Breaking News

Rainon Soja 58-59

58~59

*Don Allah masu karantarwa basu biya ba ku dakata da yin hakan , Allah fa akace , Allah ya wuce Abin Wasa. Magana ta ?arshe da xanyi shine duk Wacce ta karanta ko ya


karanta wannan labarin na Rainon soja bai biyani ha??ina ba na bari da ALLAH . Haka masu sharing password na book 2 a dakata a bari idan book 2 ?in kake da bu?ata ?500 ne kacal . Haka ga masu bu?atar payment na littafin nan soja duka ga yanda tsarin yake…. Regular group ?500 Vip group ?1000 SPC payment ?1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 only WhatsApp please.*

#Book 3.
Wani irin sarawa kan sa keyi, a hankali ya ke zuba mata manyan idanun sa da suka ?ara rinewa tamkar garwashi. “Ma’eesha ….Wani irin kyarma jikin sa keyi , ya rasa ta ina ma zaiyi mata Magana duk don ta fahimce shi. Ja baya tayi tana komawa tare da ?wanciyar ta tana lumshe lumsassun idanun ta tare da cuno masa ?aramin bakin ta wanda yaji tamkar ya cafka….Ni barci nake ji yanzu ”. Ohk! Ya furta yana kai hannun sa tare da ja mata blanket. Tana jin sa yana kissing ?in saman goshinta kana ya juya jiki a sanyaye yana fucewa daga Bedroom ?in.

Ba tare da ta bu?e idanun ta ba , Take tunanin Rayuwar ta. Ni har Abada ba zan ga kowa nawa ba kenan ? Ba zan taba ganin mahaifiya ta ba , da mahaifi na bare kuma ?an uwan su … Magana Doctor Isma’il ne ya dawo mata a ?wanya….“ Kar kiyi ma kanki sakiyar da ba ruwa, ke yarinya ce , amma ki tsaya kiyi tunani da hankalin ki, ki aje maganar yarinta saka ma kanki ?wa?walwar manya. A ta?aice Abun da zance Miki shine , a ko wani hali kada ki ta?a Rabuwa da Haidar….ki ?auke shi numfashin ki. Domun haka yayi Miki lokacin Yarintar ki. Har mutuwa ya kusa yi saboda ke , da taimakon Allah da kuma dabarun mu na likitoci muka ceto rayuwar sa. Duka akan kowa baya son ya Amshe ki ya Raine ki , A lokacin da har Iyayen sa suka karkata akan a mi?a ki gidan marayu , babu Azaban da bai sha ba a cikin wannan gida duka saboda ke! Shawara ya rage naki a yanzu a falo ana gab da warware wannan Auren da aka daura shi a yau ….zaki iya zuwa don dakatarwa don aka Warware wannan Auren to ki sani tamkar Rayuwar ki ce aka Datse babban gi?i aka yi Miki……….Huwm” Ma’eesha ta sauke Wani irin dogon Ajiyar zuciya. Kan ta ciwo ma yake yi , abubuwan har yanzu ta rasa fahimtar farkon su bare karshen su ,wannan shine iyakar Abin da Doctor Isma’il ya fa?a mata na Rayuwar ta da Aliyu bayan nan bata san komai har yanzu. To amma me yasa yake Azabtar damu, kullum fa burin shi yaga ya ?untata mun bai son farin ciki na duka ”.

Humm To amma a Wancen lokacin har ta mami da Daddy ya Khalil suna ina ne ake shirin kaini gidan marayu? Sannan a wurin waye Uncle Aliyu tasha Azaba a saboda Ni? Dole na san komai , nima a yanzu ina so na san rayuwata da abun da ya ?unsa na baya .

A falo ?angaren Su Hajiya kaka abun ka ga tsohuwa mai hangen nesa , Tuni su Alhaji muddasir suka shawo kannta tare da nuna mata idan zuri’arsu bata Auri Ma’eesha ba to waye zai aure ta su samu kwanciyar hankali kamar jinin su ? A yanzu Ma’eesha ta zama su , don haka hakuri shine ya zama dole….Itama Abun ayi mata kuka ne rashin a hali da zafi ,duk da har yanzu bata san ra?a?in ba , sakamakon yanda Mami ke kulawa da ita tare da bata gata .

Ita dai Mom Hajara takaici da bakin ciki ko mintuna Goma bata ?ara ba ta bar cikin gidan , haka Maryam da mahaifiyar ta Wanda suka tafi suna sambarka. Dama lokacin Auren ka?an ya rage a cewan su wata mai tsayuwa .

Tun daga Wannan Rana gidan General Saleh babu wani walwala irin ta da. Gaba ?aya iyayen sun kasa fahimtar kan gadon yaran nasu. Kowa da Abin da ke ran sa . A haka Aka kwarari sati biyu , A gaban mutane Ma’eesha bata nuna ma Aliyu komai ,sai sun kasance daga shi sai ita ,anan zata fara bijiro masa da Tsiya iri iri na nuna ?i da halin ko in kula. Gaba ?aya yayi yaushi ya sauya . Don a yanzu koda ?ammatan sa sun kira sa tsakanin sa dasu ya? Ina son ganin ka ….sai yace bani da time . Ya datse kiran , a haka Yake rayuwa duk da shi mutum ne mai shegen son mata amma a wannan kwanakin sam basa burge shi , damuwar sa Guda Ma’eesha, Wacce a yanzu ta warware jiki babu ciwo sai godiyar Allah. Yaso tun a Wancen Satin ya ?auke ta ya koma bakin Aiki da ita ,amma Mami tace sai ta kara samun sau?i taga kuma sakin jikin ta dashi . Wannan yasa Aliyu duk abun da take masa ya kwantar da kai bai ?aga mata murya bare ya kai mata duka irin da baya .

11:pm ”…. ?wance yake yana Sauke numfashi sama sama , ?ara gudun A.C yayi yana rage hasken Bedroom din zuwa dumb light. Wani irin maran sa ke ciwo tamkar zai haukace ya mutu don azaba haka yake ji. Tabbas yasan yayi ha?uri da tsawon wannan lokacin yake tare kan sa akan ko wacce ?a mace! Fiye da mintina sha biyar , yana a haka kamin ya fara jin sasauci yana fara motsa idanun sa a hankali tare da kai hannun sa yana ?aukar Wayar sa tare da fara kiran numbern Ma’eesha don a jiya ya cire a wayan Mami.

Sosai tayi nisa a barcin ta mai da?i ta nitsa cikin blanket, sai dai tana da ?abi’ar Barci da Waya a jikin ta , Wannan yasa yana fara bugu gigif ta mi?e don tsoro taji ganin kira a wannan lokaci. Mutsike idanun ta tayi tana ?ara kyaf² da su tare da kallon ba?on numbern da ake kirannta da wannan dare haka. A haka wayar ta katse batare da ta ?aga ba. Tana ?an jan tsaki kenan wani kiran ya ?ara shigowa . Cike da ?an sanyi irin nata na masu barci ta ?aga wayar tana furta “ Hello! ….Come to my room now! ”. Saurin kallon wayar tayi tana bin numbern da aka kira ta da kallo , cikin Muryar nan nasa na gadara wai tazo ?akin sa yanzu ?? . Mamaki ne yasa Ma’eesha furta “ Waye wai ? Uncle ne? ” . A maimakon ya bata amsa sai ji tayi yace “ Ina jiran ki yanzu don’t keep me waiting…kit Taji ya datse kiran…turusss tayi tana bin Wayar hannun ta da kallo.

Wani irin jan numfashi tayi tana motsa la?ban ta tare da magana tamkar da wani a gaban ta “ I should go to his room in this midnight ? No……………!
[1/25, 4:21 PM] Real~Mamanteddy: *???RAINON SOJA???*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

 

No comments