Breaking News

Jarabta 43


Parking Abba yay yafuto yazagayo ta inda take ya budemata kofa, tama kasa tashi tana mamaki mekuma sukeyi anan ga Khaleel, inane ma nan, hannu Abba ya mikomata yace “sakko” ahankali ta sakko da kafarta dake sanye cikin flat shoe dinta black, maida kofar Abba yay yarufe sanan yafara tafiya tana biye dashi abaya dan dukar dakai kadan Khaleel yayi yace “sannu da zuwa Abba” murmushi Abba yamai ya shiga gaba Abba da Islam na biye dashi abaya ya bude musu kofa suka shiga wani babban falo dayasha kujeru ash color ansa labulaye masu kyau baki da ash, dakin sai kamshi yake ga sanyin ac dayakara karama dakin dadi, ga babban tv bango dake aiki saidai babu kara, zama Abba yay akan kujera har lokacin yana rike da hanunta ya zaunar da ita a gefenshi, karasa shigowa Khaleel yayi yaje zai zauna akasa Abba ya nunamai dayan gefenshi ahankali yazo ya zauna yanadan satan kallon fuskar Islam wacce kanta ke kasa.

Gyara murya Abba yayi sanan yafara da addu’oi ya kalli Islam yasa hannu yaciro bandir din yan dubu daidai a aljihunshi ya ijiye akan jikinta yace “Ummi ga sadakin kinan, dazu aka daura aurenki da Khaleel” da sauri ta dago kai ta kalli Abba jikinta har bari yake murmushi Abba yamata yace “nariga nasan komi, yanzu dai abinda nakeso dake shine kibi mijinki sau da kafa karki manta aljannarki na karkashin kafarshi, Koda wasa karki batama mijinki rai ki kasance mace mai addini, ibada hakuri da jarumta dakuma tsafta, har mahaifiyarki ta koma ga Allah bazan iya tuna randa ta taba batamin raiba” murmushi yadanyi sanan ya mike tsaye, ahankali Khaleel ya mike, hannu Abba yasa ya dagota sanan yarike hannunta ya kamo na Khaleel yasaka hanunta aciki ya Kalli Khaleel yace “ga amanar yata nan nabaka Muhammad ka kular min da ita, Allah ya baku zaman lpy Allah ya albarkaci auren, Abban ka yacemin ran Sunday zaku wuce Abujan ko” Ahankali yace “eh Abba sati daya kawai zamuyi anan” murmushi Abba yay yace “to shikenan ubangiji Allah ya kiyaye yakuma baku zaman lpy ka kular min da amanata na yarda da tarbiyanka Khaleel” murmushi yay yace “in sha Allah Abba” “to masha Allah nabarku lpy” yajuya zai tafi sai alokacin taji wani mugun kuka yazo mata fizge hanunta tayi daga hannu Khaleel da gudu taje ta rungume Abba tabaya tana kuka sosai tace “Abba dan Allah karka tafi kabarni, dan Allah” dan juyowa Abba yayi danba karamin karyarmai da zuciya tayi ba, ahankali ya dagota ya sharemata fuskar tareda sumbatar goshin ta ya girgiza mata kai yace “ai auren kenan Ummi, kiyakuri kinji dole natafi ki zauna da mijinki, haka iyayenmu duk aka musu, take care daughter” alamu Abba yamai da hannu ya riketa hakan yasa ya rikota Abba yajuya yatafi, sosai tafashe da kuka harda majina tureshi tayi ta zube a wajen tana kuka.

Farida takira Khaleel yayi sau goma baya dauka, daga bayama saitaga bata iya kiranshi dan kaman ma yay adding dinta a black list, mutanen dazasu kai Amarya sun gaji da jira suka fara watsewa dai dai yarage daga Mumy sai wasu kawayen ta guda biyu da ita Faridan dake sanye da lapaya ajiki duk tai sukusuku gabanta sai faduwa take idanun nan sun fiffito waje.

Shigowan Abba yasa Mum da Farida suka mike batare daya kallesu ba yace “kusame ni afalo na” yay gaba suna biye dashi abaya, zama yay a babban kujeran shi ya nuna musu waje, kofa Anty Hindu ta bude ta shigo dakin cike da murmushi ta kalli Abba tace “harka kaita kadawo?” gyada mata kai yayi tareda cire hular dake kanshi ya ijiye a saman kan kujera Mum ce tace “Alaji naga kana cire hulane, kiran mutanen nan fa yakamata kayi azo atafi da amarya wanan wani irin abune, ko sai gobe zasuzo ne” wani irin kallo Abba yamata sanan yace “ai anriga ankai amarya tun dazu” batare daya sake kallon Mum da fuskarta ya nuna alamun tambaya ba yacema Farida “zonan” tashi tayi jikinta a sanyaye taje gaban Abba ta zauna, ahankali yasa hannu a aljihun shi yaciro ticket din makka dakuma car key yabama Farida yana murmushi yace “kinga wayan nan duk nakine mota sabuwa, ga ticket din makka wanda ranan lahadi mai zuwa jirginku zai daga ko Faridan babanta” murmushi tama Abba tace “nagode Abba” gyara zama Abba yayi yace “Farida yanda nake sonki haka nakeson Ummi, saisa nake kokarin yin adalci atsakaninku, kinsan hadarin auran mijin dabaya sonka kuwa? Ai yaro kodan gidan kirki ne inhar baya sonka gwara ka hakura dan duk yanda zuciyar shi take dole saiya cutar dakai dan zuciyar nan dakike gani bata da Kashi Farida, ko yayyinki maza Abdallah da Ibrahim wlh bazan taba bari su auri wacce basaso ba sabida nasan zasu cutar da itane” ajiyar zuciya ya sauke sanan ya dafa kanta kaman yanda ake lallashin yaro yace “Farida nariga nasan komi, Khaleel bake yakeso ba Islam yakeso saisa nahada auren shi da ita bawai da wani abu ba, saidan shine abu mafi alkairi agareki, amma yanzu ga ticket dinki idan kinje Umarah kiyi addu’a in sha Allah mijinki na nan zuwa, and Koda banma hadasu aure bayau one way or d other saiya aureta dan Matar mutum kabarin sa, kiyakuri kinji karki bari komi ya tsaya miki arai, aure lokaci ne, wani rashin alherine kinji” gyadama Abba kai tayi tana hawaye, Mummy da duk ranta ya dagule yanzu mezatace ma kawayen ta ta kalli Abba tace “gaskiya Alhaji anzuba sonkai awajen nan, kirikiri shikenan kanuna kafison Islam, yarinya tama Farida kwacen saurayi Kuma ka auramata ha…” tsawa Anty Hindu tamata tace “kwace saurayin gidan ubanwa eh? To bari kiji jiya yaron nan saida na aika aka kiramin shi bayan kun watse kun tafi walimar ku, har cikin falon nan na Abba ya shigo saida nasa shi yafadiman gaskiya, ni tun bayau ba nasan Islam yakeso, Islam yafara haduwa da a garin nan, sanan maganar so baitaba hadashi da Farida ba daga taimako ta likemai, ai har labarin haukan datayi nacin shinkafar bera saida nasamu” takalli Farida dawani mugun ido tace “ba shinkafar beraba ko taliyar bera ce kije kisiyo kici dan uwaki kezaki mutu kafira kinji ko walakiri ya narkeki ehe mara hankali kawai” da gudu Farida ta tashi tafita daga dakin tana kuka, tsaki mum taja tamike tabi bayan yarta, Anty Hindu ta kalli Abba tace “tana dawowa daga Umarah kanemi Yaron kirki mumata aure kafin tajawo mana abin kunya tunda dai zuciyar uwarta ta dauko” ta wuce tafita daga dakin tana masifa, Abba ya girgiza kai wanan yayar tashi hmmm ba’a cewa komi.

No comments