Breaking News

Cuta ta Dau Cuta 6

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_


 

_ _

 

_Shafi na shida_

 

*UMMUL~ADNAN DATA SERVICE*
We offer you the most affordable and cheapest data
*MTN*
500mb ➖ 170
1gb➖340
2gb➖640
3gb➖940
4gb➖1250
5gb➖1550
10gb➖4000
Check balance=*131*4# or *460*260#
*GLO* *CORPORATE GIFTING*
500mb➖150
1gb➖270
2gb➖540
3gb➖790
5gb➖1300
Check balance=*127*0#
*AIRTEL*
500mb➖150
1gb➖270
2gb➖530
3gb➖800
5gb➖1270
10gb➖2510
Check balance=*140#

*9MOBILE*
☑️500mb➖140
☑️1gb➖240
☑️2gb➖480
☑️3gb➖660
Check balance = *228#

All network valid for 30days

*PAYMENT*
Through this acct
7032785536 ZAINAB SARKI AHMED
OPAY
CABLE SUBSCRIPTION ARE ALSO AVAILABLE
Phone no 07032785536

____________

…….Kaff-kaff jikin nashi ke cigaba da rawa tamkar mai jin sanyi. Yayinda lips nashi ke nasu karkarwar suma. Sai ya kalli ƙofa ya kalli tsakkiyar falon, yanayi yana jan jikinsa baya da rarrafe. Hawaye tuni sun wanke masa fuska. Bammm ya dangane da kujerar 2sitter dake bayansa. Duk da azabar zafin data ratsa masa gwiwar hannu bai damuba. Sai cigaba da raba kallo yake tsakanin Alimah da Anoosh da har yanzu ke tsaye a inda suke suna kallonsa kawai. A karan farko tamkar wanda aka matsa ya fara karanta ayatulkursiyyu. Wata irin mahaukaciyar dariya data sake wargaza ƙwaƙwalwar JJ suka kwashe da ita su duka biyun. Sai kuma suka shiga takowa da wani irin salo a tare har zuwa gabansa. Zama sukai gefe da gefensa suka sakashi a tsakkiya.
“JJ angon Alimah!”.
“Ko kuma na Anoosh ba”.
Dariya suka kwashe da shi a tare har ɗakin na wani irin jijjiga suka kuma tafa. Tsuuuu kakejin JJ na sakin gudawa a wandonsa. Fitsari kam dama tuni shi ya fara yin gaba. Kallon wandon nasa sukai a tare suka sake kwashewa da dariya. Sai da sukai mai isarsu Anoosh ta kalli Alimah. “Amarya! Ya kamata ki kawoma angonki abinci yunwa yake ji”.
“Hakane fa”.
Alimah ta faɗa tana juyawa ga kulolin abincin. Daga inda take ta miƙa hannunta sai gashi yayi dogo ziriri har inda kayan abincin suke. Yatsanta manuniya ta dangwala a samansu tayo baya da hannunta sai gasu sun biyota ta dire a gaban JJ da ya sake diriricewa. Ƙular data buɗe a ɗazun yaga shinkafa a yanzu data buɗe sai ga kunamu baƙaƙe kirin na motsi da ransu cike da kular. Kula ta biyu mai ɗauke da miya kam wani irin abune kore shar baima san yanda zai fassarashi ba. Kofi mai ɗauke da zoɓo kuwa ya koma jini. A yanzu Anoosh ce ta zuba kunamun a plate, tare da koren abunnan, Alimah kuma tasa jini a kofi. Jikinsa suka sake matsowa gab suna wani irin mugun murmushi.
“Haaah!”.
Cewar Anoosh tana ɗebo kunamun nan da wani irin zabgegen cokali zuwa bakin JJ. Kansa ya shiga jujjuyawa hawaye na zubo masa. Tsawa mai firgitarwa Alimah ta daka masa, tuni ya wangale bakin yana fashewa da kuka. Anoosh ta zuba masa kunamun a bakinsa. Cikin sauri ya fara taunawa yana wani kalar ɓarkewa da kukan azaba dan suma kunamun kamar jira suke ana zubasu suka fara ɗalla masa harbi a bakin.
Cike da shaƙiyanci Alimah ta kai hannunta saman kansa tana shafawa. “Yauwa My D maza kaci mana kasha magani, ko kanaso Yaya Mujee ya ɗauka banji maganarsa ba. Haba ɗan sumilmilin mijina ƙyaƙyƙyawa tauraron ƴammata moouuch!!!”. Takai masa wani irin kiss mai shegen ƙara a gefen kumatu tare da ɗaura masa kofin nan mai ɗauke da jini cikin baki. Wata iriyar gigitacciyar ƙara ya saki na azaba. A take ya fara zazzago harshe waje zufa na wanke masa jiki. Sai kawai yay baya zai sume musu..

Saukar ruwa mai masifar sanyi a jikinsa ta sakashi buɗe idanunsa a hankali. Zumbur ya miƙe yana ware idanunsa, sai kuma ya ƙwalla ƙara da faɗin, “Na shiga uku na lalace ni Jazool. Dan ALLAH dan ALLAH azo a taimaka min. Wayyo Baba. Na roƙeku ku faɗa min ku su wanene? Dan ALLAH Alimah ina kika san Anoosh, ta mutu fa ta mutu, kice min ba ita bace wannan, zaku haukatani wlhy na haukace kodai mafarki nake…..”
“Ai baba bazai taɓa jinka ba anan. Bama shi ba ko maƙwaftan da ke katanga ɗaya da kai bazasu taɓa jinka ba JJ. Ka ɗauka nan ɗin lahirarka ce, kasan kuwa ai duk wanda ya tafi lahira ba’a sake jin labarinsa kuma. Anoosh kuwa ashe baka manta da ita ba hhhhhh” Ƙatuwar magen dake a saman kujera zaune baƙa ƙirin da jajayen idanunta tamkar wuta ta faɗa cikin muryar Alimah.
Gaba ɗaya ƙarfinsa ya gama ƙare wa. Ga harshensa dake masa wata irin azaba dama bakinsa gaba ɗaya. Mugun ƙanƙame jikinsa dake karkarwa yake waje guda ko kaɗan baya fatan ƙadangarun dake yawo cike da falon su taɓashi. Dan a rayuwa JJ na matuƙar tsoron ƙadangare da mage. Suko sai su taho kamar zasu taɓashi, sai kuma su zagayesa suna kaɗa kai. Gasu wasu irin tuma-tuma babu ko ƙyan kallo.
“Dan ALLAH ku kasheni kawai na huta. Ku kasheni zaifi min sauƙi da wannan azabar da kuke min”.
“Hhhh mutuwa kuma. Ai idan ka mutu a yanzu JJ kaci riba kenan. Dan koba komai ka kuɓuta da ga tari-tarin buhunan azaba dake zaman jiranka. Yanzu lokacin ɗaukar darasin rayuwane bana mutuwa ba.” sai tai wani irin kuka na maguna da ya sashi fashewa da kuka. A take ƙadangarun nan suma suka shiga rige-rigen nufar JJ. Ihu yake sosai yana ƙanƙame jikinsa. Suko suka shiga hayesa yuuuuu kamar an kori tururuwa da ga rami. Tsaff suka yanyamesa yanda kiyashi ke yanyame abu mai maiƙo. Wasu har cikin wandonsa da rigarsa. Harsunansu suka shiga zarowa suka fara lasheshi. Yayinda wasu ke ƙoƙarin shiga masa cikin bakin daya wage yana ihu iyakar ƙarfinsa. Miƙewa yay ya shiga zagaye falon yana tsalle-tsalle da ihu da ƙoƙarin kakkaɓesu a jikinsa. Da ƙayar ya iya kama rigarsa ya saɓule ya watsar ƙasa. Wandon ma ya saɓulesa. Cigaba yay da dire-dirensa yana kaɓar dana jikinsa. Sai da ya gama galabaita da jigata ƙarfinsa ya ƙare tasss ya zube ƙasa yaraff sannan magen nan tai kuka ƙadangarun suka ɓace ɓat. Gaba ɗaya jikinsa raɗaɗi yake masa na bala’i. Dan duk sun karceshi da jikinsu da farcinansu. Da ƙyar yake numfashi idanunsa nayin kamar zasu rufe sai dai sun gagara rufuwar. Sai buɗesu yake da rufewa kamar mai shirin suma. Ji yay ana wani kalar siɗeshi tun daga yatsan ƙafarsa. Yunƙurin zabura yayi sai hakan ya gagara. Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa da sukai masa masifar nauyi da ƙyau kan abinda ke suɗesan.  Wata irin mummunar hallita ce da tunda uwarsa ta haifesa bai taɓa gani ba duniya. Jikinta tamkar jan nama, kai irin na jaki, fuskar mutane da ƙahuna irin na shanaye. Tayi wani kalar tsaho mara misali da daɗin kwatamtawa. Idan ta lashesa ta lasa ta lasa saita fesa masa wani irin ruwa a bakinta mai azaba da raɗaɗi aka ciwukan nashi kamar ruwan attaruhu. Azaba ta hana JJ ko kuka. Jikinsa kam ya gagara koda motsawa. Sai hawaye da ke rige-rigen sakko masa a idanunsa. Zuciyarsa na addu’a da zuwan mala’ikan mutuwa ko hakan zai zama sauƙi a gareshi. Ji yake inama uwarsa bata haifeshi a wannan duniyar ba. Inama ya mutu kafin ya girma…..

(JJ na buƙatar malamai a gidansa)

★★★★….

“Dan ALLAH ka taimakeni ka faɗamin yanda akai Husby. Wlhy gaba ɗaya zuciyata ta kasa samun nutsuwa, a tsorace nake, a firgice nake.”
Sai da ya haɗiye laumar shinkafa da waken da ya zuba a bakinsa sannan ya saki ƴar dariya idonsa a kanta. Cikin nuna alamar rashin damuwa ya ce, “Tsoro kuma Dijoh, minene abin tsoro ko firgita anan. Gida fa nace miki an bamu halak malak da motar hawa ga kuma aiki da za’a dinga biyana albashi mai tsoka. Ai nakega abin muyi farin ciki ne mara misali”.
“Dafeeq wake garemu a garin nan dazai mana duk wannan? Sannan karka manta iyakar karatunka secondary ne kawai balle muce ko girman takardunka zai baka wannan nasarar. Dafeeq ka faɗa min gaskiya mana!”.
Yanda ta ƙare maganar kamar a tsawace ya sashi tsayawa cak da ga yunƙurin kai abincin da ya ɗibo bakinsa ya kalleta. Spoon ɗin ya ajiye a hankali yana mai harɗe hannayensa a ƙirji ya cigaba da kallonta. “Khadijah!” ya kirayi sunanta a hankali idanunsa na sake tsatstsareta. Nata idanun ta rissinar ƙasa, sai kuma ta amsa shi a hankali.
“Ihu fa kike min kamar?”.
“Kayi haƙuri. Wlhy hankalina ne a tashe. Ina jin tsoro Dafeeq matuƙar tsoro. Karka manta nabar komaina da kowa saboda kai tsahon shekara uku batare da nasan yaya suka kasance ba. Taya kake tunanin bazan shiga ruɗani ba a lokacin da naga sabon abu a wajenka tunda nasan mun bar komai namu ne a yanzu kuma bamu da komai sai kammu.”
“Humm hakane, na fahimce ki. Sai dai ki sani barin komai da mukayi bashi ke nufin bazamu samu komai ba a gaba. Itafa duniyar nan da kike gani Khadijah tamkar tsanin hawa gini take. A lokacin da kika bar step 1 zaki ci karo da step 2 ne har zuwa ƙarshe kafin ki kai ƙarshen ginin da zai kaiki rufin soron. Naji bamu da wani karatu mai zurfi da zai iya bani aiki mai girma haka, amma kada ki manta mutanen kirki basa ƙarewa, sannan nasan abinda nakeyi fa ni ba shahsha bane…..”
“Miya kawo zancen shashanci anan kuma. Indai maganata ce nikan ta ɓata maka rai ALLAH ya baka haƙuri. Gida da mota kuma bazan sake magana a kansu ba ALLAH ya sanya alkairi. Ya kuma sa matakin nasararmune su ɗin”.
A ɗan gatsine ya ce, “Amin”. Da ga haka ya ɗauka spoon ɗin ya cigaba da cin abincinsa fuskarsa a ɗaure, bai kuma sake kallonta ba duk da ita yana jin idanunta a kansa alamar shi take kallo. Tsaff ya cinye abincin dan yana cin abinci sosai dama shikam. Batare da ya sake mata magana ba ya miƙe ya haye doguwar kujera ya kwanta ya lumshe idanunsa. Nata idanun kawai ta zuba masa zuciyarta na rawa sosai….

________★

“Wai mi kike shirin yi da wannan yaron da kika danƙarama wannan ƙyautar haka? Kainaat!. Ni gaba ɗaya kin birkita min lissafi wlhy”.
Murmushi ƙyaƙyƙyawar matar da zata iya kaiwa shekaru talatin da huɗu ta saki. Sai kuma tai wani irin juya lafiyayyar kujerar office ɗin nata da salo irin na isa da ƙasaita tana kai bayanta kwance da lumshe idanu. Tsahon mintuna biyu kamar bazatace komai ba sai kuma ta buɗe idanunta a hankali akan wadda tai mata tambayar. Murmushi ta sake saki da motsa lips ɗinta dake ta shining na jambaki maroon ta ce, “Nadwa!”.
“Na’am”.
Nadwa ta amsa mata idanunta ƙyar a kanta.
“Auransa zanyi”.
Ta faɗa kanta tsaye babu shakku ko nuna damuwa balle kwana-kwana a zancen nata.
A zabure Nadwa ta ce, “Aure!! Fa Kainaat? Da wannan abun dana tabbatar kin girma da kusan shekara goma? _Don_ ma da kuke shekarunku dai-dai da shi an miki sutu balle wannan jaririn. To ke da baki gama idda ba ma miya kawo miki wannan tunanin haka?”.
Murmushi Kainaat ta saki tana wani limshe idanunta da sake buɗesu cike da yanga da ƙasaita. “Nadwa kenan, ai ƙarancin shekarun nasa ne suka ja hankalina da yin hakan garesa. Dan zan samu damar tafi da shirina yanda nake so. Rashin gama iddata kuwa ba matsala bace tunda ba yau nace a ɗauran aure da shi ba. Ina yin sharar fage ne kawai yanzu dan so nake ina gama idda a washe gari a ɗaura min aure da shi”.
“Hummm wannan wane irin tunani ne yazo miki na rashin mafaɗi Kainaat? Kamarki matar riƙaƙƙen attajirin matashi ɗan ƙwalisa irin _Don Abaan_ ki rasa a inda zaki ƙare sai auren wannan gajan yaron da ko shekarun balaga bai gama cikawa ba. Anya duniya bazata miki dariya ba da kallon kinyi faɗuwar baƙar tasa kuwa? Ai shi kanshi Abaan zai sake jin izza da yarda ya fi ƙarfin naki kamar yanda yay iƙirari. Uwar tashi da ƙanwarsa da suka zama sanadin rabakun kuma sunci riba.”
Murmushi Kainaat ta saki saki mai faɗi har ƙyawawan farare haƙoranta dake jere reras na bayyana. Idanu ta zubama aminiyar tata cike da ƙasaita. “Nadwa kenan, na fahimci har yanzu baki gama haddace ilimi akan halayena ba kenan. Ban so nace miki komai ba a wannan gaɓar amma ya kamata nace mikin domin ki tabbatar da ni Kainaat ba shasha bace. A tunaninki zan iya haƙuri da 1-0 a fagen wasa ne? Ai in har ba’ai 2-0 ba sai dai ayi draw wlhy, ko kuma a tashi babu ko ɗaya zai fi sauƙi ga abokin karawa. Bari na fito miki a mutum, saki ukun da Abaan yay min zan gyara na sake komawa gidansa dan aure ni da shi yanzu ne zai fara. Wlhy wlhy kinji na rantse, sai na raba Abaan da uwarsa da wannan shegiyar ƙanwar tasa mai kama da aljanu har abada. Sai na sakashi ya wulaƙantasu fiye da yanda suka sa ya wulaƙantani. Sai na shafe babinsu a zuciyarsa fiye da yanda ruwa ke shafe garin da aka gina akan hanyar wucewarsa. Zan ɗanɗana musu azaba sannan na wawashe kaf abinda ya mallaka a duniya ta yanda almajirin saman titi sai ya fisa kima da darajar kallo. Zan tabbatar musu ni Kainaat annoba ce a rayuwarsu. Talauci ga talaka kuma ba tambari bane adone”
“Kin daina son Abaan ke nan?”.
Wata siririyar dariya ta saki mai faɗin gaske. Kafin ta furta, “Bazan taɓa daina son Abaan ba har ranar mutuwata, sai dai kuma hakan bazai hana ni ɗan ɗana masa hukuncin laifinsa ba da na uwarsa da ƙanwarsa dan sabo da kaza a wajena baya hana na saka mata wuƙa a maƙoshi na yanka banza nai farfesunta na cinye”.
“Humm amma kin san shi wannan yaron da kike son aure yana da mata? Sannan ba ɗan garin nan bane zuwa sukai nan aka ɗaura musu aure a gidan hakimi saboda mugun son da sukema juna shi da matar tasa”.
“Wannan dalilinne yasa na zaɓesa ai. Batun matarsa kuwa idan ta kwantar da hankalinta ƙaruwarta ce. Dan bani da wata matsala da ita sai idan ta shiga gonata ne fa tabbas bazan barta ba koda ace zaman sati ɗaya nayi niyyar yi da mijin nata kuwa. Soyayya da kike magana kuma ni ban yarda akwaita ba. Dan naga abubuwa masu yawa a cikin idanun wannan yaron na hatsabibanci. Inda ace sonta yake da gaskiya bazai rabota da iyayenta ya kawota nan ya aura ba. Da sonta yake bazai dinga zubar mata da ciki ba a duk sanda ta samu….”
“What! Zubar mata da ciki fa kika ce? Ke ko ina kika san duk wannan Kainaat?”.
Wani shegen murmushi Kainaat ta saki tare da maida bayanta jikin kujerar ta wani kwanta……..✍️

 

_(Tofa wata sabuwa. Khadijah da Dafeeq laila da majnoon yaya dai?)._

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

No comments