Breaking News

Cuta ta Dau Cuta 16

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_


 

_ _

 

_Shafi na goma sha shida_

…….Sannu a hankali JJ ya cigaba da rungumar Anoosh. Abu kaɗan sai ya rungumeta yace cikin murna ne. Riƙe mata hannu kam ya sumbata yanzu ya zama ba komai ba. Tun tana noƙema rungumar harta fara jin daɗi itama tana biye masa. Idan ko suna zaune hannunta na cikin nasa. Ko shi bai kama ba ita zata kama nasan cikin dabara. Ranar sai gashi da kissing ɗinta wai yana tayata murnar ƙara shekarar haihuwa. Duk da taji abun wani iri sai ta samu kanta da jin daɗi. Da suka rabu ya kirata a waya ya dinga maimaita mata daɗin da yaji akan wannan kiss yana hura mata kai akan ita ta musamman ce, baida kamarta, har abada bazai iya ya rabu da ita ba. Kaza-kaza dai irin zantukan mayaudaran maza.
Ya tunkari Hajiya Lailah kan sake kawo kuɗi harda sadaki a kuma saka rana, sai dai an samu akasi a satin Gwaggo ta tashi da ciwo har aka kwantar da ita asibiti. Hajiya Lailah ke jiyyarta, dan haka har Anoosh a asibiti take kwana, da rana ne dai take zuwa gida tai ayyuka tai musu abinci ta wuce makaranta, idan ta dawo ta wuce asibiti Mom taje gida tai wanka itama, idan ta koma sai JJ ya ɗauki Anoosh da suke tare a asibitin wajen Gwaggo ya maidata gida ya jirata ta shirya abinci ya maidota asibitin ya wuce gida.. Wannan yanayi shine ya bama JJ damammaki masu yawa akan Anoosh. Dan babu kunya a gidan nasu zai matseta yay kissing. Tun ana iya haka harya fara kai hannu a sassan jikinta. Idan ta nuna damuwa ya marairaice mata wai ta tausaya masa ko tana son yaje ya nema matan banza ne. _(Kuji shege fa. Da yaya yake yi kafin ya sanki, ƴammata wlhy kusan inda ke muku ciwo. Duk shegen namijin da zai kawo miki irin wannan ƙauli da ba’adin tofa ba sonki yake ba jikinki yake so kawai wlhy. Ku daina yarda wannan soyayyar iskar na kwasarku ana lalata muku rayuwa a barku da kuka ku da iyayenku. Mutuncinki shine kimarki a gidan aure, karki yarda wani shasha ya zubar miki da wannan kimar saboda farin cikinsa da biyan buƙatarsa. Duk namijin dake sonki dan ALLAH da aure tun kina waje zai kasance mai jin kishinki, idan ma kikai shigar da bata dace ba zai tsawatar miki ne, namijin ƙwarai duk ƙarfin buƙatarsa ko taɓa hannun budurwa tsantsenin yi yake wlhy. Sai ku nutsu ku dawo hayyacinku dan da yawanku ana yaudararku ne da ƙananun abubuwan dake buɗe hanyoyin zina koda ba’a kai babban ba).
A ranar da JJ yaci galabar keta mutuncin Anoosh a ranar ALLAH yayma Gwaggo rasuwa. Wannan ruɗanin ya hana Hajiya Lailah fuskantar halin da Anoosh ke ciki. Yayinda Anoosh ke kuka biyu, sai dai JJ nata faman mata daɗin baki ta waya harda kukansa shegen. Ganin yanda ya nuna nadamarsa a zahiri ya sakata jin ɗan sassauci harta saki jikinta. A haka ranar addu’ar bakwai ya sake samunta ya more. Nan ma ta rikice masa da kuka ya koma lallashinta. Al’amari kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba, dan kuwa dai JJ ya gama cin nasara akan Anoosh. Yakai yanzu idan ya ɗauketa maimakon makaranta sai ya kaita wani waje daban. Tun abin na damunta harta fara jin daɗinsa itama. Dan kullum magana ɗaya ce yake mata idan bata bashi ba zai je ya nema matan banza. (Kuji shege. Jeka nema mana bakai da ALLAH ba dan buhun bakon gidanku). Sannu a hankali JJ ya gama sauyama Anoosh alƙibla. Sai ya gama moreta ta koma tana kuka da istigifari. Gefe kuma ya saki maganar kawo kuɗin aure. Idan ta tuna masa sai yace ta sake haƙuri rasuwar Gwaggo ta sake nisa kar ace bai damu ba. Ya riga ya ɗaureta da jijiyar kanta, dole take binsa da to kawai.
Ita kanta Hajiya Lailah da abun ke damunta a rai ranar dai ta fidda kunya taima JJ magana, sai yace zasu zo a cikin satin zuwa weekend. Ta ɗan ji nutsuwa, dan burinta a yanzu kawai shine Anoosh tai aure itama ta samu tayi auren dan zama haka bazai cigaba da mata ba ana kallonta wani abu daban a anguwa, ga shi yanzu babu Gwaggo mai tsaya matan. Kwana uku da haka Anoosh ta fara ciwo, Hajiya Lailah bata kawo komai a ranta ba sai zazzaɓin cizon sauro kawai da canjin yanayi, dan haka takai ta camix. Ganin har washe gari zazzaɓin yaƙi sauka ga amai tanayi yasa ya ɗauketa suka nufi asibiti.
Hankali tashe suka dawo gida sakamakon abinda likita ya sanar musu cewar Anoosh nada shigar ciki wata biyu da satittika. Daina gani Hajiya Lailah ta kusan yi, da ƙyar da addu’a suka iso gida. Anoosh nada matuƙar tsoro, dan haka Hajiya Lailah na tsareta da kurari bayan shigarsu gida babu wani ja’inja tace JJ ne. Sumar tsaye Hajiya Lailah tayi, ga hawaye na kwaranya a idanunta. Cikin rawar jiki ta ɗauka waya tai kiran JJ. Batare da tace masa komai ba akan ciki ta ce tana buƙatar ganinsa dan ALLAH. Haka kawai yasha jinin jikinsa da jin muryarta, amma sai yace mata zai zo zuwa gobe ko jibi yanzu yayi tafiya ne Babansa ya aikesa Kaduna. Dole ta danne tace masa babu damuwa har ya dawo ɗin.

Hankalin JJ ya matuƙar tashi, dan ya fahimci Hajiya Lailah fa ba kanwar lasa bace ba. Sannan kanta a waye yake dan tanada iliminta gwargwado.  Dan haka ya tattara ya gudu da ga Kano a ranar yacema iyayensa zaije Abuja wani abokinsa na nemansa akan aiki. Sun masa fatan alkairi ya tafi da shirin sai bayan wata guda zai dawo, dan yasan su Hajiya Lailah ba gidansu suka sani ba…….

(Hummm)

____________★

Wani irin kalar rawa jikin Khadijah keyi fiye da farko. Ta ƙurama Dafeeq idanunta dake mar-mar kamar zasu zubo ƙasa. So take taji ya musa, so take taji yace ma Hajiyar nan ƙarya take ba haka bane. Amma harta wuce bai ce ba. Sai ma tana fita wani zabura da yay zai bita. Ƙarfin bugu zuciyarta ta ƙarayi jiri na neman ɗibarta. Batama san lokacin data buɗe baki cikin ƙaraji da karkarwar jiki ta furta, “Dafeeq da gaske kana zuwa duba iyayenka?!! Da gaske kaike zubar da cikin da na dinga samu?!!”.
Harara ya juyo ya watsa mata tamkar zai cinyeta da idanun nasa. Sai kuma ya buɗe ƙofar a zafafe ya fita. Dama yana gab da fita ne tai maganar. Ihu Khadijah ta kurma jikinta na girgigizawa. Gaba ɗaya jitake kamar ta haukace ma ita kam…

Da bibbiyu Dafeeq ke haɗa steps ɗin benan. Jikinsa na rawa kamar wani mayuncin zaki. Yanda yay wani irin kumburar ɓacin rai bazaka taɓa ɗauka yaron nan ɗan shekara ashirin da huɗu bane ba. Kai tsaye ɗakin kainaat ya nufa, sai dai yana ɗora hannunsa a handle ɗin ƙofar ya jita a rufe. Cikin ɓacin rai da ihu ya ce, “Hajiya buɗe ƙofar nan kona ɓallata!!”.
Wani shegen murmushi Kainaat ta saki tana taɓe baki. A ranta tace haba yaro bakai kana jin kai ɗan iska bane kana a ganiyar balaga. Indai takamarka kai shege ne nan ma gidan ka taras, waya gaya maka ana shiga gonar Kainaat a fita lafiya babu tabon sarin maciji koda a yatsan ƙafa ne. Ai wasan yanzu ma aka fara, da kanka zaka min abinda nake so kafin ma cikar sati ɗaya. Amma hakan bazai hanani hukunta shegiyar matarka ba tunda ita batasan taci arziƙin a rabu lafiya ba. Taja tsaki tare da fisgar wayarta ta shiga danne-danne tamkar batajin hargowar da yake da jijjiga ƙofa. Wayar na gab da tsinkewa Nadwa ta ɗauka. Cikin yanayin barci ta ce, “Hello”.
“K malama watsakke a wannan barcin nice”.
Da mamaki Nadwa dake tashi zaune tana murzar ido tace “Amarya a wannan daren, ina kika bar mijin naki ke kuwa dan ALLAH. Wai badai da gaske kike bazaki bashi kanki ba?”.
“Humm share ba wannan bane yasa na kiraki Nadwa, so nake da safe ki sanarma Mommy ina son a aika matar nan taje min wajan malamin nan da yay min aiki akan Abaan ina amarya. Ina son a gobe Dafeeq ya saki matarsa”.
“What! Haba! Haba Kainaat mi kuma ya kaiki wannan tunanin? Dan ALLAH kada ki raba ma’auratan nan Please and please. Keda ba zama kikaje yi ba miya kawo miki wannan tunanin a daren nan? Ni dai babu ruwana dan ALLAH kada kiyi haka akan yarinyar nan da abinma tausayi ce. Ki barta da zalincin da yake mata ma na zubar mata da ciki”.
“Haba kema kin san ganganne na ƙyale cuta ban rama ba. Ai rama cuta ga macuci ibada ce. Har ke kike tunanin wai babu ruwanta. Wlhy duk da ban auri mijinta dan na rayu da shi ba ita bata isa ta shiga gonata na ƙyaleta ba. Da ga safiyar yau zuwa daren nan tamun abinda sai ta san ta shiga gonata wlhy”.
“Ya ALLAH calm down mana Kainaat. Mita miki?”.
Kamar bazata faɗa mata ba sai kuma ta kwashe komai ta sanar mata. Tare da ɗorawa da wannan hukuncin nasu ne su biyu, duk da kuwa shima na tabbata dama wannan shine burinsa a kanta ƙarshe. Dan maza irinsu da sukai auren wuri kuma irin kalar auren nan daga ƙarshe mawuyaci ne basu sake su ba kosu ƙaro musu kishiya. To ni zan rabasu ne a gaɓar da suke buƙatar junansu dan ubansu. Duk da ban auresa dan na zauna dashi ba shi har ya isa ya ɗauki kwanana ya kai mata, tsabar son zubar min da mutunci a wajen ƴar cikina kwana ɗaya da auro ni. Ai wannan cin mutunci yakai cin mutunci”.
“To amma baki ganin kema akwai laifinki? Maybe a matse yake bawon ALLAH kin hanashi kanki kin bashi kuɗi tayaya kike ganin tunda yasan yanada wata matar bazaije gareta ba. Ni dai dan ALLAH ki barsu, abinda kika faɗa mata ma kawai ya isa punishment a gareta, shiko nanda sati ɗaya zaki masa nashi punishment ɗin tunda ya saki jiki aure yay kamar kowa zaici banza, bai san nan da kwanaki komai daya samu ba ma zai rasa shi. Hakan kawai ya ishesa ai”.
“Ina hakan yamun kaɗan, idan bazaki min yanda nake so ba barshi, bara na kira Mommyn da kaina dama dan naga darene bana son tadata a barci, kuma so nake tunda safe aje a amso min”.
“A’a miyay zafi, saƙonki kam zan isar in dai nice. Ni dai shawara na baki dan ina tsoratar miki abinda zai iya zuwa ya dawo. Tunda ba gama sanin halin yarinyar nan kikai ba. Koda kike ganinta ƙarama maybe itama ta iya nata kalar hatsabibancin. Kigafa yanda ta maida miki magana har sau biyu”.
“Mtsoww! Riƙe shawararki malama”.
Kainaat ta faɗa tana yanke wayar. Jefar da ita tai gefe tayi kwanciyarta batare fatabi takan Dafeeq dake cigaba da kiran sunanta yana ƙwanƙwasa ƙofar ba. Sai ma taja headphones dake cikin bedside drawer ɗin ta ta saka abinta, daga haka tabar jinsa gaba ɗaya…

Matuƙar tashin hankali Dafeeq ya shiga. Ta ina matar nan ta samo wannan sirrin nasa da yasan da ga shi sai ALLAH sai likitan nan suka sani. Sannan zuwa gida da yake yi kuwa shi kaɗai ya sani sai UBANGIJI. Dan tun bayan aurensu da wata biyar ya yanke shawarar zuwa ga iyayensa kasancewar labari ya sameshi mamansa ta samu karaya a ƙafa. Koda yaje bai wani sha wahalar shawo kansu ba dan suna son sa kamar mutuwa sakamakon shi kaɗai suka haifa a duniya. Bai yarda ya faɗa musu a ina yake ba, ya kuma sanar musu ya saki Khadijah tun kafin yazo garesu saboda yaga basa so, yanzu neman kuɗi yake yi dan ya koma karatu. Sun ji daɗi sosai suka dinga saka masa albarka. Kwanansa biyu batare da ya yarda kowa ya gansa ba ya dawo. Yayinda babansa ya shirya har gidan su Khadijah yaje yayima mahaifinta tas yace kuma su nema ƴarsu acan gidajen karuwar dan ɗansu ya sanar musu ya saketa. Hankalin iyayen Khadijah ya sake tashi, jikin babanta ya sake rikicewa sosai harta kaisa da samun paralysis. Yanzu haka yana kwance gefen jikinsa baya aiki. Karatun ƙannenta ya tsaya, sai da taimakon wani bawan ALLAH da yaga ƙanwarta mai bimata yana so ya maida yaran makaranta, ya kai Baba asibiti. Yanzu haka yana amsar magani jikinsa da ɗan sauƙi, ƙannenta biyu sun kammala secondary sun cigaba da karatu, an kuma saka musu ranar aure dan dama burin mahaifinsu shi dai su fara karatun sannan ya aurar dasu sa ƙarasa a gidan miji, amma Khadijah ta nuna masa bai isa ba. Ƴan anguwar su Khadijah kam da mutane da yawa sun yarda Khadijah tabi duniya saboda tsoron kada ta dawo gida Dafeeq ya saketa a mata dariya ko iyayenta suƙi karɓarta.
Tun daga lokacin duk wata sai Dafeeq yaje gida, dan hatta auren nan na Kainaat iyayensa sun san zaiyi, hasalima a kuɗin data dinga bashi har gidansu yaje ya gyara tare da ƙarama babansa jari……..✍️

_ Dafeeq anya zakaga ANNABI ALLAH kuwa_

_Khadijah ke kuma ƙya dawo hankalinki ai yanzu. Koda yake baki ji sauran labari ba ma_

_Ke kuwa Kainaat bakiyi wawtaba kuwa?, dan Dafeeq fa Hummm_

_JJ banda abin cewa a kanka kai kam yau, na barka da masu karatu da su Alimah suci min ubanka bunsurun banza‍_

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

No comments