Breaking News

Jarabta 58


Daga Abban Yusuf harna Khaleel jiki asanyaye suka dawo gida kowanne su na zargin mutum dayane amma kasancewa babu proof yasa kawai suka share suka dawo gida.
Da sallama ya shiga part dinta, dakinshi direct yay niyyar wucewa ganin bai ganta a palour ba, daidai ta kofar dakin ta dake rufe yazo wucewa dariyar dayaji tanayi yasa ya mika hannu zai bude handle din tsayawa yay chak batare daya bude kofan ba jin tai dariya tace “ai ingaya miki shinai niyyan kashewa amma na rasa ta yanda zan shiga gidan, kinsan ba shiri nake dashiba idanma na shiga nace mene, saiko ga kanwar matan, kinsan ko lokacin datazo gidanmu nazaci itace yakeso ashe ba itabane kanwartane yakeso, dan naji lokacin dasu Ihsan suke labarin yanda yar ke sonshi kazakaza kaza, shine Ina ganin yar nai instigating dinta sosai, na bata abin nace tabama kanwar tasha kinga ai idan tamutu zai aureta” dariya tasake yi sosai sanan tace “wawiyar ta yarda not knowing fully dat kaina nake taimaka nasan dai yanda yakeson mai kama da Eeeshan nan tunda bansami daman kashe shi ba idan na kasheta kinga ai za’a koma gidan jiya” wani dogon uban tsaki taja tace “ke bata mutu bafa, amma dai rai a hannun Allah dan mutum mutumin ce yanzu, batada amfani” Ahankali yaji tace “hmmmm bazaki gane bane takano, wlh Allah ya jarabce ni dason kaninshi ne tun randa yazo dashi tadi wajena, na fadinma kanin amma shi yama tsaneni haka na auri wanshi Ina dawainiyar sonshi kirikiri sabida ni yadena zuwa yola yanzu ma badadan bikin danshi ba da bazai zoba Kuma wlh bakigani ba ko kallo ban isheshiba saisa nace zan dandanamai azabar rayuwa, zanso yasan yakake ji idan karasa abinda kake mugun so, Kuma Kinga yanda yakeson yaronne shikadai ne namijin shi, ai kinga idan na kashe Yaron koya karashe rayuwan nashi a haukace sabida mutuwar mai kama da Eeshan ainaci riban abinda mahifin shi yamin, yanzu ma idan bata mutuba zansan abinyi” dan dariya tayi tace “to shikenan ki gaidamin dashi idan yafita ki kirani, takano tawa kenan” tai wani uban shewa. Shirun dayaji yasa ya bude kofa ya shiga dakin adan firgice ta kallai tanadan murmushi tace “harkun dawone Alaji?” yafi minti biyu yana kallonta sanan yace “na sakeki saki biyu, ba wanan kadai ba zanje nai filling complain akanki a police station ba Khaleel kadai ba koma waye awanan family wani abu yasake sama keza’azo akama, kije keda Allah” yana fadin haka ya rufomata kofar bam yabuga yawuce, da gudu tabiyoshi har tsakar gida tana bashi hakuri amma ko sauraronta baiyiba saima sake juyowa dayayi yace “kifara tattara yinaki yinaka kibar min gida, karki sake kitafin min da ya” yana gama fadin haka ya shiga mota yabar gidan, ahanya ya kira Abban Khaleel yace “maisa baka taba fadamin halin Mujiba ba, abinda tama” dariya yadanyi sanan yace “Yaya nazaci yarinta ne” murmushi Abba yayi yace “kazo kasaman a office muyi magana”.
[6/25, 2:17 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

No comments