Breaking News

Munayamaleek 43


XLIII….
(43)

 

*MunayaMaleek is Five hundred naira only, via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, shaidar biya ta 07082281566(dan girman Allah idan baki shirya siya ba, don’t chat Me)*

 

 

Tsaye munaya take jikin motar doctor Abbas, yayinda Abbas din ke fuskantar ta, soyayyar sa yake kara shigar wa a zuciyar ta, ita kuwa tayi kasa da kanta Cikin jin kunya tana sakin murmushi, little Amnah na gefe tana wasa da teddy din ta.

“Dago ki kalli ni da kyawawan idanun ki kafin na tafi” Abbas Yace yana leken fuskar ta, ta kara boye fuskar Cikin jin kunya, shi kuwa Abbas yayi dariya cikin nishadi, sosai yake kaunar Munaya har cikin ransa.

Ya kalli little Amnah Dake faman yi wa teddyn data sanya wa suna amal surutu kamar mutum, yayi dariya yace “hira ake da baby amal din?”

“Eh! Daddy doctor wai yunwa take ji”

“Ita din?” Yace zaro idanunsa cikin dariya, munaya na taya shi, caraf idanun ta suka tsarke dana Maleek dake tsaye, dariyar ta ɗauke, ta kuma dauke kanta daga kallon sa.

Maleek kuwa yana tsaye daga ta cikin motar, yayinda kofar motar ta ƙare Wajen cinyoyin sa, hakan ya sanya daga fuskar sa sai faffadar kirjin sa ake gani daga ta sama, daga kasa kuwa kafafun sa ake iya hango wa, yana rike da car key din sa, fuskar sa a daure tamau.

“Little ga fa Daddyn ki can” little ta yar da teddyn hannun ta ta nufi wajen baban ta da gudu, ganin ta taho ya sanya shi fitowa gaba-daya yana rufe motar, ta rungume shi ya duka ya ɗauke ta, yace “little ki daina guduwa kinji kada ki fadi” ta lafe a jikin sa tana jinjina masa kai.

Munaya ta girgiza kanta, ta durkusa ta ɗauki teddyn little din, Abbas Yace “Toh baby ni zan wuce”

“TOH ya Abbas, bye”

“Bye bye baby na” ya fada yana huro mata kiss, ta rufe idanun ta cikin jin kunya, karaf a idanun Maleek.

Yace “soon zan cire miki kunyar nan gaba-daya” ya fada ya fadawa motar sa, ita kuwa kunya kamar ta nutse.

Maleek ya bi motar Abbas din daya wuce da mugun kallo, daga can Kasan zuciyar sa ya san cewa bai masa laifin komai ba, amma baya son sa tun daga ranar daga fara zuwa Companyn sa, sam Baya kaunar zuwan sa gidan nan, ba kuma ya son yin tozali da shi, amma Meyasa ya tsane shi, Meyasa baya kaunar ganin sa? Shine amsar da bai samu ba har yanzu.

 

Munaya kuwa ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya a lokacin da doctor Abbas ya gama fita daga gidan.
A nutse ta juya domin komawa ciki, tana jin little na cewa “mummyyy ga Daddy na” ta yi kamar bata ji ba, ta rasa yanda zata yi da little Amnah ta daina mata maganar baban ta amma yarinyar nan taki daina wa.

Tana daf da dora hannun ta a kan handle din kofar shiga falo ta ji yace “hey!” Cikin daurarriyar Murya.

Ta juyo cikin sauri domin bata ji takun tahowar sa ba, and she wasn’t expecting him.

“Wanna ya zama karo na ƙarshe da zaki ƙara fito min da ya wajen wani kato, dole sai kin fito da ita ne? Karki kara fito min da yarinya ta idan zaki yi zance”

Munaya ta juyo da kyau, ta kafa masa manya kana fararen idanun ta da suka dan rine da ja kadan sakamakon maganar daya gaya mata.
Ya ƙara rungume teddyn little da kyau tace “idan na ki fa?”

“Munayaaa You re trying my patient, kina gwada hakuri na fa” yace cikin kankance ido, karon farko data ji ya ambaci sunan ta and it sounds different to her hear, ba kamar yanda ta ji an saba kiran ta ba.

“Sai ka daina shiga harka ta, ko ka ga ina kula ka ne?”

” Na sha gaya miki times without number ke baki isa in shiga rayuwar ki ba, I just want the best for my daughter, duk abinda zan yi ko nace miki akan ya ta ne, ko na taɓa miki wata maganar?”

“Toh tunda kana nuna kamar ka fi son ta sai ka fadawa yar taka ta daina biyo ni idan zan fito wajen masoyina”

“Masoyi?” yace, kamar yau ya fara jin kalmar, tace “eh masoyina”

Sai bayan data maimaita kalmar ya fahimci subutar da ta yi.
Ya ɗan dafe kansa da hannun sa kana ya kalli cikin idanun ta sosai yace “karya kike bakya son sa, sai dai idan yaudarar sa kike, amma babu son sa a zuciyar ki”

“Ni kuwa nake son sa, so mai tarin yawa, za kuma ka tabbatar da hakan idan aka yi auren mu”

Buga kofar da ya ji ya sanye shi bude idanunsa daya runtse, haka kawai yaji zuciyar sa ta motsa data ambaci kalmar auren. Ya yi tsaye kamar mai neman wani abu, sai kuma ya juya zuwa wajen motar sa, ya bude Bayan motar ya fito da lunch box din little Amnah daya manta dazu lokacin ɗaya dawo ta, ya mika mata, sannan ya duka ya sumbaci kamatun ta yace “bye angel, I will see you tomorrow morning”

“Bye Daddy” tace tana rugawa.

Yace “stop running angle karki fadi faa” duk lokacin daya ga tana gudun nan zuciyar sa bugawa take, sam Baya kaunar wani abu ya same ta.

Ta tsayar da gudun data fara, sai ɗaya ga shigar ta sannan ya tada motar sa ya fice, tunani masu yawa suka cakude a ransa.

A wanna daren sai ya ji bacci ya kauracewa idanun sa, yana tsaya a jikin window’n Dakin sa, yana kallon daidai inda kabarin Shakur yake tunanin sa yayi nisa, shi kanshi idan aka tambaye shi dalilin daya sanya zuciyar damuwa bai sani ba, har karfe biyu da rabi na tsakar dare yana tsaye wajen kana kafafun sa suka yi nauyi, tilas ya dawo tsakiyar dakin ya hau kan gadon sa ya kwanta.
Tsawon mintuna goma kana idanun sa suka yi nauyi, suka kuma lumshe kansa, bacci ya dauke shi, a cikin baccin yayi mafarki… kiran sallar asuba ya katse masa mafarkin, ya mike hadi da sauke kafafun sa kasa, ya dauro alwala a toilet, kana ya fita a dakin, a falon ya hadu da Alhaji Dawood dake rike da shi, ya gaida shi kana suka nufi masallacin.

Bayan ya iddar da sallar asuba mafarkin daya yi yazo masa. A mafarkin an ce masa Shakur ne, amma bai ga fuskar sa ba, domin ya juya masa baya ne yana daga zaune, duk da bai ganin fuskar mutumin amma yana da hasken fata sosai, yayinda yake sanye da farar jallabiya, ya ji ya fara cewa “Assalamu alaikum ya kai dan’uwana, lokaci bai kure maka ba, Hakika babu wani abu da zuciya zata haddace mafi falala da daukaka, ta sami matsayi mafi girma kamar haddace maganar Allah, alqurani shine yake raya zuciya ya sanya ta samu nutsuwa da rabauta anan duniya da lahira, haddace alqurani ba karamar falala bace da matsayi wanda babu wanda yasan iyakar falalar da matsayinsa sai Allah, Allah yayi yabo na musamman ga bayinsa masu haddace littafinsa alqur’ani. Allah yace
( ﺑﻞ ﻫﻮ ﺁﻳﺎﺕ ﺑﻴﻨﺎﺕ ﻓﻲ ﺻﺪﻭﺭ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺃﻭﺗﻮﺍ ﺍﻟﻌﻠﻢ ).
Sannan Ana daukaka daraja da matsayin wanda ya haddace alqurani acikin aljanna
Manzon Allah s.a.w yana cewa
Za’ace ga ma’abocin alqurani karanta ka rera kamar yadda kake karantawa a duniya, domin matsayinka a aljanna yana tsayawa akan ayar karshe da ka karanta.
Ana sanyawa Mahaddacin alqurani kayan ado na karama da yardar Allah agareshi.
Manzon Allah s.a.w yana cewa Alqur’ani zai zo a ranar alqiyama yace ya Ubangiji kayi masa ado wanda ya haddace Ni, sai a sanya masa kambi na Karama, sannan sai Alqurani ya kara cewa ya Ubangiji ka kara yi masa ado, sai a sanya masa kayan ado na karama,sai Alqurani yace ya Ubangiji ka yarda da shi,
Mahaddacin Alqurani yana tare da tawaga ta Mala’iku ma’abuta karamci da daukaka.

Manzon Allah ya ce a wani kyakkyawan hadisi
idan mutum ya mutu danginsa sun shagalta da jana’izar sa wani kyakkyawan mutum zai tsaya a kansa a lokacin da aka rufe jikin mamaci, wanna mutumin yakan shiga tsakanin mayafi da kirjin sa, bayan an binne sa Mala’iku munkar da nakeer zasu zo cikin kabarin sa suna kokarin raba wanna kyakkyawan mutum da mamacin domin yiwa mamacin tambayoyin game da imanin sa, amma kyawawan mutumin nan zai ce abokina ne shi, bazan barshi ba shi kaɗai, idan an naɗa ku domin tambayoyi ku yi aikin ku, bazan iya barin shi ba sai na shigar da shi aljanna.
Sai kyawawan mutumin nan yace wa mamacin nine Alqur’ani, wanda ka saba karantawa wani lokacin da babban murya wani lokacin da kamar murya, karka damu, bayan munkar da nakeer sun gama maka tambayoyi bazaka sami bakin ciki ba, bayan nakeer da munkar sun ƙare tambayoyin su, sai kyakkyawan mutumin nan ya shirya masa daga al-mala’ul a’alaa, wato shimfidar siliki cike da Muski. Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace a ranar sakamako, a gaban Allah babu wani mai ceto da zai samu matsayi sama da mai karatun Alkur’ani, dan haka dan’uwana ka tashi, Domin lokaci baya hannun ka.

Maleek ya sauke numfashi bayan ya gama tunanin mafarkin da yayi, ya waiwaya jin Muryar wani mutum na karanta Kur’ani daga bayansa, ya ji abin ya burge shi matuka, yana kara jin ciwo rashin iya karanta Kur’ani, har yau bai san Meyasa bai iya ba, ko harafi daya bazai iya karantawa ba idan an buɗe masa Kur’ani, ya furzar da numfashi mai zafi daga bakin sa, kusan kowa ya fice daga masallacin, shima ya mike ya fita, yana buɗe gate direct bayan gidan ya wuce domin yiwa Shakur ɗin sa addu’a kamar yadda ya yi alkawarin yi masa, wanda hakan ya zame masa tamkar al’ada duk bayan sallar asuba sai yace kabarin na sa, yana tsugunne gaban kabarin har karfe takwas saura mintuna goma sannan ya mike domin yayi shirin zuwa Company.

Bayan yayi muhimman aikin dake gaban sa ya janyo wayarsa, islamiyya yayi browsing, nan aka watso masa kala kala, a ƙarshe ya zabi wanda yafi kwanta masa, ya kuma duba address din, karfe 12 ya bar office dinsa zuwa makarantar, a takaice yayi registration a makarantar, kasancewar Companyn kansa gareshi bai da matsala da wurin aiki.

A ranar daya fara zuwa islamiyya sai ya ji shi tamkar wani sabon halitta, domin tamkar yanda ake fara koya wa kananan yara karatu haka akayi musu.
Cikin sati Daya yaji shi wani daban, nutsuwa na saukar masa, duk da cewa iya kananan surori kadai ya iya.

 

*Bayan shekara biyu*

Munaya ta gama makarantar ta, inda satin ta biyu kacal a gida doctor Aaban ya samo mata aikin a wani Babban Asibitin hakori dake nan Abuja.
Munaya ta ƙara wani kyau da cika, farar Fatar ta sai sheki, idan mutum ya ganta bazai taba cewa ita ta haifi little Amnah ba, tsakanin ta da Maleek kuwa har yanzu bata sanja zani ba, kullum Cikin gindaya mata sharudda akan yarsa yake, ita kuwa ta kauracewa duk wata hanya data san zai ganta, ɓalle har ya mata magana, sai idan bisa kuskure ko rashin sani suke ganin juna.

A yau doctor Abbas ya zo gidan doctor Aaban, suna cikin hirar su yace “jibi in sha zan tafi Kano domin ina son gabatar wa mahaifiyata maganar auren mu. Domin na matsu na ganki a gidana, kada wani ya kyalla ido ya kwace min ke, domin na ga take-taken yan garin nan kenan”

Munaya tayi dariya cikin jin kunya tace “kwantar da hankalin ka, Ni taka ce, bazan taba juya maka baya ba”

“Naji dadin wanna kalaman na ki, Kinga da barrister zata bani aron ki ai da kin min rakiya zuwa Kanon, amma na san bazata taba yarda ba, amma ba komai, kwana nawa ne zan dauke ki a gidan nan, domin bana son maganar auren ya ja lokaci sosai.

Munaya tayi shiru wanna karon doctor Abbas Yace “menene, why the sudden change?”

Ta dago idanun ta ta kalli shi, yace “oh na gane, little ko? Matukar baban ta ya amince tare zamu tafi gidana da ita, idan kuma bai amince ba dole kiyi hakuri.

“Dole ma ya amince, ai na san little bazata zauna wajen sa ba”.

“Idan ta Gwale ki fa” ya ce yana mata murmushi.

Sanin irin son da little Amnah take wa uban ta sai ta kwabe fuskar ta kamar zata yi kuka, ya saki dariya cikin kara jin son ta, domin shagwabar ta na daya daga cikin abinda ke burge shi gami da ita.

 

_na san bakwa son Maleek ko? Su team Abbas how far? Ya kuke ganin auren Abbas da gwanar taku zai kasance_ _

No comments