Breaking News

Kanwar Maza 17

P 17

 

 

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*


*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHEƘI TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haÉ—a 1k subscribers a channel É—ina ba, anya akwai amana kuwa*

Ku yi subscribing  YouTube channel É—in
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.

*Ina yiwa ‘yan uwa musulmi barka da shigowar, sabuwar shekara musulunci, Ubangiji Allah ya sada mu da alkhairan da yake cikinta, akasin haka kuma Allah ya iya mana*

 

Shiru ta yi ta kasa cigaba da maganar, ta zuba masa ido ta na jiran ta ji mai zai ce.
Ya tako a hankali ya zo gabanta ya tsuguna, ya na kallon idonta. Cikin sauri ta sunkuyar da kan ta ƙasa, tana jin yadda abincin da ta ci ya tsaya mata a ƙirji, ga wani irin ƙugi da cikinta yake yi mata saboda tsoro.

“Aure ko, shi ki ke so?” Da sauri ta girgiza masa kai alamar a’a.

“Ki je ki dawo daga makarantar, za mu yi magana in dai aure ne baki da matsala, za’a aurar da ke tun da shi ki ke so” da sauri ta É—ago, ta kalleshi za ta yi magana, amma ya sanya yatsansa a kan leÉ“ensa ya ce “Shhh, tashi ki wuce ki tafi makaranta”
Kamar wadda aka gayawa mummunan saƙo, jiki babu ƙwari ta bar gidan ta tafi makaranta, sai dai kamar ta faɗi a hanya, dan jefa ƙafarta kawai take yi, maganar mai sunan Baba ta tsaya mata da yawa.

***
Samha ce zaune a kan gado, hannunta riƙe da waya, ɗaya hannun kuma tana wasa da gashin kanta, amma hankalinta ba a kan wayar ba, zancen zuci take yi.
Ƙarar buɗe ɗakin ne ya dawo da ita hayyacinta.
Fauziyya ce ta shigo, ta ajiye jakarta ta zauna a kan gadon, ta dubi Samha ta ce “Ke jiya ki ka shanya ni ina jiranki, amma ki ka Æ™i zuwa”
Samha ta É—an lumshe ido, ta buÉ—e tare da ajiyar zuciya.

“Ke wai meye haka ne?”

“Ke bari kawai”

“Ban gane in bari ba, kin san ba ma ‘yar haka da ke, explain kawai madam”

Samha ta dubi Fauziyya ta ce “Jiya na je mun haÉ—u da gayen nan fa”

Fauziyya ta waro ido wace ta ce “Ki na da hankali kuwa? Mutumin da baki sani ba ki ka je wurin sa?”

“Eh tare da security na je, sai dai ban bari ya sani ba, kin san waye ma tukuna?”

“A’a, sai kin faÉ—a”

“Khalifa Usman wakili”

“Meye haÉ—inki da shi? Ko ya na ciki ne?”

Samha ta yi tsaki ta ce “Ke ba wannan ba, wai yayi bincike a kaina, so yake na taimaka masa ya kai takawa Æ™asa, saboda yana barazana ga feature É—in sa, da mahaifinsa”

Fauziyya ta zaro ido ta ce “Yaya Adam dai?”

“Shi fa”
“To me ki ka ce masa?”

“Fauza, kin san ina son Adam, ba zan goyi bayan a cutar da shi ba, dan haka nace masa ba zan iya ba, kar kuma ya sake nemana”

“To meyasa?”

“Fauza yayanki ne fa, kuma kin san abin da yake zuciyata game da takawa”

Fauziyya ta jinjina kai ta ce “Na san yayana ne, amma ke yanzu haryanzu ki na nan a kan bakanki kina son sa, ana barin halak dan kunya fa”

“Ke ki ka san ta, ita halak É—in, bari na shiga wanka” ta yi maganar tana miÆ™ewa.

ÆŠan shiru Fauziyya ta yi, ta fara zancen zuci ‘wannan ai wata damar ce ga Mummy, tabbas Khalifa wakili zai yi wa mummy amfani’ da hanzari Fauziyya ta tashi ta fice daga É—akin.

***
Yau wunin ranar ruma ba a hayyacinta take ba, duk ta rasa abin da yake yi mata daÉ—i. Allah ya taimaketa mai sunan Baba bai dawo ba sai dare, tun da ya dawo ta rasa sauran nutsuwarta, tana jiran mai zai ce mata.
Sai da ya gama abin da yake, har ta kwanta ta fara bacci, ta ji ana dukan gefen katifarta.
Gabanta ne ya faÉ—i da ta yi tozali da shi, ta tashi zaune tana rarraba ido.
Da hannu yayi mata nuni da ta fito ta biyo shi.
Haka ta fito ya na gaba tana baya, zuwa tsakar gida.
Ya ja kujera ya zauna, ita kuma ta zauna a ƙasa tana sunkuyar da kai.

“ÆŠago ki kalleni” ya faÉ—a a kausashe, amma ta kasa ta sake sunkuyar da kanta Æ™asa.

“Aure ki ke so ko?” Nan ma ba magana sai girgiza kai.

“Shikenan, na fahimta na baki nan da kwana uku, ki kawo wanda zaki aura É—in, ranar juma’a in Allah ya kaimu sai a yi miki auren kowa ya huta”

Da sauri ta É—ago ta kalleshi, “Wallahi yaya ba haka nake nufi ba, wallahi ba aure nake so ba”

“Ƙarya ki ke yi, baki da aiki sai zance da tambayoyin batsa, aure ki ke so”

“Wallahi a’a, ban san batsa nake tambaya ba”

“Na gaya miki, sai kin fito da miji, ranar juma’a za a É—aura miki aure”

“Wallahi bani da saurayi, saurayina bai sanni ba”

“A ina saurayin naki yake?”

“A cikin tv nake ganinsa, É—an wrestling ne, amma ban san a ina yake ba”

Mai sunan Baba ya kalleta ya ce “To tun da baki da saurayi, ni zan nemo miki, ba har da mafarki ana bikinki ba, to saÆ™onki ya isa za ayi abin da ki ke so”

“Wallahi yaya ba haka nake nufi ba”

“To ya ki ke nufi? Da kunnena fa na ji ki na cewa, ayi miki aure ayi addu’a ki yi tsawo ayi miki aure, tukuna ma me ake yi a auren da ki ke son auren?”

Cikin kuka ta ce “Wallahi ban sani ba”

Ya sake tsuke fuska ya ce “Ƙarya ki ke yi, sai kin gaya mini ko na taka cikinki a wurin nan”

“Wallahi ban sani ba, ‘yan ajinmu na islamiyya dai sun ce ana soyayya, kuma ina son in ga an sai mini kujeru da kuma sabuwar katifa”

“Wace irin soyayya?”

“Wallahi ban sani ba, na ji dai suna cewa, soyayya ta na da daÉ—i, kuma ana soyayya idan an yi aure, shi ya sa nake son na yi saurayi na ji me ake a soyayyar, amma wallahi ba aure nake so ba”.

Ya yi ajiyar zuciya ya ce “Shikenan, yanzu dai tun da baki da saurayi, ni zan samo wanda nake so na aura miki, tashi ki je ki kwanta, ranar juma’a É—aurin aure”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan girman Allah ka yi haÆ™uri, manya ake yiwa aure ban da yara”

Cikin zafin rai ya ce “Ni zaki gayawa abin da zan yi, tashi ki bani wuri” jiki na rawa ta tafi É—aki, tare da fashewa da kuka.
Gaban mama ta je tana kuka ta ce “Mama dan Allah ki saka baki, wai aure mai sunan Baba zai yi mini”

“To ai haka ki ke so ruma, Allah ya sanya alkhairi, duk wanda ya zaÉ“a miki shikenan”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan Allah mama ki saka baki, wallahi wasa nake yi, ni ba da gaske nake ba wallahi”

Mama ta ce “Maganarku ce ke da shi, babu ruwana, ni gafara nan na kwanta, gobe in Allah ya kaimu na tafi kasuwa na fara yi miki sayayya”

Mama tayi kwanciyarta ta bar ruma, kuka wiwi kamar ba gobe, haka ruma ta din ga yi, ƙarshe a nan wurin bacci ya kwasheta.
Da safe kuwa wasan ɓuya aka shiga yi tsakaninta da mai sunan Baba, taƙi yadda su haɗu, ko karyawa ta kasa yi, haka ta tafi makaranta.

Ruma fa gaba É—aya hankali ya tashi, ta rasa nutsuwa ko maganar kirki ba ta iya yi, tamkar wadda wani mummunan abu ke shirin faruwa da ita.
Mama tana kallonta, abinci sai dai ta cakala idan ta É“uya sai kuka, duk ta rasa sukuni.
Mama ta shiga banɗaki ta lallaɓa ta ɗau wayarta, ta kira Abubakar.
Yana É—agawa ta fashe masa da kuka, har sai da gabansa ya faÉ—i “Ruma, menene? Meyafaru?”

“Yaya, mai sunan baba ne”

“Me ya same shi, me ya yi miki?”

“Wai aure zai yi mini, dan Allah ka yi masa magana, mama taÆ™i hana shi, dan Allah ka ce masa ni yarinya ce, dan Allah kar ayi mini auren nan bana so”

Cikin rashin fahimta ya ce “Wani irin aure kuma?”

“Haka ya ce wai ranar friday zai mini aure da wani, dan Allah ka hana shi”

“Kwantar da hankalin ki ‘yar gudaliyar, zan kirashi in sha Allah, ki daina damuwa”

“A’a ba zan iya dainawa ba, ka kirashi yanzu kawai”

“To an gama, kiyi haÆ™uri babu mai yi miki wani aure yanzu”.

Ya yi ta kwantar mata da hankali, har ta samu ta É—an nutsu.

***
Yana zaune a falo, yana duba labarai a wayarsa, Mummy na gefe tana shan fruit, ta kalli yadda ya sha fararen kaya, da shuɗiyar alkyabba hannunsa ya sha zobbunan azurfa, sai kaɗa ƙafa yake a hankali.

Ta yi murmushi ta ce “Ka ga kyan da ka yi kuwa? Sai ka fito a basaraken ka na asali jinin galadima, Allah ya kawo gingimemiyar kujera”

Bai kalleta ba ya ce “wace irin kujera ce gingimemiyar?”

“Ka gaji Galadima mana, ko ma kujerar garin gaba É—aya”

Mahmud ya ce “Mummy you are funny, ni fa sabgar sarautar nan ba ta dameni ba, ki bar ni da karatuna, na kammala na samu aikina period, shi dai da yake ta zazzare ido, na san bai wuce a kan sarautar ba, sai ya je yayi ta yi”

Cikin mamaki ta kalli Mahmud ta ce “Mahmud, wai kai meyasa ba ka da kishin zuci ne, sarautar nan fa taku ce, ta mahaifinku ce gaba É—aya a ka É—auka aka kai wani gidan, kuma muna saka ran za ta dawo mana, tun da galadiman yanzu shi ma yana can babu lafiya, kuma da zarar ya mutu babu batun wani ya gaje shi, tun da duk ‘ya’yansa mata ne, Jabir kuma bai isa ya saka rai ba, dole gidan nan za ta dawo. Dan haka ba zan zuba ido a bawa Adam sarauta bayan ga ka ba, kai ma É—an galadima ne, dan haka kai ma ka cancanci ka gaji sarauta”.

Mahmud ya É—an yi shiru ya na tunani, amma bai ce komai ba.

“Mahmud, kar ka watsa mini Æ™asa a ido, idan ba haka ba, haka fa zamu cigaba da zama Giwar Galadima ta mamaye komai, ta cigaba da juyamu yadda take so, yaka ke gani idan sarauta ta dawo Adam ya samu, kai menene naka, a wani babin ka tashi?”

Ajiyar zuciya Mahmud ya yi, ya fesar da iska daga bakinsa, ya kalli agogon hannunsa sannan ya kalleta ya ce “Mummy, zan je salla daga nan zan É—an shiga gari, sai na dawo” yana gama maganar ya miÆ™e a hankali ya bar falon.

Fauziyya da ke laÉ“e take jin su ta fito, ta nufi wurin Mummy ta zauna tana murmushi ta ce “Hajiya Mummy, mai abubuwan ban mamaki, irin wannan famfo haka?”

Mummy ta yi murmushi ta ce “Ai ba ayi komai ba ma tukuna, dole sai na sakawa Mahmud Æ™awazucin kujerar nan, yaron nan akwai baÆ™in taurin kai, É—an uwan É—ayan ne a taurin kai, tun da Æ™uruciya nake kwaÉ—aita masa daÉ—in mulki, amma yaÆ™i ganewa, amma zan cigaba da gwada masa fa’idar ace mulki yana hannunsa, in sake rura wutar Æ™iyayya a tsakaninsa da Adam, kuma in toshe kafar da sarautar za ta dawo gidan nan, dan ita ma Hajiya Lubabatu kwaÉ—ayi take na ta É—an ya gaji sarautar idan mahaifinsa ya mutu”
Fauziyya ta jinjina kai ta ce “Mummy kenan, akwai lissafi, na zo miki da wani labari ne mai daÉ—i”

“Wani labarin kenan?”

“Khalifa Usman wakili, kin san case É—in su da takawa, kusan shi ne yake trending a media yanzu”

Mummy ta jinjina mata kai.

“To dai in gaya miki shi ne ya gayyaci Samha, wai yana son su haÉ—a kai, su kawo Æ™arshen yaya Adam, ita kuma ta ce bata yadda ba, kin san son shi take yi”

“Eh, na sani, ai itama Samha wata makami ce da nake amfani da shi ta Æ™arÆ™ashin Æ™asa, amma labarin nan yayi mini daÉ—i sosai, ke dai ku cigaba da baza kunnuwa, duk abin da ku ka ji, ko kuka gani kawai ku sanar da ni”

“In sha Allah Mummy, Allah ya ida nufi”

Suka yi murmushi gaba É—aya.

Takawa ne zaune a wani ƙaton falo, mai ɗauke da kayan ado na gidan sarauta, gefe gud kuma tarin litattafai ne a jere a cikin wata drower.
Ya sanya system a gaba, yana dannawa yana É—an juyi a jan kujerar da yake kai.
Jabir na zaune a kan kujera yana facing É—in sa. Jabir ya tattara nutsuwartsa a kan Adam ya ce “Takawa, kana bibiyar shafukan sada zumunta kuwa?”

“Meyafaru?”

“To ai gani na yi ka yi burus, kamar baka bibiyar meke faruwa”

“Shi ya sanya na tamabayeka, meyafaru?”

“Tone-tonen da ka ke Æ™oÆ™arin yiwa Senator usman wakili, akwai Æ™ura fa sosai da sosai”

Ya É—an É—ago ya kalli Jabir ya ce “Ai ni Æ™urar nake son ta tashi, ta hana kowa nutsuwa, saboda haka nake wannan aikin”

“Duk da haka, ko dan tsaron kannka da lafiyarka, yakamata ka san yadda zaka din ga gudanar da ayyukan ka, taÉ“a manyan nan ba abu bane ba sauÆ™i ba fa”

Adam ya yi murmushi ya ce “Na fahimce ka mutumina, kar ka wani damu, ka tayani da addu’a kawai, amma dole mu yi wa Æ™asarmu hidima”

Jabir ya jinjina kai ya ce “Haka ne”.

***

Bil haƙƙi mai sunan Baba ya nunawa ruma aure zai yi mata, ya je ya a sayo sabuwar katifa ta ‘yan makaranta, ya ce wa mama gata nan a ajiye ta ruma ce, ya sayo kwano da kofin silba mai murfi da sabuwar buta, shi ma ya ce na ta ne.
Hakan ya ƙara dugunzuma hankalinta, cikin dare mama ta na bacci ta ga ruma tana shimfiɗa sallaya tana kuka.

Mama ta ce “Ke lafiyarki kuwa?”

“Sallar dare zan yi, na roÆ™i Allah a kan mai sunan Baba, tun da kin Æ™i ki hana shi, an rasa wanda zai hana shi yi mini aure”.

Mama ta yi murmushi ta ce “Ke fa ki ka ce kin ji kin gani, ki yi addu’a kawai Allah ya baki zaman lafiya da ke da wanda zai aura mikin”

Zaman dirshan ruma tayi, ta É—ora hannu a ka tana kuka, mama ta rufe fuska tana yi mata dariya ba tare da ta sani ba.

Ruma ta daÉ—e a sujjada tana addu’a, sannan ta koma ta kwanta.

A islamiyya kuwa, malamin ajin da take ne, ya lura yana ƙari tana kuka, dan yanzu a ɗan samu cigaba, ta daina guje-gujen aji, a babban aji da ajin su Yasir take zama, kuma yanzu tana iya karatu ba kamar da ba.

Sai da ya kammala Æ™arin Alqur’ani, sannan ya kira ruma yana tambayarta me ya sa take kuka?
Ba ta gaya masa ba, ta ce mai babu komai, ƙarshe sai ƙyaleta yayi.

Ranar juma’a kuwa da farar safiya da kuka ta tashi, dan yau ne kwanakin da mai sunan baba ya É—ibar mata suka cika, ba tare da ta samu wanda za ta kawo ba, a matsayin wanda take so, to ita wa ma take da shi.

Mama sai fama take da ita ta shirya ta tafi makaranta, amma ta rungume uniform É—in tana kuka.
Umar ya fito fuska a haÉ—e ya daka mata tsawa, cikin tsuma ta hau saka kayan ba tare da ta yi ko wanka ba.

“Ki fice ki tafi makaranta, idan kin je can sai ki yi musu kukan, shi ne ki ka gayawa É—an uwa wai zan yi miki aure ko? To shi ma bai isa ya hanani abin da na yi niyya ba, ai ke ki ka nuna ki na son auren, wuce ki bawa mutane wuri”

Kamar korarriya, ta É—au jakarta ta tafi makaranta.

Bayan fitarta, mama ta kalleshi ta ce “Babana, a sassauta mata ta horu haka, kwanaki uku kenan ba ta ko cin abinci, ayi mata afuwa babana”

“Ƙyaleni da ita, horata kawai nake, amma yau zan Æ™yaleta in sha Allah”

Ƙin shiga makarantar ta yi, ta tsaya a waje tana kuka, mai gadi ne ya ganta, ya ja ta ya kaita ofishin Headmaster, ya sanar masa da a waje ya ganota ta tsaya ta na kuka.

Headmaster ya ce “Ai ni rigimar yarinyar nan nake tsoro, ke me aka yi miki?”

“Yayana ne ya ce zai yi mini aure yau”

Waro ido ya yi ya ce “Aure kuma? Waye zai kwasa? Ke bana son wasa”

“Wallahi haka ya ce”

Headmaster ya kalli ruma, sai ya kawo ko rashin hanklin ruman ne ya motsa, dan haka ya ce “To shikenan, ki yi haÆ™uri ki tafi aji, zan kira gidan na ku mu yi magana da su” yayi ta lallaÉ“a ruma ya kaita aji.

Ba ta sake tsinkewa da lamarin ba, sai da ta dawo gida ta tarar mama tayi tuwon shinkafa da miyar taushe, da wainar masa wai azo a kai maÆ™wabta ace na auren ruma ne, mai sunan Baba ya ci farar shadda ya fito tsakar gida ya ce “Mama, idan an idar da sallar juma’a za a É—aura mata aure, sai ayi mata addu’a”

“Na shiga uku, mama wai da gaske ne? Mama ku yi mini rai ban isa aure ba wallahi”

Wani mugun kallo ya yi mata, ta shige É—aki da gudu tana kuka, ya fice ya bar gidan.
Dariya Huzaifa ya din ga yi mata yana “Ruma, Allah ya sanya alkhairi zan kawo miki goron É—aurin aurenki har gida ki tauna, dan mijin naki ma tsoho ne, malam labaran ladan ne”

Ruma sam ba ta shiri da malam labaran ladan, saboda ya taÉ“a tsula mata carbi, wataran yana kiran salla, ta taÉ“a tsayawa a Æ™ofar masallaci tana  kiransa da Æ™arfi, wai saboda muryarta ta fito a sufika, ya idar ya kamata ya zane ta da carbi, gashi tsoho sosai.

Mama ta shiga É—aki ta tarar da ruma sai rizgar kuka take.

“Haba amarya, ya da kuka kuma kamar ba amarya ba?”

“Dan Allah mama ki bani kuÉ—in mota na gudu”

Mama ta kwashe dariya ta ce “Dama ruma akwai abin da zai baki tsoro haka?”
Rungume mama tayi cikin kuka ta ke faÉ—in “Dan Allah mama kar ayi mini aure, wallahi na daina rashin ji, ina sonki sosai, bana son na rabu da ku, mama zaki yadda a aura mini wanda ya dakeni dan Allah mama ki hana shi aurar da ni”

Rungumeta mama ta yi tana murmushi, tausayin ruma ne ya kamata, dan har ramar dole ta yi, saboda damuwa.
Mama ta zubo mata abinci, ta zaunar da ita ta bata, amma ruma taƙi ci.

Mai sunan Baba suka yi sallama, duk suka shigo a tare daga sallar juma’a, duk sun sha kwalliya.

Aliyu ya ce “Amarya kin sha kuka, to Allah ya sanya alkhairi” ta rirriÆ™e mama tana girgiza kai tana zubar da hawaye.

Mama ta kalli mai sunan Baba ta ce “Tuba muke babana, Allah ya bada haÆ™uri duk ta rame, ayi haÆ™uri”

Yasir ya ce “Haba mama, ya zaki yi mana haka?”

Mama ta yi masa daƙuwa tana harararsa.

Umar ya ƙarasa gaban ruma da ta takure a jikin mama, tana share hawaye.

“Kalleni” yayi maganar yana tsareta da ido.

Ta É—ago a hankali ta kalleshi, idanunta sun yi jawur.

“Daga rana mai kamar irin ta yau, idan na sake jin ki aikata wani abu na rashin mutunci, ko wannan shegen surutun naki, to ki tabattar aure babu fashi, kin ji na gaya miki?” Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana sake rungume mama.

Mama ta ce “To madalla godiya muke, Allah ya rayaki, ya kaimu auren ki na gaske, da miji na gari ko?”

“Ni ba zan aure ba, bana so da ma da wasa nake, kuma ba zan auren ba”

Mama ta ce “Tashi ki yi godiya, tun da dai ya janye maganarsa”

“Na gode” tayi maganar tana É“oye fuskarta.

Tashi yayi ya bar É—akin ba tare da ya ce mata komai ba, ta din ga sauke ajiyar zuciya ta ce “Amma an shiga hakkina, Allah zai sakawa marainiya”

Yana tsaye a bakin ƙofa, karaf maganarta a kunnensa.

(BOOK 1 FREE NE, BOOK 2 PAID, BOOK1 YA KUSA KAMMALA IN SHA ALLAH, GODIYA TA MUSAMMAN GA MASU BIBIYAR LITTAFIN ƘANWAR MAZA)

Ayshercool
08081012143
[29/07, 7:26 pm] JAKADIYAR AREWA:                    ƘANWAR MAZA

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

No comments