Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 16


MIJIN MALAMA
Paid book ne
Book 1 and 2 1kne
Pay….0811923761617
Tafiya suke a nutse duk da ya yi mata nauyi a baya shekarun shi biyar a duniya amma yana da girma jiki ga shegen wayo. Ya Æ™ara shigewa bayanta ya ce “Mamina”
“Little babe” ya leÆ™o ta gefen fuskarta ya ce
“Mamina ke baki da mota? Me ya sa baki zo wajena ba, me ya sa kike mini faÉ—a ai nayi Æ™arfi duka nakewa yara, I will fight, and I will win”
Murmushi kawai ta yi masa a zuciyarta tana mamakin yadda da yawan lokaci turanci ke zama a bakin shi, bai ci ace daga fara karatun shi ya fara turanci har haka ba. Jin ta yi shiru ya ce
“Get me down, Mami”
“No, little ba zaka iya tafiya ba” ya fara buga Æ™afa a bayanta tare da Æ™oÆ™arin sakin kuka. A hankali ta tsaya tana mai da numfashi kana ta sauke shi a Æ™asa ya yi mata murmushi yana rufe Idanu tare da suÉ—e baki na daÉ—in ice-cream. Gani tayi ya durÆ™osa a gabanta ya ce “Ni ma zan rama muki, haka muke a school”
“What! wa zaka goya?’
Ya tura baki gaba ya ce
“Ke Ƴar madara, ai duk wanda ya goyaka kai ma kai masa haka ko Mami?” Ta tsora masa idanu surutun shi na bata mamaki Æ™warai ta sunkuya daidai tsayin shi ta shiga kaÉ—e masa gasar jikinsa tana shata samar kan shi daya hana a aske ta ce “To ai uwa duk abin da ta yi wa É—anta daidai ne”
“Kyautatawa nada daÉ—i kin ce Mami?” Ta jinjina masa kai cike da jin daÉ—i tana faÉ—in “Shikenan ka bari idan ka sake girma ka goyani” ya dinga tsalle da murna zai goya Maminsa Æ´ar madara.
“Promise?” Ta miÆ™a masa hannu ta ce “Promise” ta kama hannunsa suka cigaba da tafiya tana jin zuciyarta daÉ—i ga wani farin ciki yau zata kwana da Little daman sabgar shagalin musabaÆ™a ya sanya ta kai shi can tunda ba kowa yake kula da shi a gidan nasu ba. Tun daga can har gida suka Æ™arasu a Æ™afa suna tafe yana mata surutu wasu ta gane wasu kuma kamar wani yare nada ban haka yake. A daidai Æ™ofa Majeederh taci karo da Latifa taja baya tana Æ™ara riÆ™e hannun Little dake Æ™oÆ™arin tafiya wajan daya hango yara age mate É—in shi suna faÉ—a. “Yanzu na shiga ake ce mini bakya nan” cewar Latifa. Ta lumshe Idanu cike da gajiya ga azumi don ma rana ta fara sanyi a gajarce ta ce “haka ne” Latifa ta ce “Ki ce É—an rigima kika É—akko daman tun da mu ka yi waya nake son tambayarki shi sai kuma naga you’re not on the mood na share” Majeederh ta ce “Ayya, muje” suka shiga cikin gidan a tare tana shiga ta jiyo muryar Uncle Isma’il ta faÉ—aÉ—a murmushinta tana sakin hannun Little ta shiga parlourn Abbu. Uncle Isma’il ne da Uncle Bello suna zaune suna tattaunawa akan maganar Widad da kuma kuÉ—in Ruma da za a kawo. Ya Uncle Bello ya dubi Majeederh ya ce
“Hawwa’u an dawo? Yanzu ake ce mana bakya nan” ta sunkuyar da kanta Æ™asa cike da ladabi ta ce “Eh Uncle, an yini lafiya” “Allahamdu lillahi” ya bata amsa yana mai jin tausayinta har ranshi sbd zurfin ciki da take da shi ga yadda duk al’amarin rayuwa yake jirkice mata. “Uncle..,” Uncle Isma’il ya yi saurin É—aga mata hannu cike da É“acin rai da damuwa ya ce “Kin kyauta tunda tsarin da ki kaiwa kanki kenan, ba bu abin da zamu iya ikon ki ne ke kike da kanki Hawwa’u” zuciyarta ta buga tsoro da fargaba suka risketa a wannan lokacin idan aka tsaga jikinta ba lallai a samu jini ba sbd tsabar fargaba. Amma sam fuskarka ko yanayinta bai nuna hakan ba. Cikin sanyin murya ta ce “Me nayi Uncle?” A hassale kamar zai daketa ya ce
“Ni kike tambaya me kika yi ko Hawwa’u? Yanzu yaron nan Imran kwanaki yazo yana son ki har iyayensa ya fara yunÆ™urin turawa, ban san mene ya faru ba naji maganar shiru, yanzu kuma na samu labarin zai kawo kuÉ—in Rumana na tambayi Abdul’aziz ya ce da kanki kika cewa Imran bakya son shi kada ki sake ganin Æ™afar shi?”
Duk da sanyin shigewar hadari bai hana Majeederh jin wata zufa ta yanko mata ba, daga ina wannan al’amarin ya bayyana waye ya shirya mata maganar da bata san da ita ba, waye yake shirin wargatsa burinta?. Ta kasa cewa komai yawun bakinta ya maÆ™ale ga Æ™ishin azumi ganta ya shiga juyawa. Uncle Isma’il ya gyara zama domin ya fi kowa zafi akaf familyn Khan.
“Duk abin da ya faru ki kuka da kanki, ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka, itikafi rayuwa kaÉ—ai zai sanya ki kai kanki tubalin tundun mun tsira, idan ba sukike rayuwar duniya ta baki naki kason ba, ina cewa akan idanunki aka haifi Widad? Sa’ar Aaliyyah ce amma aurenta za ayi, akan idanunki aka haifi Du’a Yaronta É—aya ciki ne da ita yanzu, shi ne kin samu mijin aure zaki wasa da damarki akan wani karatu? Anya lissafi da burin zuciyarki da kwaÉ—ayin ganin kin samu wadatacce ilimi ya miki adalci? Hawwa’u aure da haihuwa da arziÆ™i na Allah ne, kuma lokaci ke wanzar da samuwar su kada ki rufe idanunki akan wani abu wanda bashi da wani muhimmaci, ke ba a bin kunya bane ace saurayin da yake son ki ya koma wajan Æ™anwarki, baban abin takaici ma wai ke ce da kanki kika lamumce masa auren Rumana, Goodness what noises? Meke damunki ne?” Majeederh ta fara shiga ruÉ—ani da fara kokwanto anya ana sonta a gidan? Me ya sa ake shirya mata abin da bata sani ba? Ta É—ago kai a hankali tare da zare liÆ™ab É—in kanta, fuskarta ta yi jajur cikin muryarta mai sanyi kamar wacce take shirin yi musu shagwaÉ“a ta ce “Uncle ka yi haÆ™uri, ka zaÉ“a mini mijin ko a gobe ne” Rashin sani ya fi dare duhu, rashin sani baÆ™o ya sha ruwa wanka, sun kasa fahimtar ita kanta a É“ukace take da yin aure, babu abin da take sha’awa irin ta ganta gidan mijin babu abinda ke birgeta irin ta juya taga nata mijin a gefenta. Uncle Bello ya numfasa a lokacin ya ce
“A’a ba ayi haka ba, ai darajarki da kimarki ta shige a nema miki mijin aure, kaf yaranmu ba wanda muka sadakar ko zaÉ“awa miji ba zamu fara a akanki ba, kin yi kuskure tun farko sai ki gyara ki je Allah ya zaÉ“a mafi alheri” Uncle Isma’il ya ce “Wallahi kin É“ata rawarki da tsalle Majeederh iliminki bai amfana miki da komai ba…..” “Uncle Mami na kakewa faÉ—a?”
Siririyar Muryar yaron ta tsayar da Uncle Isma’il daga yin magana. Sai a lokacin Abbu ya É—aga kai ya ce “To rasai yanzu za a san ka dawo, ko zaka rama mata?” Little ya dinga kallon Uncle Isma’il yana huci idanunsa suka kaÉ—a tare da yin jaa wata kalar zuciya ce da yaron kamar kuturu ya shiga surutu a ranshi bakinsa kawai ke motsawa.
Cikin sauri Majeederh ta kama hannun shi ta ce “Say sorry to him” ya yi shiru idanunsa Æ™uri akan Uncle Isma’il ganin yadda ya sanya Maminsa a gaba yana mata faÉ—a gashi har fuskarta tayi jaa daman ta haka yake gane kukan zuci take. Majeederh ta finciko Little ta ce “Ka bawa Uncle haÆ™uri” ba tare daya kalleta ba ya ce “He is shouting at you”
“He’s my Father, am i your mother, na ce ka bashi haÆ™uri, say sorry to him” ya kafe yaÆ™i cewa hannu Majeederh ta É—aga hannu ta zabga masa mari nan take yatsun hannunta ya bayyana a fuskar shi duk da kasancewar fatar shi baÆ™a. Cikin É“acin rai ta jawo shi har gaban Uncle domin gani take idan bata hukunta shi ba a haka zai tashi da rashin kunya da shiga sabgar da babu ruwan shi.
“….Say sorry to him..”
“Uhm, Allah ya shirya ya kyauta, tun baki haifi naki ba kin fara dakon wahala Majeederh?” Cewar Uncle Bello Abbu ya ce
“Hankaka mai da É—an wani naka kenan, kin kyauta kina riÆ™e wanda yake zagine yayyina”
Idanunta ya kaÉ—a sosai ta ce “Don Allah Uncle ka yi haÆ™uri ba zai sake ba”
Ta miÆ™e tana kama hannunsa lokacin Latifa ta gaji da jiranta har ta tafi gida. Ta samu Aaliyyah ta dawo daga makaranta tana shirya abincin rana lunch. Raihana na zaune ana waya da saurayi. Babu wanda ta kula sai Aaliyyah dake cewa “Sannu da dawowa Anti Jeederh” ta shige É—aki tana jinjina kanta alamar “Yawwa” suna shiga ta saki hannun Little tare da É—akko bulala ta waya ta kama hannunsa ta zirara masa guda É—aya
“As form today na Æ™ara jin kayi magana da babba sai jikinka ya faÉ—a maka” ta Æ™ara zirara masa hannun ya taro jini amma bai motsa ba sai cewa ya yi “FaÉ—a ya miki Æ´ar madara” Majeederh ta ware Idanu tama rasa me za tayi sai kawai ta miÆ™e tare da shigewa Bathroom tayi wanka da Alwala ta wanke fuskarta sosai har jan fuskar ya daidaita domin ta fahimci sauyin fuskarta yake sawa Little ya fahimci halin da take ciki, bata taÉ“a ganin yaro mai fikira da shegen wayo kamar shi ba ga É—an banzan wasa da shiga faÉ—an da bana shi ba. Duguwar riga ta sanya ash ta saka hijabi a kan idanunsa tayi sallah har sallar Asr tayi Asstagafirullah na lattin da tayi kana ta fara azkar na yamma ta dube shi fuska a haÉ—e ta ce “Sallah” da sauri kamar zai kifa ya shige bathroom. Babban abin da yake bata mamaki kafin ya yi sallah sai ya duba ko’ina yaga ita kaÉ—ai ce a É—akin yake yi jikinsa har rawa yake sbd tsoro ta rasa dalilin haka. Yana idarwa ta dawo kusa da ita a hankali ya ce “Sorry Mami”
Tayi shiru fuska haÉ—e sosai ya marairaice ya Æ™ara cewa “Sorry”
Sai a lokacin ta ce “Uncle zaka bawa” ya maÆ™ale ka faÉ—a ya ce “I hate him, faÉ—a yake miki” wata kalar tsawa ta daka masa tare da nuna masa waje ta ce “Out”
Dai-dai lokacin Aaliyyah na shigowa ta ce “Mun shiga wannan tsaiwar ai ta sa na kusa sakin fitsari a wando, wai little kikewa tsawa haka?” Idan Majeederh ta gini ya motsa Majeederh ta motsa. Aaliyyah ta ja hannunsa suka fita yana tirjewa shi a wajan Majeederh zai zauna duk da tsawar da tayi masa. Har akai sallar Magriba Majeederh ta sha ruwa tai sallah Idanunta bai Æ™ara ganin Little ba, a wajan Mami take ji wai ko abinci yaÆ™i ci ya fito waje sun yi faÉ—a an fasa masa kai. Sosai tai mamaki babu yadda za a yi aci galaba akan Little a kullum ita take bada haÆ™uri ta tabbatar hakan baya rasa nasaba da faÉ—an da tayi masa. Tana son ta tambayi yana isa amma girman kai da nauyin baki irin na Majeederh sai kawai tayi shiru. Cikin dare wajan Æ™arfe É—aya taji saukar numfashi a jikinta, Numfashin mai É—auke da zafi da buÉ—e Idanunta da suke ciki da bacci ganinta ya sauka akan Little dake rawar sanyi kayan safe ne a jikinsa har yanzu ta buÉ—e ido da kyau tare da taÉ“a wuyansa jikinsa zafi zau bakinta har É“ari yake ta ce “Little, little” ya buÉ—e ido yana ganinta ya ce “Sorry Jee Mami” bata kula shi ba ta É—auki paracetamol na ruwa tare da É—ora shi a cinyarta zata bashi maganin ya girgiza kai ya ce “Ba zan sake ba Æ´ar madara, na daina Jee” jin ana ce mata Anti Jeederh shi kuma ba zai iya faÉ—a bakiÉ—aya ba ya sa yake cewa Jee, sai watarana data bashi alawar madara ya ce da Maminsa da alawar madarar suna kama tun daga nan yake cewa Æ´ar madara. Ta É—auke kai ya Æ™ara sakin jiki yana kwaÉ“e fuska ya ce “Zan sake ba Mami, zan sake ba” ta saki fuska tana murmushi ta ce “Ok good boy I forgive you” da sauri ya shige jikinta ya rungumeta jikin nan nasa zafi sosai ta shafa kansa taji ya saki ajjiyar zuciya da sauri ta taÉ“a cikin shafal ba komai da alamar yadda yunwa ke damunsa ta É—ago shi za tayi magana taga har bacci ya É—auke shi a hankali ta É—auke ajjiyar zuciya tare da jansa jikinta ta rungume shi wani irin son shi na Æ™ara ratsa zuciyarta…

No comments