Breaking News

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 2

_~*✊BOSS LADIES WRITERS✊*~_

*KURKUKUN ƘADDARA*

 

_The Prisoners 2_

*Daga alƙalamin Hafsat Bature*


~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

 

 

Bayin Allah su Batul zullumi da fargabar Halin da Angel zata shiga Ya hana su runtsa a daren ranar, A É—akin tsohuwa Tamira su ka zazzauna saman floor, zuciyarsu na harbawa da faÉ—uwar gaba, Sun yi shiru kowa da a bun da ya ke saÆ™awa acikin ranshi. Deeja ce tai Æ™oÆ™arin tunasar dasu akan su yi mata addu’a. Su ka amsa mata da toh, nan fa kowan nan su ya soma karanto addu’o’in da Angel ta koya ma su.

Dare ya nutsa sosai Azeeza tuni ta koma bacci, a saman ƙirjin Gabriel ta kwantar da kanta, Hannun shi na dafe da bayanta kamar zai mai da ta cikin sa.

Jemimah tana a kwance saman cinyoyin Batul ta ƙi yin bacci, ba yadda ba su yi da ita ba akan ta runtse idon ta ta yi bacci amma ta kafe akan sai Genie ɗinta ta dawo, a ƙarshe ma da su ka matsa mata sai ta sanya masu kuka, Tsananin tausayinta ne ya kama su, Haris yace ku bita a hankalin ni banga laifin ta ba, saboda ita yarinya ce ta saba kwana rungume da Angel dole taji ba daɗi, Rarrashin ta ya kama ta mu yi, Amsa mashi su ka yi da toh, atare su ka haɗu suna rarrashin jemimah daƙyar su ka shawo kanta.

Parveen sai hammah ta ke yi Ga yunwa ga Bacci, Naufal da ke zaune a gefenta Yace da ita Ki kwanta ki yi bacci mana, Kin ishe ni da hammah” harara ta É—an jefa mashi tare da cewa”in yi bacci fa ka ce? Sai kace bansan ciwon kaina ba, Ta ya zan iya runtsawa bayan yan uwar mu tana acikin kurkuku….” ta6e la66ansa Yai”Naji daÉ—i da ki ka yi Hankali” bata tanka mashi ba sai ma É—aura kanta da ta yi asaman laps É—inshi.

“Batul mu tashi mu bi Genie mu É—auko ta” Muryar Jemimah ce ta yi maganar Fuskar ta ta yi sumtum saboda kukan da tasha, Lallashinta Batul ta yi” Ki yi haÆ™uri kin ji, In sha Allah zata dawo Cikin Mu, Badajimawa ba,” Zumbura ba ki ta É—anyi “Toh idan ta dawo zamu gudu ko”? gaba É—aya hankalinsu Haris ya dawo kanta

Murmushi Batul ta sakar mata”Eh mana da zarar ta dawo zamu gudu mubar kurkuku….” tunkan ta kai Æ™arshen maganar Jemimah ta katse ta da cewa”Zamu koma gidan daddyn Genie Ko? In da zamu sakata mu wala mu yi rayuwar mu babu takura Allah yasa genie É—in mu ta dawo da wuri na Æ™osa muje inga gidan daddyn ta”

farin cikin da su ka gani akan fuskar jemimah a yayin da ta ke yin maganar yai matuƙar karya masu Zuciya, Har sai da suka ji hawaye sun cika idanuwansu, cikin rauni na murya Deeja tace da ita

“Jemimah Pray for Her! Tana buÆ™atar addu’ar mu, mu dage da yi mata addu’a har sai ta dawo Cikin mu” jinjina kai jemimah ta yi tare da cewa”tom zan mata addu’a” ta ambaci hakan tare da lumshe idanuwanta, acikin zuciyarta tana ambaton Ya Allah ka dawo min da Genie É—ita in dai kana son farin ciki na….”

“Gabriel Ka tada azeeza ta tashi Mu haÉ—u mu duka wurin yi mata addu’a ba yadda za’ae muna acikin tashin hankalin nan ita tana bacci, ko dai jemimah da ta ke Æ™arama a cikin mu ta kasa runtsawa balle ita” Rubina ce ta yi maganar, Girgiza mata kai Gabriel yai alamar Bazai tayar da ita ba

“I’m sorry to say I can’t wake her I don’t want to worry her, Just Let her sleep.” É—aure fuska Rubina ta yi jin a bun da yace, ita haushinta yadda suka tashi hankalin su akan Angel amma ita Azeeza ta lafe jikin shi Hankalin ta kwance ta ke sharar bacci.

“Akwai matsala fa! Dare Yana Æ™ara nutsawa babu alamun Angel zata dawo” Sarah ce ta yi maganar tana daga zaune Ta jingina bayanta jikin bango, Ta saki dogayen Æ™afafuwanta Æ™asa.

“Duka yaushe ta tafi da har za ki fara tunanin akwai matsala! Pls mu yi mata fatan Alkhairi, Ni gajan haÆ™uri ke bana so” acewar Haris.

To jama’a abu fa kamar wasa A Æ™alla Angel ta É—auki tsawon awanni babu ita babu alamarta, Idanuwansu sun kaÉ—a sunyi jawur dasu ga bacci ga yunwa ga zullumin rashin ta atare da su, sun dage sai addu’a Su ke Yi mata, Ba zato ba tsammani Hasken ÆŠakin su ya gauraye ko’ina, ta jikin Æ™ofar É—akin tsohuwa da bata Æ™arasa datsewa ba su ka hango hasken da ke kurÉ—aÉ—owa, Hankalinsu Ba Æ™arami tashi yai ba, A kiÉ—ime su ka mimmiÆ™e tsaye hatta Azeeza da ke bacci sai da ta farka tana faman murza idanuwanta da yatsun hannayenta.

kallon kallo suka shiga jefawa junansu fuskokinsu É—auke da matsananciya damuwa
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un;’ shine kalmar da ta fara fitowa abakunansu Deeja, Yayin da su ke a tsaitsaye cirko cirko, Bakomai ne ya tayar masu da hankali ba face ganin Safiya ta yi ba tare da Angel ta dawo ba. Nan ta ke ransu ya basu cewar wani abu ya faru da Æ´ar uwarsu……………..

Shine meke Faruwane ata 6angaren Angel!?

Ai tun lokacin data watsa da gudu ta nufi Cikin kurkuku, Sautin kururuwa
Mai ƙaraji da gurnani ya cika kunnuwanta, ga wani azababben San yi da ya addabe ta, kamar jaura ta gifta Cikin duhu ta ke gudu

Adai dai lokacin da ta ɗaura ƙafarta saman ground floor ɗin nan Inda ke kewaye da dogayen benaye Ba zato Ba tsammani idanuwanta su ka sauka akan ƙafafuwan Tsohuwa Zafreen Lamarin yai matuƙar gigitar da ita, sam Ba ta yi tsammanin Zata ci karo da wani abu ba ita kawai ta sanyawa ranta cewa Danish ne kaɗai mutumin da zata haɗu da shi.

Mummunar faÉ—uwa gabanta yai, Æ™irjinta ya hau bugu da Æ™arfi da Æ™arfi A firgice ta É—ago da idonta akan tsohuwa zafreen da ke a ruÆ™e da sanda, Kasancewar Filin Yana da Fitilu masu haske can saman silin ya gauraye ko’ina, daga Æ™asa har sama shigar Jajayen kaya ne a jikinta kamar kullum Fuskarta na asanye da takuntumi.

“Ya Allah saida nayi addu’a kafin in fito but why na fara Cin karo da mummunar tsohuwar nan Ina lillahi…..” acikin zuciyarta ta ambaci hakan, Kafin ta yi wani yunÆ™uri tsohuwa Zafreen ta soma tunkarota sautin takalmanta Æ™was Æ™was har cikin dodon kunnan Angel, Duk ta ku É—aya idan ta yi sai gaban Angel Ya faÉ—i, tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba.

Ko da ta ƙaraso gabanta, Bata tanka mata ba, Sai bin ta da tayi da wani matsiyacin kallo irin na marasa imani, Shuɗayen idanuwanta sun Ciza launinsu.

“Ban yi mamakin Ganin ki ba Unaisah! Ina ji arai na ba yau ba ne rana ta farko da kika fara Æ™etare Iyakar Ki, Taurin kan ki da kafiyar ki da kuma rashin tsoron ki su ne suka Æ™arfafa maki gwiwar shigowa Cikin prison! Ko a tarihi ba a ta6a samun prisoner É—in da ya ta6a Æ™etare Iyakar shi ba sai Akan Ki”!

Magana ta ke yi muryarta na fita da sauti mai amo.

yawu Angel ta haɗiya, tuni tasha Jinin jikinta, Ido ya raina fata sam ta kasa magana, Zufa sai tsastsafo mata ta ke yi kan fuskarta har ɗiɗɗiga ta ke a ƙasa.

“Ko za ki Iya faÉ—a min menene Ya fito da ke? Kuma Ta yaya akai Kika tsaga bangon É—akin ku kika fito”? Muryar Angel na rawa ta soma magana”Tsautsayi ne da Æ™addara, dan Allah kada ki cutar dani, Zan koma inda na fito, Kawai Inason ganin É—an uwana Danish ne shiyasa na fito neman shi…..” kasa Æ™arasa maganar ta yi sakamakon sautin Dariyar tsohuwa zafreen da ya tari numfashinta.

Tsagaitawa ta yi da yin dariyar, ta soma matsawa tana ƙara kusanta kanta da Angel, A tsananin tsoroce Angel ta ke Ja da baya tana girgiza mata kai

“Tun jiya dana shigo É—akin ku Raina ya bani cewar Wani abun ku ke shiryawa kuma ke ce jagora a cikin tafiyar, Saboda prisoners basu da wayan da zasu Iya ta6uka wani abu, Unaisah ke ce Æ™warin gwiwar su, Babban kuskuran da ki ka aikata shi ne Æ™etare Iyakarki! Hakan Ya sa6awa dokar Kurkuku! Na yi imanin babu mai Iya Æ™watarki daga hannu na! Saina rushe duk wani sashe na Jikin Ki da ke da Æ™arfi zuwa mai rauni……” Zazzare ido Angel ta yi tamkar Æ™wayar zata faÉ—o Æ™asa Jikinta sai kerma ya ke yi.

“Kin jama kan ki bala’i da masifa! Not only u! Hatta Ƴan uwan ki da Ki ka baro É—aki, suna cikin masifa, Zanje gare su Bayan na gama da ke, duk saina tarwatsa farin Cikin da ku ke da shi” Muryarta a kausashe ta ke furta maganar.

Hawayen da su ka taru a cikin idonta ne suka soma gangarowa saman kuncinta da wani irin rauni na murya ta furta”duk horon da za ki yi mani kada ki haÉ—a da Æ´an uwana, Ni ce mai laifi don haka Ni za ki hukunta”

Fuskar Tsohuwa Zafreen a murtuke ta jinjina kai tare da cewa “Umarni ki ke Bani? In yi abunda kike so”? A ruÉ—e Angel ta girgiza kai ba tare da ta iya furta mata komai ba.

“Zan jaraba Ki inga idan zaki Iya ceton Kanki, Nasan baki ta6a shaÆ™ar Æ™amshin mutuwa ba amma yau zansa ki shaÆ™eta sosai, waÉ—annan Idanuwan naki launin ruwan toka yau zansa su koma launin Ja, Hawayen da ke fito wa ta cikinsu zansa su janza launi zuwa na Jini, La66an ki da su ka saba gaya wa Mutane magana Ayau É—in nan zan canza masu kamannin…..” Hankalin Angel idan yai dubu to ya tashi tarasa gane inda kalaman tsohuwa Zafreen suka dosa.

Ja da baya tsohuwa zafreen ta soma Yi yayin da ta ke sakin Shu’umin Murmushin nan nata na tantiran Ƴan duniya waÉ—anda su ka ga jiya su ka ga yau

Juyawa Baya ta yi tare da nuna ma Angel Third floor da sandar hannunta

“ÆŠan Uwan ki da ki ke nema Yana a hawa Na Uku, Za ki Iya zuwa gare shi, Fatan Nasara” Kalmar Æ™arshe da ta furta mata kafin Ta buga sandar hannunta Æ™asa, Nan ta ke hayaki Mai kamar an watsa tiya gas Ya cika idanuwan Angel, bata Iya ganin komai amma taji aranta cewa tsohuwa Zafreen ta 6ace daga wurin da ta ke a tsaye, a hanzarce ta kamo sunan Allah taci gaba da ambaton duk wata addu’a da tazo bakinta, Cikin Æ™ankanin lokaci Æ™urar ta washe Idanuwan ta suka dawo dai dai. A lokacin ta riga ta yanke shawarar komawa É—akin su gurin Æ´an uwanta saboda gudun kada tsohuwa zafreen ta cutar mata dasu kamar yarda ta furta mata cewa zata je gare su, A hautsine Ta juya da niyar tabi hanyar da ta 6ullo don ta koma É—akin su, Rass gaban yai mugun faÉ—uwa ganin babu corridor É—in kwata kwata kamar ba’a ta6a yinta ba, Yawu ta haÉ—iya zuciyarta na harbawa da sauri da sauri tamkar zata faso Æ™irjin ta.

A fujajen ta mayar da dubanta ga dogayen benayen da tsohuwa Zafreen ta faÉ—a mata cewa É—an uwanta na anan A hankali ta ke tafiya tana tunkarar benan Yayin da ta ke cigaba da karanta addu’o’in neman tsari a cikin bakinta, firgita ta yi sakamakon Jin sautin shessheÆ™ar kukan Su Azeeza a cikin kunnanta, ta ko’ina sautin kukansu ne kamar zasu zautar da ita, Tunawa da barazanar da aka yi mata acan lokaci na farko data ta6a shigowa prison yasa ta yardarwa kanta cewa ba kukan su bane Anayi ne don a tsoratar da ita, hakan yasa ta samu Æ™warin gwiwa, Watsawa ta yi da gudu ta Haura saman benan Har ta yi tsakiyarshi Taji ya soma motsawa Matakalarshi ta dinga komar da ita baya kamar dai yadda ya faru a jiya, Gudu ta dinga yi tana haurawa, wata uwar zufa ta wanke fuskarta, daÆ™yar ta samu ta haye saman Second floor.

Numfashi taja tare da fetsar dashi, sai faman yin haki ta ke yi, Tsawon mintuna takwas kafin taci gaba da tafiya tana bin hanyar, wani abu daya Æ™ara rikitar da ita, Ginin wurin ya dinga canza mata hanyar da take bi, Sai ta yi nisa taga an dawo da ita Baya, hakan ba Æ™aramin gigitar da ita yayi ba. Tarasa ina zata dosa, Tamance ma hanyar da zata bi ta isar da ita hawa na Uku, tana Cikin yin tafiyar kamar zautacciya ita kanta batasan inda ta ke jefa Æ™afafuwanta ba, Cikin rashin sa’a ta faÉ—o cikin wani É—aki.

Idanuwanta basu sauka a ko’ina ba sai akan wasu tsoffin mata da ke agaban manyan tukwanan girki, An É—aura su saman murhu Wuta sai Ci ta ke, Hannuwansu ruÆ™e da ludayi Suna Juya naman da ke a cikin Tukunyar girkinsu, Gabanta ne ya faÉ—i ganin Naman mutun yatsun hannun da ta gani ne cikin romar miyarsu ya tabbata mata da cewa Naman mutunne su ke yi. farfe sun shi.

Basu lura da ita ba sai da ta daddage ta kwatsa ƙara Mai sautin gaske silar hakan Ya janyo hankulansu ga kallonta, zaro ido waje ta yi ganin sun ganta, a kiɗime ta manne ma bango ɗakin, jikinta sae kerma ya ke yi Tamkar a mafar ki ta ke kallon su.

Halittarsu gwanin ban tsoro Munanan gaske, ga Uban tamoji tamojin akan fatar fuskokin su, kamar jijiyoyin jikin bishiya ƴan rigunan da ke sanye a jikin su launin Ja Kamar yar shara ta maza da su ke sanyawa, Ga uban gashi a hammatocinsu sai ɗoyi suke Yi. a ƙalla sun kai su Shida, uban fason da ke a tafin ƙafafuwan su kamar Kwanannar Fura da ta bushe ta tsastsage.

Kamar mahaukata haka suka fashe da dariya mai sautin gaske Muryoyinsu ne suka Cika mata kannuwanta.

“Laah ga Unaiserh Ta kawo mana ziyara, yau zata sha farfesun Ƴan Ci ki, Zonan Unaisah Yarinyar mu, Zo ki sha roman nama”

La66anta na kerma ta furta”Bazanci ba, Ni ba wurin ku nazo ba, Dan Allah Ku Æ™yale ni In tafi….” Tun kan ta Æ™arasa maganar É—a ya daga Cikin tsoffin ta É—ebo farfesun a cikin ludayi hada Yatsun hannun mutun, tunkaro Angel ta yi tare da miÆ™a mata Ludayi” Kar6i nan Æ´ata ki sha Roman Farfesun Mutun akwai daÉ—i” Tashin zuciya ne ya farma mata, a matuÆ™ar firgice ta juya tana Æ™oÆ™arin buÉ—e Æ™ofar É—akin don ta gudu, sai dai kash Æ™ofar ta Æ™i buÉ—uwa.

Fashewa ta yi da matsanancin ku ka tamkar ranta zai fita, da hannu ta dinga Bugun ƙofar kamar zata 6alle ta ko motsi ƙofar ba ta yi ba har sai da tsoffin nan suka cimmata, Ta ƙarfi Suka zaunar da ita tare da rurruƙe mata hannayenta da ƙafafuwanta ta yadda ba za ta Iya ƙwatar kanta ba. Tsohuwar da ke a ruƙe da Ludayin ce ta zuƙunna agabanta tare da tsoma hannayenta masu zaƙo zaƙon akaifa ta ɗebo Ƴan hanjin Cikin sai tiri suke Yi, runtse ido Angel ta yi sosai ta guntse bakinta zucuyarta na tashi kamar zata yi hauka, Bata ta6a ganin masifa ido da ido ba sai yau da Allah ya haɗa ta da tsoffin nan, Duk yadda tazo ta kufce masu abun ya faskara kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, Ta ƙarfi suka 6are bakinta har saida gefe ya dinga fitar da jini, baiwar Allah taji raɗaɗin azaba, duk ta ciccije la66anta da tsiya su ka dunga tura mata ƴan hanjin abakinta, don dole ta dinga haɗiyarshi da zafinshi harshenta duk ya sale haka la66anta ma sun yi suntum.

Kamar zautacciya haka tsoffin nan su ka maida ta, Sai da su ka gama azabartar da ita kafin suka saketa Anan ƙasa ta shiga kwarara amai suna kallonta suna dariya, kaf saida ta amayar da ƴan hanjin da su ka bata, wani azababben ciwon kai ya farmata, Ga jiri da ta ke gani acikin idanuwanta

“Lami ba ta Æ™oshi da farfesun ba, A Æ™aro mata wani” maganar su taji a cikin kunnanta, a galabai ce ta miÆ™e jiki ba Æ™wari ta dinga bugun Æ™ofar É—akin har sai da ta samu daÆ™yar ta buÉ—e ta, gudu ta ke yi jini na wanke rigar Jikinta saboda bakinta da suka sanya Æ™arfi wurin 6are shi gefe ya tsage bleeding ya ke kamar jinin jikinta zai Æ™are.

Baiwar Allah ga zazza6i mai zafi daya rufar mata, Jikinta sai kakarwa ya ke yi, ta gama fita hayyacinta, Neman hanyar da zata koma cikin Æ´an uwanta ta ke yi saboda ta riga da ta sare da kurkukun, mutuwa ka É—ai ta ke gani acikin idanuwanta gashi ba ta son ta mutu ba tare da ta yi bankwana da Æ´an uwanta ba.

Tsabar raÉ—aÉ—in da bakin ta ke yi mata ne ya jaza mata rauni da rashin kuzari a jikinta Ƙaffuwanta suka harÉ—e Gaba É—aya ta kife saman floor, kanta ya daki Æ™asa sosai, runtse idanuwanta ta yi yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta miryarta babu sauti take ambaton sunan Æ´an uwanta tana neman taimakon su akan su zo su taimake ta, kada ta mutu ba tare da sun gana da junan su ba, Babu alamun hankali atattare da ita, sai sambatu ta ke yi ita kaÉ—ai, Addu’o’in da ta ke Æ™okarin yi yanzu sun kufce mata……

Sautin tafiya ta soma Ji kamar motsi motsi saman jikinta, a daddafe ta miÆ™e tana faman yin nishi, Ras taji gabanta Ya faÉ—i ganin wasu Girgizo kwafta kwafta a kewaye da ita, Tashin hankalin da ta shiga ne yasa ta fasa Æ™ara tare da yunÆ™urawa ta miÆ™e da gudun gaske ta miÆ™i hanya tana gudu tana waiwayon su gaba É—aya sumar kanta mai tarin yawa ta rufe mata idanuwanta, Cikin rashin sa’a Ta 6urma cikin wani É—aki tare da Jan Æ™ofa ta datse, ba tare da ta ankara da inda ta faÉ—o ba, Jikinta sai kerma ya ke Yi.

“Barka da zuwa ÆŠakin FiÉ—a, Ga dukkan Alamu mun samu wata sabuwar ma’aikaciyar” Muryar matashin saurayi taji acikin kunnanta, Tun kafin ta juya ta kalle su Jikinta ya hau tsuma, A furgice ta waiwaya tare da sanya hannu ta nannaÉ—e sumar kanta da ta rufe mata idanuwanta, Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un bakomai ne yasa ta ambaton hakan ba face Matasan Æ´an matan da ta gani kwance saman gadaje kalar na marasa lafiya, zindir babu kaya a jikin su hada masu ÆŠauke da juna Biyu, gwanin ban tausayi, Giants ne tsaitsaye akansu Hannayensu ruÆ™e da kayan theater suna acikin shigarsu ta baÆ™aÆ™en Kaya.

“Ƴar uwa dan Allah ki taimake ni, ki fitar dani daga wurin nan kada su kashe ni” waro ido sosai Angel ta yi akan matar da ta yi mata magana, Ita ce mai É—auke da juna biyu Daga ganin cikinta tsoho ne Ya shiga wata na tara. Sun tu6e mata kaya tsiraicinsu duk abayyane, Wannan wata irin masifa ce? Hasbunallahu wa’ni e mal wakeel Lahaula wala Æ™uwata Illa Billah, Allahumma ajirni fil musibati wa aklif ni khairan min ha,’ adabarbarce Angel ta ke ambaton hakan. Matar sai kuka take yi tana rokonta akan ta taimake ta ko dan saboda yaron da ke a cikinta, rushewa Angel ta yi da kuka ba tare da ta Iya furta magana ba.

Ɗaya daga Cikin Giant ɗin dake a ɗakin tiyatar ne Ya tunkarota Hannun shi ruƙe da wuƙa, Tunkan yai magana ta fahimci abinda ya ke nufi, aiko Jiki na 6ari ta juya tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin don ta gudu, sai dai ina kafin ta yi hakan ta ji Ya damƙi hannunta, ruƙo bana wasa ba, ta ƙarfi ya dinga janta har sai da ya kai ta bakin gadon da matar nan me ciki take kwance.

Zura mata wuƙar ya yi a cikin hannunta Ya damƙe shi da nashi hannun, Ta ƙarfi ya soma ƙoƙari sanyata farke cikin matar, Kamar zata zauce saboda tsabar kiɗima har Allah ta dinga roƙo akan ya ɗauki ranta kafin faruwar hakan, Bata ta6a danasanin zuwanta duniya ba sai yau, ta yi fatan ace bata ta6a wanzuwa acikinta ba, ta yi kuka kamar ranta zai fita tayi haukan tayi borin duk abanza, ta ƙarfi giant din nan ya ɗaura hannunta saman cikin matar nan da ke ta kuka tana roƙonta akan ta taimake ta, Saboda rashin imani Ya yi amfani da hannun Angel wurin farke cikinta Kamar an fasa pipe ɗin ruwa Haka jini yadinga tsastsafowa yana wanke fuskar Angel har ta cikin bakinta ya dinga fallasa yana shiga.

Hatta jaririn da ke acikinta bai tsiri ba, Biyu suka raba shi da wuƙar, Allah sarki Angel Gani ta yi kamar ita ta aikata kisan kan, Wata irin kururuwa ta saki da iya ƙarfinta na karshe ta bangaje giant ɗin da ke a ruƙe da ta ita Amakance ta dinga Tafiya tana neman Hanyar fita, muryarta da sautin kuka ta ke faɗin.

“Nashiga Uku na bani na lalace Inalillah wa’inna ilaihirraji’in Na aikata kisan kai! na yi kisa da hannayena Shikanen Na mutu, nasan Allah ba zai Æ™yale ni ba, Na kashe mashi baiwarshi da bata ji ba bata gani ba, Wayyo Allah Na……”

Yatsun hannayenta ta É—aura asaman kanta kamar Aljanna Jinin matar duk ya canza mata kamanninta, duhu ya mamaye idanuwanta da zuciyarta.

Giants ɗin da ke Yin aikin fiɗar sai tiƙar dariya su ke Yi, Hankalinsu kwance su ke Cigaba da gudanar da aikin su, yadda su ke farke cikin mutun kamar dabba babu imani ko misƙala Zarratin.

Da wata irin raunatacciyar murya ta ke faÉ—in”Allah ba zai ta6a barin ku ba, Mugaye Azzalumai, Tun agidan duniya za ku fara gir6ar abunda ku ka shuka Æ´an iska fasiÆ™ai masu zuciya irin ta kafuran farko, In sha Allah Ni ce Ajalin ku, Sai kun É—anÉ—ani kuÉ—ar ku sai kun gane ba ku da wayau, kamar yarda kuka sa na zubar da hawaye na in sha Allah kuma za ku zubar da naku hawayen Na jini ma, Yadda ku ka cutar dani ku ka sa na aikata kisa kuma sai an yi maku mafiyin shi……” Æ™ululun baÆ™in Cikine ya tokare maÆ™oshinta, silar hakan yasa ta kasa Æ™arasa maganar.

Hannayen ta biyu ta sanya saman wuyanta, ta shaÆ™e shi sosai cikin fitar hayyaci kamar zata kashe kanta, tsabar raÉ—aÉ—in da Æ™unar da zuciyarta ke yi mata ne yasa ta ke Æ™okarin aikata hakan, tana a cikin wannan mawuyacin halin taji An sunkuce ta kamar ÆŠiyar roba haka aka É—auke ta sama, wani gabjejen giant ne yai mata wannan É—aukar, fucewa yai da ita daga Cikin É—akin ÆŠauke saman kafaÉ—arshi bai nufi ko’ina da ita ba sai cikin wannan Ƙaton palourn Da taron matsafa su ke gudanar da Bautar su, Wasu dogayen mutane masu sanye da jajayen kaya ko’ina na jikin su arufe ya ke, sun kai su talatin, Agaban dodon tsafin su, Anan Ya sauke ta saman floor, a durÆ™ushe ta kife kasa saboda rashin Æ™warin Jikinta, Hatta numfashinta a hargitse yake fita Jikinta yai zafi rau kamar wadda aka tsomo daga cikin wuta.

A lokacin ta kai maƙura bata iya ta6uka komai, motsin hannun mutun ta ji ajikinta, saboda duhun da idanuwanta su ka yi mata yasa ta makance, bata ganin komai, kayan Jikinta suka cire mata gaba ɗaya iya pant ɗin ta su ka bar mata, duk da bata acikin hayyacinta sai da ta shiga matsanancin tashin hankali tunawa da robar ruwan zamzam ɗin da ke a cikin wandonta, rarrafe ta dinga tana laluban suturarta don ta mayar dasu a jikinta sai dai kash bata samu damar ganin inda aka jefa mata kayanta ba. Kukan zuci ta dinga yi, duk wani motsinta akan idon matsafan, ita damuwarta ba akan tsiraicinta da suke kallo ba, robar ruwan Zam zam ce damuwar ta, Ya za ta yi idan ta rasa ta? Ita kaɗai ce damar da suke da ita.

Kunnuwata ne suka soma Jiyo mata Sautin muryoyinsu Marasa daɗin ji magana su ke yi da yaren su na matsafa gur6ataccen yare mara daɗin ji, kamar zata haukace, Lallai yau Angel ta shaida tana acikin kurkukun ƙaddara.

Ƙwaryoyin ne ruÆ™e a hannun matsafan masu É—auke Da zallar Jinin mutane mai Æ™arni, Layi suka jera agabanta suka tsaya tare da Kwarara mata Jinin A saman kanta, Wa’iya zubillah Numfashinta ya gauraye da Ƙarnin Jinin Nan ta ke Ta Æ™ara sa faÉ—uwa Æ™asa tana fitar da numfashi sama sama, basu Æ™yale ta ba sai da su ka yi mata wankan tsarki da jinin da ke a hannunsu, wani kalar Jini mai wari da Æ™arni daga gani sun tsuma shi sosai, ba Æ™aramin zautar da ita su ka yi ba, Kwakwalwarta bazata Iya jure abinda suke yi mata ba, Tana jin motsin hannayensu a jikinta saÆ™o da lungu su ke cuccuÉ—ata kamar suna yi mata wanka, Sun goga mata najasa a jikinta sun wulaÆ™anta Martabar jikinta. Allah ne bai nufa Angel zata mutu ba da tuni ta jima da mutuwa lokacinta ne bai yi ba, domin kuwa warin jinin da suka yi mata wanka dashi kaÉ—ai ya isa ya halakar da É—an adam. Bayan sun kammala yi mata wankan tsarkin nasu na matsafa, Giant É—in da ya kawota Ya sanya hannu tare da tattareta kamar tsumma Ya É—auke ta, Ya fito da ita daga Cikin Falon Ya nufi Hawa Na uku da ita, ba tare da sun mayar mata da uniform É—in ta ba, ko yatsun hannunta bata Iya motsawa, Sautin tafiyar shi ka É—ai ta ke iya ji acikin kunnuwanta, Æ™ofar Wani É—aki Ya tura da Æ™afarshi Ya shigar da ita, Katafaren bedroom ne na zamani kamar ba’a cikin kurkukun Ya ke ba, Da jinin jikinta da komai Ya jefar da ita saman gadon tare da Juyawa Ya buÉ—e Æ™ofar Ya fuce.

Kaɗan daga Cikin Abunda ya faru da Angel kenan A cikin Daren ranar, Shin me kuke Tunani zai biyo Baya? Bayan gaba ɗaya Shirinsu Ya tarwatse Babu alamun zata haɗu da Danish, Ko da ta haɗu dashi daƙyar ma Ta iya gane shi saboda bata a cikin hayyacinta babbar matsalar babu ruwan zamzam ɗin da zata Iya shawo kanshi, saboda kwalbar tana a cikin aljihun uniform ɗinta, Ya salam!! Wannan wace irin mummunar ƙaddarar rayuwace!!! Me zai faru da su Azeeza? Me tsohuwa zafreen zata yi masu

*Boss Bature✍️ Mu haÉ—u Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun Æ™addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuÉ—in*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number É—ina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

No comments