Breaking News

Yanci da Rayuwa 21


Arewabooks; hafsatrano

Page 21

****Washegari Mummy ta tashi da wani irin karsashi dan tabbas ta riga ta san burin ta ya gama cika. Gyaran gidan kawai ma’aikatan gidan keyi kamar za’a sauya shi saboda yadda Mummy take so komai ya zama in place kafin lokacin yayi. Hajiya Lubabatu ce ta fara zuwa sai sauran kawayen Mummy din da yan uwa da abokan arziki da ta gayyato domin tayata farin cikin danta duk ta kasan zuciyar ta ba wai na farin cikin Rafeeq din bane na farin cikin cikar burin ta ne musamman da AJI ya dauki Asim suka tafi tare wannan rana ce me muhimmanci a gare ta ko ba komai tasan duk dauriyar Rafeeq din sai ya zubda hawaye a yau.
Shewa suke da hayaniya har basu san da shigowar Laila da Ummita ba sai da suka karaso tsakiyar falon fuskar Lailan tayi wani irin tashi saboda kukan da ta shaka.

“Sannun ku da zuwa.” Mummy tace tana kallon fuskar Lailan dauke da murmushi

“Mummy magana zamuyi.”

Ummita tace tana wuce wa ciki Lailan ta bi bayanta. Tashi tayi tabi bayansu ta tarar dasu a dakin Aneesa Laila na cigaba da dirzar kuka kamar wadda uwarta ta rasu.

“Ke lafiya? Kukan me kike hala?”

“Mummy wai da gaske yau za’a je nemar wa Ya feeqq aure?”

“Eh da gaske ne, me ya faru?”

“Mummy Laila fa?” Ummitan tace tana zaro ido

“Hakuri zatayi kawai, yace baya so ya zan masa? Kinga ai baa wa namiji dole.”

Tace tana yin gaba ta fice daga dakin cikin jin haushin Lailan da kukan da take yi wai akan Rafeeq sai kace wani kanin ubanta. Tasowa Aneesa tayi suka sakata a tsakiya suna bata baki har tayi shiru ta tashi ta shiga toilet ta wanko fuskarta tazo ta shafa mai da powder kamar ba ita ta gama cin uban kuka ba, dole ta cije ta daure domin cikar burin ta dan Rafeeq ita ya fara so kuma tasan har gobe yana sonta kawai dai yana fushi da ita ne amma zata dawo da tsohuwar soyayyar tasu duk da ya jaddada mata ya kara ba zai iya soyayya da ita ba, infact ya tsaneta ma tsana irin wanda ko kusa ko nesa baya son ya ganta, duk da hakan ba zata karaya ba, zata jira taga kalar yarinyar da ya kwaso daga nan zata san abinda zatayi ta sake winning zuciyar sa duk da a chan bayan ma kamar tausayin ta kawai yake amma dai ko me menene dai ba zata karaya ba.
Suna zaune a dakin Ummita da Aneesa suna hira ita kuma tana chatting a Instagram mummy ta sake shigowa dakin ta same su.

“Kin gama kukan?” Tace tana kallon Lailan sai ta gid’a mata kai alaamar eh.

“Good for you, ku taso kuzo falo.”

Tace tana juyawa ta fice tasha kwalliya cikin yan ubansun kaya masu matukar tsada da kyau. Tashi sukayi suka fita falon suka zauna aka cigaba da hira.

***Da duku duku Baba ya tashi, yace wa Noor zai je unguwa ya dawo, taso ta rakashi amma sai yace mata ta zauna ta gyara gidan ba dadewa zai ba. A hankali yana lallabawa ya fito titi ya sanu taxi ya hau ya fada masa in da zai kaishi, suna isa ya bashi kudin sa sannan ya karasa gaban tankamemen gate din gidan ya kwankwasa ya tsaya kadan kafin gate man din ya leko sannan ya taso yazo ya bude masa.

“Welcome Sir.” Yace masa yana bashi hanya

“Thank you.” Baban yace ya wuce gaba zuwa in da ake ajiye motocin gidan sannan ya ciro wayar Noor daga aljihu ya kira number tasa.

“Ina harabar gidan.”

“A ah ba sai na shigo ba, nan din ma yayi.”

Katse wayar yayi ya goya hannun sa a baya yana jiran ya fito. Yana tsaye ya fito ya zo ya same shi yana kallon yanayin fuskar sa da take da karancin walwala.

“Sannu da zuwa Yaya.”

“Yawwa sannu, kuna lafiya?”

“Lafiya lou, ka shigo ciki dan Allah.”

“Karka hada ni da Allah domin ba shiga zan ba, nan din ma yayi muyi maganar dan sauri nake a hanya nake.”

“Toh bari a kawo kujeru.”

“Bani da bukatar sai dai idan kai ne zaka zauna.”

“Shikenan a barsu.”

“Madallah, akan maganar da na kiraka dai ce, sai dai inaso na jaddada mahanar ne yasa na tako kafa da kafa nazo, kasan cewa bani da kowa a duniyar nan sai diyata, Kuma zan iya komai domin farin cikin ta. Toh yau za’a zo tambayar aurenta, inaso ka shige min gaba ka zame mata uba kayi mata duk abinda zaka yi ma yayanka, nayi maka alkawari idan har kayi min wannan ba zan sake neman wata alfarma a wajen ka ba.”

“Zanyi iya kar kokari na, nayi mata duk abinda ya dace irin wanda uba yake wa yarsa, amma dan Allah Yaya ka zauna mu fuskanci juna, na gane kuskure na wallahi kuma nayi nadama…”

Hannu ya daga ya dakatar dashi yana girgiza kai

“Ban tambaye ka wannan ma sama’ila, abinda na roka shi kawai nake da bukata, idan har kayi min shi ka gama min komai.”

“Zanyi Yaya, zanyi komai da ya dace. Nagode da bani dama da kayi, wannan ya nuna har yanzu kana jin ni din jinin ka ne…”

“Kayi min lissafin duk abinda aka kashe zanyi kokari na biya ka, in sha Allahu.”

Daga haka ya soma tafiya yana nufar gate din gidan, bishi yayi da kallo har karasa ficewa. Jiki a sanyaye ya koma ciki yana jin nadama sosai.

***Karfe biyu manyan bakin suka iso gidan Alhaji Isma’il Gashash cikin tawagar manya manyan motoci na alfarma, sun riga sun san irin gidan da suka zo dan haka a shiryen su suke musamman AJI ya dinga jaddada musu kar su bari a samu wata matsala a shirya sosai ayi komai na girma da kasaita. Hakan kuwa akayi suma bangaren Alhaji Isma’il din a shirye suke dan suma sun riga sun san kalar mutanen da zasu zo gidan nasu. Duk yawan motocin da suka zo dasu sai da suka shiga tsaf cikin harabar gidan kowacce ta samu matsuguni a wajen suka fito suna saba babbar riga akayi musu iso zuwa tangamemen falon gidan da yake shirye tsaf cikin shirn zuwan nasu. Gaisuwa ce ta soma gudana a tsakani manyan yan siyasar da kuma manyan yan kasuwa sai aka hadu aka dinke baka jin tashin komai sai dariya da hira irin tasu ta manya kowa yana jin tabbas an bi tsarin nan na kwarya ta bi kwarya domin dai duk wanda ya kwana ya tashi a kasar yasan su waye Gashash Family, babban family ne da sukayi suna wajen tarin dukiya kuma yan boko ne na bugawa a jarida shiyasa abun yazo daidai. Bayan zaman gabatar da kai da juna bangaren AJI suka sanar da abinda ya kawo su kuma cikin rashin son bata lokaci tunda dai dukkan su a shirye suke suka gabatar da kudin tambaya da na sadaki a take.

“Ina ganin Alhaji ai ba sai an tsaya jiran wani abu ba, tunda dai duk mun amince kuma ga shaidu da kowa me zai hana kawai a daura auren kowa ya huta, idan yaso shagalin biki daga baya sai ayi shi tunda dama mahaifin dan namu baya kasar.”

Wani abokin AJI yace sai aka saka dariya gaba daya.

“Idan kun ce hakan ai sai ayi hakan kawai.” Alhaji Isma’il yace

“Hakan yayi kam.”

Duk suka amsa, nan da nan sai abu ya juya ya aka hau maganar yadda zata kasance. Wakilta wani cousin din AJI sukayi a matsayin wakilin Rafeeq din nan da nan aka gama komai kafin kace menene an daura auren. Ana gama daurawa kowa a cikin abokan AJI suka dinga fidda kudi suna ajiye wa a matsayin kyauta ga amarya cikin bajinta wasu kuma suka rubuta cheque kowa yana son lallai sai yayi abin da yafi na dan uwansa domin yanzu komai ya zama kamar yi min inyi maka ne. Kudi sosai aka tara masu yawan gaske sannan sukayi sallama bayan an sheke musu mota guda da kayan da Alhaji Isma’il ya tanada a matsayin shi na uban amarya suka rakosu har compound din gidan sai da suka ga tafiyar su sannan suka koma ciki kowanne bangare yana yabon dayan bangaren.

***Alhaji Isma’il na komawa ciki ya kira Baba a wayar Noor lokacin wayar na hannun ta tana kallon text message din da Asim yayi mata, ta gwada kiran sa sau ba adadi ana ce mata switch off sai ga kira ya shigo. Da farko ta zata ma shine ganin number da baban ya kira ce yasa ta tashi ta fita tsakar gida taje ta kai masa.

“Waye?” Yace yana karbar waywr

“Number da aka kira ce jiya.”

“Ok. Sai ya daga yana sakata handsfree

“Yaya barka da rana.”

“Barka dai.”

“Alhamdullillah, mutanen nan sun zo har sun tafi ma, anyi komai cikin mutunci da girma sai dai nayi maka wani karambani guda daya,sun nemi a daura auren ba sai an ja abun ba ni kuma na amince musu, dan dama da sadakin su suke tafe.”

Plate Noor ta dauko kenan taji an ce an daura auren, sakin sa tayi Baba ya kalle ta da sauri kafin yace

“Allah yasa hakan ya zama alkhairi.”

“Amin ya Allah,.”

“Kalou kike uwata?” Yace yana mika mata wayar. Jiki a mace ta karbi wayar bata ce komai ba ta wuce daki, ta zaina jigum tana mamakin yadda komai ya kasance a dan kankanin lokaci, anya batayi shirme ba kuwa? Ya zata yi saurin amincewa bayan babu wata magana da ta shiga tsakanin su da Asim din wadda ke nuna kai tsaye son ta yake yi. Tasan dai yace ta jira shi, amma bata san me ya shirya ba. Sake gwada kiran sa tayi amma switch off sai ta ajiye wayar kawai ta dauki Hijab dinta tace ma Baban zata je gidan Malam hamza dan ji take kamar an daddaure ta da jijiyoyin jikin ta. tafiya ta dinga yi a cikin layin nasu taje ta dawo har ta gaji sannan ta dawo gida ganin lokaci na tafiya.

***Gud’ar da Mummy ta saki tana daga kiran da akayi mata ya saka yan falon gane abunda ya faru, wata cousin din AJI wadda ba wani shiri suke sosai da Mummy din ba tace

“Uwar taro dai ba’a santa da rashin kara ba.”

Wani banzan kallo Mummy ta watsa mata kafin ta sake wata gud’ar tana cewa

“An daura auren dana idan banyi guda ba me zanyi?”

“Gaskia ne Hajiya, daga tambaya sai a daura aure kawai. Da yake harka ce ta masu farcen susa.”

“Eh mana, akwai arziki ba sai an je ana taro taro ba a hado da kyar, irin wannan ne zaki ga an saka rana shekara guda ma kowanne bangare sai ya shiga adashi, mu kuwa fa?”

“Toh Allah ya sanya alkhairi, Allah yasa murnar har zuci ce.”

Matar ta fada tana gimtse fuska. Danne wa kawai Mummy tayi ta rabu da ita dan yanzu a farin ciki take bata da wani lokacin bata wa akan ire iren su amma tabbas ko ba dade ko ba jima sai ta bata amsa daidai da ita.

***La’asar sakaliya suka baro Lagos, yaso ya kara kwana amma kuma yana da abun yi dole ya taho ba dan yaso ba. Suna sauka Saddam da driver sa suna jiran sa fuskar Saddam tamkar gonar audugu haka yake kallon ogan nasu amma shi tashi fuskar sam babu walwala a dinke take tsaf kamar wanda aka aiko ma da sakon mutuwa.
Sai da suka hau titi suka daidaita sannan Saddam ya waigo ya kalle shi sannan yace

“Yallabai ina zamu?”

“Office.”

“Office sir, why not ka huta da safe sai ka shiga.”

“Ok, muje family house.”

“Ai sir gidan cike yake da mutane kasan yau aka je tamb…”

“It’s ok… Muje Apo.”

Yace yana tunawa yasan tabbas sai Mummy ta gayyato mutane kamar wani biki shi ya rasa irin wannan. Sun kusa isa yaje yana bukatar tambayar Saddam yadda ake ciki sai yace

“Sun je tamhayar?”

“Eh sir, sunje.”

“Ina ne?”

“Gidan Alhaji Isma’il Gashash.”

“Isma’il Gashash?” Ya maimaita yana son tuna sunsn

“Eh sir, wannan oil mogul din.”

“Oh yeah, na tuna. Chan suka je kenan.”

“Eh sir, kuma an..”

“Bana son ji.”

Ya katse shi sai yaja bakin sa yayi shiru, be sake magana ba har suka sauke shi ya shige ciki. Murmushi kawai Saddam yayi, he can’t wait yaga yadda zata kaya.

Yana shiga ya cire rigar saman ya zauna yana daukar wayar sa ya kunna data dan yana so ya kira Asim facetime dan tunda yayi masa message yace sun sauka basu sake magana ba. Yana kunna data din messages din Asim din ne ya fara shigowa. Na farko ya karanta

_”Congratulations bro, Allah ya sanya alkhairi.”_.

sai ya dauka dan an je masa tambaya ne Asim din yake masa congratulations. Tsaki yaja cikin jin haushi ya cigaba da duba message din, amma sai mamakin ya kama shi ganin ya kara cewa

“Yanzu AJI yake fada min daga tambaya wai sai kawai aka daura, ashe gidan Alhaji Isma’il Gashash ne kai I’m so happy for you wallahi, Allah yasa kyakkyawa ce dan family din ba dai kyau ba.”

Wurgar da wayar yayi da sauri, kamar wanda wayar wuta ta ja ya mike yana yarfe hannun sa kafin ya hau girgiza kai yana jin duk dauriyar da yake da ita na zagwanye wa, duk da yasan za’a yi hakan tunda ya basu go ahead amma be taba tunanin abun nan kusa ba, ya dauka komai zai tafi ne a tsare kamar yadda al’adar malam bahaushe take yasan by then kila ya samu ya karasa zare ta daga ransa dan bashi da buri da muradin auren wadda baya kauna. Zagaya dakin ya dinga yi amma sai ya kasa sukuni ya rasa me ma ya kamata yayi ne wai.

No comments