Breaking News

Daurin Boye 28

28

 

Kafin a kammala daura auren tuni zazzabi da ciwon kai ya saukar mata mai zafi,haka ta samu can lungun gadon inna yelwa ta lafe,wanda da qyar ta yadda ta hau,gado ne da iya tsahon rayuwarta bata taba hawanshi ba koda da qiriniya irin ta quruciya saidai


taga ‘yan uwanta na hawa,kusan duk abinda ke faruwa daga cikin dakin zuwa farfajiyar tsakar gidan tana iya jiyowa,hayaniya ce kala kala cakude da muryoyin mawaqa da kidan qwarya wanda tun safe idan waccan ta tashi wata sai ta dasa nata,tana mamakin irin cikar data ji garin yayi,kusan gaba daya qauyen ya hade da hayaniya da dumin maganar daurin auren,duk wanda baka gani ba a wajen to bai kusa ne ko bai cikin garin,gayyar sodi kuwa ba’a maganarsu
“Sai yau kuttun farinjinki ya fashe ne indo?” Mero keta fada cike da al’ajabin halayyar dan adam,karadin maroqa kuwa har wani bai gane na wani,a haka ne ta jiyo sanarwar daurin aurenta daga bakin daya daga cikin maroqan wanda yafi kowa karadi da zaqin murya.

Idanunsa ya lumshe sanda aka kammala karanto siga aka shafa fatiha,yana jin kaman gaske wani b’ari na zuciyarsa na gaya masa ba gaske bane,Koma meye yana jin dadi cikin zuciyarsa,ko babu komai ya cikawa anni burinta na kawo yarinyar cikin ahalinsu,burin annin shine nashi,bai fatan taso wani abu guda daya da bazai iya bata shi ba koda kuwa rayuwarsa ce,ta damu da ita sosai kaman ma bashi yazo da zancanta ba itace tazo da shi,kullum zancanta take da sauran kwanakin da suka rage mata da zata bar gidan daddyn ta dawo cikin nasu gidan,ta dokanta sosai,tana ganin kamar hajar dinta ce zata dawo,ya tabbatar zatayi farinciki a sanda labarin daurin auren ya isa kunneta,yanajin wannan farincikin ne yake tayata shima.

Wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata ta gefan idonta,ta cusa hannunta qasan filo ta ciro wayarta,lambar wayar umminta ta lalubo sannan ta shiga wajen rubuta saqonni ta fara rubuta mata

_duk da na sani bani daga cikin yara masu ‘yanci…bani daga cikin yaran da za’a nemawa albarka saboda laifukansu ga iyayensu…na sani fadar bata da wani amfani a gareki,amma a dai dai wannan lokaci ina neman alfarma a gareki karo na biyu a rayuwata,ki sakawa rayuwata albarka a ranar da aka dauran igiyar wani…ki nema min afuwa da albarkar rayuwa wajen ubangijinmu,koda cikin zuciyarki ne keda ubangiji…koda wannan ce alfarma ta farko kuma ta qarshe da zaki yiwa rayuwata,na barki lafiya,daga ‘yarki mai mafarkin watan watarana zaki rungumeta kamar sauran zuri’arki_

Tura mata tayi,sai data tabbatar yaje sannan ta maida wayar qasan filo ba tare data saka ran samun amsa ba.

Duk yadda aka dinga hada hada da shigowar tawagar ango cikin gidan tayi luf babu inda ta motsa,duk da tana jiyosu suna cigiyar angon,har sukai suka fice taqi ta fito ko nan da can,kusan aliya ce ta zama uwa ta zama makarbiya.

Qarfe hudun yamma inna laraba mai aiki ta iso,tuni maman aliya suka juya ita da abbanta bayan ta saka mata kudi masu yawa a hannunta tace ta riqe,da hanzari aysha ta diro daga gadon ta rungume innar tana sakin kuka,lallashinta ta dinga yi tana mata fadan kukan da tayi daya sauya mata fuskarta ga zazzabi a jikinta,sai data nutsu sannan tayi mata nasiha gami da jan hankalinta,nasiharta tayi mata tasiri matuqa saboda ta tunasar da ita abubuwa da yawa,wannan shi ya taimaka ya riqeta har zuwa dare bata sake zubda wata qwalla mai yawan da zai mata illa ba,saidai kawai gatanan ne sukuku,wanda mutanen qauyen da yawa ke ganin rashin ganin mahaifiyarta da kalar alaqar dake tsakaninsu ne yake haifar mata da sanyin jiki.

Tun daga zuwansu zuwa dawowa yake karantar abubuwa da dama daga cikin rayuwarta,yaga gaskiya zalla,yaga ainihin labarinta da take bashi qarara kusan a aikace,baya manta zuwanshi na farko tattakin da yayi yaje qauyen nasu cikin gidan nas a zuwan mai bincike kan wace indo ba tare da sunsan kowaye shi ba,maganganu marasa dadi da yaji a kanta da mahaifiyarta daga bakunansu,abubuwan daya karanto daga idanunsu,amma ga mamakinsa zuwa na biyu da yaje da sabanin abinda yaje muau da shi da farko sai gashi ta farad daya komai ya canza,cikin qanqanin lokaci ya siya mata qauna da soyayya mai tarin yawa,duk da idean anni ce wadda Allah ya sallada mata qauna da soyayyar ayshan duk da bata taba sanyata a idonta ba,da gaske ne kaso mafi yawa na mutanen duniya sun sauya,babu mutunci babu qauna babu soyayya,komai suna aunashi ne kan mizanin me kake da shi?,me ka mallaka?,waye kai?,waka sani wa yasanka?,zaka iya siyan komai idan kana da kudi,zaka iya mallakar komai komai yana iya zama naka idan kana da abun hannunka,yakan kwatanta yanzu da rayuwarsu ta baya,sai yake ganin banbaci na zahiri mai tarin yawa,ya sauya abokan rayuwa da yawa,da rabu da wasu mutane da yawa ya sauyasu da wasu…saboda walqiyar da akayi suka ga kowa quru quru,kusan shirunsa yafi maganarsa yawa cikin motar,saboda tsohon ciwon kansa dake son ya tashi,wanda hayaniya da kuma tarin tunanin dake cunkushe a kwanyarsa keson tayar dashi,da fari mahmoud bai gane ba,ya addabeshi da tsokanar kodai kewar amarya yake,bai samu ya ganta ba,sai daga bisani ya gane matsalar ciwon kan nashi ce keson tashi,tilas ya tsaida ayarin motocin suka koma mota daya shida khaliphan iya su biyu,yadda hakan zai bashi damar hutawa sosai.

***********************

Qarfe takwas na safiya suka gama shirin komawa gidan daddy wanda haka su inna yelwa suka zartar a cewarsu a gidan mutumin daya riqeta kamar diyarsa za’a dauketa a miqata gidan mijinta,itakam bata da wani tsari sai yadda suka tsara,wannan karon ma ce musu kawai akayi su fito ga mota,wannan karon bata musa ba bata ce komai ba suka fito,motocin guda biyu ne wannan zuwan,guda daya ita da aliya ne da mero sai larai da bahijja yayan baba auwalu,daya motar kuwa gimbiya inna yelwa ce da inna kulu ga mamakin aysha inna yelwan bata ce komai ba ko tayi wani abu na tada hankali kan an hadasu muhalli daya da inna kulun ba,sai kuma lanti matar baba sadisu da kuma qannen ummi mata su biyar jimillar wajen su goma suka nufo gidan daddyn.

Kamar wancan karon wannan ma tafiyar bata wani wahal dasu ko sunga nisanta ba,cikin mintoci zuwa awa guda suka isa gidan,suma gidan a cike yake da ‘yan yinin biki,hakanan suka ratsa zuwa cikin gidan ayshan na musu jagora,bata wuce dakinta ba sai da suka soma zuwa wajen mummy don su gaisa,sama sama ta karbesu kafin daga bisani su wuce zuwa dakin ayshan su yada zango.

Qarfe biyu na rana ya shiga bangaren annin,ya kasa daurewa duk da yawan jama’ar dake gidan da sunan ‘yan biki da kuma ciwon kanshi da yakeson ya dawo,ciwo ne daya sameshi kusan shekara goma baya bisa wani dalili,tun jiya rabonshi daya ganta abinda bai saba yi ba indai yana gari ko yana qasar,a kasalance yake takowa zuwa bangaren nata sanye da farar shadda riga iya gwiwa mai dogon hannu da wando da alama masu hade babbar riga ne,wanda ya barwa mahmoud ajiyarta a guest house dinshi da suka sauka shi da sauran abokanshi da suka halarci bikin,duk da ba yadda baiyi dasu suyi zamansu ba amma kowanne sai dayazo mishi,kanshi babu hula hannunsa daya saye cikin aljihun wandonsa,yayin da daya hannun yake riqe da hular da bai saka din ba,duk inda ya gifta ido ake binsa dashi kaman yadda akasan amarya da ango da farinjini haka aka dinga tsokanarsa,murmushi kawai yake wanda kusan na yaqe ne saboda ciwo da kanshi keyi,yakan tsaya wani wajen su gaisa wani wajen kuma ya wuce abinsa,da yake yasan kowa yasan kuma dalilin da yasa mafi yawancinsu suke tarayya da su,a haka ya cimma anni a falon ta zaune ita da sauran ‘yan uwa kowa na sabgar gabansa,falon ya cika da hayaniya da surutu dalili kenan da yasa yaji bazai iya zaman falon ba bayan sun gama gaisawa ya miqe,inda wasu mata dake zaune su uku kowacce idonta ke kasa taba qissima abinda zata fada wanda zahiri abinda kecin zuciyar kowannensu ne,inna maryam wadda kusan tafisu rashin haquri kuma mahaufiya ga zeenart tace
“Kadaiqi ‘yan uwanka khalipha qarfi da yaji…duk dadin bare ai dan uwa ya fishi ko?,da cikin ‘yan uwanka ka auri daya kai kanka kasan yanzu farinciki da ake yafi haka….” Murmushin gefen baki yayi wanda yafi kama daya motsa fuskarsa ne kawai,baisan me yasa wasu mutanen sam Allah bai halicci kunya aqwayar idanunsu ba,baisan me yasa wasu suke da saurin manta bara ba,bai cancanta idan ka aikata sharri ka mance da kayi ba,domin shi din dan aike ne,duk daren dadewa watarana zai dawowa mai shi,ta manta lokacin da ‘yan uwan suka kasa tabuka komai ga rayuwarsu?,ta manta sanda suke gudunsu kowa ke qyamar hada muhalli da su?,ta manta cewa bare…baren da basu san daga ina ya fito ba shi ya tallafi rayuwarsu?,ya musu abinda kaf dinsu suka kasa yi musu?zaiso ya jefa mata dukka wadan nan tambayoyin saidai kuma a yanzu baijin yana da lokacinta,sai kawai ya saka kai ya shige dakin gadon anni.

Saman gadonta ya xube plat yana tallafe da qeyarsa da tafukan hannunsa daya hada guda biyu waje daya idanunsa a lumshe,kunnuwansa na masa tariyar kururwar maroqa dake faman kiransa da angon aysha a wancan awannin da suka shude,yana tariyo yawan jama’ar da suka halacci wajen,manyan mutane a qasar nan da wajenta,mutanen da bai taba tsammatar a rayuwarsa zaiyi tarayya da wasunsu ba.

“Lafiya dai khalipha?” Yaji muryar anni na ratsa dodon kunnensa,idanunsa da suka dan kada ya bude ya kalleta da su,sannan ya miqe ya zauna sosai saman gadon
“Ba komai….kaina ne yake dan ciwo kadan…”
“Hayaniya ko?….dama nayi xaton faruwar hakan..kasha magani?”kai ya gyada
“nasha….”
“To Allah ya sawwaqe”
“Amin”
“Batun dauko amarya….” Anni ta fada tana dubansa,baisan sanda murmushi ya subuce masa ba mai sauti,shi shaf ya manta da agender ta gaba ma ta dauko amarya
“Anni….kina son yarinyar nan da yawa…Allah yasa itama haka ne” murmushi tayi
“Khalipha yarinyar ta wahala da yawa…ya kamata zuwa yanzu tasan akwai soyayya qauna da tausayi a ban qasa….ya kamata taji yadda sauran mutane suke ji idan suka samu mai nuna musu qauna….kasa a ranka amana ce zaka riqe saboda Allah,kar ka sanya cutarwa ko matsantawa a tsakaninku,ka bata ‘yancinta wanda bai sabawa addini da shari’a ba” hakanan yaji zuciyarsa na bugawa da kalaman anni…yanajin kaman ta dora masa wani qaton dutse saman kanshi,sai kawai ya miqe
“Qarfe nawa zasu je tahowa da itan”
“Kaman biyar ko shida”
“Ba damuwa……” Tare suka fito da annin ya fice daga sashen nata ya koma nashi bangaren don yana buqatar kadaicewa baya son hayaniya ko zai damu ciwon kan nashi ya sauka,bai jima da shiga ba bacci yayi awon gaba dashi mai nauyi,bai tashi farkawa ba sai qarfe hudu da rabi,subhanallahi ya ambata ganin lokacin sallah ya qwace masa,da sauri ya dira daga gadon ya wuce toilet ya kama ruwa yayi alwala ya fito ya tada sallah.

Yana tsaka da azkar din yammaci biyar saura mahmoud ya kirashi
“Wai ina ka shiga ne?”a kasalance yace
“Ina cikin gida”
“Anya kuwa?….irin wannan murya kodai amarya ce….” Tsaki khalipha yaja,mahmoud yana magana kaman baisan komai kan auren ba
“Me yake faruwa?” Ya jeho masa wata tambayar daban
“Maganar dauko amarya fa?….sai yaushe?”
“Biyar zuwa shida anni tace”
“Toh ba damuwa…ciwon kan fa?”
“Da sauqi dai…baikai na dazu ba”
“Allah ya qara afuwa…zan sake nemanka”
“Okey” ya fada yana katse wayar yaci gaba da azkar dinsa kafin daga bisani ya lula duniyar tunani.

Qarfe biyar da rabi yana shirin shiga wanka ko zaiji qarfin jikinsa kiran mahmoud ya sake shigowa
“Mun fito da dukka motocin nan fa yau ne yafi cancanta ayi amfani da su,dasu xamu tafi daukota” idanuwa ya zaro yana mamakin mahmoud
“What….mahomud dukka sababbi ne…kasan me zanyi da su,wai kana nufin duk yawansu dasu zaku tafi kaman zaku taron president?”
“Tafi president ma” ya fadi yana katse kiran,sauke wayar khalipha yayi yana binta da kallo cike da mamaki,kada kai kawai yayi ya shiga toilet din ba tare daya sake bi ta kan mahmoud ba.

Gaba daya layin ya dinke tsaf da jama’a,koda bakasan wajen ba idan kazo wucewa zaka san cewa biki ake,daga cikin gida kuwa bangaren asma’u amarya an gama shiryawa tsaf,ko irin kunyar nan tsoro da fargaba na amare babu ita tattare da ita,kwalliya ta tsara sosai kamar ranar ne ma ake dinner din tata,qawayenta ‘yan bana bakwai kewaye da ita suna sake tunzurta tare da hirarrakinsu,lubna qawarta wadda itace ta biyu baya ga mai sunanta husa ta shigo tana cewa
“Guy din nan ya gama fitowa dake asma…ke kinga sabbin motocin da suka jere a layin nan kar da su,da alamu ma ba’a taba hawansu ba,iya ganinka sune kala daya yadda kikasan za’a rakiyar shugaban qasa?,wata boyayyar ajiyar zuciya ta saki sannan a fili tayi far da ido,dukkan fargabarta na tafiya,ta boye dukkan wani gata da aysha ta fita tsoronta kar a barota ranar da za’a kaisu,ta toshe duk wata kafa da zata fidda labarin aljannar duniyar da aysga ta samu,tana tsoron kar a daukan amarya suyi shirin da zai rusa nata,wanda kallo zai koma sama,maimakon a kalleta ya zama ayshan itace abar kallo,ashe da wasa hamid yake mata daya gaya mata cewa mota biyu xai kawo shi baya son hayaniya azo a cika masa gida a bata masa waje,tunda ya fada ta kasa challanging dinsa don kar yayi fushi,amma kuma a farga take na kada ya aiwatar da abinda ya fada din,ashe ma wasa ne
“kice yau muma ranarmu ce…idan da rabo muma sai kiga mun dace da wani don din fa” inji nusaiba wanda maganarta ta farantawa da yawa a wajen rai,shewa suka saka sannan suka shiga tafawa cikin walwala da nishadi,asma’u kam ji take kaman ta shide don dadi,kanta ya sake fasuwa,taji ba komai bane don aysha ta fita da gida tundaya kankarota a nan,kuma zata ci gaba da toshe duk wata hanya da qawayenta zasu san mijinta sama yake da nata mijin.

Ta bangaren aysha kuwa tana yin komai ne bisa umarnin aliya,tun dazun da daddy yazo ya musu nasiharsa da bankwana na qarshe take jin kamar idan ta fita daga gidan ba zata dawo ba,kaman tace ta fasa auren…kamar tace ta fasa tafiya,suyita zamansu dasu asma’un tana daurewa halayyarsu,tabbas sabo mugun abu ne,sabo turken wawa ne,batasan da wanne baki zata yiwa daddyn godiya ba,batasan cikin addu’o’i wacce addu’a ya cancanta tayi masa ba,saidai kowa tayita roqa masa gafara da rahamar ubangiji har qarshen rayuwarta,tana zaune saman doguwar kujera a gaban mudubi aliya na shiryata,sunyi fada yafi sau nawa,duk abinda ta saka mata sai ta cire,duk abinda ta goga mata saita goge,saida aliyan ta nuna fushinta sannan ta tsaya ta mata madaidaiciyar kwalliya wadda ba qaramin kyau tayi wa ayshan ba,kamar ka sace ta ka gudu,kwalliya mai sanyi babu hayaniya ba cin waje,tana tsaka da fesheta da turare wayar aliya ta dauki ruri,da hannu daya ta daga saboda dayan ya baci da hoda ta kara akunneta
“Okey…okey to shikenan” ta ambata,wayar ta datse tana fidda murmushi idonta akan aysha
“Ko iya haka aka tsaya khalipha ya faranta min….na gode masa qwarai” saita dubi ‘yan uwan ayshan dake dakin tace
“Duk motar da kuka gani baqa mai dauke da wani tambari a jikinta motocin daukar indo ne…ku shiga duk wadda kuka ga dama,ko kowacce mutum mutum daya zata dauka motocin sun mana yawa….duk wanda ya muku magana koya gaya muku maganar banza ku mayar masa” dariya suka sanya aysha na binsu da kallo,tun jiya aliya ta zige su baki daya,sun kuma hau,kowa yasan yanayin yadda wasu yaran karkarar suke bare yanzu da aliya ta sake tunzurasu,murya qasa qasa don sam bata son magana tace
“Aliya….kin zama babbar kwabo…ke kike sake tunzurasu” idanu aliya ta fito da shi tana tsayawa daga rolling mayafinta da take tana duban aysha
“Kin manta abinda hausawa suka ce?…rana dubu ta barawo rana daya tak tamai kaya…shekara nawa ana abu daya…so ba ruwanki malama ki barmu yau mu huce takaici” bakinta kawai taja ta tsuke,tasan tunda ta niyyata sai sun adar,tana kallon aliyan ta fice daga dakin.

A corridor ta samu mamanta wadda daga dakin mummy take tayi mata Allah ya sanya alkhairi,aliya na ganinta ta mele baki
“Kai mama…sai da kika mata Allah ya sanya alkhairi bayan baso take ba na ‘yarta kawai takeso” daquwa maman ta watsa mata
“Gidanku ja’ira…koma meye ba daga yau ya qare ba?,Allah ya qaddarawa kowa qaddararsa?”
“Shikenan mama….ga masu daukan ayshan can sunzo bari na yiwa su gwaggonta magana…..”
“To shikenan…bari na shiga mu gaisa”.

Wayarta ta daga ta kira mahmoud wanda suka jone a matsayinsa na babban abokin ango ita kuma babbar aminiyar amarya,bakin daya daga cikin motocin ta qarasa tana qarewa motocin kallo a fakaice,ita kanta abun ya qayatar da ita,yawansu da kyan motocin da yadda suke daukar ido,magana sukayi da shi ta gaya masa duk matar data shiga motarsu gidan aysha za’a wuce kawai sannan ta dawo ciki,tun daga farfajiya zuwa falon godan take jin ana zancan motocin da suka zo daukar asma’u,kowa na zuzutasu hadi da yabawa,dariya take sosai cikin ranta tana qissima yadda dramer zata kaya,lallai yau akwai film guda a sanda asma’u ta fahimci meke faruwa,yau zata gane a rayuwa kafi wani ne wani ya fika,kuma dole kai qasan wani kake komai kyanka,iliminka dukiyarka ko nasabarka.

Sanda ta shiga dakin bata taddasu aysha ba,su gwaggo sun miqa ta wajen mummy da nufin suyi sallama,kalaman da aysha tayi ga mummy ba ita kadai ba har wanda ke wajen ya tabasu,wannan karon duk da yadda mummyn kejin zafin aysha…jin zafi mara dalili ta daure tayi mata fatan alkhairi,kuka take sosai cikin mayafinta,kukan rashin uwa,uwar da zata tallafeta ta rungumeta,kukan rashin uwar da zata gaya mata dokoki da hanyoyin zaman gidan auren,uwar da zata nuna alhinin na haqiqa saboda sun raba muhalli…uwar da zata roqa mata salama da samun tabbatuwa da zaman lafiya a sabon muhallin da zata soma rayuwa,yau jinta take cikin matsanancin quncin da zata iya cewa tamkar ninka mata shi akayi,a haka take takawa tana ficewa daga gidan,kuka na sarqe numfashinta kamar zata shide.

Kowa ya san yadda mata keda kwadayi da rububin zuwa gidan amarya,hakan ce kuwa ta kasance sanda aka soma bude motocin daukar aysha,dangi da ‘yan uwan da kaso tara cikin goma na asma’u ne suka soma duruwa ciki,suna tsammamin motocin rakiyarta ne,don da yawa daga cikinsu suna da kabarin irin mijin da ayshan zata aura,basu da labarin yadda lamari ya sauya lokaci daya,so babu wanda ya kawo cewa mijin nata zai iya aiko da wadannan motocin bare suyi tunanin nata ne,a haka labari ya bazama cikin gida masu son zuwa kai amarya wadanda basu da ababen hawa suka soma fitowa.

Farida ce ta shiga dakin da asma’u da qawayenta suke ta sanar musu an soma tafiya fa,a sannan wata yayar mummy ta shiga ta kai asma’un wajen mummy don suyi sallama,ba wata sallama bace ko wasu kalamai illa kuka da suka dinga yi,saida aka riqe asma’u wanda kusan rabi pretending ne,don dai kawai kar aga rashin kunyarta,bata tunanin don zata koma zama da masoyi kuma ya zame mata abun kuka,a haka aka lullube asma’u aka dannata cikin daya daga cikin motocin daukar amarya da zasu gidan aysha ba tare da sun sani ba.

*_Ya Allah,ya ubangiji ka rabamu da sharrin mutum da aljan_????????*

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 9:02 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*DB*

No comments