Breaking News

Ameenatou 27

 *_Arewabooks@Mamuhgee_*


27

Wani mummunan jiri ne ya dibi Jamaal din Wanda sai alokacin ya fashe Da kukan Daya girgiza Haroon da mum dinsa da isowanta kenan asibitin cikin tashin hankali da tsananin tsoro sbd Kwana sukai itama da Dad din cikin tashin hankalin fitina da maganganun da suka Sakata Jin son barin qasar a ranar.


Duk wani sheda ko alaman inda poison din ya samu shiga oxygen dinta Jamaal yayi daga daren zuwa safe Bai gane ba sai Abu Daya wato yawan zuwan BB asibitin Wanda ya samu tabbacin duk karshen wata yake zuwa so Daya dubiyan kaninsa yaronsa da suka karya da gangan suka ajiyesa asibitin yaqi warkewa sbd Daya kusa warkewa saisu sake lalata gyaran.


Hakama mum dinsa ta kasa fada masa komai taqi sake maimaita masa tabbas mahaifinsa ne yayi Hakan,


Wane asalin rashin Imani ne zai Saka a taba fadila macen da numfashin duniya Bata iya shaqa saina Siya,


Gida suka dawo Kai tsaye palon Dad dinsa ya nufa zuciyarsa na qunan dayake Jin har wata wuta ce take cin kansa.


Babban abinda fara bawa su Dad din mamaki da shakka shine Kai tsaye kafin goman safe tini akaiwa su BB da yaransa kaf mugun Kamun Daya fara yaduwa a labari tareda tabbaci akan zargin kamasu da sirka poison acikin oxygen na asibitin SEELAHs Wanda yayi sanadin rayuwar matar Dr Jamaal Seelah din,

 Hakan ya qarawa labarin saurin yaduwa sosai da gudu kaman wutar daji take Yan jarida sukaiwa asibitin da gidan kawanya.


A yanda Jamaal ya nufo su Dad din mum dinsa ce tayi saurin Shan gabansa tareda riqe hannunsa Dan duk mugun halin Dad bazata so yayanta suyi sa'insa da mahaifinsu ba bare maganar datai da Dad a ajiyan ta tabbatar mata da Dad Babu abinda bazai iyaba Dan haka ta riqo hannun jamaal ta girgiza masa Kai cikin qaramin sauti ta Bude Baki tace Karkayi komai karkace komai wannan umarni nane,

Haqqin dayake hanunusu bazai taba taba yayana ba kaman yanda bakuda sani bakuda haqqi bazanso ka taba gurbata kanka aikinsu ba.


Cikin Bacin Rai me tsananin gaske Dad da Alh Lameenu suke kallanta zaiyi magana cikin hada zufan tashin hankali mum Atee ta shigo cikin tashin hankali tana sanar musu ga asibitin SEELAHs can ana kokarin Banka mata wuta.


Dayake tini Jamaal ya Saka Aka sallami kowa tareda dauke gawar fadila tana can anai mata sutura baice komaiba Se hannun mum din Daya kama ya juya suka bar palon sbd ta dauresa da maganarta da alkawarinta bazaicewa su Dad komai ba Amma yayi alkawarin sai ya tabbatarda basuda komai,

Ahankali zai tabbatarda yasan komai da mum taqi fada masa da abinda su Dad din ke boyewa,

Bai damu da dukiyar seelahs ba Saiya tabbatarda Babu komai Daya rage acikinta sbd da ita akai kisan fadila.



Karfe goma da Rabi Akai janazan fadila aka rufeta,

Ana dawowa ya sallami su umman da kudi me yawa da zaa kula da umman kafin ya waiwayosu.


Siddeeq kuwa anan Lagos din ya samar masa gurin zama kafin daga baya zai bisa idan anmasa komai.


A wannan mummunan ranar baa kwana ba SEELAHs suka rasa asibitinsu tareda shiga shakku a zuciyoyin mutane da take abin yafara kokarin tabasu duk da su Dad din sun tashi tsaye kada Hakan ya tabasu Dan kuwa sunfara ganin matsala babba na Neman tinkaro su.



A wanna mummunan ranar Dr Jamaal Mamman seelah ya Yanke duk wata alaqarsa da ahalin seelahs ya goge sunansa daga kudin tarihin gidan Dan har abada bazai taba sake hada alaqa dasu ba kowace iri ce ya yanketa Baya buqatanta.


 Haroon ya shiga Mummunan tashin hankalin wannan masifar data fadowa familynsu a Rana Daya lokaci daya,

Tayaya zai iya rayuwa a tsakanin mutum biyu dayafi so a rayuwarsa sun rabu sun yanke alaqa a tsakaninsu,

Kaman yanda Jamaal din ya Yanke alaqansa da Dad Kai tsaye Dad din cikin fushi da bacin Rai ya yanke Shima alaqansa dashi sbd Hakan ne kadai zai rufa asirinsu su tsira a yanzu sbd a wuni Daya yayi qasa da asibitinsu ga faduwansu na Neman tasowa a qanqanin lokaci Dan haka nesantar su da Jamaal din kadai zai sakasu samun tattara mutuncinsu su dawo dashi a idon mutane da abokan kasuwancinsu kafin manyan sirrikansu su bullo komai ya lalace batareda sun shirya ba Dan Basu hango wanna masifarba su kansu a yau din.


Dr Aleena kanta Hakan shine nutsuwa da Kwanciyar hankalin datai shekaru Bata samu ba yanzu da alaqa ta Yanke kwata kwata tsakanin Jamaal dinta dasu Mam din Dan haka ta tattara itada Jamaal a ranar suka bar qasar a cewansu har abada bashi ba dawowa bare alaqa tsakaninsa dasu,

Haroon na ran Mum Amma Kuma koyaushe Haroon din zabar mahaifinsa yakeyi akan mahaifiyarsa Amma Kuma kaunar Dan uwansa ta take ta kowa da komai Dan haka tafiyar Jamaal ta jijjiga duniyarsa Dan baisan ya zaiyi rayuwa babu Dan uwansa dayake kalla kaman Yana kallan mahaifiyarsa da Bata taredashi.


Jamaal Koda yabar qasar Nigeria yabarta cikin tsananin ciwo da quncin zuciya da tarwatsewanta,

Abinda yakeji a zuciyarsa wani dutse ne da bazai taba sauka da zuciyansa ba,

Son fadila yayiwa zuciyarsa mummunan illan busar masa da ita da bazai taba hucewaba bare son wani abin ba daban bama mace ba wadda wannan Kuma wani Babi ne Daya rufe ya kona bare ma ace akwai ranar budewansa.


Ita kanta mum tabaro kasar cikin tsananin damuwa da ciwon Rai sbd sun ringa sun sauya mata 'da da dawowansa daidai Kila har abada Se Kuma wani ikon Allah datake fatan yazo,amma Jamaal Kam ya koma Asalin Dr jeey dinsa babu wata sakewa ko walwala Se kamewa.


Suna Isa Poland ko wata Bai rufa ba ya tafi Umrah daga can ya wuce Hutunda Bai dawo ba sai bayan watannin dasuka sauyasa ya koma wani lafiyayyan balareban bature ya sake budewa sosai sbd geamin da sauya rayuwarsa da yayi gaba Daya.


Ita kanta mum din ganinsa Saida ya Sakata Tara hawayen farin ciki a cikin  idanuwanta na ganin wata irin kyau da tsantsan hutun Daya bayyana a tareda shi da wata lafiyayyar qasumbar data kwanta a fuskansa farinsa yayi mugun bayyana.


Sabuwar asibitinsa akai bikin budewa take yafara aikinsa tareda Bude Babin sabuwar rayuwa.




**************

Ameenatou,Ameenatou wlh idan na kamaki a hannuna saina balla hannunki"


Hafiz ne ya fada Hakan Yana daga takarmansa Da baa Saka musu ruwa a jiqe suna tsiyayar ruwan wankan datai masa dasu zuciyarsa kaman zatai bindiga ta fashe sbd takaici.


Dadah Dake tayata Saka zip din doguwar rigar atampar data Saka sbd duk girmanta da zamanta budewar komai yi mata akeyi sbd tsaban gata da sangarta hatta ruwan wanka wani lokacin se an Saka yananta sun Kai mata tace


"Meenon Dadah wanka kikai masa da takarma ko sbd Neman magana?.


Dariyar data lotsa dimple dinta sosai tayi tana yin Dan qasa da murya sbd kada Yaya Hafiz din ya juyota tace


"Dadah bansan takarman basason ruwa bafa Kuma tin safe yau fada kawai yaketa yi dukana yakeson yi kawai"


"Duka dai? Kaman wata babyn roba Saiya dakeki Ina kallo.


"Eh Dadah nidai wlh karki bari ya dakeni tinda dai na zama budurwa kaman yanda Babbah ya fada."


Kaman Yaya Hafiz din yaji abinda ta fada ya shigo dakin da takarmin Yana cewa


"Wlh bazan yadda ba tinda aka hanani dukanki se anbiyani takarman Nan,

Kunsan nawa na siyesu kuwa?

Idan ban ballaki ba zuciyata bazaitai sanyi ba"


Kanta yayo tayi saurin yin bayan dadah tana cewa


"Wlh bansan sabo bane bafa"


Wani sabon takaici ne ya ciyosa yace


"To dole Se kinmin wanka da takarma tsaban reni"


Kallansa dadah tayi zatai magana yace


"Allah dadah Kun gama Saka yarinyar Nan ta Rena ni,

Kwata kwata Kun sangartata Bata ganin girmana,

Yanzu fa wannan takarman bayan daurin auren da zani sbd zuwan Asalin me gidanmu na aikin site da zaiyi a kwanakin Nan ya sakanu siyansu sbd zaa dibi ma'aikatan da zaa tafi dasu can kamfaninsu na Lagos aiki ni inason zuwa shiyasa nakeson fitowa fes Amma tsaban mugunta yarinyar Nan ta jiqamun su"


Daga bayan dadah so takeyi tayi magana tana gudun ya jefota da takarman Dan haka Saida ta sake shigewa sosai tace


"Wannan baturen Dana taba Gani a site din da dadewa danaje karban kudin tafiya makaranta gurinka shine ze sake zuwa?

Dan Allah zanje kaje Dani Yaya Hafiz zan shanya Maka takarmin.....


Cikinta yayo cikin takaici kafin ya kamota Babbah ya shigo gidan take ta Bude Baki daga bayan dadah tace


"Babbah gashinan Yaya Hafiz ze taba baka yar budurwa"

#MAMUH#



*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

 _Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments