Breaking News

Kanwar Maza 15

P 15

 

Gaba É—aya aka juyo ana kallon ruma, mutanen wurin suka hau dariya.



Shi kansa Jamil da yake ango, da sauri ya ƙara rufe fuksarsa da rawani yana murmushi, dan saura ƙiris dariya ta ƙwace masa.
Adam kuwa sake tsare gida yayi, kasancewar dama can ba mai yawan fara’a bane ba, jin muryar ruman yake a wani abu daban, anya mutum ce?. Kamar zai juya domin ganin fuskarta, sai kuma ya fasa ya sake rufe fuskarsa da rawaninsa, yayi gaba.

Ƙawar Hauwwaliya kuwa É—an zaro ido ta yi ta ce “Ke kin san waye wannan kuwa?”

Ruma ta ce “Ba shine sarki ba?”

“Ba sarki bane ba ai, É—an gidan marigayi Galadima ne da ya rasu, sunan sarki ne da shi, Takawa ake ce masa, wallahi ki ka bari ya kamo ki, sai kin gayawa mutanen garinku, ba ki san yadda muke jin tsoronsa ko a family ba, hmmm su Ummanmu sun girme shi amma tsoronsa suke ji, ba ya wasa da mutane”

Bayan gama jin jawabin da aka yi mat, ta taÉ“e baki ta ce “TaÉ“, na gama yaya umar, ni gani nake kamar na taÉ“a ganinsa ma, ko a ina oho mini dai na manta, so nake na ga fuskar sa”

Dariya yarinyar ta yi ta ce “Ki zo wataran mu je gidansa, ko gidansu sai ki ga fuskar sa amma daga baya zan laÉ“e ke ki shiga” ruma ta kwashe da dariya ta ce “Ke da wasa nake miki, amma dai zan zo wataran a É—anani a doki”

Yarinyar ta dubi Hauwwaliya ta ce “To yaushe zaku kuma zuwa?”

“Ke, ita fa ruma ba a nan unguwar take ba, zuwa ta yi yau zata koma gida, a É—orayi take fa”

“Haba, idan mun zo hawan salla wataran, sai na zo gidanku”

Ruma ta yi murmushi ta ce “Allah ya kawo ki, amma baki gaya mini sunanki ba”

“Sunana Jannah, ke kuma ruma ko?” Ruma ta jinjina mata kai alamar eh.

Ta miÆ™owa ruma ledar viba ta ce “Ga saÆ™onki” ruma ta karÉ“i ledar ta yiwa Jannah godiya, suka tafi gida.

Allah ya taimaketa, Abdallah bai dawo ba sai bayan salla magariba, sannan ya É—auketa suka tafi gida.

Tun a hanya yake tambayarta meye a ledar hannunta, amma tayi mursisi ta rungume ledarta taƙi nuna masa, har suka je gida.

Mama sai da tayi mita “Abdallah ka É—aukar mini ‘ya ka tafi da ita, tun É—azu nake zuba ido in ga ta ina zaku dawo, ka san da wuri take bacci, kun je kun yi dare”.

Abdallah ya ce “Mama wai dama kina son yarinyar nan?”

Mama ta buÉ—e baki, tare da yin murmushi ta ce “Dan Æ™aniyarka in haifi ‘yar a cikina ka ce dama ina son ta, ni duk cikinku waye bana so, ai banda hali irin na ruma son da nake yi mata daban ne, kasancewar ta mace É—aya tilo a cikinku, amma sanin halinta ya sa wasu lokutan nake kamar bana son ta, idan ba haka taÉ“arar da zata yi sai Allah”

Ruma ta ce “Kai ban taÉ“a jin kin ce kina sona ba, ashe idan na mutu zaki yi kuka”

Mama ta ce “Ke rabani da shiririta, tashi ki yi sallar isha’i ki zo ki ci Abincin dare ki kwanta, gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta”.

Ruma ta tashi ta ce “Ai ni yau ba abincinki zan ci ba, na gidan sarauta zan ci” mama ba ta É—au maganarta da muhimmanci ba, sai da ta idar da salla, ta janyo viva, tana firfito da Abinci.
Mama ta matsata da tambaya, ta bawa mama labarin abin da ya faru.

Abdallah ya ce “Wallahi mama ban ma san ta je ba, na Æ™arasa na gaisa da abokaina na tsohuwar unguwarmu, shi ne ta samu ta tafi, yanzu da doki ya takaki ki ce me?”

“Doki bai takani ba, sai abin arziki da na samo, kun ga gidan sarautar nan, wai gidan Turaki, gaskiya suna da kuÉ—i, mama kalli kaza guda ta sako mini, kalli kayan gara, ya ma sunan wannan dunÆ™ulellen abun mai kamar kashi?” Ta yi maganar tana nunowa mama Alkaki, gaba É—aya ko a jikinta, dan ita ba ta ji a jikinta ta yi laifi ba.

Mama zurru kawai ta yi da ido ta na kallon ruma, mama ta gaji da faÉ—a a kan halin ruma, dan haka ta yi shiru ta na faÉ—in Allah ya shirya.

******

Yanayinsa ne ya nuna wa Ammi cewar ya na cikin damuwa.

“Takawar ka lafiya babban mutum, basarake kuma jinin sarakai, me yake faruwa ne?”

Adam ya yi murmushi ya ce “Bakomai Ammi, gajiyar bikin nan ce ta Jamil, kuma kwana biyu ban hau doki ba yau na hau doki, duk jikina ciwo yake”

Ammi ta yi murmushi, a dole wai sai ya É“oye mata akwai abin da yake damunsa, dan haka ta yi murmushi ta ce “Shikenan, ka je ka É—an watsa ruwa ka kwanta ka samu ka huta” ya jinjina mata kai, yana shirin tashi ta ce “Yauwwa Takawa, ni ko tun da ka dawo, ka je ka gaida babarka?”

Take É—an ragowar annurin fuskarsa ya É—auke, ya É—an É“ata fuska tare da girgiza kai alamar a’a.

“To ka san dai yakamata ka yi hakan, bana son Æ™ananan maganganu, tun da yanzu a gajiye ka ke, kuma kana gidan nan yakamata in an jima ko da safe dai, ka je ku gaisa ka ce mata ka dawo”

“To” ya amsa a taÆ™aice.

*****
Mama sai fama take da ruma a kan shirin makaranta, sai laƙai-laƙai take yi, sai ta fara shiri, sai ta tafi banɗaki yawon kashi, saboda ciye-ciye da ta yi, ya ɓata mata ciki. Mama ta kai matuƙar ƙuluwa sai faɗa take yi, ruma kuwa ko a jikinta.

Har ta É—au jaka, sai ga kira a wayar mama.
Mama ta É—aga tare da yin sallama.
“Da ga makarantar su Rumaisa ne, dan Allah idan za ta taho, a haÉ—ota da wani babba daga gida”

A É—an ruÉ—e mama ta ce “Lafiya, wani abun ta yi?”

“A’a, a dai haÉ—ota da wani babba, ko babanta ko wakili”

“To shikenan, babu laifi, za ta taho in sha Allah” mama ta ajiye wayar ta kalli ruma. “Ruma, me ki ka yi a makaranta?”

“Ni kuma? Ni babu abin da na yi”

“Ki gaya mini tun kan raina da na ki su É“aci”

“Wallahi mama ni babu abin da na yi”

“Amma aka ce ki je ke da wani babba, anya ruma ke fa ba gaskiya ki ka cika ba”

Ruma ta ce “Ni dai wallahi na san babu abin da na yi”
Mama ya gyaÉ—a kai ta ce “Ai shikenan, zamu gani”.

Ta Æ™arasa Æ™ofar É—akin ‘yan mazan, ta ce “Waye ba zai fita ba yau a cikin ku? Wani ya zo ya je mini makarantar su yarinyar nan, an kira ni an ce ta je ita da wani”

Yaya Aliyu ya ce “Mai sunan Baba dai ya tafi makaranta, ni ma ina da lectures Æ™arfe goma sha biyu, amma bari na zo mu je na ji menene”

Ita kanta ruma tunani take Meyasa ake neman wani a gidansu a makaranta?

Suna tafe a hanya da Aliyu yana mita “Ke, kawai kin sa an katse mini bacci na, Allah ya sa na ji wani rashin jin ki ka yi, na samu abin duka na zane ki”

Ta tura baki ta ce “Ni dai na san ban yi komai ba, wataÆ™ila ma wani abun arzikin na yi ake nemanku, amma kowa ba ya kyautata mini zato”

“Ruma ai ke abin arziki  bai karÉ“e ki ba, sanin halinki ne ya sanya ake tsoron lamarinki”

Suna tafe a hanya, yara da manya mata da maza kusan kowa ya san ruma, suna tafe ana kiranta ta na É—aga wa mutane hannu, har suka isa makarantar.
Ofishin Headmaster suka je, ruma sai rarraba ido take tana ‘yan ciye-ciyen ta.
Aliyu suka gaisa da Headmaster, ruma ma ta gaida Headmaster ta koma gefen Aliyu ta tsaya.

Headmaster ya kalli ruma ya ce “Waye ya sallameki jiya ki ka tafi?”

Ruma ta sunkuyar da kai ba tare da ta ce komai ba.

Headmaster ya dubi Aliyu ya ce “To, a gaskiya Æ™anwarka ce ko ‘yar ka ba ta jin magana, sun samu saÉ“ani da abokiyar karatunta, an yi musu sulhu amma ba ta ji ba, sun kuma faÉ—a jiya, ta karyata a hannu, kuma ta bita hanya ta din ga jifanta da dutse wai jifan shaiÉ—aniya. To uwar yarinyar nan ta ce ba zata yadda ba, yanzu haka tana division ta kai Æ™ara, suna jiran mu, ka san Æ™abilu wasu lokutan basu da tawakalli ba su san Æ™addara ba”.

Aliyu ya ce”Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ke dan ubanki a garin yaya ki ka karya ‘yar mutane, kuma baki faÉ—a ba?”

Ruma ta zare ido ta ce “Kaii Innalillahi, wannan É—an dukan da na yi mata ne ta karye, zagina fa tayi ta zagi mama, ta dakeni shekaranjiya waccan, amma aka bani rashin…….”

Cikin tsawa Aliyu ya ce”Rufe wa mutane baki, sai ki tashi mu tafi idan kulle ki za su yi ke ki ka jiyo, tashi mu tafi”
Ai ruma ko a jikinta, ta turɓune fuska.

Haka suka tasa ruma a gaba, zuwa police station. Mama sai kiran waya take ta na tambayar meyafaru, Aliyu ya na ce mata babu komai.

Ko da suka je police station, suka tarar da Asiya, an naÉ—e hannu, ga fuskarta duk a kumbure. Ruma ta kalli babar Asiya, kujera ba ta É—auketa ba, sai wani benci aka saka mata ta zauna, fuskarta ta sha uban tsagu kwaya-kwaya.
Ruma ta sunkuyar da kai ta na so ta yi dariya.

Suka nemi wuri suka zauna, wani É—an sanda ya kalli ruma ya ce “Yanzu wannan ce ta karya ta?”

Cikin gurÉ“atacciyar hausa, babar Asiya ta ce “shi ne ya karya É—ana wannan, ke ni ki ka zana a allo, ban fi babarka kyau ba? Ka zana katuwar mace wai ni ne, kuma ka karya mini É—a, wallahi ba zan yarda ba, yaro ba tarbiyya”

Ruma ta ce “Ni fa mace ce ba namiji ba, kuma ita ta cewa babata tsohuwa, kuma wallahi mama ta fi kyau”

ÆŠan sandan ya dakawa ruma tsawa, amma ko gezau ta tsatstsare shi da ido.
Ta tsuke baki, tana cigaba da zazzago madara a hannunta tana sha.

Aliyu ya yi ajiyar zuciya ya yi Æ™asa da murya ya ce “Wallahi idan ba ki nutsu ba, sai na bar ki a wurin nan, su yi miki duk abin da suka ga dama, kuma wallahi matar nan ta zauna a kan ki sai dai buzunki”

Ta waro ido ta ce “Kai dan Allah ka bata haÆ™uri, ai sai na mutu idan ta zauna a kaina”

Aliyu ya gyara murya, ya dubi É—an sandan ya ce “Dan Allah YallaÉ“ai, a yi maganar nan a kasheta a yanzu”.

ÆŠan sandan ya ce “A’a, case É—in a hannun DPO yake, sai kun jira ya zo”

Aliyu  da Headmaster sai bada haÆ™uri suke, Headmaster sai  cewa yake a samu a rufa maganar nan, a rufe case É—in tun da abu ne na yara. Amma babar Asiya ta ce ba ta san zancen ba, sai an biwa ‘yar ta hakkinta.

Aliyu suka É—an fara hira da É—an sandan da yake wurin, ruma kuwa da sun haÉ—a ido da Asiya, sai ruma ta zare mata ido. Aikuwa suka haÉ—a ido da babar ruma, tana zarewa Asiya ido. Aikuwa ta taso tana tafe da Æ™yar tana bala’i, ta yo kan ruma.
Ruma ta zabura ta miƙe, ta haye bayan Aliyu ta na ihu.

“Wanna yaron ba shi da mutunci, ba shi da tarbiyya wallahi sai na yi shari’a da baban shi, ya karya mini É—a kuma yana zare masa ido”

Aliyu ya janyo ruma daga bayansa, ya tankaÉ—ata gaban babar Asiya, ya ce “Ga ta nan ci ubanta tun da ba ta da kan gado”

Ruma ta din ga kurma ihu tana “Na shiga uku, dan girman Allah kiyi haÆ™uri, ki yi mini rai babarmu” babu kunya babar Asiya ta taso tana Æ™oÆ™arin make ruma.

Ganin rashin dacewar abin da babar Asiya ke shirin yi ne ya sanya, ɗan sandan shiga tsakani yana bawa babar Asiya haƙuri.
Ta hau ta din ga bala’i a kan ko sisi ba zata yafe ba, sai an biya kuÉ—in maganin da suka kashe.

Aliyu cewa yake “Dan Allah YallaÉ“ai ka bari ta jibgeta, yadda gobe ba zata Æ™ara ba”

“A’a gara dai a bata haÆ™urin, kar karyayyun su zama biyu”

Ihu ruma take yi tana faÉ—in “Dan Allah babarmu ki yi haÆ™uri, wallahi ba zan Æ™ara ba”

DPO ne ya yi sallama, gaba É—aya hankalinsu ya koma kan sa.

Nan ɗan sandan ya ƙame tare da sarawa DPO.

DPO ya Æ™are musu kallo, sannan ya ce “Sannunku”

Aliyu ya ce “Yauwwa YallaÉ“ai sannu da zuwa”

Ruma ta durÆ™usa har Æ™asa ta ce “Ina kwana”

“Lafiya lau Baby girl, me ki ke yi a nan ba ki tafi school ba, na ganki da uniform?”

Ƙarasowa babar Asiya ta yi, tinkis-tinkis “YallaÉ“ai, shi ne yaro da ya gaya maka jiya, ya karya mini yaro a school”

BuÉ—e baki ya yi, ya na kallon ruma ya ce “Ke, ke ki ka karya musu ‘ya Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ku shigo daga ciki mu yi magana “.

Suka shiga ofishin DPO, ruma sai maƙalewa Aliyu take yi, tana sunkuyar da kai kar su haɗa ido, da babar Asiya.

Tun da suka shiga babar Asiya take mayar da yadda aka yi tana masifa, DPO mamaki yake yadda aka yi ruma ta iya karya wata, ba da abin duka ba da hannunta. Sai da ta gama banbamin bala’inta, sannan ya dubi ruma ya ce “Yarinyar kirki, zo nan”

“Dan Allah ka yi haÆ™uri kar ka kai ni prison” Ruma tayi maganar tana tauna kwakwa a bakinta.

Yayi murmushi ya ce “Ai ba prison zan kai ki ba, magana za mu yi”

“To rantse” kallon ruma suka yi gaba É—aya, wai DPO take cewa ya rantse.

Aliyu ya ce”YallaÉ“ai, dan Allah ka yi haÆ™uri yarinyar ba ta da cikakken hankali, magani ake nema mata”

Ta yi farat ta ce “Wallahi lafiyata Æ™alau”

Aliyu ya kai mata duka ya ce “Ni ne nake yi miki Æ™aryar?”

DPO Ya ce “Na fuskanta, zo ki ji kin ji baby girl, magana za mu yi” Ruma ta É—an matsa gaban teburinsa, amma taÆ™i Æ™arasawa in da yake.

“Garin yaya ki ka iya karya mata hannu?”

Ruma ta ce “Ka na kallon wrestling?”

Ya ce “Sosai makuwa”

“To a nan na koyi Æ™arfi, kuma yayyena fa maza ne, su bakwai ne ni ce ‘yar auta a gidanmu, ina da Æ™arfi sosai, irin yadda shemaus yake yi a wrestling na gwada ban zaci ana karyewa ba wallahi ”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, kun ga kaÉ—an daga rashin fa’idar kallon irin wannan abubuwan ga yara kenan. to meya haÉ—aki da ita ki ka karya mata hannu?”

“Zane ta yi mini a littafina, na yi mata magana ta yaga min  littafi, na rama, shi ne ta din ga zagina, tana yi mini ashar ni kuma bana zagi, ta ce wai babata tsohuwa, shi ne ni kuma na zana babarsu a allo, ta dakeni kuma aka bani rashin gaskiya, ni kuma washegari na rama, ina ga aljanuna ne suka tashi, na yi mata irin na ‘yan wrestling, amma wallahi ban san za ta karye ba, raina ne ya É“aci sosai”

Headmaster da tun da aka zo bai ce komai ba, sai girgiza kai kawai da yake yi, dan ya rasa me ma zai ce, bai taɓa zaton haka rumaisa take ba.

Headmaster ya numfasa ya ce “Yanzu dai tun da sabga ce ta yara, ayi Æ™oÆ™ari a sulhunta kowa ya yi haÆ™uri”

Babar Asiya kuwa kallon ruma kawai take, yadda take bayani da confidence, tana ciye-ciye kuma aka rasa mai tsawatar mata, sai ma nema ake a goyi bayan ruman.

DPO ya kuma kallon ruma ya ce “Matso nan kusa da ni ‘ya ta, magana za mu yi”

“A’a, ba na zama a kusa da maza, Huzaifa ya ce idan ina zama a kusa da maza haihuwa zan yi, kuma korata za ayi daga gidanmu, idan aka koreni kuma ban san in da zani ba, rannan ma Allah ne ya taimakeni, da malam Habibu ya taÉ“a mini hannu ban haihu ba, mama ta ce lafiyata Æ™alau ba ni da ciki”.

ba Æ™aramin dariya ruma ta basu ba, Aliyu ya dafe kai ya sunkuyar Æ™asa, ita ruma ba ta san rufi ba, ko zaka kasheta za ta faÉ—i gaskiya ne”.

Duk yadda aka so yin sulhu, babar Asiya taƙi yarda.

DPO ya ce “Yanzu Madam, so ki ke a kai ku kotu ke da wannan yarinyar jikarki ko kuwa?”

Aliyu ya ce”YallaÉ“ai, ta Æ™irga abin data kashe, in sha Allah ba zai gagara ba sai a biyata”

Sai da ta ji haka hankalinta ya É—an kwanta, ta lissafa kuÉ—i dubu talatin da biyar ta ce a biyata.

Aliyu ya ce”YallaÉ“ai a nema mana sassauci, wallahi yarinyar nan marainiya ce, kuma na gaya maka, tana da matsalar Æ™waÆ™walwa, ana kai ta shan magani, ana ta abin da za a ci ga karatun ta, ga rashin lafiya abun da yawa”

“Wallahi lafiyata Æ™alau, ni bana rashin lafiya sai zazzaÉ“i, ko gudawa, amma dai wataran idan raina ya É“aci sai na ji aljanuna sun tashi, Æ™arfina ya Æ™aru, idan na kama mutum na dunÆ™ule hannu na dinga dukansa ko hmmm ba a magana, da na ce na daina dambe saboda mama ta daina fushi, ita Asiyar ce ta janyo muka yi faÉ—a”.

Aliyu ya ce “Dalla rufewa mutane baki, YallaÉ“ai ba ta da cikakkiyar lafiya”

Headmaster ya ce “Amma ai mu da ku ka kawota makarantar baku gaya mana ba”

Babar Asiya ta dage, ba zata rage ko sisi ba, DPO ya ce zai biya dubu ashirin a aljihunsa, su ruma su biya dubu goma “.

Aliyu ‘yan kuÉ—in registration É—in sa ne da yake tarawa, haka ya biya, suka din ga bada haÆ™uri shi da ruma.

Duk da wannan abu, babar Asiya ba ta huce ba, dan ta so a zane ruma, sai dai bisa ga mamakinta yarinyar sa’ace da ita, babu wanda ya daketa, sai ma nasiha da DPO ya yi mata, yana cewa Aliyu “Ka ga irin wannan yaran, idan aka yi haÆ™uri, suna da É“oyayyiyar baiwa da Allah ya yi musu, da al’umma za iya amafana, ku yi haÆ™uri ku cigaba da kai ta Asibiti tana ganin likita, da sauÆ™i tun da har tana iya zuwa makaranta, sannan ku kiyaye abin da zata din ga kallo”.

“Kaii wallahi ni babu wani likita da nake gani, nifa lafiyata Æ™alau, wato Yaya Aliyu kana nufin ni mahaukaciya ce?” Harar ya watsa mata yana yi mata daÆ™uwa suka cigaba da magana da DPO.

bayan sun fita daga ofishin, Headmaster ya ce ruma ta zauna a gida, sai wani satin sa duba su gani idan zasu iya bari ta cigaba da zuwa makarantar.
Tsalle ta yi tana faÉ—in Alhamdilillah.

Aliyu ya girgiza kai ya ce “Mara hankali kawai”

******
“Takawarka lafiya magajin galadima, Allah ya baka yawan rai, ya ja kwanan hajiya” É—aya daga cikin hadiman Mummy kenan, da ta ware maÆ™ogwaro, take ta zabga wa Adam kirari kamar za ta dungura, maÆ™ogwaronta ko zafi ba ya yi mata.
Hannu ya É—aga mata, ya cigaba da tafiya zuwa cikin falon.

Sanyi A.C ya cika ɗakin, ga ƙamshin turare da ya haɗu ya gauraye falon.

Risunawa ma’aikatan da ke cikin falon suke yi a gareshi, tamkar sun ga sarki.

Jinjina musu kai ya yi, ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon. Ya shafe a ƙalla mintuna takwas, sannan ta fito cikin wata haɗaɗiyar shadda sai ɗaukar ido take yi.

Ta na ganin Adam, ta yalwata murmushin fuskarta ta ce “Hutawarka lafiya takawa, fatan ana lafiya? Kuma ina fatan ba a gaji da jirana ba, ina shiryawa ne”

Girgiza mata kai yayi ya ce “Barka da wannan lokacin”

“Yauwwa barka dai, an dawo lafiya ya ibada?”

“Alhamdilillah”

Ta sake yin murmushi sannan ta ce ‘Ai har na fara shirin zuwa da kaina na kwashi gaisuwa, na ji labarin ka dawo, amma ba ka zo mun gaisa ba, kuma har aka yi bikin gidan Turaki aka gama ban ganka ba, ko jikin ne?”

Ya É—aga idanuwansa ya kalleta, amma bai bata amsa ba.

“Well, kun haÉ—u da Mahmud kuwa?, yazo gari shima ya kusa komawa ma, ya dawo lokacin kana saudiyya”

“Dama zuwa na yi na gaishe ki, and a gayawa su Fauziyya ba na son yawan fitar nan” yana kaiwa nan a maganarsa ya miÆ™e, ya fara takawa sannu a hankali.

Murmushi ta yi ta bi bayansa da kallo. “A zahiri mutum har mutum, amma baÉ—ini ba wanda ya san cikakken waye, kamar bil adama kamar kuma wani abu daban, da ni ki ke zancen Binta, sai na rabaki da komai sai na tabattar da na huce a kam abin da kk ka yi mini” ta yi maganar a hankali tana bin bayan takawa da kallo.

Ya kai tsakiyar falon, Mahmud ya buɗe ƙofar ya shigo, ganin junansu ya sanya suka yi turus, suna musayar kallo, kamar abokan gaban da suka yi shekara da shekaru ba su haɗu ba sai yau.

LITATTAFAN DA NA RUBUTA SUN HAÆŠA DA.

ABDULJALAL (FREE BOOK)
AƘIDATA (BOOK1 FREE 2 PAID)
WATA KISSAR SAI MATA (FREE)
WUTA A MASAƘA (FREE)
RUƊIN ƘURUCIYA (BOOK1 FREE 2 PAID)
GABA DA GABANTA (1FREE 2 PAID)
ƘANWAR MAZA (1FREE 2 PAID)

Mai buÆ™ata ni zai tuntuÉ“a ta lambata Please, a din ga biya kan a karanta, in kin sai littafi baki faÉ—i ba, atleast kin taimaki marubuciyar da bata Æ™warin gwiwa 

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haÉ—a 1k subscribers a channel É—i na ba, anya akwai amana kuwa*

Taku har kullum
Ayshercool
08081012143
[24/07, 7:43 pm] JAKADIYAR AREWA:                     *ƘANWAR MAZA*

 

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHEƘI TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haÉ—a 1k subscribers a channel É—ina ba, anya akwai amana kuwa*

Ku yi subscribing  YouTube channel É—in
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro

No comments