Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 4


*4……*
Mummunan hatsarin ya ja hankalin mutane da yawa, hatsari ne wanda za a iya cewa tsautsayi ne da kuma gangan cin driver da yake driving yana waya. Da gudu babbar mota tayi gaba bayan tayi wurgi da Tajju zuwa gefe guda, nan take kan Tajju ya fashe jini ya fara zuba hannunsa guda É—aya ya fita fit daga jikinsa ko shurawa bai ba rai ya yi halinsa. Motar dake bin bayan babbar motar data buge Tajju ce ta tsaya, cikin sauri driver da wanda yake gefen mai zaman banza suka fito bakinsu É—auke da sallati “General kira mana Ambulance” cikin sauri General ya É—akko wayarsa tare searching asibiti mafi kusa da kuma motar asibitin. Hammad ya ce “Allah sarki, haka rayuwa take Allah ya jiÆ™ansa ya yi masa rahama” General ya amsa da “Amin” da sauran jama’ar wajan suka amsa.
Har Hammad zai juya idanunsa ya sauka akan Envelope dake can gefe guda iska na kaÉ—ata a hankali ya Æ™arasa tare da É—auka, a ransa yana tunanin maybe a samu wani bayanai akan mamacin. Ya ware Envelope É—in first abin da ya gani shi ne ring irin na al’Æ™awarin nan, ya juya ring É—in sosai sai kuma ya zura acikin aljihu, gently idanunsa ya sauka akan headline na wasiÆ™ar kamar haka.
*_BAD MAN, THE STUBBORN BOY, CRIMINAL, GANG BOY, THE LEADER_*

Daga wannan rubutun idanun Hammad ya sauka Æ™asan headline É—in inda aka rubuta “The memories, was going on my mind, har abad, nasan ni mahaukaci ne da gaske kamar yadda ki ke faÉ—a Jee” jikin Hammad ya shiga rawa ganin General na Æ™ara suwa ya tura wasiÆ™ar Aljihu “Lafiya?”
“Actually, good”
Kafin suyi magana Ambulance ta Æ™ara su aka É—auki gawar Tajju tare da sanyata ciki, Hammad ya buÉ—e ya É—auki wata number da yaga ana ta kira anyi saving da “Bad boy”
“His phone” cewar Hammad bayan kammala komai Ambulance suka tafi asibiti da shi. Suma su Hammad mota suka shiga driving kawai yake amma tuni ya yi losing mind É—insa, fatan sa kawai ya isa Gov. Abu-turab AlÆ™asim, ya san cewa yanzu ya koma gida kasa jurewa ya yi ya É—auki Wayarsa tare da kiran keÉ“antacciyar number Abu-turab kusan kira uku kafin ya É—auka cikin nutsuwa ya ce.
“Uhm” Hammad ya ce
“Your Excellency, akwai damuwa” a taÆ™aice ya ce
“Kace komai, banda rasa Majee” cikin ladabi ya ce “Am very sorry for that, amma bamu sameta ba, amma mun sami maganin matsalarta, É—an waye, cikin waye, yadda aka samu cikin duk yana ciki” Abu-turab ya miÆ™e daga zaunan da yake ya shiga zagaye haÉ—aÉ—É—an parlourn nashi fuskarsa tayi jajir. “Ok, meet me at my house” yana faÉ—in haka ya kashe kiran. Tafiya kaÉ—an ce ta Æ™ara su da su cikin gidan Abu-turab wanda yake zaune tare da iyayensa, sojoji birjik ta ko’ina daka nuna rashin gaskiya zaka ji maza akan ka. Girman gidan ya zarce tunani, motoci kala-kala na kamfani daban-daban.
Ko a jerin masu kuÉ—i ba kowa zaka samu da wannan haÉ—aÉ—É—an gidan ba, gida ne 200by 200 iya compound na gidan zai ja hankalinka balle ciki. Kasancewar ba wanda bai san Hammad ya sa ba wani wahala ya nufi cikin gidan, a Main parlour ya samu Mama na sakkowa daga bene ya yi murmushi ya ce
“Sannu da gida Mama” kallonsa kawai take fuskarta kwance da annuri amma kana ganin sanyin jikinta kasan akwai damuwa, kyakkyawar dattijowa mai nutsuwa da sanin ya kamata,ga ilimi na iya zama da ko wanne mutum ga kyakkyawar mu’amala. “Na É—auka mun yi laifi yau ne” cewar Mama bayan ta zauna.
“Laifi kuma Mama?” Ta dubesa kafin ta É—auke kai ta ce “Naga babu ko mai kama da kai, hala wani aikin ka ke” ya shafa kai yana rusunawa ya ce.
“Haka ne kam, ina Yake?”
Ta É—aga kai zuwa part É—in dama da yake upstairs ta ce. “Ina son tambayarka dama, meke damun shi? Tunda ya shiga part É—in sa bayan ya dawo bai fito ba, hatta wajan art É—in da yake shiga yau shiru, lunch ma bai ci ba na kira phohe number sa na gida a kashe” ta tsare shi da idanu ya ce “Akwai wata tattaunawar sirri da yake da ita, maybe shi ne yake duba muhimman abu kasancewar tattaunawar sai 12 na dare”
Ta jinjina kai tare da faÉ—in “Allah ya taimaka, kasan Æ´ar rigimarsa ta hanani sakat ita dai Abbi” Hammad ya yi dariya sosai ya ce “Jiddatul-khairi ai ya saba mata ne” kafin Mama tayi magana sai gata ta fito da gudu ta faÉ—a jikin Hammad ta ce “Uncle, Abbina” ya É—auketa ya shiga hawa upstairs yana faÉ—in
“Daughter me, bari muje muga Abbi sai muje siyan chocolate ko?” Tayi murmushi dimples É—inta soka loma tana ta masa surutu har suka isa haÉ—aÉ—É—an part É—in da kana ganinsa kasan Gov. Abu-turab AlÆ™asim ne a ciki. Hannu Hammad ya saka cikin wani screen dake Æ™ofar nan take ta fito da bayanan Hammad a hankali kuma Æ™ofar ta buÉ—e.
Jidda ta ƙwace daga hannun Hammad tayi cikin parlourn da gudu tana kiran sunan Abbi, yana zaune saman kujera daman alrdy ya san da zuwan Hammad ɗin, kayan shan iska ne a jikinsa fara Armless da black ɗin 3 gauter.
Hannunsa É—aya riÆ™e da Black tea wanda aka sanya masa zuma a ciki, news yake kallo har Jidda ta faÉ—a jikinsa hankalinsa baya tare da shi. “Abbina”
Ya ware idanunsa idanunsa da suke a É—an lumshe ya dubeta “First love” sunan da yake faÉ—a mata kenan, duk da kasancewarta Æ´ar shi guda É—aya. “Abbi”
Ya juya bayan ya gyara mata zama a cinyarsa tare da kallon Hammad yana son ya ji wanne labari ne da shi wanda yake da alaƙa da Majeederh.
“Your Excellency barka da yammaci” jinjina kai kawai Abu-turab ya yi.
“Ga wannan wasiÆ™ar, idan ka karanta sai ka É—auki matakin daya kamata akai, ita kuma zamu nemota In sha Allah” hannu ya sa ya amshi wasiÆ™ar tare da warewa zuciyarsa na harbawa, bai san mene ya sanya duk abinda ya shafi Malama Majeederh ya ke jinsa har Æ™asan zuciyarsa ba, barci ya Æ™auracewa idanunsa, ga ciwon kan dake Æ™oÆ™arin kwantar da shi.
Duk Yadda ya so ya daure da riƙe kansa ya kasa ya miƙe tsaye da sauri yana ware idanunsa akan paper ɗin, tsoro,fargaba damuwa da kuma firgicin rashin sanin makomarsa wajan Majeederh ya taro ya haɗe masa waje guda.
Ya sanya hannu ya share zufar daya yanko masa, lokaci ɗaya ya hargitse wani zazzaɓi na neman kawo masa farmaki.
“Your Excellency, lafiya dai?” Ba tare daya kalli Hammad ba ya ce
“Ham…mad” “Yes, Your Excellency”
Ya juya gabaÉ—aya fuska a haÉ—e ya ce “Tun yaushe nake baka labarinta?”
Kai tsaye ya ce “Shekaru wajan biyar, tun ranar daka halarci musabaÆ™ar da aka yi ta Æ™asa”
Abu-turab ya jinjina kai, Elxty 5yrs kenan, a wannan musaÉ“ar ya ji muryar Majeederh, muryar data sanya masa dafin so a zuciya ta zautar da duk wani tunaninsa, ya wanzu cikin muradinta a zuciyarsa, shi kansa ba zai iya sanin abinda ya sanya bai tun kare ta da wannan maganar ba, samun Majeederh Abdul’aziz Khan a garin nan ba wahala zai masa ba. “Har abada Majeederh kada ta san da wannan wasiÆ™ar” da mamaki fal fuskar Hammad ya ce “Your Excellency amma kamar ba a kyauta mata ba, wannan wasiÆ™ar ita zata fitar da ita daga zargi, kuma ita ce zata gane waye ya aikata mata haka” Abu-turab ya koma ya zauna kawo yanzu yasan Bp nasa tuni ya hau cikin kamilalliyyar muryarsa mai tsafta ya ce “Me ka ke nufi?”
“Ba mu yi mata adalci ba” cewar Hammad.
“So baya buÆ™atar adalci, kansa kawai ya sani, ayi hakkan ya tsaya ni da kai” Hammad ya kalli Abu-turab yana girmama yadda yaso kansa a fili sbd soyayya,idan har son gaskiya ne ba zai taÉ“a bari Majeederh taci gaba da zama da zargi akanta ba. “Shikenan, Your Excellency. Maganar meeting naka an gama shirya tattaunawar a guest house É—inka, da kai da Deputy Governor, Secretary to the state of Government, Chief of staff” hannu bibbiyu Abu-turab ya riÆ™e kansa kana ya jinjinawa Hammad kai ganin yanayinsa ya sa Hammad cewa “yana da kyau ka huta haka, Jidda zo muje” ta maÆ™ale ka faÉ—a jikin Abu-turab.
“Abbi baya jin daÉ—i” Abu-turab ya ware idanuna ya ce “Go”
Ta kwaÉ“e fuska cikin zafin zuciya ya ce “I said Go Hawwa’u Abu-turab AlÆ™asim!” Tsawar ta gigita mata lissafi ta fashe da kuka tana Æ™anÆ™ame Hammad ta ce
“Uncle” ya É—auketa yana girgiza yana mamakin sauyawar Abu-turab lokaci É—aya.
Dukkan abinda ya faru akan idanun Malama Majeederh Abdul’aziz Khan ya wakana, kasancewar bata fahimta kusan tunaninta duk ya jirkice Æ™waÆ™walwarta na gab da fara daina aiki yasa bata fahimci su waye ba, motsi kaÉ—an zata Æ™anÆ™ame jaririnta kamar zata bayar da shi ciki, wani zubin kuma tayi ta surutu ita É—aya sbd tarin abubuwan da suka cunkushe mata, yunwa ba a maganarta jikinta ya fara tashi sbd jini da rashin wanka.. bata shagala azkar, istigifari da addu’ar neman samun sauÆ™i wajan Ubangiji bai bar bakinta ba.
Washe gari Abbu ne zaune a parlour da Mami sai Ruma da Raihana wanda aka kira su daga gidan mazajen su, sai kuma Aaliyyah dake zaune tamkar marainiyya Idanunta a kumbure ko gani ba tayi sosai, sai Uncle Isma’il da Uncle Bello. “Yanzu har a ranka kana jin kayi daidai?” Abbu ya dubi yayan nasa ya ce “Majeederh dai ni na haifeta, ni na samar da cikinta na kuma raineta, kuma na dawo na ce bani da haÉ—i da ita don haka a bar wannan maganar” Uncle Isma’il ya ce “An barta, amma ka bani mamaki a matsayinka na Uba kuma dattijon Æ™warai har ka iya shafawa idanunka toka ka ce wai ka sallamawa duniya Majeederh, sbd kawai kada sunan family da naka ya É“aci? Familyn bazan sunanka É—in banza, da rayuwar mace kamar Majeederh ta É“aci ba gwara duka sunayenmu su É“aci ba, wata rana dalilinta sunan namu ya samu É—aukakar damu kanmu ba muyi zato ba, mai ya sanya mu iyaye idanunmu ya kan rufe idan tsautsayi ya samu yaranmu? Yanzu Majeederh ko tana sane wannan abun ya faru ba zaka iya yi mata uzurin akan rashin auren da take da shi ya ja mata wannan Æ™adsarar ba? Ita É—iya macace duk runtsi duk jimawa dole ta É“ukaci É—a namiji wata rana” Uncle Isma’il ya girgiza kai sbd tsabar takaici ya ce “taya Æ™asa zata gyaru bayan mu da kanmu bamu gyara zamantakewar data yaranmu ba, fine ka kori Majeederh zan nemota na riÆ™eta a wajena….,”
“Yin hakan zai ja mana babban kuskure yaya, duk wanda zai so ta bayana yake bi, don haka a barni kawai” Abbu ya tari numfashi Uncle Isma’il da faÉ—in hakan. Uncle Isma’il da ransa ya fara É“aci ya ce “Zan taimaketa kamar yadda take taimakon addinin Musulunci, bawai sbd data kasance Æ´arka ba Abdul’aziz Khan” Abbu rai É“ace shi ma ya ce “Kana iya yin haka amma daga ranar babu ni ba kai, ka cire ni matsayin Æ™aninka, ka yanke mu’amala ta dakai” murmushi sosai Uncle Isma’il ya yi wanda ya fi kuka ciwo yana girgiza kai ya ce “In sha Allah, idan kero na yawo zabo na yawo tabbas za a gamo Majeederh zata baka mamaki” Aaliyyah dake kuka sosai ta ce “Abbu don Allah ka bawa Yaa Nura dama ya kawo kuÉ—in aurena, na ga ji da zaman gidan nan na tsani komai dake cikinsa” kai tsaye Mami ta ce “Fitowa za kiyi ki ce kin tsanemu, aure kuma dole sai kin kammala makaranta daman ke É—aya ki ka rage cikin gidan..” sai a lokacin Uncle Bello ya ce “Aaliyyah aure ki ke so?” Duk kawaicin Aaliyyah ta shanye ta ce “Eh, Uncle”
“Ki faÉ—awa Nura ya zo ya saman a gida nan da sati mai zuwa In sha Allah zaki bar wannan gidan” yana faÉ—in haka ya miÆ™e tsaye ya kalli Uncle Isma’il ya kalli Abbu ya ce “Yaya taso muje, Allah ya bada ladan zumunci Sunan family kuma a rubuta a gaban Æ™oshi ana yawo da shi”
Suka fice tare da barin gidan,Abbu ya nufi part É—in sa zuciya babu daÉ—i shi kam Majeederh ta zame masa annoba, Aaliyyah ta shige nata bedroom É—in tana zuwa ta É—auki wayarta ta kunna network ta shiga facebook inda labarin Majeederh da Bar Aliyu Sufyan Alhassan yake ta trending a media. Ko photon Majeederh ta gani da gudu take skipping ta shige sbd tsaron zagi da mugun alkaba’in da ake mata, tana cikin dubawa taci karo da wani posting photon Majeederh ne sanye da abaya fara mai kyau fuskarta rufe hannunta riÆ™e da loudspeaker. An yi rubutu a saman photon tare da saka.

*She’s Innocent*
_Malama Majeederh Abdul’aziz Khan babbar malamar musulunci da muke da ita a wannan jiha, wacce ta samu damar zama zaÆ™aÆ™ura wajan lashe musabaÆ™ar Alkur’ani ta Æ™asa, ita kuma ta Æ™ara jawo kima da martabar jiharmu, wacce take taimakon marayu, marasa gata take nutsuwar da matan aure akan darajar da aure yake da shi, duk da kasancewarta budurwa. Abin tambayar shin ta cancanci haka kowa? Kai da ka ke zaginta ko ki ke zaginta kina da tabbaci akan abinda ya faru, ko kina da hujja? Ko labarin Æ™azan kurege aka baki har kike É—orawa tare da aibatar Æ´ar jama’a, ta haifi wasun ku da yawa, ta fiki ilimi tunani da sanin ya kamata, ta fika kusanci da mahalicci amma kazo media ko sallar kirki a rana baka yi ka É“uge da zagin babbar Malama? Ashe muna rayuwa da dabbobi bamu sani ba? Ko masu aikata zina sai an same su turbi da taÉ“arya tare da shaidu 4 sannan za a É—auki mataki. MALAMA MAJEEDERH ABDUL’AZIZ KHAN SHE’S INNOCENT I STAND BY HER SIDE._

#Mrs No name

Wani murmushin jin daÉ—i Aaliyyah tayi 5 minutes da yin posting É—in amma comments wajan 1k hakan ya tabbatar mata da Mrs no name yana da followers kuma babban mutum ne tunda har ya iya É“oye sunan shi, kai tsaye profile ta shiga ya rufe komai da komai ko message ba za a iya yi masa ba, dole sai dai tayi magana ta comment section.
Har aka kwana aka tashi Bar Aliyu Sufyan Alhassan bai farka daga suman da ya yi ba, hankalin Hajia ya tashi tana da Papi tare da Almustapha, hatta korar da aka yi masa wajan aiki bai sani ba.
Misalin 8 na dare wahala tayi wahala jikin jaririn ya yi zafi kamar wuta, a yanzu ji take ko jama’ar gari za su kasheta babu abin da zai hanata fita ta nemi ruwan da zata bawa babyn nata, ta miÆ™e da Æ™yar kusan gabaÉ—aya kayan jikinta sun É“aci tana bin gefen hanya harta isa wani wajan da ake siyar da tsire kanta Æ™asa tayi sallama, gabaÉ—aya mutanen da wajan suka dubeta wani ya ce “Baiwar Allah lafiya?” Ta jima kafin ta ce “Ruwa nake nema, zan bawa yarona” wani saurayi ya dinga kallonta kafin ya miÆ™e tsaye ya ce “Mene na rufe fuskar?” Ta É—auke kai cikin sa a ya gano rabin fuskarta da jaririn hannun da Æ™arfi ya ce “MasiÆ™a la’ananniyya mazinaciyya ku je feta ita ce Malama Majeederh” yana faÉ—in hakan ya sauke mata wani dutse a Æ™oshinta ji ka ke tauu!! Nan take ya fashe jini ya dinga zuba, kafin ka ce me mutane sun cika kowa ya É—akko duwatsu suka fara jifanta ta ko’ina ta durÆ™oshe ta rungume jaririn da jikinta, jama’a sunfi ashirin idan wannan ya jefa mata dutse aka sai Wannan ya jefa mata a baya…

Na’ima Sulaiman Shu’aibu
Nimcy sarauta
08119237616*MIJIN MALAMA*

Nimcyluv Sarauta
_*Follow my account*_
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv

African Queen products
Sabulun matsi
Garin matsi
Humra
Turaren wuta
Maganin Infection
Ga number wayata…08130269641

 

No comments