Breaking News

Ameenatou 2

 *_AMEENATOU_*

_Mamuhgee_

#ZafafaBiyar

#blackMoneyLove






2

Kaman yanda suka Saba duk zasu shiga Rami a tare suke shiga basa yadda su shiga ba tareda Dan haka Basu taba shigar ba tareda junansu su biyar din ba.


Gyara tsayuwa mamman yayi Yana Dan gyarawa daurin jakar kayansa a qugunsa Yana kallan omer da kusan shine koyaushe me zama karshen Shiga Dan ya yaddarwa kansa idan kullum suna shiga su fito wataran yasan idan suka shiga bazasu fito din ba.


Shiga sukai da karfin gwiwansu tareda qarfin zuciya Dan kuwa ginar zinari Se me taurin zuciya da rashin tsoro,


Rami ake ginawa me zurfin gasken da idan ka shiga zafinsa da duhunsa kadai zai iya kashe me qaramin karfin jini ko me tsoro,

Da fitila ake shiga tareda batiran fitila da ruwan Sha duk a jikinka daure sbd idan ka shiga bawai Kai tsaye kake fitowaba wasu sai suyi kwana Daya a ciki wasu fiyeda kwana Dayan da kwanaki ma duk sunayi a ciki sbd ba wai Rami ne da zaka ringa shiga Kai tsaye kana fitowa ba,

Idan wainda suke ciki suna ciki to ko magana zaayi musu Saida loudspeaker sbd sunyi Nisa a cikin qasar da ba zasuji magana Kai tsaye ba.


Aduk lokacinda zaa samu zinari ko ginosa to tabbas jinin rayukan mutane da dama zasu salwanta sbd hadarin Dake ciki tareda wani irin son zuciya me qarfin gaske,

Rijiyar Gino zinari bawai Rami ne na qasa ba zaa ringa ginawo Rami ne dazaa ringa ginawa a cikin qasar tareda dutsina masu karfin gaske Wanda shiyasa hadarinsa yakeda yawan gaske sbd wani dutsin kana bugosa a cikin ramin zai rufeka gaba Daya ya zubo ya danneka ba iya Kai Daya ba zai iya zubowa ta koina yayi sanadin Rai fiyeda adadi Wanda da yawa ana ji ana Gani za'a samu Ciro wasu wasu kuwa qasa ta ciny shikenan sbd bazaa iya cirosu ba alokacin,

Idan zaa haqo rijiyoyin zinari a gurinda ake da tinanin akwaisa ana haqo akalla rijiyoyin da fadinsu da zurfinsu bamai misaltuwa bane a gurin akalla daga rijiya goma Sha biyar zuwa sama har dari biyu Wanda jiri ma zai iya Kamaka idan ka tsayu a gurin.

Zinari nada wani Sirri Wanda shine a duk lokacinda jinin wani ya zuba to takan qara yaduwa ne tamkar Shukan da ake bawa ruwa.


Su mamman tin iyayensu na raye suke yawon nahiyoyi daban daban dan Gino zinari Wanda idan suka bar gida akalla sukan shafe watanni da yawa basu dawo ba sunacan cikin daji da Sahara da yawon kauyuka masu Nisa da hatsarin gaske Dan Neman zinari Amma har Allah yayi musu rasuwa Daya bayan Daya duk a harkar Basu samu komaiba bare Tarawa Dan haka yayansu suka dauki Niya da damara tareda alkawarin ko da dadi ko ba dadi,Koda jinin wasu ne saisun samu bazasu qare a wahalce kaman yanda iyayensu suka qare a daji da nahiyoyin nesa Dan Neman zinari ba.


Mamman a cikinsu shine Wanda yafi kowa karfin hali da rashin yadda Koda wasa a tauyi haqqinsu Dan haka suke Dan samun na abinci a harkar duk da Suma har lokacin Allah Bai Basu tasu nasarar ba Amma Basu cire Rai ba Dan yanzu suke matasansu.


Omar a cikinsu Kuma shine Wanda yafi kowa sonsu,

Yana tsananin kaunarsu fiyeda kansa sbd shi Kuma duk abinda ya samu su yake miqa Se yanda Akai dashi duk da Suma sauran suna tsananin kaunar junansu.


Dukkaninsu dai marayu ne tinda Babu me Uba a cikinsa hakama iyayensu mata biyu rasu, mahaifiyar Omar da mahaifiyar mamman,

Tinda suka fara Dan tasawa Suma idan suka bar gida suka kutsa nema saisu share watanni fiyema da yanda iyayensu ke dadewa batareda sun dawo ba sedai duk inda dayansu ya Saka kafa suna nan a tare kaman kashin awaki a manne da juna shiyasa kusan ake da saurin saninsu a duk inda suka yada zango sbd Yan biyar seelahs da ake kiransu.


Shekaransu bazasu wuce Sha takwas zuwa ashirin ba a lokacinda Allah ya bayyanar musu da babbar sa'ar rayuwarsu Kuma babbar musibar rayuwarsu ba.


A babban dajin kauyen ashalawa Dake wani yankin Daya raba shiga nijar da Nigeria suka yada zango kusan shekara Daya har sun zama Yan gari Yan gida Dan kuwa duk kusan da yawan jamaa sun Sansu Kuma suna Jin dadin aiki dasu Dan kuwa sunada karfin halin gaske da taurin zuciyan neman arziki ido rufe Dan kuwa sun dauki alwashi sun duqufa bazasu koma gida ba batareda arziki ba Wanda kusan zuciyar kowannensu ta sauya kudin arzikin zinariya kawai kota yaya.


A ashalawa wata babbar duniyar Neman zinari ce sbd asalinta ba gari bace bare kauye,

Tarin matafiya da Yan kwadago da Yan cin kasuwar gari gari tareda asalin buzaye masu harkar danyar zinari da Yan Nigeria Suma masu harkar rijiya da Kuma danyar zinari ne suka taru suka Maida asalin dajin da aka Gano tarin arzikin zinariya acikinsa gari guda,

Sun Maida dajin ya koma kusan babbar garinda kasuwar duniya kawai akeci a cikinsa,

Ashalawa baida dare baida Rana bare asuba,

Kowanne lokaci su a gurinsa lokacin harka ne Dan haka Koda yaushe a hargitse yake kowa na abinda yake gabansa,

Babu Mai auren da zaka samesa da iyalinsa a ashalawa sbd gurine da babi yiyuwar kawo iyali Dan kuwa Babu kalar kaddararrun mutanen da babu masu rayuwa daban daban,


Tarin karuwai masu aji da masu saukin kudi Babu kalar wadda babu a ashalawa,

Idan Maza kake so kayi muamala dasu akwaisu,

Akwai matasa akwai manya,

Hakama ta bangaren yare da kabila kusan Babu kalar Wanda Babu,


Babu wasu gine gine a ashalawa sai runfuna da tinti da kusan sune suke cikewa ashalawa sunfi dari biyu zuwa dari hudu ma,

Gine ginen Dake ciki ko dozin bazasu kaiba Suma na wainda suka riqa ne suka samu zinariya sosai suka Gina suka zuba karuwansu da suka koma tamkar matayensu Dan kuwa duk Wanda ya jiqa a ashalawa bazai rasa akalla karuwan kansa kusan guda shida zuwa sama ba,

Marasa karfi sosai sune suke da karuwai bibbiyu haka ko Daya zuwa uku Amma dai sauran har me goma akwai.


Masu siyar da abincin ashalawa dukkaninsu Suma kaman mata Maza suke wasu kuwa karuwan ne Dan kuwa idan baka bazaka iya kashewa ko illatawa ko zama busashiyar zuciya bazaka taba iya zama a ashalawa ba.


A garin ashalawa Babu ranar da zinariya Bata kisa hakama Babu ranar da wani Baya illata wani ko kashewa,

Idan baka zuciyarka bata bushe qamas ba Kokuma Daman Tim farko Kai din me busashiyar zuciya ce zaka iya komai Dan ka tsira to bazaka rufa sati Daya a ashalawa ba batareda ka Isa kofar barzahu ba Dan kuwa rayuwa ce akeyi ta ko ka kashe ko akasheka Dan haka zinariyar ashalawa take sake habbaka da yaduwa koyaushe sbd jininda babu ranar da Baya zuba Kuma jini irin Wanda takeso wato me zafi na fitar rashin Imani maana jinin kisar gilla.


Tafiya me tsayi ta kwanaki da satika harma da wata ce ta kawo su mamman Ashalawa inda sukaga duniyar da Basu taba Gani ba Dan kuwa ashalawa wata duniyar ce ta daban me zaman kanta.


Da farko sunsha wuya sosai daqyar suka tsira suka Kai lokacinda suka fara gane kan rayuwar tsira ko mutuwa akeyi a Ashalawa Dan haka mamman ne ya fara tsayuwa ya jefar da tausayinsa gefe ya dauki rashin imaninsu da rashin tausayinsu ya tsayawa Yan uwansa suka fada harkar  haqar rijiyoyin zinariyar ashalawa wainda akalla akwai rijiyoyin da aka Tona a gurin sunfi dari uku Kuma Babu wadda idan ka tsaya gefenta zafin ciki kawai idan ya huro Maka zaka iya Yanke jiki ka Fadi sbd tsananin zufinda zaka share fiyeda awanni masu yawa baka Isa kasanta ba.


Duk bulayin yawon shekaru masu yawa da iyayensu sukai harma dasu wanda sukai sai da suka iso Ashalawa suka San sun iso inda ya kamata ace sun samu isowa tin lokacin iyayensu Dan haka gabaki dayansu su biyar din Babu Wanda baisan a yanzu duniyar dasuke buqata ce suke.


Tinda suke a rayuwarsu tin daga lokacinda suka fara takawa da kafafunsu Basu taba zuwa koina ba batareda juna ba har suka girma wanka ne kawai yake rabasu Shima ba koyaushe ba sbd a ruwan gulbi suke wanka a tare sai Kuma su share kwanaki kafin su sake samun wata damar wankan sai zuwansu Ashalawa suka fara abubuwa ba tareda Shima shiga rijiya ne kawai sukeyi Hakan Wanda idan sun shiga sukan kwana Basu fitoba Dan haka kowa ya dage Dan kuwa yanzu kowa arzikinsa na hannunsa idan ya dage musamman Omar Dake da burin bawa kansa ilimin boko sosai da tasa dukiyar sabanin sauran da babu me dogon alkhairi a ransa.


Shekaransu Daya a Ashalawa sun goge sun zama gaba gaba acikin matasan da ake ji dasu a harkar,

Ba wasa ko tausayi aharkarsu,

Mamman kaf ashalawa bayan Yan uwansa seelahs babu Wanda bazai iya zubarda jininsa a qasar Ashalawa.



Kaman yanda kowa arzikin da Allah yayi masa daban haka Allah ya fara bayyanarda arzikin Dake tattareda kowannensu sbd sun fara Tara abin kansu suna samun zinariya sosai Dan yanzu zubar jinin a ashalawa yawa yake sake yi Kuma kullum samun baqin da Suma imanin Bai ishesu ba akeyi suna zama Yan gari Suma.


Turawa da labawa dakuma wakilansu sosai suke shigowa ashalawa wasu ma da helicopter ake kawosu suyi huldan su hau helicopter din su koma.

A taqaice ashalawa headquarter ce me zaman kanta ta huldar danyar zinariya wadda ake hadawa da gudanarwa cikin rashin gaskia Dan haka turawa da labarawa sosai suke Hulda da Yan Ashalawa Kuma Suma Yan ashalawa sunfi Hulda dasu sosai Dan baka iya fita Ashalawa da danyar zinari idanma ka hada sbd ta kowanne dajin da zaka fita masu jiran ka fito su kasheka su karbe suna Nan suna Jira.

#MAMUH#

#BESTLOVE

#ZAFIN KAI

#BLACKMONEYLOVE

#ROMANCE

#JAMAAL JEEY SEELAH

#TOOTOOHOT

#ZAFAFABIYAR



*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

 _Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*O

No comments