Breaking News

Kanwar Maza 34


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI’IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA’A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA’IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA’IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin*

*5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.  Supplements na karin ni’ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.  Supplement na whitening/glowing skin*

*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau’in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

 

 

 

Sha tara ya ce “A’a sule, ka san yadda mu ka yi da su barde, ka É—an Æ™ara haÆ™uri, bana son fitina ta shiga tsakaninmu da su ne”.

“Wallahi na tsani yarinyar nan, iskancinta yayi yawa, tun da na fara harkar nan ban taÉ“a haÉ—uwa da É—an rainin hankalin da yake abin da ya ga dama ba irin ta”.

Banza ruma ta yi masa, kamar ba ta san me yake cewa ba, ta rungume jariri ta cigaba da kuka, ji take ina ma tun kan ta san Aisha suka kasheta, wani irin so da tausayin jaririn nan suka rufeta, haka yake tik jikinsa babu kaya.

Sule kuwa a Æ™ule ya ce “Yanzu haka zamu cigaba da zama wannan É—an tayin yana cika mana kunnuwa, uban me zamu ba shi?”.

“To ba ita ta ga zata iya ba, sai ka Æ™yaleta ai”.

“Amma mun riga mun yi da su a kan cewa zamu kashe yaron nan, yanzu me zamu ce musu?”.

Sha tara ya ce “Ai babu lallai su dawo, ko ma zasu dawo kan su dawo É—in zamu san abin yi”

Sauran matan wurin babu yadda ba su yi ba, a kan ruma ta bayar da jaririn su tayata rarrashinsa, amma ta ce ba zata bayar ba, dan bata yarda da kowa ba, gashi ɗan ruwan da take ɗaɗɗaka masa ya ƙare.

Haka dare yayi, salla idan zata yi, sai ta bayar a goya mata shi, jaririn yana kuka ita ma tana kuka, gwanin ban tausayi.

Dare yayi sosai, amma ruma tana tsaye, tana aikin jijjiga yaron nan, sha tara ya kalleta ya ce “Wannan Yarinya da gani irin maita ce, kalli dan Allah dan bala’i yaro ya hanata bacci ya hana mutane sukuni, amma taÆ™i bari a kashe shi, sai wahala take yi, shegiya taurin kai kamar jinjirar jaka”.

Sule ya ce “Ko kuma kafuran farko ba, wallahi da ka barni da saina harbesu su duka, kowa ma ya huta”.

“Ƙyaleta dai tukuna, mu ga iya gudun ruwan barde”.

Haka ruma ta shafe awanni ta na fama da yaron nan, ta roƙi su sha tara su bata ruwa ta kuma bashi, amma suka ce ba zasu bayar ba.
Sai da yayi mai isarsa, sannan ya yi shiru, ta koma wajen bishiyar da Aisha ta mutu, ta jingina tayi shiru tana tuna yadda suka yi ta hira daren jiya, amma yanzu wai babu ita a doron duniya sai É—an ta. A haka wani É“arawon bacci ya kwashe rumaisa.

****

“Yaya Jamil, ya jikin takawa kuwa?” Samha ta yi maganar tare da tattara hankalinta a kan Jamil.

“Ya ji sauÆ™i”.

“SauÆ™i sosai dai, ni fa na tsorata da yanayin da na ganshi a ciki, kaga abun da yayi wa iman kuwa?”

“Kenan kune ku ka je ku ka ce yayi shaye-shaye yayi yinÆ™urin yi wa iman fyaÉ—e, kun sanya ‘yar mutane a wahala jikinta ya rikice”.

Waro ido samha ta yi ta ce “Mu kuma? Yaushe? Wallahi ni ban faÉ—a ba”.

“To yaya aka yi wannan banzan zancen mara ma’ana ya fita, ke kin san dai takawa ba ya shaye-shaye, idan ma kin yi haka ne dan cimma Æ™udurinki, ba zai aureki ba, ke ma kin san ko da aure bai haramta a tsakaninku ba, amma a al’adance takawa ya haramta a gareki a yanzu dan haka tun wuri ki shiga hankalinki, kuma ki nemi wani a manemanki ki yi aure ki huta, ko kuma ki cigaba da dakon soyayyar sa a banza da babu abun da zata amfana miki”.

Shiru Samha ta yi, ta san babu tantama makircin Mummy ne da Fauziyya.

“Kun fara wuce gona da iri, ina bin ku ne don kawai na ga in da ku ka dosa, amma kina zaÆ™ewa hajiya Jamila ” tayi maganar a zuciyarta.

“Ai kai Jamil wataÆ™ila idan ka gaya mata ta ji, tun da ni ban isa na gaya mata ba, tun wuri na ce ki fita a sabgar yaron nan, komai ki ke yi ba kya gabansa, amma ki nace samha kamar shine autan maza, yaron nan bashi da mutunci ko kaÉ—an, ni kaina uwarku wani gani-gani yake mini, amma daga ke har Jamil sai wani shishshige masa ku ke yi”.
Jamil ya ce “Mama, kin san halinsa yana iya Æ™oÆ™arin sa wurin mu’amalantar kowa yadda ya dace, amma tare muka taso, dan haka bashi da wasu abokai sai mu, tun da duk tsatso É—aya muke, wannan yarinyar ce dai idan har bata shiga hankalinta a kan sa ba, zata cigaba da shan wahala ne”.

Zumɓura baki Samha ta yi, ta tashi ta bar ɗakin, dan babu mai gaya mata ta ji, in dai a kan takawa ne, son sa ma yanzu ta fara.

***
Da sallama takawa ya shiga É—akin ammi, in da iman ke kwance a kan gadon ammi, ta rufe rabin jikinta da bargo, Nusaiba na ta jera mata sannu.
Yana shigowa suka Æ™ara nutsuwa suna gaishe shi, ya amsa musu sama-sama, ya Æ™arasa gaban gadon ya ce “Iman, ya jiki?”

“Da sauÆ™i yaya” ta amsa a sassanyar muryarta.

Yayi Æ™asa da murya ya ce “Am sorry, duk laifina ne abubuwa suke ta faruwa a haka, amma dan Allah ki yi haÆ™uri kin ji, bana son wani abu ya sameki, ba zamu iya jurewa ba, ki mayar da komai ba komai ba, sannan ki toshe kunnenki a kan duk abin da za a faÉ—a”.

Ta jinjina masa kai ta ce “Ina sha Allah yaya, kuma kar ka damu, in sha Allah komai zai wuce ne”.

Ya ce “Ina fatan hakan, ga jabir can yana son yayi miki sannu, taso mu je falon”.

Ji ta yi kamar ta ce a’a, amma ta san ba ta isa ta ce a’a É—in ba, dan haka ta É—au hijjabinta ta saka, Nusaiba ta rungumo iman suka fito falon tare.

Sai dai da suka fito, takawa ya tarar da Samha a falon a zaune.

Basarwa yayi bai ko nuna ya ga samha ba, Jabir kuwa ya kafe iman da ido kamar maye.

Samha ta gyara zamanta cikin iyayi ta ce “Yaya ya Æ™arfin jiki?” Ya É—ago ya kalli Samha, ya É—an Æ™ura mata ido, amma bai ce komai ba.

Nusaiba ta ce “Uncle J ina kwana?”.

“Lafiya lau, ya gida ya Ammi?”

“Ammi na lafiya, ta fita ne”.

Jabir ya mayar da idonsa kan Iman ya ce “Iman, ashe baki ji daÉ—i ba, ya jikin?”

Cikin yanayinta na rashin son magana da kuma Æ™osawa ta ce “Da sauÆ™i”

“Allah ya baki lafiya autarmu, duk na kasa sukuni tun da aka ce mini jikinki ya motsa, amma na yi mamakin da na ganki a gida, takawa ba za a kaita asibiti ba?”.

“Eh na za a kaita ba, amma tun da ha ka ka zo, sai ka kaita?”.

“Kar ka gaya mini magana mana, daga tambaya, dole na tuhumi yadda ake nema ayi sake da lafiyar auta”. HaÉ—e rai iman ta kuma yi, ba ta ce komai ba, dan gaba É—aya ta Æ™osa da zaman.
Samha kuwa da zancen iman ya fara Æ™ular da ita, ta yi gyaran murya ta ce “Takawa duk ka rame wallahi”.

Jabir ya ce “Ba dole ba, ya sanya tunani da damuwar a ransa, gaba É—aya ya koma wani iri”.

Samha ta din ga zubo zance, amma takawa ya ƙi kulata, ya kashingiɗa yayi musu shiru.

Iman ta ce “Ni dai zan koma É—aki jiri nake ji, sai anjimanku”.

Takawa ya kalleta ya ce “Ko na mayar da ke É—akin?”.

Samha ta yi zumbur ta tashi, ta nufi iman ta na faÉ—in “Haba dai, gani a zaune, bari na rakata tun da jiri take ji” sai da gaban iman ya faÉ—i, sam ba ta so haka ba, dan ta san da biyu ta ce zata kaita É—aki.

Ta rungumi iman, ta nufi sashin Ammi da ita, iman ta ce “A’a É—akina zan koma”.

Samha ta ce “Bakomai, bari na rakaki” tayi maganar kamar gaske.

Sai da suka shiga ɗakin iman, sannan ta taƙarƙare, ta hankaɗa Iman kan gadon, ba tare da tausayin halin da iman ɗin ke ciki ba.
Ta murtuke fuska ta ce “Ke ‘yar tsintuwa, kalleni da kyau, ya muka yi da ke?”.

“Anty Samha me na yi miki?”.

Cikin Æ™ulewa Samha ta ce “Ke fa tsohuwar munafuka ce, kullum na yi magana sai ki ce mini, ke babu komai a tsakanin ki da takawa, amma kullum cikin naniÆ™e masa ki ke, ko abun da ake faÉ—a É—in gaske ne, kina kai masa kanki?”

Iman ta yi shiruu, zuciyarta na yi mata wani irin zafi, amma ba ta da bakin magana, ‘yar tsintuwa ce kamar yadda Samha ta faÉ—a.

Maganar samha ce ta dawo da ita hayyacinta, “Wallahi idan ki ka cigaba da shishshige wa Adam, sai na sa kin yi dana sanin zuwanki duniyar nan, sai na mai da ke matacciya da rai, sai na yi miki illar da ba kya zato, ki kiyayi adam ki daina yi masa shishshigi idan ba haka ba zan aikata abin da na faÉ—a, banza mai kyan banza ‘yar tsintuwa, ke ban da abinki ma, har kina tunanin haÉ—a jiki da jinik sarauta Æ™asÆ™antacciya irinki, da babu wanda yake da taabbcin ‘yar halak ce ke, Æ™ila ma ‘yar gaba da alfatiha ce”

Duk yadda Samha ta din ga yi wa iman baƙaƙen maganganu, ba ta tanka ba, tayi ta gama ta fita. Sai da ta fitan sannan iman ta bawa hawayen idonta damar zubowa.

Tana tsaka da kukan baba uwani ta shigo É—akin ” ‘yar auta ya jikin naki?”.

Iman tayi maza ta rufe idonta kamar tana bacci.

Ta leƙa fuskar iman, ta ga idonta a rufe, cikin sanɗa ta koma gaban mudubin ɗakin iman, ta hau laluben mukullin drower mudubin iman.

A hankali iman ta buÉ—e ido tana kallon baba uwani, tare da tunanin binciken me take yi mata a É—aki haka.

Tari tayi tare da Æ™oÆ™arin gyara kwanciyarta, ta buÉ—e idonta tana kallonta, nan da nan baba uwani ta diririce, ta fara kame-kame “Amm..amm…’yar auta dama idonki biyu ne? Dama na ce bari na zo na yi miki sannu, sannan na É—an tattare miki É—akin”.

Iman ta ce “Bakomai baba uwani, ai gyaran É—akina ba aikin ki bane ba, ke da ki ke a kitchen, kuma ga hadimai, an gyara É—akin da safe karki damu”.

“To..to…toooo shikenan, Allah dai ya baki lafiya iman, Allah ya yaye miki ya baki lafiya, bari na koma kitchen É—in” ita da iman ta bita da kallo, ba ta ga alamar gaskiya a tare da ita ba.

***
Cike da wata irin mummunar faÉ—uwar gaba, rumaisa ta farka daga baccin da ya É—an É—auketa, ta ga jaririn nan dai yana rungume a jikinta, idonsa biyu sai cin hannunsa yake, kai da gani babu tambaya ka san yunwa yake ji.

Tana É—aga ido ta hango barde a kan babur shi da wani, sule na ganinsa ya ce “Yauwwa dama kai muke jira”.

Su ka yi parking ɗin baburin, barde ya sauka hannunsa riƙe da leda.

Ya ƙurawa rumaisa ido, ya nufi in da take, ya durƙusa a gabanta, ya saka hannu ya ɗaga zanin da jaririn ke ciki, ya kalli yaron. Bai yi magana ba ya ga ruma tana zubar da hawaye.

Bai ce mata komai ba, ya kwance mata ledar gabansa, koko ne da Æ™osai a ciki, sai madarar peak guda biyar ya ce “Gashi nan, na ga da ki ka yi rashin lafiya kina ta amai, wataÆ™ila har da ulcer, ga madara nan ga kuma abinci ki din ga kula da abinci, in anjima zan aiko yarona da abinci, ba a samo waina a in da ake sayo miki ba”.

Maimakon ta yi masa godiya cikin kuka ta ce “Aisha ta mutu fa, jaririnta ne wannan”.

“Na sani, ita tata ta Æ™are, Allah ya karÉ“i shahadarta”.

“Shikenan haka zan ta zama a nan wurin sai wahala ta kasheni? Ku baku kasheni ba, ku baku sakeni ba”.

“Ke, ki mayar da hankali ki ci abinci na ce”.

“Ba zan ci ba, ka kwashe tsiyarka” kallonta ya yi a fusace ya ce “Ni ki ke gayawa haka?”

“Eh É—in” sai kuma ta É—an yi shiru ta ce “ka yi haÆ™uri dan Allah, na gaji ne ban san a halin da mama da yayyena suke ciki ba, na gaji da zaman wurin nan, dan Allah a tunaninka abin da ku ke yi É—in nan kun yi mana adalci, kalli fa jaririn nan, ya rasa mamanshi an haife shi a tsakiyar daji, ko kaya babu a jikinsa fa, ga yunwa yana ji, kalli wurin kwananmu, yau a kashe wannan, gobe a wulaÆ™anta wancan ya kuke so mu yi? Galibinmu fa duk talakawa ne, ba ‘yan masu kuÉ—i ba”.

“Kin san meyasa nake ta baki kariya kar a kashe ki?” Ta girgiza masa kai.

Ya ce “GyaÉ—ar da ki ka bani a kasuwa, ki ka ce idan ina da ‘ya’ya in kai musu, na gaza samun tsaro a Æ™asata, a kan idona na rasa iyayena, da ‘ya’yana biyu da yunwa ce ta kashe É—aya, saboda hare-haren ‘yan ta’adda bana iya fita samo musu abun da zasu ci, aka sace É—an uwana, sai da na sayar da komai nawa domin karÉ“o shi, aka kashe shi, shiyasa da aka yi mini tayin wannan harkar ban ji ko É—ar ba na karÉ“a na shiga, idan ya so duk ayi mutuwar kasko, kuma na samu Æ™warin gwiwa ne, tun bayan da na san iyayen gidanmu su ne tsaro a Æ™asar nan….. Sule ne ya kaste barde ta hanyar cewa “Kai fa nake jira mu yi magana, ya za ayi ka karÉ“o mana jaririn nan mu kashe shi, mun riga mun yi wa mutanen smoke wannan alÆ™awarin, yarinyar nan ta Æ™eÆ™ashe Æ™asa ta hana yaron nan, ina tsoron muyi mata illa, mu saÉ“a waccan yarjejeniya da ke tsakaninmu da ku”.

Barde ya kalli rumaisa, sannan ya kalli sule ya ce “Kar ka damu, gobe zamu kawo muku mutanenku, ku bamu ita, mai gida da kansa zai zo wurin nan”

Sule ya yi murmushi ya ce “To madalla, ai hakanma yayi”

Suka cigaba da tattaunawa, ruma kuwa ta samu wata ledar pure water, ta zuba kokon nan a ciki, ta zazzaga madara, ta dinga bawa jaririn nan.

Haka nan yaron nan ya din ga shan kokon da ruma ke ɗura masa, ba ta san ya ƙoshi ba, sai da ya din ga kwarara amai ta hanci ta baki.

“Rumaisa ya zaki bawa jaririn kwana biyu koko, ai sai ki ja masa wani abun” cewar wata dattijuwar mata.

“To baba ko in baki shi ki shayar da shi ne? Idan ban bashi koko ba mai zan bashi, da ma aka samu kokon, tausayinsa nake ji, da mamansa na nan, da ya samu sauÆ™in wani abun, ka yi haÆ™uri ka ji yarona, Allah ya kula mini da kai, ya jiÆ™an anty aisha” tayi maganar tana zubar da hawaye tana goge masa aman da yayi da zanin da yake ciki.

Bayan tafiyar barde, sule ya cewa ruma “Sai ki gode Allah, gobe zasu bamu mutanenmu dan su karÉ“eki, mu kuma a goben zamu kashe ki, ba zamu basu ke ba”.

Duk da tsiwar da ruma take yi musu, a kan su kasheta, sai da gabanta ya faÉ—i jin ya ce gobe zasu kashe ta, to yaya jaririn nan zai kasance kenan? A zahiri kuwa ko gezau ba ta yi ba, sai cigaba da gogewa jaririnta amai da ta cigaba da yi.
Azabar galabaita ta sanya yaron ko kukan kirki ya daina yi, sai dai yai kaɗan yayi shiru, ga wani irin numfashi da yake yi, iya ƙirjinsa kai da gani ka san ba shi da cikakkiyar lafiya.

Yau tun da garin Allah ya waye, bayan rumaisa ta yi sallar asuba, ta zubawa wurin da suke zama ita da aisha ido,, sai wasi-wasi take yi, tayaya jaririn nan zai rayu? Ance kasheta za ayi, waye zai kula da ɗan ta san dai ƙarshenta shi ma kashe shi za su yi, ga wata irin soyayyar yaron da ke ratsa zuciyar rumaisa.

Tana zaune a gefe, tana saÆ™awa taan warwarewa, ta ji tamkar ta tashi ta gudu, amma ta san da ta gudu zasu harbeta, sun ce yau za su kasheta, amma ta ga cikinsu babu wanda ya saurareta. Sha tara ne ma ya dubeta yana dariya ya ce “Duk shirin tafiyar ne na ga kin nutsu, sai ki bi masoyiyyar taki, Æ™arshen Æ™auna har É—an naku ms zamu haÉ—a mu turo muku ku ci soyayya” tsaki tayi ta kawar da kanta gefe. Ya din ga Æ™yaÆ™yata mata dariya.

Sai dai wunin ranar ya shuɗe barde bai dawo ba, balle ta san matsayarta, peak ɗin nan ta dinga zubawa a pure water tana ɗurawa jariri, sai dai duk girman nan nasa ya sace, fatarsa ta fara yamushewa, idanun jaririn suka yi yellow, ga zafi da jikinsa yake ɗauka, ga fatar jikinsa duk ta yi alamar ƙarancin jini da oxygen, idan jikin nan nasa yayi zafi, sai dai ta saka shi a gaba, tayi ta uban kuka, ba ta taɓa tsammanin cin karo da ƙalubale mai girgiza zuciya irin wannan ba.

A kwana na huÉ—u, tun safe sule yake masifa, ya ce idan har barde bai zo ba, sai ya kashe rumaisa, saboda ya riga ya sanar da mutanen smoke cewar ya kashe rumaisa da jaririn nan, babu babban abun da ya sake girgiza rumaisa, irin yadda suke commanding É—in ‘yan uwan aisha su kawo musu kuÉ—i, kuma da alama masu hali ne, dan miliyan ashirin suka caza, kuma sun haÉ—ata, suna ta yi musu kwatancen in da zasu kai kuÉ—in, gobe da yamma.

Rana ta karya ta kusa faɗuwa, rumaisa ta jiyo ƙarar babura da yawa, tare da harbe-harbe.

Duk da ba yau ta fara jin Æ™arar bindiga ba, amma ta É—an razana, take ‘yan bindiga suka zagaye su ruma, suka saita bindigoginsu, da shirin ko ta kwana suna saka ran idan jami’an tsaro ne, su kashe kowa a wurin.

A ƙalla sun kai babura goma duk sanye da kayan sojoji, sai dai fuskokinsu duk a rufe, sai manyan makamai da suke riƙe da su.

Suka yi parking baburan, suka sassako, sai a lokacin su sule suka nutsu, suka sauke makaman, kasancewar sun gane ko suwaye.

Barde ne ya fara buÉ—e fuskarsa ya ce “To yaya, kun shirya ayi musayar ko kuwa? Kun tattauna da iyayen gidan naku?”

Sule ya ce “Ai ba yau muka yi da ku ba, tun bayan kwanaki uku baya muka yi, amma ka saÉ“a alÆ™awari”.

ÆŠaya daga cikin mutanen ne, ya tako a hankali zuwa gaban sule ya tsaya nesa kaÉ—an da shi ya ce “Rumaisa zaka bani kawai, maganar mutanenku, ma yi daga baya”.

Sule ya dube shi a fusace ya ce “Amma ka raina mini hankali, ba zan bayar da ita ba, kuma a yanzun nan zan kashe ta, yarjejeniyar ta watse, a cigaba da faÉ—an tsakaninmu, ko mu….

“Shhhhhh, ka san da wa ka ke magana kuwa?” Mutumin ya katse sule.

“Ban damu ba ko kai waye, yau zan kasheta kowa ya huta, na gaji da yi muku biyayya ina saÉ“awa iyayen gidana”. Ita rumaisa mamaki ne ya kamata, duk a kanta ake wannan taÆ™addamar, shi kuma wannan mutumin ko a ina ya san sunanta oho.

Sule ya nufi ruma gadan-gadan, sai dai kan ya ƙaraso gawarsa ta faɗi a gaban rumaisa, tare da watsuwar jininsa a wurin mutumin nan ya harbe shi. Ware ido ruma ta yi jiki na rawa take kallon gawar. Kan kace kwabo, sun fara harbe-harbe a tsakanin su, sai dai mutanen sule na ta ƙoƙarin su harbe rumaisa kawai.
Sauran mutanen da suke tare da rumaisa, sai ihu suke yi, mutanen da suka zo a babur, suna kama su, suna ta É—aurewa.

Mutumin da ya harbe Sule ya kalli ruma ya ce “ÆŠauki yaron ki tashi ki tafi”.

“In tafi ina?”.

“Koma ina ne, ki tashi ki bar wurin nan kawai, saboda ke na zo” ya Æ™arasa maganar yana sauke takunkumin fuskarsa, wa zata gani, mutumin nan da ya bata kaza a hanyar zuwansu katsina.

Kan tayi magana ta ga ya saka bindiga ya harbe Barde, ya furta ‘Kai ma amfaninka ya Æ™are”

Sake gigicewa ta yi ta ce “Na shiga uku, meyasa zaka kashe barde, ya taimakeni sosai, meyasa zaka yi haka, ta nufi gawar barde tana kuka.

Fincikota mutumin yayi ya ce “Rumaisa, ki tafi na ce, mu a irin wannan aikin namu, babu tausayi ko sanayya, barde yana da alaÆ™a da iyayen gidan su sule, yarona ne, shi ya yi mini kwatancenki na ganeki, na shirya yadda zan kuÉ“utar da ke, da ya karÉ“eki kin zama mallakinss, ko kina so ki rayu da É—an ta’adda babu aure?” Cikin tsuma ta girgiza masa kai.

“Dan haka maza ki bar wurin nan, na san yanzu za a kawo musu É—auki, Allah ya tsare” tsyawa ta É—an yi tana kallon gawar barde, da ke yashe a wurin da aisha ta mutu.

“Ki tafi ko in kasheki da hannuna!”

A hankali ta juya, ta É—au hanya, hannunta rungume da jariri, É—anyen goyo.

AYSHERCOOL

*₦paid book ne, 500 via 0009450228 aisha adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143*

 

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI’IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA’A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA’IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA’IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin*

*5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.  Supplements na karin ni’ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.  Supplement na whitening/glowing skin*

*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau’in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

 

 

 

 

No comments