Breaking News

Garkuwa 8

PAGE 8

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

️連老

Kada dai ku mance Free page ne, yana kuma gab da karewa.

*Ga mai buƙatar saya ga number ta, 09097853276 turo ɗari uku ko dubunki ɗaya kacal domin samun damar karantawa cikin salama, Ga Ac ɗina 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, in kin biya sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276 in ba halin turawa ta ac bisa dole turo katin mtn.*

 


Ta saki kwaryar, a sorace, da sauri yasa tafin hannunshi, biyu ya tare kwaryar.
Cikin tsoro jiki na rawa ta zazzaro idanunta woje kana murya a hargitse tace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun, Ya Ba’ana mekabani? Me ka shayar dani? Na shiga uku me kasa nasha?”.
Gaba ɗaya ta gigice tana rawan jiki da murya, ga hawaye kuma tuni suke shatata.
Ganin yadda ta firgitane ya sashi matsowa gabanta cikin ɗaga murya yace.
“Ba komai ba abinda na shayar dake Mata, wallahi Allah ki yarda dani wancan da kikasha babu komai a ciki”.
Da sauri taja da baya tare da cewa.
“Ban yardaba me ka shayar dani?”.
Sai kuma ta fara kakarin amai da ƙarfi, ganin kamar aman bazai zo bane yasa ta tura yatsunta biyu a baki, amman ina aman yaƙi zuwa sam.
Kawai sai tasa mishi kuka.
Cikin tashin hankali yace.
“Kiyi haƙuri Mata wlhi bazan taɓa shayar dake wani abu na guba, ko na ƙiba, duk abinda nasan bazaki shashi da sanenki ba bazan taɓa bakishi a ɓoyeba.
Ki yarda dani wlh ban shayar dake komaiba”.
Ina taƙi ta saurareshi sabida tayi matuƙar firgita da tsananin razana da ganin abinda ke cikin kwaryar, cikin sauri yasha gabanta tare da cewa.
“Ki gani mana ki duba babu komai a ciki fa madarar shanunce”.
Tsayuwa tayi tare da zubawa cikin kwaryar ido tas farin nonone kamar ko wanne nono da bashi da gamin komai”.
Hannutasa ta mutstsuke idanunta tare da kuma sake kallon, cikin tuhuma ta maida idanunta kanshi tana mishi kallo mai cike da tuhuma.
A hankali ya sunkuya ya ajiye akwaryar kana ya taso ya fuskanceta da kyau fuska ya haɗe tare da cewa.
“Sam bakya min adalci Mata, na lura dake, wani mugun zato da zargina kikeyi.
A zatonki wai zan iya cutar da kene? Shin kin mance tun kina ƴar tatsitsiyarki nake sonki ne? Da inada mummunar niya a kanki da na cutar dake tun kina ƙarama.
Kullum idanunki na nuna min baki yarda dani ba. Me kike nufi?
ko dai wani kikeso ba niba?”.
Ya ƙarshe tambayar da taune bakinshi kana ya tsareta da idanunshi, da sauri ta sunkuyar da kanta tare da cewa.
“A a ni kam babu wanda nakeso.”
Kanshi ya ɗan rausayar kana ya dawo ya zauna a bakin bukkar tashi, cikin kakkausar murya yace.
“Dawo ki zauna”.
A hankali ta dawo gefen gaban bukkar ta zauna,
shi kuwa wani ɗan randar ƙasan dake gefenshi ya buɗe, cikin haɗe fuska ya ɗan kalleta tare da cewa.
“To zakiyi sabon Saurayi. Salmanun Arɗo Yabani, zai fara nemanki, kamar yadda munafukan tsoffin rugar nan suke tsarawa, dan ana son rabani dake”.
Da sauri taketa jujjuya kai tare da cewa.
“A a Wallahi ni Yaya Salmanu, ba sona yakeba, ka sani tun ina ƙarama duk abinda ya shafi karatuna shike koya min har dai yasa aka sani.
Makaranta kai kuma baka hanaba”.
Cikin haɗe fuska yace.
“Ehh ai nasan ke baki san yana sonkiba, amman na lura shi yana sonki, kuma zanci ubanshi da bulalin shaɗi bashi babu sake kallon duk wani abu da nakeso”.
Cikin tarin tsoron kada a cutar da Yaya Salmanun tace.
“Wallahi ƙarya ake mishi, baice yana sona ba, shi yama tsaneni ne yanzu, dan Allah Ya Ba’ana kada ka yarda da ƙaryar mutane”.
Kai ya rausayar tare da cewa.
“Uhum kinga nan cikin ranɗar nan, to bulaline wanda nake shaɗi dasu, yanzu tsawon shekaru biyu kenan da aka hana shaɗi basu samu wanda suka dakaba, na tsumasu da tarin tsumi mai zafi, wanda muddin na zana jikin mutun dashi sai ya fashe,
Kuma gasu a ƙalla sun kai tamanin a cikin randar nan kuma a ƙa’ida da guda goma sha bibbiyu kawai zakayi shaɗi to kinga kenan zan iya shadi da mutun sama da shida dasu basu ƙareba”.
Kanta taketa jujjuya mishi tare da cewa.
“Ya Ba’ana kada ka yarda da sharrin mutane kasanfa Yaya Salmanu shike karantar dani, tun ina ƙarama kuma ko yanzu dana girma tunda shi ya rigada ya gama digiri ɗinshi shike fahimtar dani duk abinda ya shige min duhu, kuma tunda nazo hutun nanma ban haɗu dashiba”.
A hankali yace.
“Eh ai yau kam zaki haɗu dashi”.
Yunƙura tayi ta tashi tare da cewa.
“Uhumm, shike nan ni bari in tafi gida an fara kiran salla.”
Da sauri ya miƙe ya fito yabi bayanta tare da cemata.
“To Mata jirani inzo in rakaki Mana”.
To kawai tace mishi, a haka suka jero suna tafiya yana gaya mata irin tsumin da yayiwa bulalin nashi.

Suna isa dai-dai garken su Shatu, ta ɗan tsaya hango yayunta sun dawo daga kiwo,
cikin jin daɗi ta ɗan juyo ta kalleshi tare da cewa.
“Bari inje wurinsu Ya Giɗi, in tayasu ɗaure shanun”.
Murmushi yayi kana yace.
“To Mata ki kulan min da kanki kada shanu ya taɓa min ke, dan akan ɗan mai shanun zan rama miki ba kan shanu ba”.
To tace tare da juyawa ta nufi cikin tsakiyar taron dabobbi su da aƙalla zasu kai guda dubu da yan ɗaruruwa tsakanin shanu, tumaki, awaki, rakuma.
Da sassarfa take kutsa tsakiyar dabobbin tana cewa.
“Yaya sannunku da dawowa”.
Da sauri Giɗi da Seyo suka juyo murmushi sukayi tare da cewa.
“Yauwa ƴar ƙanwarmu, daga ina kike?”.
Da ido ta nuna musu Ba’ana dake tsaye can gefe ya zubawa dabbobin nasu idanu tamkar mai ƙidanya su.

Gaini ne da Lado suka zuba mishi ido domin gaba ɗaya ya shagala da kallon da yakeyi, har wani ƙan-ƙance idanu yakeyi.
Sam bayaji kiran da Babanshi Bukar ke auna mishi.
Har saida Giɗi yace.
“Heyy Ya ba’ana Ubanka na kiranka”.
Ya ƙirishe mgnar da bagwariyar hausarsa.
Shi kuwa Ba’ana da sauri ya juya ya nufi wurin babanshin da yanzu ya dawo kiwo.

Cikin sakalci da gajiya Giɗi ya kalli yayunshi mazan tare da tura baki gaba yace.
“Wayyoooooooo Allah bayana zai karye, Ni dai na gaji bazan iya sunkuyon ɗaure shanu ba, ga Shatu zata tayaku”.
Sai ya kuma kalli yadda duk suka sunkuya sunata ɗaure dabobbin suna ɗan dariyar yadda itama Shatu ta dage tana tayasu.
Junainah ce wace dama duk lokacin dawowarsu zata kawo musu sassanyan kindirmo susha tun a nan kafin su koma gida.
Da saurinta take ratso cikin shanayen tana cewa.
“Ya Giɗi tareni, na gaji ga damunku”.
Da sauri ya nufi inda take kwaryar ya amsa kana suka dawo gaban bukkokin da nanne ma kwancin masu gadin dabobbin suke.

Zama sukayi ludeyayen dumar dake kan fefeyin daya rufe kwaryar ya ɗauke kana ya buɗe kwaryar, ludeyi ɗaya ya sa musu a ciki.
Aysha dake kusa da sune ta zauna tare da cewa.
“Ya Giɗi kama ka bani”. Kai ya gyaɗa mata kana ya cika ludeyin yasha sannan itama ta ɗebo rabin ludeyin tasha, kana ta bawa Junainah itama ta kamfato ta cika ludeyin ko rabinshi bata zuƙaba.
Ta miƙawa Ya Seyo dake tsaye gefensu, da murmushi a fuskarshi ya amsa ya sha, sauran nata,
Shatu ce ta gyara zamanta ta matso kusa da ɗan uwanta tsokonta Giɗi abokin tsamarta, gyara zamanta tayi kana tace.
“Ya Seyo zauna ga fili.”
To yace kana ya zauna suka fara sha,
Lado ne ya kallesu cikin gajiya yace.
“To wai mu aka kawowa ko kune?”.
Shiru babu mai magana sai kamun ludeyin da sukeyi,
Gaini ne ya matso gefe shima ya zauna kusa da Junainah yasa hannu ya ɗauki wani ludeyin, nan suka zauna suna sha, ganin hakane, Ya Lado yace.
“To ni naci girma”.
Da sauri Shatu ta mike wurinda ta tashi ta nuna mishi tare da cewa.
“A a ya Lado zauna kusha ni na ƙoshi”. Murmushi Bappa dake gefensu yayi, wanda yanzu ya iso da jarkan ruwa a hannunshi,
Cikin kallon so da tausayin yaran nashi yakeyi,
Cikin kula yace.
“Sannunku- sannunku da rana, Allah yayi muku al’barka”.
Amin Amin suka amsa baki ɗayansu,
Sai kuma ya kalli Aysha da Junainah yace.
“Ayshatu maza kama hannun Junainah ku koma gida, kinji an fara kiran salla”.

To tace tare da kamo hannun ƙanwar tata suka nufi gida.

Su kuwa Bappa da yaranshi da makiyayanshi anan sukayi al’wala, kana suka juya suka nufi cikin Rugar tasu dan zuwa masallaci.
Yayinda ko wanne garke an bar mutun ɗaya sabida tsaro…

Bayan sallan isha sunci abinci sun ɗan taɓa hira, kaɗan kana Bappa ya tarasu yana karantar dasu kamar yadda ya saba duk dare, da kuma safiya kafin a tafi kiwo shiyasa sam ahlin wannan Rugar Bani ba jahilai bane.

Suna zaune, yaro yayi sallama, yace.
“Wai ana kiran Shatu a woje”.
Ummey ce ta ɗan juyo ta kalli yaron tare da cewa.
“Wake kiranta?”.
“Wai yace ince mata inji Ya Salmanu ne”.
Yaron ya faɗi.
Da sauri Ummey tace.
“A a Salmanu ne ya zobe? To maza kace ya iso mana ya zai tsaya a waje kamar baƙo”.
To yaron yace kana ya juya ya fita.
Jim kaɗan sai gashi ya dawo gefen Ummey ya rusuna tare da cewa.
“Yace wai ince mata, ta fito woje”.
“Da mamaki Ummey tace to gata nan zuwa”.
Sai kuma Inna ta ɗan kalli Shatu tace.
“Tashi kije ai mun gama aikin ma”.
Ita kuwa Aysha dake zaune gaban Inna suna gasa tattabarun da aka yanka tunda yamma,
kwano ta ɗauko a konɗonsu kana tasa gasassun tattabarun guda biyu.
Tasa yaji a gefe, ta rufe, kana ta gyara wuyan hijabinta sannan ta miƙowa Junainah kwanon.
A hankali ta ratsa gefen su Ya Giɗi ta wuce.

Ummey kuwa da ido ta rakasu tana fatan Allah yasa fata da shirin Bappa da Arɗo Yabani ya tabbata.

Suna fita suka sameshi zaune bisa dakalin ƙofar gidan nasu.
Da sauri Junainah ta isa gareshi tare da cewa.
“Oyoyo yaya Salmanu”.
Ajiye kwanon tayi a gefenshi.
Da sauri yasa hannunshin suka tafa da hannunta data miƙa mishi, cikin sakin fuska da nitsuwa yace.
“I miss you ƙanwali”.
Dariya mai ɗan sauti tayi tare da cewa.
“Miss you too my dear”.
Dariya mai sauti sukayi a tare cikin jin daɗi wanda aka kira da Salmanu ya lakace hancin Junainah tare da cewa.
“Alhamdulillah alama ta nuna ƙanwaliya tana zuwa makaranta babu wasa”.
Cikin jin daɗi tace.
“Sosai ma ya Salmanu yanzu ajiyana huɗu fa, yanzuma dan hutu mukeyi, kuma gashi ko a gidama Ina karatu”.
Jinjina mata yayi da hannunshi kana, ya jawo kwanan data ajiye tare da cewa.
“Ƙanwaliya me kika kawo mim ne?”.
Cikin murmushi tace.
“Gasheshen naman tattabarune Ya Salmanu barima in koma ciki inci rabona inci na Addana”.
Kafin ya ankarama tuni ta juya da sauri tayi cikin gida.

Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da kallon Aysha dake jingini da bakin kofar zauren,
Cikin sanyi yace.
“Kamar bakiyi farin ciki da zuwana ba? Ko dai in komane?”.
A hankali tace.
“A a Ya Salmanu nadai ga kamar kafi farin cikin ganin Junainah ne akai na”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Kin rama kena”.
Murmushi sukayi dukansu, cikin sanyi yace.
“Ga wuri kizo ki zauna mana”.
A hankali tace,
“A a Ya Salmanu mu shiga cikin gida mana”.

“Kina tsoron kada saurayinki yazo ya ganmune?”.
Salmanu ya faɗa a hankali.
Da sauri tace.
“Eh”.
Kanshi ya ɗan rausayar tare da cewa.
“Babu abinda zai faru sai al’khairi zoki zauna, ki gayamin me kike tsoron?”.

A hankali ta zauna gefenshi ɗan nesa dashi.
Shi kuwa juyowa yayi ya fuskanceta a hankali yace.
“Gaya min me kike tsoro?”.
Kallonshi tayi cikin yin ƙasa da murya tace.
“Ina tsoron kada Ya Ba’ana ya cutar da kai, ina gudun kada sakaiyar alaƙarmu ya zama cutarwa, sabida Ni kamin rana a rayuwata, rana kuma ta al’khairi shiyasa bana son abinda zai cutar da kai”.
Murmushi mai yelwa yayi kana a hankali yace.
“Ina sonki zan kuma aureki da izinin Ubangiji zan rabaki da wannan taƙadirin, domin baki cancanci zama matar mushurkiba”.
Da sauri tace.
“Kada kace haka Ya Salmanu Wallahi zai cutar da kai, kada ka bari wani yaji, bare mgnar ta koma kunnenshi”.
Murmushi yayi tare da jawo kwanon ya buɗe. Numfashin yaja jin ƙamshin naman a hankali ya fara ci, saida yaci ɗaya kab sannan ya rufe kwanon yace.
“Ga rabonki dan nasan Junainah ta cinye naki rabon”.
Cikin yanayin nitsuwarta tace.
“A a kaci kawai Ya Salmanu”.
Da sauri yace.
“No kada kimin musu”.
Shiru tayi jin yaci gaba da cewa.
“Muddin dai ina raye in sha Allah.
wallahi Allah bazan bari Ba’ana ya aureki ya lalata miki rayuwaba, zan jure duk azabar da zai shayar dani na shaɗi in Sha Allah zan aureki”.
Ido ta zuba mushi tana kallon shi cikin kamalarsa, ganin sam hankalinta ba’a kwance yakeba, yasashi ce mata ta shiga gida zasuyi mgna a waya, haka kuwa akayi, ta juya ta shiga gida shi kuma ya nufi hanyar gidansu.

A dandalin wurin da yake kamar kasuwar garin nasu ya samu abokanshi, kowa da budurwarshi suna ɗan hirarsu
Can gefe kuma ga yara nata wasansu, ga farin wata ya fito yayi ras, kana iya ganin komai.

Ita kuwa Shatu, bayan sun gama shirin baccinsu, ta kalli Ummey tare da cewa.
“Ummey”.

“Na’am”. Ta amsa mata cikin kula, sai kuma tayi shiru, ita kuwa Ummey ido ta zuba mata,
ganin hakane yasa a hankali tace.
“Ummey Ya Salmanu”. Still kuma tayi shiru,
Cikin kulawa da shaƙuwa wanda ke tsakanin uwa da yarta Ummey tace.
“Gaya min mana, me Ya Salmanun yayi?”.
Konciya tayi gefen Ummi dake bisa sallaya, kana a hankali tace.
“Wai yana sona, Ummey ina tsoro Ya Ba’ana zai illata mishi rayuwa, gashi kwanan nan Ya Hashimu ya rasu, kuma shima ance kasheshi akayi, Ummey ki cewa Bappa na, yacewa Baba Arɗo ya hana Ya Salmanu cewa yana sona, kinji ko Ummey?”.
Kai Ummey ta jinjina mata tare da cewa.
“To zaki aureshi kenan duk da kinsan baya salla kuma yana tsafi”.
Kai ta juya tare da cewa.
“Bazan aureshiba Ummey, amman ya Salmanu yayi shiru, bari in gama karatuna, in sha Allah akwai mafita in na gama karatuna, Ummey kin gane ai ko? Kin tuna ko”.
Murmushi Ummey tayi kana tace.
“Eh na gane, yanzu konta kiyi baccinki”.
da haka suka konta bacci.

Bayan kwanaki, sosai lamarin Ba’ana yake bawa mutane tsoro, mutun kamar ifiritu, dan yanzu yanayin sihirinshi ƙaruwa yakeyi sosai,
Wasu lokutan ba hawa ba sauƙa sai dai kawai ka ganshi a gabanka sabida yanzu layan ɓatarshi tama fi ta baya ƙarfi, ya dage wai zai bawa Shatu taƙi fir daya matsama kuka tasa mishi hakanne yasa ya hakura ya barta.

Ya Salmanu kuwa yanzu ya dage kan batun soyayyarsa da Aysha, ita kuwa tsoron abinda zai faru ya hana yarda da kowa, gaba ɗaya kuma yanzu Ƙabilar ɓachamawan nan masifa tuƙuru suke neman fulanin Bani dashi sabida baƙin ciki da hasadar ganin yadda shuke-shuken wurin fulanin yayi kyau, shinkafa, masara, dawa, gero, maiwa, wake, gyaɗa, gujjiya, riɗi, da dai sauransu.

Ga tarin bishiyoyi dorowa da suke zagaye da garin wanda kan ko wacce bishi akwai jingogin zuma, shiyasa garin suke da tarin zuma.
To waɗannan abubuwan sune suke ƙara tunzura kafuran, sabida gani suke aifa da filin nasune, sun mance kafin a saida wa fulani filin kufayine, fulaninne suke tafe da al’barkasu a jikinsu.

Zuwa yanzu kowa na Rugar Banin da kewaye yasan masoyan Shatu biyune, kuma za’ayi shaɗi, wanda tsawon shekaru biyu kenan ba’ayin ba.
Kowa in yaji da Salmanu za’ayi ana tausaya mishi domin shi mutunne mai laushin jiki shiyasa tun yana ƙaraminshi aka meda hankali kan karatun da yakeso, hakane yasa yayi karatun shi yanzu haka yana zama cikin Shikan ne inda yakeda shagunan kayan tireda sabida bazai iya noma da kiwo ba, kuma Alhamdulillah kasuwar ta amsheshi. Shiyasa shi zuwa yakeyi Rugar Bani ɗin.

A can ƙasa mai tsarki kuwa,
Yau kwanansu Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero da Sittinshi goma da zuwa, to kasan cewar zasu gudanar da aikin Umarne yasa tun randa suka cika kwana uku da zuwa suka tafi, Madina,
Kuma sun bar mgnar batun Jazrah cewa sai sun gama gudanar da aikin Umararsu kafin su shaida mishi, kana in sun dai-dai ta da Jazrah sai su shaidawa Mai alfarma Sarki Jalaluddin, shi kuma yaje har Ɓadamaya ya shaidawa mai daraja sarki Nuruddeen Bubayero, da kuma Habeebullah, batun auren in yaso su shirya suzo ayi ɗaurin auren.

To yau kwanansu takwas a Madinah kuma yaune suke shirin dawowa makka.

Kullum sai sun gaisa dasu Hajia Mama dasu Jalal.
Kullum yakan kira Juwairiyya.

Da maraicin suka isa cikin Makka kai tsaye masarautar suka wuce.

Bayan sun gaggaisa, Sheikh Aliyu yace suje su huta, kafin su gaisa da Sheykh Abdulkareem domin yana tare da manyan baƙi.

Haka kuwa akayi, bayan duk sunyi wonka suka dawo falon Sitti.

Suna zaune cikin shiga ta al’farma a wuri na al’farma, an zagayesu da dukkan kayan jin daɗin rayuwar duniya,

Sitti na zaune bisa tsakiyar falon akan wani tattausan carpet, Jannart da Jazrah suna gefenta, cikin shiga ta al’farma,

Sheykh kuwa zaune yake bisa wata lumtsimemiyar kujera kana sawunshi na kan wasu tim-tim masu masifar kyau da taushi, wasu kyawawan larabawane guda biyu suke zaune a gaban Sitti sawunta dake bisa tim-tim ɗin sukeyiwa tausa.
Yayinda wasu hadiman kuma ke shirya musu ababen ci dasha dangin yayan itatuwa kamarsu, Inabi, tupa, ayaba, dabino, gabaruwa, sai zam-zam kana, saisu shawarma and pizza da kuma wasu irin manyan Foodflaks da aka cikasu da danƙawa-ɗanƙwal dajaja sai sauran abincinsu na larabawa.

Haroon kuwa gefe yake kusa da Jannart suna ɗan taɓa hira.

Wayarshi ce ta fara ringgin a hankali, idonshi ya ɗan juya ya kalli wayar ba tare daya juya kanshiba,
Da idonshi ya nunawa hadimin dake gefenshi wayar,
da sauri ya ɗauko wayar ya miƙa mishi, ganin Hajia Mamace ya sashi amsa kiran.
Kara wayar yayi a kunne cikin girmamawa yace.
“Barka da dare Hajia Mama”.
A can gida kuwa cikin wani irin salo na musamman Hajia Mama ta rufe idanunta tare da cewa.
“Uhum ka manta Jabeer mu nan yammane”.
Idonshi ya ɗan ɗago ya kalli agogon dake jikin ginin, a hankali yace.
“Haka nefa Hajia Mama. Ya gida yasu Jalal”.
Murmushin jin daɗi tayi tare da cewa.
“Suna lfy gasuma nan kusa dani, Jamil ne ya tsokano Jalal shine suka shigo sunata muzurai”.
Kanshi ya jingina da jikin kujerar, a hankali yace.
“Hajia Mama kiyi musu faɗa kice su barifa sun girma”.
Murmushi mai sanyi tayi tare da cewa.
“Na gaya musu sunma daina gasu nan sunata hira kuma”.
Gyara zamanta tayi kana taci gaba da cewa.
“Ina Sitti na?”. A taƙaice yace.
“Gata nan kusa dani”.
Cikin yanayin jin daɗi tace.
“Bata waya”. To yace kana ya miƙa Sitti daketa kallonshi wayar, da sauri ta amsa tare da karawa a kunne, murmushi tayi jin muryar Hajia Mama na cewa.
“(Allah beddu sabbugo Sitti), Allah ya ƙara nisan kwana Sitti”. Amin Amin tace, kana suka gaisa cikin tsananin jin daɗi.
Bayan sun gama wayarne kuma Juwairiyya ta kira Jannart nan suka gaisa ta bawa Sitti wayar hirar tasu kab kan ya Jafar ne. Saida suka gama wayarne ta kalli Sheykh dake kishinƙiɗe ya lumshe ido a hankali tace.
“Juwairiyya tace , yau tun safe Jafar ya shiga sashinka yayi ta nemanka ɗaki ɗaki, da bai gankaba yaƙi fitowa sai kuka yake tayi, har saida yammane da Jalal ya dawo gida shine ya lallasheshi ya maidashi sashinsu.
Hannu tasa ta share hawayenta da ke kwaranyowa, Haroon ma hawayen ne ke zubo mishi,
Haka Jazrah da Jannart,
Shi kuwa Sheykh cikin sanyi yace.
“Lamiɗo ya gaya min ɗazu da mukayi waya”.
Shiru sukayi baki ɗayansu, a hankali Haroon ya miƙe kwance tare da faɗawa nazari mai zurfi.
Nan kuma kiran Umaymah ya shigo wayar Sitti still hira sukayi sosai wanda ta kontar musu hankali kafin, sukayi sallama da juna.

 

Yau jumma’a ne gajeren lokacine basa kai yamma a wurin kiwo, kafin azahar suke dawowa, shiyasa yau Shatu tace da ita za’aje kiwo.
Dariya kawai sukayi mata dan sun san ba iya jurewa zatayiba amman tunda ta kafa ta tsare cewa dole zataje, sai aka barta.

Kasan cewar basu kai yamman bane yasa kuma suna tafiya da wuri.
Bayan duk an kunce dabobbin gaba ɗaya, hakama sauran makiyayan baki ɗaya, sahu- sahu shanayen keta wucewa.

Sun tafi tun shida da rabi na safe,

Kafin zuwa tara na safe sunyi nisa cikin wurin kiwonsu, inda nan kuma Aysha ta samu su Hindema sunzo kiwo, wanda su kullum dama suna zuwa.

Wani irin hadarine mai ƙarfi ya taso daga ƙasa, ganin hakane yasa, Gaini kwallawa Shatu kira wacce take can cikin ƴan uwanta mata makiyaya, jin shiru bata amsa bane ya nufi wurin da suke zaune,
Cikin kula yace.
“Aysha tashi keda Hinde dasu Mero duk ku tafi gida, kunga hadarine mai ƙarfi ke tasowa daga ƙasa da alamun za’ayi ruwa mai ƙarfi”.
Cikin ƙarfin hali da son wasa cikin ruwan da taketa hari murya a sanyaye tace.
“Ba komai ya Gaini zamu jiraku ai lokacin tashi kuma ya kusa ko?”.
Su Giɗi dasu Aro da sauran makiyayan ne sukace.
“Ya Gaini barsu mana ba kiwo zasuyi ba ai makiyayin shanu da tumaki baya gudun ruwa duk yawa shi”.
Cikin jin daɗi sukace, eh mana,
Shi kuwa Ya Gaini murmushi kawai yayi tare da cewa.
“Shike nan yau zakusha dukan ruwa”.
Murmushi sukayi sukace “Babu matsala”. daga nan mazan duk suka koma wurin kula da dabobbin nasu da suka duƙufa cin koren ciyawa.

Su kuwa Shatu da Hinde a hankali sukaci gaba da tafiya, sosai tsarin wurin da yanayin shigar suturar dake jikinta yayi tsananin dacewa da ita.
Doguwar rigace irin tamu ta fulani, yadin farine, sai daga samanshi akayi mishi kolliya da zaron huɗu, mai color red white, blue, yellow, and green, wanda aka ƙawata saman rigar da kolliyar zanen ɗawisu, inda daga kafaɗunta har zuwa saman ƙirjinta, duk an shimfiɗa zaren, bisa wuyan rigar mai V.
sai kuma hannun rigar shima duk an zagayeshi da kolliyar,
Kana sai tsakiyar rigar dai-dai kan ƙugunta shima an ƙawatashi da wannan kolliyar ulu irin namu na fulanin daji,
Kana sai ƙasar rigar can itama an ƙawata da wannan zaren.

Sai dogon gashin kanta da yake zube a kafaɗunta, yayinda daga saman goshinta kuma tasa, bandana amman irin namu na fulani mai kalolin ƴaƴan tsakiya, ta zagaye kanta dashi, sai kolliyar da tayi a fuskarta irin ta asalin fulani, a goshinta zanen kan shanu tayi, shaidar cikekkiyar bafulatanace, sai kuma ƙasan lip ɗinta na ƙasa zuwa kan ɗan gemunta shi kuma taja zane da kuma yin ɗigo-ɗigo a gefenshi.
Sai wata kekkewar jakar sakan ulun mai kalolin kolliyar jikin rigarta data rataya a hannun damanta, wanda cikin jakar kuma ruwan shantane a ciki sai sassanyan kinɗirmo da goran zuma, sai ɗan sandar mu ta gado, takalman sawunta irin sau cikin nanne daku mutanen cikin birane kuke masa laƙabi da tashi kabi shanu.
Tayi masifar kyau a cikin wannan shigar tamu ta gado, kyau iya kyau farar fatarta ta baiyana tamkar balarabiya gashin girarta ya konta lib lib.

A hankali suke ɗan tattaki a cikin dogayen saunukan, da koriyar ciyawa da tayiwa ƙasanshi ƙawanya. suna ɗan tafe
Suna ɗan tsinkar ya’yan kanya da gwandar daji da suke cike da wurin Chaɓɓulle wato tsada.

Hadari kuwa sai gamgami yakeyi gabas da yamma kudu da arewa, ko ina yayi dib babu motsin komai sai nasu dana dabobbin su,
Iska ta tsaya cak koda ganye ɗaya baya kaɗawa duhu ya kareɗe illahirin yankin.

A hankali Hinde ta kalli sararin samaniya cikin tsoron ganin gaba ɗaya duniyar tayi baƙiƙƙirin ko ina yayi dib, hakanne yasata ɗan zaro ido tare da cewa.
“Kai Shatu, kalli sama, fa hadarin nan yayi duhu da yawa gsky mu tafi gida”.
Da sauri ta ɗago kanta kana tasa hannunta na hagu ta ɗan kare saman goshinta kaɗan, ware idanunta tayi ta kalli sararin samaniya, wani irin azabebben firgita da tsorone ya rufeta wanda yasa ta juya da azaban ƙarfi ta ruggume Hinde dai-dai lokacin, sukaga wani irin tartsatsin azabebben igiyar…!

 

 

Dan Allah da Manzonsa in dai kin san zaki sayi littafinane ɗan ki fiddashi na roƙeki da Allah da Manzonsa da darajar su. Kada ki saya bana so, ki riƙe kudinki.

 

By
*GARKUWAR FULANI*

️連老

*GARKUWA*

No comments