Breaking News

Zarrah 19-20


19-20*_

 

Buda idanunsa yayi akanta yana mata wani kallo daya sanyata saukar da kanta qasa ta kama handle din motar zata bude yayi mata key ya tasheta ta dago da sauri ta kalleshi idanunsa nakan tuqin da yake amma hankalinsa na kanta cikin sanyin muryarta ta kuka tace “Ina zaka kaini?” Bai kulata ba kuma bai daina tuqin ba har saida suka isa wani gurin kwalliya ya bude motar ya fita bai jima ba ya fito ya bude mata yanayi mata kallon dake firgitata ta fito a sanyaye yayi gaba tana binsa a baya har suka shiga ciki ya samu guri ya zauna tana tsaye yana qare mata kallo har saida daya cikin ma’aikatan gurin tace “yallabai meye ake buqata?” Numfashi ya sauke ya nuna Asmah dake tsaye kamar dashe tanabin gurin da kallo ya yatsina fuska yace “wai Amarya ce wannan din so jibi zaa fara bikin zasuzo su biyar ayi musu kwalliya nawa ne zai isa?”
Nan sukayi masa bell ya biyasu ta shiga wani daki tace ta biyota sharewa tayi kamar bazata ba ta tsinkayo muryarsa ya daka mata tsawa jikinta na tsuma tabi bayanta suka shiga ciki kanta ta bude gashinta dake nade cikin dankwalin ya baje Matar tace “masha Allah Amarya angonki zai huta da gashi” itadai bata saurareta ba saima tagomashin harara data samu ta wucce ta dauko mata wasu turaruka ta bata tace “gashinan dukkanku Ku rinqa wanka dasu qamshi zai kama jikinku gobe kuzo da wuri ayi tsifa jibi ayi gyaran gashi jikinki zai dauki gyara sosai inajin gobe zamu fara”

 

Bata qarasa jin abinda take cewa ba tayi ficewarta, ganin fitowar natane yasa shi miqewa ya biyo bayanta ta tsaya jikin motar yana zuwa ya bude

 

Ya Shiga itama ta shiga yaja suka tafi sunyi nisa sosai ya magantu da cewa r“anar Friday akwai dinner da dare ki zama ready” shiru ce ta bashi amsa takaici ya cikashi a duniya yana baqin cikin yayi mgn a shareshi qwafa yayi dole ya gogewa yarinyar raini ya fahimci ta gama rainashi tun yanzun parking yayi a qofar gdan kafin ya gama tsayawa harta fice tabar masa ledar turarukan da aka basu ta shige gdan Hajar.
Qarin takaici ya cikashi ya cije lebe a fili yace meye take taqama dashi ne?” Bashi da me bashi amsa dole ya kira wani Yaro yabashi ledar turarukan da Wata qatuwar Leda da shi Kansa baisan meye a cikin ba Aunty Aseemah CE ta bashi tace yakaiwa Asmah juyawa yayi ya tafi zuciyarsa cunkushe da takaici koda ya shiga gda bai nemi Mimee ba itama bata nemeshi ba ya shige dakinsa ya kwanta ya rasa meye yasa idan Asmah tayi masa wulaqanci abin yake kasa gogewa a ransa a hankali yaja qwafa ya miqe ya watsa ruwa ya dauki wayarsa ya hau online kusan sati biyu kenan daya bata waya baitaba ganin ta a bude ba sai yau tunda ya hau ya bude kyakkyawan hotonta da tayi tana murmushi ido hakanan yake jin gabadaya lakar jikinsa na tsinkewa tunda yake da ita baitaba zubanta ido ya qurewa kyawunta kallo ba sai yau tabbas Allah yayi halitta a gurin shiyasa take shuka tsiyarta son ranta.

 

Agogo ya duba yaga goma harda kwata yaja fasali so yake yayi mata mgn amma ya rasa me zaice mata ya jima yana tunanin me zaici kafin dabara ta fado masa ya rubuta mata _“ki sauka haka dare yayi”_ iyakar abinda ya rubuta kenan bayan kamar minti uku ta duba batare data bashi amsa ba ta kashe datarta ta sauka hakanma baiyi masa ba yaso ace tayi mgn

 

Hakan bata samu ba ya lura yarinyar yar izza ce ta bala’i dole sai yayi shiri me kyau domin zama da ita sai an shirya, tsaki yayi kawai ya gyara kwanciyarsa washegari da wuri ya tashi ya fice saboda yanada abubuwan yi da yawa kuma yanaso a gama aikin bangaren da zata zauna a yau gashi dai yau yake son ya turawa da Mal Husaini kayan dakin su Dijah, ya manta da batun zuwansu gurin gyaran jiki sai wajen 1:30pm aka kirashi daga gurin ake fada masa mutum uku sunzo amma wacce sukazo tare jiya bata biyosu ba,
Takaici ya cikashi ya dauki wayarsa a fusace ya lalubo number ta ya danna kira yajita a kashe baqin ciki ya hadashi sosai ya miqe tsam daga inda yake zaune ya figi motarsa a guje ya nufi unguwar cikin saa kuwa ya tarar da mal Husaini a qofar gda suka gaisa nan yace ya shiga dakin zaure bari ya kira masa ita, da Kansa ya shiga ya fara qwalanta kira tanaji gabanta ya fadi don tasan bana Lfy bane ta fito a salube ya harareta yace “yar baqin ciki to kije Alh nason ganinki” kamar tace masa Mal bazani ba amma batada iko hakanan ta dauki mayafinta tasa ta dauki wayarta dake saman window ta fita.

 

Ta jima a zauren tabarshi tsaye sai faman duba Agogo yakeyi kafin tayi qarfin halin buda labulen tare dayin yar siririyar sallama itama saboda ta zama dole ne, ba kwalliya ce a fuskarta ba hakan ya matuqar burgeshi tunda yake da Asmah baitaba ganin ta da kwalliya ba. Ya shagala da kallonta kusan 15 minutes itakuma ta qosa da kallon ta dubesa a kaikace tace “zan iya tafiya?” Yanda tayi mgnr da muryarta me kama da me shirin yin kuka yasa shi zama a kusa da ita da Sauri wani gumi ya karyo masa ta goshi itakuma jin baida niyyar mgn yasata miqewa ta saita hanya zata fice yayi azamar riqo hannunta ba shidinba hatta ita saida taji wani shocking a gabbanta ta dago idonsu ya gauraya da juna sai wani lumshe fararen idanunsa yakeyi yana bude su akanta.
Hakan yasata qoqarin janye hannunta daga nasa maimakon hakan kawai saijinta tayi zaune a saman cinyarsa gabanta yabada wani rass abinka da matsoraciya gabadaya lkc guda ta hargitse shikam gogan qara gyara zamansa yayi hakan da yayi yasamu yanda yakeso manyan faffadan mazaunanta masu tudu suka danne masa burarsa da take ta qoqarin miqewa taimako daya Allah yayi masa yasa boxes daya kamashi kota miqe bazata nuna shi ba saidai yaji a jikinsa, sake sanya hannunsa yayi ya harde qugunta ya sanya su saitin Cikinta ya dora kansa saman kafadarta yana sauke mata wani huci me dumi da dumama yanayi.

 

Cikin dabara ta rinqa qoqarin zame jikinta yaqi bata dama har saida yaji ta soma shassheqar kuka sannan ya fahimci abinda yake shirin aikatawa ya sake ta ta zame a hankali ya kwanta saman kujerar three sitter din da yake kai tare da harde qafafunsa yana qoqarin aro kwarjini yasawa Kansa yace “meye ya hanaki zuwa gdan kwalliyar dana kaiki jiya?” Sunkuyar da kanta tayi har yanzu qirjinta lugude yakeyi itakam ta hadu da masifa wannan mutumin wanne irine me yake nufi da ita wanne salone wannan yake son zuwar mata dashi da yake Neman zarta girman kwanyarta a mizanin hankali…….
Ji tayi hannunsa na yawo a fuskarta ta dago da Sauri sukayi ido hudu yasa yatsansa

 

wasa da ruwan hawayenta yayi murmushin da yasa kuncinsa lomawa sajensa ya hadu da gumi ya kwanta luf a fuskarsa yace “Asma’uh Ma’un Innah Mara kunya fitsararriya wacce bata barin kowa idan tsautsayi yasa ya shiga gonarta am don Allah ki daina kuka kuka bai kamaci fuskar jaruma kamarki wacce ta shiryawa fito na fito da mutum kamata ba ki jira lkcn kuka na gaba lkcn da zaki gane shayi baikai matsayin ruwa ba domin shi ruwa haka ake buqatarsa shayi ko sai ansa masa Lipton da suger yake shawuwa, Kalmomin qarshe da nakeson sanar dake banson jayayya akan abinda yake hurumi na dole ne idan nasaki Abu kiyishi ko bakyaso kina nunamin jin dadinki kuma komai wahalarsa idan kin gama kiyimin godiya sannan koda wasa kada ki qara kashemin waya na kira ban sameki ba saboda banson shigowa wannan lungun talakawan dole ce take biyo dani am akwai sauran dokoki da sharruda na zama dani a matsayinki na baiwa don baki isa nayi miki kallon mata ba ke kanki kin sani zan baki jadawalin ayyukanki ranar da kika tare a gdana”
Shiru ce ta ratsa ta tsayin lkc har yanzu hawayen bai daina zuba a idonta ba yayi ajiyar zuciya ganin yanda ta lumshe manyan idanunta gashin idonta ya sauka saman kuncinta abin ya bashi nishadi bude bakinsa a saitin kunnenta yace “wannan dogon surutun ma da kika sani kiyimin gdy”

 

*_Oum Hairan_*
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_

 

_*Oum Hairan*_

No comments