Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 12


MIJIN MALAMA na kuÉ—i ki biya ki karanta….If you read for free路‍♀️路‍♀️路‍♀️路‍♀️0811923761613
Abraham ya zubawa Maminsa Malama Majeederh narkakkun idanunsa, a hankali ya Æ™ara tura hannunsa cikin sumar kansa cikin huci ya sa Æ™afa ya daki frame É—in gadon ya ce “Ki daina” ya furta yana Æ™ara matsawa inda take zaune. Ta É—aga Idanunta da yanzu su ka yi farare tas babu alamun tashin hankalin sai jaa da fatar fuskarta tayi. Ciki nutsuwa ta kame kanta da kyau ta kalli yatsun Æ™afafuwan shi da suke dogwaye masu tsari da fasali, da sauri ta É—auke Idanunta jin tsigar jikinta na ta shi ba tare da sanin dalili ba. Ta miÆ™e a hankali zata bar wajan ta ji ya yi saurin tare ta Æ™amshin Boadicea The Victorious ya daki hancinta cikin ranta take furta “Asstagafirullah”
“What? Magana kina yi?”
Still tayi ignore na shi
A yanzu gani take kallonsa ma Haramcin ne a gare ta tunda da igiyar wani a kanta, wanin data rasa ta ƙamaimai abinda take ji a gare shi, So ne ko tausayi? Ko kuma karamcin taimakonsa a gareta?. she did not want her marriage with Abuturab to be a marriage of mutual help,bata son aurenta da Abuturab ya zama auren taimakon juna. Tana son ya zama auren da zai kafa tarihin rashin abokin rayuwa da ta yi tsayin shekaru talatin da biyar, tana ta samu nutsuwa, nutsuwa tare da mijinta Abu-turab, It is a very difficult thing.
Ciki yanayi na jin tausayin kansa na irin tsanar da Maminsa tayi masa ya kama hannunta ya riÆ™e cikin nasa, ta runtse idanu Muryata a É—an rarrabe sbd faruwar wani al’amari daya shuÉ—e mata ta ce “Kada ka bari tsanarki ta fi t da, bana son ganinka ka rabani da Mahaifina” Ya ware idanu yana sakin hannunta ya ce “Wow, that’s the reason? I’ll Tajju before I leave na bar masa wasiÆ™a” ya zura hannunsa a aljihu ya ji ba wayar shi. Da hannunta ta nuna masa Æ™ofa tana rufe jikinta. Ya yi cute smile wanda ya saba tun yana yaro idan yana son abu ya ce “Uhm, ni wannan abin yana sunan shi, in Hausa language? I like it” Malama Majeederh kamar Æ™asa ta tsage ta shige domin ta san mai yake nufi tunda tana kallon direction É—in da idanunsa suke bi.
“Get out, ka barni tsayin rayuwa” “I can’t, kene rayuwana dole zan sameki soona or later” Ya zube a Æ™asan gwiwar shi y dafa Æ™afarta yana faÉ—in. “Zan koma wajan family na, ba zan dawo ba sai lokacin daya dace lokacin da zaki san i am in love with you, madly love, crazy love, zaki ne meni da kan ki” ya kalleta duk da yadda Magana ke masa nauyi amma da yawan lokaci idan Jee ce gabansa baya sanin time É—in da bakinsa ke buÉ—ewa ya miÆ™e tsaye ya ce “At this time I will force you to marry me”
Zuciyarta bugawa take sosai bata Æ™aunar kuma ya sani addu’a take kada ta sake ganinsa a gabanta har É—aukewar numfashinta na Æ™arshe. Ya matsa daga kusa da ita tare da nufar inda Ibrahimul-khalil ke barci ya É—auke shi ya rungume a jikinsa, kana ya sumbaci kumatun shi sai a lokacin gabaÉ—aya kamanninsa ke Æ™ara juyewa irin na Abraham Daniel David. Musamman manyan idanunsa da suke farare tas kusan koda yaushe suna lumshe. Ya koma wajan Majeederh ya kalli Khalil ya kalleta cikin Æ™asan maÆ™oshi ya ce

“I love both, I love Mulumana and her son”
Ya rungume Khalil yana jin kamar zai bar gabaɗaya rayuwar shi ne zai bari a tare da Jee. Tana tsaye bata motsa tsoro take kata ta shige bathroom ya gudar mata da ɗan ta, domin akan Khalil babu abinda ba zata iya ba, akan Khalil tsaf zata haƙura da zama da Abu-turab, bata son ya gane Ibrahimul-khalil shi ne rauninta bata son yadda mahaifinta ya wofintar da rayuwarta ita ma ta yiwa gudan jininta haka.
Ya sauke shi tare da kwantar da shi ya ɗauki ƙaramin zobe ya ajjiye a gefen shi.
“.….If you miss your father, just watch this…!”
Ya dubi É—an da kyau! Ya ce “I love you Son”

Ya zuba hannu a aljihu kafin ya walking slowly ya tsaya gabanta yana kallon fuskarta tare da son haÉ—a idanu da ita. “Ƴar Madara!”
Ya furta can ƙasa, domin da iya abinda zai iya kiranta kenan, Mamina or Jee or ƴar Madara.
“I’ll leave, to my country” ya sauke numfashi kana ya tallafo haÉ“arta numfashinsa na sauka ya ce “Zan dawo, zan dawo, zan dawo, kafin nan kin gama yawon nema kina buÆ™atata, sbd ni ne namijin daya dace da duniyarki, zan dawo lokacin da zan zo miki da bazata, zan dawo lokacin da zaki san sbd ni aka yoki a mace zan dawo sbd babu wanda zai iya baki abinda na baki” ya ja aya yana riÆ™e saitin zuciyarsa baya Æ™aunar depression ya sake kama shi a wannan lokacin so yake ya sauya sauyin da dole zata dawo gare shi, zai dawo da tarin soyayya mai tsafta da nagarta.

She don’t know what comes over her ta ji gabanta ya faÉ—i, ta san barinsa alheri ne ga duniyyarta, domin ta fahimci shine Æ™addararta ta san tubalin ginin rayuwarta da farin cikinta zuwa mataki na ko wacce mace mai nagarta a gidan mijinta to dole sai babu shi. Ya zame mata kumurcin maciji, ya zama duhun damina, babu komai a cikin lamarinta sai tarin Æ™alubale da ko wacce mace kan iya fuskanta a gaban iyayenta. Shi ne ya zama tsaunin daya kai mizanin da ake mata kallon ShaiÉ—aniyya uwar shaiÉ—anu ya sa ake mata duba irin duban da akewa Magajiya.

“If I don’t come back, I was already dead, Let see waye MIJIN MALUMA” Yana faÉ—in haka he just give a small deep kiss in her lip’s tare da side hug he quickly leave the room.
Ji ta yi kamar ya tafi da baƙin cikin dake manne a zuciyarta wanda ya haifar mata da shi, nauyin ƙirjinta ya rago. Ta samu rauni irin raunin,rauni na ɗiya mace wanda bashi da mara ba da auren lokaci guda da akai mata. Ta sulale a wajan tare da ɗaukan Ibrahimul-khalil ta rungume tana jin shi ne abu ɗaya da yake sawa ta ji tana da raguwar farin ciki.

Abraham na fita ya samu Uncle Isma’il zaune a main parlour fuska a haÉ—e ganin yanayin Abraham ya sa ya sauke nasa fushin domin ba Æ™aramin tsoro idanunsa suka bashi ba. “Abraham”
“Uncle” Abraham ya faÉ—a yana zama a Æ™asan kusa da Æ™afafuwan Uncle Isma’il, Hajiya Luba na gefe ta dinga kallon Abraham kafin Uncle ya yi magana ya ce.
“Promise me that you will marry me Malumana, idan na sauya na amshi musulunci?”

“Yes, I promise you that but…..,” “But what?” Cewar Abraham idanunsa kamar za su faÉ—o sbd tsabar ciwon da zuciyarsa ke masa na ganin yadda Majeederh take sanya hijabi a tsakanin su speaking calmly ya ce.
“Idan bana kusa da ita, zan fi gane dalilin da ya sa nake son musulunta tunda ba ayi wa addininku wayo da dabara ko Uncle?” Uncle Isma’il ya zuba masa ido, bai damu ba ya ce.
“Ina da sa a koda yaushe, babban dalilin daya sanya na haÉ—u da Jee kenan tun ina Æ™arami, Uncle zan koma zan je wajan Daddyna duk da abinda nayi masa amma dole na je, please keep your words idan na cika sharuÉ—a zaka bani Ƴar Madara, ba zan dawo ba sai na zama yadda ka ce” yana faÉ—in haka ya miÆ™e tare da ficewa daga cikin gidan bakiÉ—aya.

“Abraham, Abraham wait tsaya akwai bayanin da zan maka…!” Amma ina tuni ya fice ko kiran Uncle da ya ji ya É—auka zai hana shi tafiya ne.
“Me zakai masa? Kayi masa al’Æ™awarin auren Majeederh shi ne ka bata Abu-turab?” Uncle Isma’il ya rasa me zai ce ya ce
“Abinda nake jira ya fito daga É—akin Hawwa’u na faÉ—a masa kenan, zan faÉ—a masa ya haÆ™ura da ita babu rabon aure tsakanin su”
“Tab É—in, ba a rabu da Bukar ba an haifi Habu, kada hangen hadari ya sa a yi wanka da kasha” Hajiya Luba ta Æ™ara da cewa “Yaron nan yana da naci da Æ™ulafucin abu baya da haÆ™uri ga taurin zuciya”
“….. Tsorona É—aya kada ya Æ™ara É“ata rawar shi da talle a wajan Daniel…”
“Yana son É—an shi” “Amma baya son addinin da É—an yake so, su É—in cikakkun mabiya addinin kiristan ne wanda sukai imani da shi imani bai tsauri, ba zai taÉ“a barin Abraham ya musulunta ba da wannan hujjar na dogara har na yi masa al’Æ™awarin aure sbd duk a rabo lafiya” Hajiya Luba ta ce “Sam ni dai banga da cewar hakan ba”

Abraham na fita akan ƙafafuwan shi ya dinga takawa, duk da irin kuɗi na mahaifinsa amma yanzu babu ko biyar a jikinsa wayar hannunsa ma babu. Abu biyu ya ke buƙata ya sha barasa ya kuma shiga church ya nemi sa a ga abinda zai yi. A Wannan lokacin ko dai ya samu Majeederh, ko dai ya rabauta da addinin Musulunci ko kuma ya samu damar kawo ƙarshen rayuwar shi Life ending.
Barrister Aliyu Zaki yana zaune cikin kyakkyawar shigar shi mai nuna zallar mutuntakar shi ya dubi Latifa cikin damuwa ya ce “Kina son rabauta da rahamar Ubangiji kowa?” Latifa ta ce
“Babu wanda baya buÆ™atar wannan” Ya ce “Banda ke, bana tunanin kin shirya samun aljanarki a wajena” Ta dube shi fuskarsa ta faÉ—a sosai ya ce “Kina sane da adadin lokacin da ki ka É—auka baki sauke hakÆ™in aure ba? Kullum idan na shigo cikin gidan nan gabana faÉ—uwa yake, bana da burin zama da mace zama da É—aya Latifa, Æ™addara ta haÉ—ani dake tare da sauyani ba tare dana sani ba, duk da cewa tun bayan zuciyata na wani wajan, Latifa ban san abinda ake ji a zaman Majalissa ba tun bayan iya ba har na saba, ke kika bani dama na zama Majalissa mata na shigewa idanunmu na gani, ki sani duk macen da ki ka sanya na ji na yi sha’awar ta to ba zan taÉ“a yafewa ba, domin kamar na yi zinar idanu ne” Lafita Shocked ta ce

“Me na yi?” “Oh! Baki sani ba?” Ya jinjina kai ta ce “Da gaske” Aliyu Zaki ya gyara zama sosai ya ce
“Firstly duk abinda ya halatta mace taiwa mijinta to ke zero ki ke a nan, ba sani ba ko baki da lafiya ne ko sha’awa ce babu da bakya buÆ™atar mijinki, baki iya girki ba kullum ina yawon zuwa restaurant sbd kunyar zuwa nake wajan Hajia na ce zanci abinci bayan ina da mata, irin kwalliyya ta mata baki iya ba, ba kitso ba wannan zanen abun Æ™unshi, sai tara Æ™awayen banza da iska da masifar kishin da bashi da amfani, wallahi wallahi ko zina na fara kece sila Latifa Allah ba zai barki ba, Allah kana kallo duk nauyin daka É—ora mini a matsayina na miji na sauke, kuma in sha Allah sai na auri Majeederh ita ce zata bani abinda nake buÆ™ata ina son mace mai Æ™arfin addini da iya soyayya amma ke text message wannan baki sani ba, Mrs zero!”
Yana faÉ—in hakan ya zari key tare da ficewa daga cikin gidan ya nufi Chikenza Park and Restaurant.
Misalin Tara na dare motocin His Excellency Abu-turab suka sauka gidan Uncle Isma’il, cikin sauri P.a ya fito tare da buÉ—e masa Æ™ofar mota a hankali ya fito yana zabga Æ™amshi Dolce and Gabbana wanda sanyin Æ™amshin ke fita a hankali cike da gamsar da mai shaÆ™ar shi. Yana sanye da wata dakakkiyar shadda sky blue É—inkin jamper da babbar riga ta zauna a jikinsa sosai a wannan lokaci babu ko hula a kansa sbd so yake yau Jiddo taga ainahin kyan da yake da shi, cikin takun Æ™asaita kamar wahainiya haka ya nufi cikin gidan Uncle dake sun da zuwan na shi, Jawaad na parlour yana kallon ball ya yi saurin miÆ™ewa ganin His Excellency Abu-turab da kan shi ya durÆ™osa da girmamawa ya ce

“Wlcm sir” Murmushi Abu-turab ya yi yana jinjina kai “Kana lafiya?” Ya ce “Allahamdulillah, sannu da zuwa” ya Æ™ara murmushi kawai. Jawaad ya yi masa rakiya zuwa parlour part É—in da Majeederh ke ciki kana ya shiga ciki ya sanar mata lokacin tana zaune har yanzu ko sauya kaya ba tayi ba ta zubawa Ibrahimul-khalil Idanu. Ta jinjina kai kawai ya san ba zatai magana ba sai kawai ya fi ce. Abu-turab ya kasa zama har tsayin mintuna kusan goma kafin ya ji motsi a bayan shi. A hankali ya sauke wata É“oyayyiyar ajjiyar zuciya ya Æ™arasa gabanta yana binta da kallo.
“Barka” ta furta can Æ™asa ya ce “Can You remove the cover? Please i want see my wife ba wannan hijabin” Ta É—ago kai ta kalle shi tana son ce masa ya jiki tunda taga harda carnoner a hannunsa. “Please Jiddo, My wife aure ya halatta mini ganinki” ta runtse idanu sosai lokacin daya zare hijabin jikinta a hankali ya jata jikinsa ya rungume sosai yana sauke numfashi da ajjiyar zuciya ya ce “Allahamdulillah, Allahamdulillah, Allhamdulillah! Ina son ki Jiddertul-khair” Rayuwa Kenan bayan tarin Æ™alubalan rayuwa data sha ta tsallake Æ™addarori da surutu da zunÉ—en jama’a yau ita ce matar babban mutum, ita ce first lady? Ita ce jikin Governor Abu-turab AlÆ™asim rungume da ita yana faÉ—a mata yana son ta? Sai a lokacin wasu hawaye Masu zafi suka shige fitowa daga cikin idanunta har bata san lokacin data É—an Æ™anÆ™ame jikin Abu-turab ba. Sannu a hankali kamar gilmar fitila cikin duhu rayuwarta ta baya ta fara dawowa cikin Idanunta da tunaninta…. THE BEGIN OF THE BEGINING. Shekaru talatin da biyar da suka shige a baya al’amarin ya fara……

 

No comments