi ya dubi Uda yace “kayi hÆ™r Baba bani na jarabci kaina da son Beebah ba Allah ne ya jarabceni inasonta kuma itama alama ta nuna ta karÉ“eni duk abinda kuke tunani bazaku sameshi daga gareni ba”
Dariya Uda yayi yace “Æ™aryar banza to bazamu bayar ba son ya kasheka in yana kisa mune sai muka haifi Habeeba munce bazamu bayar ba”

 

Miƙewa sukayi suka fice daga fadar suna ƙunkuni suna Harbin iska suna zuwa gdan kuwa suka gindaya mata sharruɗa tare da sanya mata sarka a ƙafarta gabadaya sun haramta mata fita daga gda hakan bai wani dameta ba tayi jinyar jikinta kwana biyu ta warke kullum saidai su Kande suzo su bata lbrn abinda ya faru a dandali da kuma halin da Habeeb yake ciki na irin damuwar da yayi da rashinta saidai tayi murmushi kawai ta share don tasan ajalinta ne kawai zaisa tayi karambanin fita daga wannan gida.
Kullum sai Habeeb yazo Æ™ofar gidansu Bibo haka Baba Uda da Baba Jimo zasuyi masa korar kare gashi da baÆ™in naci yaÆ™i hÆ™r haka yayita zarya tsakanin masaukinsu da gdansu amma ganinta yafi Æ™arfinsa saidai ya gaji da aikensa da magiyarsa ya hÆ™r ya koma ya zama kamar wani zautacce cikin abinda bai rufa wata guda ba Æ´a macen da yake É—auka ba’a bakin komai ba macen da abaya yake ganin bazai iya sanyata cikin rayuwarsa ba sai gashi cikin lkcn da bai shirya ba bai tsammata ba ta faÉ—o rayuwarsa tana sauya masa taswirar rayuwa.

 

Sosai Najeeb ya mayar dashi mahaukaci baya bawa duk wani abu daya shafi Habeeba muhimmanci ko zama sukayi suna tattaunawa abinka da abinda ya damu ruhin mutum indai Habeeb zai sako shafin Beebah cikin hirar to zata ƙare domin Najeeb zai kama faɗar maganganun da in yayi wasa ranar ko ɗaki ɗaya bazasu kwana da Habeeb ba wannan tasa suka raba tsaki da Najeeb mgn ma sai ta zama dole Habeeb ke tsayawa suyi da Najeeb haka dai lkc yayita tafiya duk wata hanya da yake ganin zata zame masa me sauƙi wajen haɗuwa da Habeeba ya rasa dole yaja ya dangana da gdan hakimi da rasa masa kuka yana roƙonsa ko nawa sukeso kome sukeso matsayin sadakin Habeeba a sanar dashi zai bayar kuma yayi alƙawarin matukar ba ita taso musulunci ba bazai rabata da addininta ba.
A zahiri Mati Dagaci yaji matukar tausayin Habeeb musamman dake yana yawan kawo masa gaisuwa yasanshi yana lura da yanda ya susuce ko aikin daya kawo shi garin ya dainayi shikenan daga ka sameshi a bakin kogi ya zubawa ruwa idanu saidai ace anganshi a jeji a zaune ko kuma yana gda yana karanta wasiƙar jaki.
ÆŠagowa Mati Dagaci yayi yace “Yaro hakikanin gaskiya duk da bambanci addini naji tausayinka matuÆ™a domin so mugun ciwo ne da bashida magani sai saidai samun abinda zuciya ta kwaÉ—aitu dashi Habibu banida maganin matsalarka na rantse da Allanku da Bibo Æ´ata ce nice na haife ta a yau bazaka bar gurin nan ba saina bawa Limamin Hayin Fulani damar É—aura muku aure bisa tsarin addininku amma kash banida wannan damar”
Numfasawa Dagaci Mati yayi ya sake duban Habeeb da idanunsa suka rine suka koma jajaye yace “duk da haka bazan kashe maka gwiwa ba kaje kaci gaba da addu’ar kasa malaman addininku su tayaka Habeebu inda rai da rabo”

 

MiÆ™ewa yayi cikin mutuwar jiki yace “Shikenan Baba Dagaci na gde amma bazan iya ci gaba da zama a garin nan ba zan koma Garinmu saidai inason kafin na tafi kayimin alfarma É—aya” da sigar tausayi Dagaci yace “Wacce iri ce Habeebu” sunkuyar da kansa yayi yace “Ka aika a kira Habeebah nasan idan Baba Jimo yaji kiran nakane zai barta ta fito inason magana da ita kalma É—aya tak nakeson ji daga gareta wlh indai har Habeebah tace bata sona zan hÆ™r da ita domin nasan Æ™addarar sai soyayyarta ta wahalar dani ce tasa na zaÉ“i wannan garin matsayin inda zanzo idan kuwa ta amsa min tanasona to ko duk dangina da nata zasu Æ™are saina mallaketa domin itaÉ—in mahaÉ—in raina ce”
Shiru Dagaci yayi yana jinjina kalaman can ya É—ago yace “shikenan Sarkin zagi tashi kaje ka sanar munason ganin Bibo yanzu a gabanmu” babu É“ata lkc sai gata tun daga nesa ya kafeta da manyan idanunsa da suka rine da damuwa itama shi take kallo ganin ya zabura ya miÆ™e yasata tsayawa a inda take jikinta ya É—auki É“ari saboda tuna mugun kashedin da Baba Uda yayi mata.
Ji takeyi kamar ta juya amma batada ƙarfin gwiwar hakan domin Zuciyarta tana kwaɗayin ganin ɗan birni ko ba komai tasan zata samu sauƙin abinda take ji a ƙasan ruhinta.
Takowa yayi gabanta ya tsaya ta gyara tsayuwarta cikin dakiyar zuciya ta dubesa kafin yayi mgn ta rigashi da cewa “Dan birni meye ya sameka ka rame kamar kayi jinya?” Tana mgnr tanakai hannunta fuskarsa ta shafa Æ™asumbarsa da ta kwana biyu bai gyarata ba hakan yasashi lumshe idanunsa ya kamo hannun nata yayi kissing nasa yace “Ha… Habee..bah kina iya rayuwa me daÉ—i batare da kinsan halin da nake ciki ba?” Da rashin fahimta ta dubesa zatayi mgn ya É—ora yatsansa a saman bakinta yace zo muje inason tambayarki ne a gaban Dagaci duk amsar da kika bani ita ce zatayi aiki wajen sama mana mafita Ni dake baki É—aya”

 

Kama hannunta yayi suka isa gaban Dagaci suka zauna Dagaci ya dubeta yace “Habeebah kwana biyu kin É“uya É—an goron ma da ake siyowa a kawomin na toshi an daina kodai an daina auren dani ne?” Murmushi tayi tayi Æ™asa da kanta tace “Aa su Baba ne suka tsareni suka hanani fit….” Girgiza kai yayi yace “to ai shikenan dama Habeebu ne yakeson ganinki zai koma garinsu yanaso kuyi sallama” É—agowa tayi tace “Habeeb!”
ÆŠagowa yayi tare da jinjina mata kai yace “Sunanan kenan Habeeba don Allah ki nutsu ki bani amsa É—aya tak ita kaÉ—ai nake buÆ™ata daga gareki kada ki cutar da kanki ki faÉ—a min iyakar gskyr abinda ke ranki game dani Habeebah kinaso na?”

 

ÆŠagowa tayi da sauri ta kalleshi shima itan yake kallo cikin tsoro ta kawar dakai gabanta na faduwa ta miÆ™e ya riÆ™e Rigarta ta baya yace “Wlh bazaki bar gurin nan ba saikin amsa min tambayar nan don itace hadafin mafita ta Habibah kalma É—aya ce eh ko a’a zata cireni a zullumi sannan zata Æ™arfafamin gwiwa Please ki faÉ—amin matsayin da kika ajeni kinasona zaki aureni ko baki sona?” Ido ta zubawa Baba Uda sake shigowa zauren majalisar dagacin shima ya kafeta da idanu yana nufosu tana Æ™oÆ™arin ture Habeeb ta kasa saima riÆ™on tsauri daya Æ™ara yima damtsanta wata Æ™ara kakeji kau… Kau… Abinda yasata saurin sauke idanunta kan babanta Jimo dake tsaye da wani yaro Lanti ya zare wuÆ™a yayi kan Habeeb Najeeb ya taso da gudu ya nufosu ya riÆ™e wuÆ™ar ta yanke shi hakan yasa ya saki ya sake nufar Bibo da Habeeb ya É—aga wuÆ™ar zai cakawa Habeeb Bibo tayi hanzarin tureshi wuÆ™ar ta soke ta a gefen cikinta take ta saki wata Æ™ara me nuni da irin azabar da taji hakan yasa Habeeb juyowa don shi kwata² baima lura da dalilin tureshin da tayi ba.

 

Ganinta a Æ™asa a zube cikin jini yasashi sakin ihu da dira kanta ya É—agota yana jijjigata yana kiran sunanta yana cewa “Habeebah wayyoh matata don Allah kada ki mutu bamu cika burinmu ba wlh in kika mutu nima mutuwa zanyi…..” Sunkutarta Najeeb yayi suka fice da ita da mugun gudu suka nufi gdansu Dagaci yana biye dasu saboda haukan iyayen Habibah ya wucce tunaninsa baitaÉ“a tunanin da gaske sukeyi zasu iya kashe Æ´arsu da hannunsu ba.
Tun a hanya suka rinÆ™a kiran James dake babban likita ne shine yake kula da lfyrsu suna zuwa ya dira akanta ya fara treatment nata sai bayan ya gama sannan su Jimo suka shigo Jumme ta shiga É—akin da sauri ta faÉ—a kan Habeebah da take farfaÉ—o wa yanzu tana faÉ—in shikenan nikam rayuwata ta lalace Jimo zaka kashe mana Æ´armu É—aya tilo akan wani bare meye yasa kukeson kubawa zuciya dama ta barku da nadama….”
Ajiyar zuciyar da Bibo ta sauke ce ta sanya Habeeb saurin tashi daga inda yake ya nufeta ta kuwa buÉ—e idanunta akansa ya riÆ™e hannunta yana jera mata sannu ta sake Æ™anÆ™ame hannunsa cikin kuka da Muryar jinya da wahala tace “Meye ribata idan banbi wanda naji a raina zan iya sadaukar da rayuwata don kare tasa ba? Habeeb bazan zauna dasu Baba Uda ba inka tafi kasheni zasuyi ka tafi dani garinku na amince zan aureka ina sonk…..” Tsalle Jimo yayi ya haye ruwan cikinta ya naushi bakinta jini yayi tsartuwa zuwa sama ……..
[4/7, 9:16 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2–iGyJfTwItSzAnGg

*Paid book*
Ki biya ta waÉ—annan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.

No comments