Breaking News

Tayi Min kankanta 19


19*

 

Cikin tsananin firgita jameel ya juyo yana kallon Hammad,kamin yayi wani abu hammad ya cakumoshi ya bugasa da jikin bango,ya fara kai masa duka yana fadin.

“macuci azzalumi,Allah ya toni asirinka,dama kaine ka haike mata,shine yanzu kazagayo zaka É—ora,kabani mamaki”yaci gaba da kai masa duka.

Tsananin mamaki ne yasa jameel kasa furta komai,yakuma kasa kwace kansa a hannun hammad É—in.

Zahra cikin zafin nama tayi kanshi tana faÉ—in”yaya me yayi maka ka Æ™yaleshi,ina ruwanka dashi,”tana jan rigar hammad É—in.

A fusace ya juyo kamar mayunwacin zaki ya kife ta da wani wawan mari,take yanke tasaki fitsari,sakamakom taurarin da ta gani na gilmawa a idonta.

“munafuka,ke har kina da bakin magana,shiyasa kika Æ™i faÉ—in wanda ya maidake garejin ashe wannan munafukinne,to wlh ba agidana zakuyi bariki ba sede awani gidan”

Jameel tunda hammad ya koma kan zahra ya zame jikinshi ya fice agidan ko ganin gabanshi bayayi sabida tsananin É“acin rai.

Hammad rasa abunyi yayi kawai shigewa cikin gidan yayi ya barta kwance agurin tana kuka.

A falo ya zauna yana huci kamar zaki.
Jiki asanyaye zahra ta miƙe ta nufi cikin falon,yana ganinta ya ɗauke kai.
DurÆ™usawa tayi agabanshi tana kuka,cikin kukan tace”jameel ba fasiÆ™i bane yaya,hasalima hannuna be taÉ“a riÆ™ewa ba se yau,shima nice nayi kuskuren rungumeshi,nasan shine agarinmu falgore,inda ya nemi taimakon girko abinci sabida wani abokinsa dake fama da cutar ulcer,na rabu da jameel ne ranar da Æ´an taadda suka zo garinmi suka kashemin innata,inda na haÉ—u da abokin jameel É—in sojan me ulcer daya keta mutuncina ana ruwan sama acikim wata bukka dana shiga domin ceto rayuwata,har baÆ™in mugun yace min jameel É—in ya mutu,Allah ya isa tsakanina da kai soja me ulcer bazan taÉ“a yafe maka ba mugu azzalumi,baÆ™in kare wanda baze shiga aljannah ba”ta Æ™arasa maganar cikin matsanancin kuka.

Hammad wanda yayi tsit kamar ruwa yacishi,jin abinda zahra ke faɗi,wasu hawayene masu zafi suka zubo afuskarsa,zuciyarshi ce tai masa nauyi,da ƙyar yace.

“kina nufin kece Æ´arfillo?”

“Nice yaya,hala ya baka labari na”

Wata ajiyar zuciya yaja sannan ya yanke jiki ya faÉ—i agurin ba numfashi,wani farin kumfa na fitowa abakinsa kamar yasha guba.

A gigice zahra tayi kanshi tana kiran sunansa tana girgizashi amma ina ko motsi baya yi.

Da gudu tayi gurin me gadi,ta kirashi koda yazo yaga halin dayake ciki,wayarshi ya ciro ya kira daddy kasancewar yana da numbarshi,baa jima ba,daddy ya iso da tawagarsa hankali atashe aka É—auki hammad zuwa asibiti rai a hannun Allah zahra se kuka takeyi kamar ranta ze fita,dan gani take hammad dinta ya mutu.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo:  *TAYI MIN ƘANƘANTA*


*Zahra Surbajo*

 

No comments