Breaking News

Rainon Soja 48-49


48~49

Chapter 48 #Rabi
#Aruguntsu
#Hajiya Falmata
#Nasreen
#Hajiya Atika ??????? .

*Don Allah kar ki karanta mun Wannan labari ba tare da kin biya Ni ba , Ga masu bu?atar payment regular group ?500 Vip group ?1000 SPC payment ?1500 via 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai a tura ta Wannan number 09061466409 yan Niger katin Artel na 500f kacal zaku tura???? .#mmnteddy.*
_________________________

Sanyayyar kallon nan nata Tabi su da shi kana ta ?an yi murmushin nan nata tare da cewa “ Laa! Uncle Areeef Kai ne ka zo? Ya Khalil…..zaraf Khalil ya katse ta bai barta ma ta ida zancen ba yana cewa “ ai na ?auka ta Areeef kike kin manta Dani….” ?ar Dariya tayi Kuncin ta na lo?awa kana tace “ A’a , Ya Khalil ina Mom Hajaran wannan ce? Ta furta tana kallon inda Hajiya Hajara take zaune gimgiringin . Gya?a mata kai Khalil yayi inda cikin Wannan Halin nata da Son faranfaran da mutane ta mi?e da Gudu tana nufar Mom Hajara tare da saka hannu tana Rungume ta tare da furta “ Mommy munyi kewarki sosai , Kema kin yi kewar mu kamar ……Ya isa! Ni ba Mommyn ki bane! Kinga yara na nan , ke dai ban san a ina aka ?auko ki a ka kuma kawo ki cikin Ahalin mu ba . Mu duka nan muna da gata da tushe asali”.

Wani irin Dariya Maryam da Jidder suka saka a tare har da shewa, Wanda yasa Mami jin Wani irin ?acin rai , Kasa magana tayi kurum sai Wasu irin ?wallah da suka zubo mata tana kai hannun ta tare da ?aukewa , tabbas a yanzu ta kasa Bama Mom Hajara amsa saboda kunyar yarfin da tayi mawa Ma’eesha….Hannu Ma’eesha tasa tana ?ara Rungume ta cike da yarinta, cikin Sauri Aliyu ya fizgota da ?arfi daga jikin Mom Hajara Wanda duka sai da suka tsorata yana Ha?a Ma’eesha da jikin sa tare da Rungume ta , A hankali ta ?ago idanun ta wanda a yanzu fal damuwa ne cikin su , amma tana kallon sa sai ta Wangale masa baki ….kan sa ne ya fara juya masa , tamkar hakan tayi mun a gani na farko. A lokacin da take cikin ?unci da kukan rashin iyaye amma tana kallon fuska na sai tayi murmushi har da Dariya kamar dai haka …..Ya furta yana nuna Ma’eesha da hannu idanun sa na kan Mom Hajara Wanda yake kokarin fa?a mata maganan da duk tazo masa. Kin ce bata da gata haka ne? Kin ce bata da Asali? To Wallahi indai na cika ?an halak yau sai na zama gatan ta , gata kuma na har Abada!

Aliyu!!! Khalil ya kira sunan sa yana saurin mi?a daga tsaye. Ya isa da Allah ku ?an rabu da mutane! Munafukan banza.

Ohhhhk Ya tabbata rashin kunyar naka zaka mun kenan? Tabbatacce! Mom Hajara ta katse shi tana bin sa da wani irin kallo , kana ta cigaba da cewa “ karya ne , tana da Asalin ne? Idan kuma kasan Asalin ta to ka fa?a a yanzu. Ali bana son ?arajin bakin ka , Wuce ka fita ka bani wuri . Muryar Mami ya katse shi , inda cikin jan rai da zafin zuciya , yana Wani irin Tsuma kamar zai kada Rundunar maya?a ya furta “ a lokacin da kuka ?i ta Ni naso kayana, har kuka ?aunace ta , Wallahi na rantse da ALLAH Mami a yau sai na Auri Ma’eesha fitar nan da xanyi ba zan dawo ba sai a matsayin miji gareta! Daga nan na zama mata gata da ahalin da komai.

?aaaaaaammmmm!!!! Duka suka yi , kowa da Abun da ?wa?walwar sa ke basa . Kai wannan shashanci ne! Wacce zaka Aura? Kayi ha?uri mu shiga daga ciki dai. Ya Khalil ya furta yana saurin takawa ixuwa inda Ali ke tsaye , ita ko jidder suman zaune tayi….. Da ?yau Jarumina! Haka nake so!

Su duka saurin juyawa suka yi suna bin Inda General Saleh Yelwa yake wanda ya da?e da isowa falon duk basu fargaba . Na gode Aliyu na gode Allah yayi maka Albarka, Ni ne mai bayar da Auren Ma’eesha, kuma yanzu zan kira iyayen ka don a zauna ,kamar yanda kace a yau to babu fashiiiii na baka Amana…………….!

Aure fa kace Alhaji Sale? Yanzu Aura ma Aliyu Yar tsuntuwa zaka yi wanda baku san Asalin ta ba? Mom Hajara ta katse su cike da ?acin rai tana mi?a daga tsaye a matu?ar harzu?e . Juyawa Aliyu yayi yana kallon Ma’eesha wacce hawaye duk ya gama ?ata mata fuska , Idanun ta sun kumbura fuskar ta ya ?ara haske da ja abunka ga farar fata . Yi ha?uri mu je daga ciki. Ya furta yana kallon ?wayar idanun ta. Jan Ajiyar zuciya tayi mai nauyi kamin ta motsa Jidder ta furta “ Wallahi ba zata shiga cikin ba Ya Haidar , tabbas wannan yarinyar yanzu na ?ara gasgata musiba ce a cikin Ahalin mu. Ma’eesha Alheri ce a rayuwar Haidar! Mami ta furta tana kallon Su duka , kana ta kalli Ma’eesha tana furta “ Ma’eesha kina Son Haidar? Zaki zauna dashi? . ?agowa Ma’eesha tayi tana kallon mami kawai sai ta fashe da kuka , Wannan yasa mami saurin Rungume ta duk da itama Hawayen ne ke bin kuncinta .

A hankali ta furta kiyi Ha?uri ki zauna dashi , nasan zai kula mun dake sosai , Sannan ki ri?e shi Amana ko bayan Raina, Haidar da Sonki yana ?aunar ki , duk abun da kika ga yanayi Miki SOYAYYA ce ta saka shi hakan……Mami wannan ba haka bane! Sam Haidar baya son Ta Wallhi ”. Khalil ya yi maganan cike da ?acin rai , da nuna kishin sa a sarari .
Duka kallon sa suka yi , Ma’eesha na cigaba da rera kukan ta a hankali….inda Khalil ya cigaba da cewa “ Indai nagartacen miji ake so aba Ma’eesha to Ali baya cikin su , wallahi har gwara Ni sau dubu zan fi kulawa da Rayuwar ta. Don haka Ni zan Aure ta shi a barshi yayi sabgar rayuwar sa.

Mi?ewa Maryam tayi dake zaune tana ?aura hannu aka tare da yanka ihu tana furta “ Na shiga uku , Khalil wannan wani irin cin mutunci kake ?o?arin mun? Wacce zaka Aura? Meye kuma matsayi na? . Matsayin ki na nan , a tare Daddy don Allah ka Aura mun su , amma Aliyu ya Auri Ma’eesha Tom azabtar da ita zai yi . Babu Ruwar ka Wannan! Maryam ta katse shi kamin Daddy yayi magana . Gaba ?aya wuri ya rikice. Mami dai kuka Ma’eesha kuka. Aliyu kuwa na Jaraba da masifa tare da cewa “ Babu wanda ya isa yayi masa iko da Ma’eesha.

Mom Hajara kuwa tafa hannu take yi tana salallami, Muryar Adams ne ya katse su inda sai a yanzu yayi magana cikin natsuwar sa da Ajin sa . Kuyi hakuri duka , kuna ji Daddy Mami Mom Hajara, duka ku fahimta…. inasha Ma’eesha ce bakwaso gani a halin ku , To don Allah Ni ku bani Auren ta a yanzu Nima a shirye nake , zan yi komai da ake bu?ata indai burin ku taji da?i ne , wallahi…….Kai da’alla yi mana shiru sakaran banza . Aliyu ya katse Adams yana isowa gaban sa tamkar zai rufe shi da duka . Munafuki To Aure ta idan akan ka take! Ni soja ne Aliyu na wuce ka kira Ni da Sakarai kuma Abokin yayan ka”. And so what? SOJAN banza Sojan wofi a yanzu fighting ake yi against love ba maganar soja ba . Babu wanda ya isa yayi mun iko da Ma’eesha tawa ce! Duk wanda yayi yun?urin rabani da ita wallahi ba zan bar shi ba.

Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un kalmar da Mami ta furta kenan tana Girgiza Ma’eesha tare da kiran sunan ta da ?arfi“ Ma’eesha…………”
[1/24, 6:01 AM] Real~Mamanteddy: *(Book 3 three)*
*Love and Amazing story*
*Written….??? Aysha Mamanteddy Mrs Usm*

_________________________

*RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*

*Littafin na ku?i ne please ban yarda wata ta karanta mun ba tare da Ta biyani ba , regular group ?500… Vip group ?1000… SPC payment ?1500 via 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932#?????? .*

 

No comments