Breaking News

Rainon Soja 52-53


52~53

Aure!

Muryoyin matan Falon ya amsa a tare kana Aliyu ya saki Wani irin Ihun farin ciki yana furta kalmar godiya ga mahaifin nasa tare da cewa “ That’s my Dad! Daddy na gode ka bani duk Abinda nake so tun daga yarinta na har girma kana faranta mun , Allah ya kare ka daga dukkan sharri ya kuma bamu ikon biyayya a gareku. Na gode Dad . Juyawa yayi yana kallon su Alhaji muddasir da Alhaji Kawu kamin suma ya fara kokarin yi masu tamkar zai zube yayi sijjada Saboda tsaban Farin ciki . Wani irin farin ciki ne ke ratsa Zuciyar Mami da Daddy , Tabbas a yau sun yarda Ma’eeaha rayuwar Ali ce gaba ?aya . Gaba ?aya ya Saki ya dawo tamkar bashi ba , wannan jin kan da Miskilancin babu sai zallar Annuri dake fita daga fuskar sa . Dad! Muryar Khalil ya katse su cikin sanyi , Wanda hakan yasa duka kowa mai da kallon sa gare shi. Gaba ?aya ya sauya fuskar sa babu Walwala , Ga tarin damuwa ?wance cikin wata irin nannauyar murya ya furta “ Shin Da Gaske ne Wai Ali ne kuka ba shi Auren kamilar Yarinya ?arama kamar ma’eeaha? Why baku Aurar da Jidder wacce ta kere mata Ashe karu nesa ba kusa ba ? Wannan ba kuyi san kan ku ba kuwa duka saboda ?an ku ya gyaru kuka yi hakan ba don kuna ?aunar ma’eesha ba!

Ali….Al…Muryar Daddy ne ya fara kyarma so yake ya kira sunan Khalil amma kuma maganan sa ta sanya ?aguwar hankali da mamakin furucin nasa sai yana kiran sunan Aliyu instead ya kira sunan Khalil . Fahimtar Sunan shi ?in yake SO ya kira yake kiran na Aliyu yasa ka Khalil girgiza kai tare da cewa “ Of course yes Daddy! San Kai kuka yi. Waye bai san Halin Aliyu ba tun yana ?arami? Baya ji ….Sannan mazinaci ne mai lalata yaran mutane Sannan yanzu kun ?auki ?aramar yarinya Which she’s not up to 15 Kun bashi …..Wato idan ya kashe ta Ai babu mai Asara . Sannan sha’awar ta yake ba Sonta yake ba i have since observe this……Ku mai yasa baku fahimta hakan ba Daddy kuka………..Ya isa Khalil, Ranka zai mummunar ?aci yanzu! Muryar Mami ya katse su cike da doka Wani irin rikirkitaccen Tsawa . Kallon shi take yi cike da ?acin Rai tana Wani irin Girgiza kai na tama rasa mene zata ce .

Ka ?yauta! Mami ta furta kawai tana kai hannun ta tare da ?auke ?wallar da suke zubo mata .

Koma Meye Ni Alhaji Sale na yanke Wannan hukuncin , kuma ma’eesha ?a ta ce naba Ali haidar Auren ta , idan ya cuce ta ko ya zalunceta Amana ce Allah zai saka mata bamu ba. Daddy ya furta yana kallon kowa na Falon, Inda Alhaji muddasir ya fara magana da cewa “ Wai meke faruwa ne cikin gidan nan? Shin da gaske ne Kalamar Da Khalil yayi akan Haidar? Idan kuwa da gaske ne to tabbas da A?wai tarin matsaloli. Wanda bata tunanin a ?auki yarinya ?ar teenage age a bashi . Shima bai gama hankali ba , don mai hankali ba zai zina ba.

Rintse ido Mami tayi tabbas ba zata yi shaidan Ali ba. A hankali cike da Sanyi Alhaji Kawu yace “ A’a Ni sam ban yarda da Wannan Al’amari ba , Ali yaron kirki ne …..Ga Abin da Yayan sa ya fa?a wanda suke tare tun daga Karatun Soja har yanzu , yafi mu sanin Waye Aliyu , Sannan tausayin yarinyar yasa shi fa?in haka . Dole a?wai lauje cikin na?i. Muryar Alhaji muddasir ya katse su cike da Zafin nan nasa . Don shi mutum ne mai Masifar fa?a , kowa tsoron shi yake yi , idan yace abu ba mai tsallake masa .

Maryam Jidder Hajiya kaka da mom Hajara su dai tun da suka zauna suka ji labarin an ?aura Auren Ali da ma’eesha motsawa dayan su babu wanda yayi duka sun kasa.

Cikin Tsawa Alhaji muddasir yace “ Ali bu?e baki kayi mana magana shin da gaske ne kana lalata yayan mutane? Fa?a mun yanzu naji muna saurarenka”. Dammmmm ?irjin Mami ya buga da ?arfi don tabbas ba zatayi shaidar Aliyu ba , sannan kuma ta san shi baya ?arya ko da kuwa za’a kashe shi ne , yana da Wannan taurin zuciyar .

Areeef da Adams Sada kai sukayi ?asa , don a yanzu Khalil sam bai ?yauta masu ba . Kuma basu ji Da?in Wannan Abu ba , saboda sun san Aliyu Wallahi ba zai ?arya ba koda za’a mutu sai ya fa?i gaskiya ”.

?ago da Lulun idanun sa yayi na rashin tsoro yana zuba su bisa Na Alhaji muddasir da Sauran kowa na falon . Gya?a kai yayi yana motsa la??ansa zai yi magana kenan Muryar ta ya katse su tana cewa…………………

 

*Morning ????? .*
*Don Allah kar ki karanta ba tare da kin biya ba . Regular payment ?500 Vip group ?1000 SPC payment ?1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932#Antymmnteddy*
[1/25, 8:56 AM] Real~Mamanteddy: *RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

No comments