Breaking News

Ameenatou 31

 *_Arewabooks@Mamuhgee_*

31

Bayan ficewan Haroon daga palon kallan Mam Dad Lameenu yayi cikin nauyin zuciya da rashin Jin dadin komai na duniya yace



"Dole muna buqatan tsananta binciken abinda àka haifawa Omar duk inda yake sbd sanin inda suke zai Saka Omar din dawowa daga inda yake ya dawo cikinmu sbd sanin munsan yanada 'da a duniya,


Idan ba Hakan mukaiba cikin gaggawa wlh muna gap da rasa komai munaji muna Gani Dan haka yanzu Kam dole mu tashi tsaye dakyau mu samo 'dan Omar"


Mam da zuciyarsa tafi ta lameenu tsananta a cikin baqin ciki da tafasa tareda bacin Rai baice komaiba sbd Daman ya hangowa kansu Hakan daga ranar da suka Dora Haroon akan komai nasu,

Sam baida jarumta ko amfanin da zai musu yanda ya kamata.


Ta bangare Daya yasan duk Wanda zasu Saka a magajin nasu me gudanar da komai bazasu taba samun Jamaal ba Dan kuwa shi din zakinsu ne.


Numfashi ya sauke ahankali Yana kallan takardun gabansa da idanuwansa da sukai jajir Yana kokarin daidaita tafasar da zuciyarsa keyi,

A yanzu shima Babu abinda ruhi da zuciyarsa suke tsananin buqata kaman dukiyar Omar Dan ita kadaice zasu mallaka suyi tsayuwarda Babu ranar rushewansu a kusa sbd koba komai a tsaftace take Babu jinin kowa aciki Dan haka zeyi wuya ta shiga hannunsu ta lalace kaman yanda tasu ta dauko hanyar lalacewa duk Dan sbd Allah ya basa sakaran 'da mara amfani sosai duk da Yana son dansa sosai Amma Sam Baya kaunar rashin amfaninsa har ransa yake Jin baqin ciki da tsanar Hakan.


Wayarsa ya miqa hannunsa Daya ya dauka cikin nutsuwa ya Nemo numbern BB ya Saka kira Yana dauka yace


"Ina buqatan ganinka yanzu"


"Yes Sir" ya fada Yana zare sigarin Dake bakinsa Yana zuqa cikin palon gidansa.


Cikin mintinan da Basu wuce hamsin da Yan Kai ba saigashi ya iso gidan Kai tsaye motarsa yayi parking ya nufi hanyar office dinsu Yana zare baqin glass dinsa Dake rufawa jajayen idanuwansa masu Bada tsoro asiri.


Yana shigowa ya rufe kofar tareda qarasawa ya tsaya gabansu cikin girmamawa da kulawa ya gaidasu Yana kallan fuskokinsu ya sheda akwai sabon bacin Rai da sabuwar matsala wadda kwanan wani zai qare Kila a kwanakin Dan kuwa Kai tsaye yake gane girman bacin ran uwayen gidan nasa.


Kallansa lameenu yayi cikin tashin hankali da son danne tafasar zuciyarsa yace


"Yaya ake ciki a bincikenmu??


Gyara tsayuwa yayi Yana dagowa yace


"Ranka ya Dade tsawon shekarun Nan wlh bamu taba dakatawa daga binciken inda suke ba,

Babu kalar yawon da bamuyiba state state da kauyuka gurin nemansu,

Acan Asalin kauyen na iyayen matar sir Omar din muntashi kauyen gaba Daya Dan kunasa mukayi da gidajen Dake cikinsa dayawansu ma Babu sun mutu,

Hakama itama me aikin munyi nasarar sanin inda aka daukota aiki daga Jos Amma bamu gama sanin a inane take a jos din.......


Cikin daga murya da bacin ran da suke jimawa Basu ganiba a gun Mam ya katsesa idanuwansa na qara yin jajir yace


"Ko nawa zaa kashe a kashe a Nemo mana matarnan Ina buqatan Jin komai daga bakinta zuwa kunnuwana,

A yanzu wannan aikin shine tabbatuwar arzikinmu da tsayuwarmu,

Samun wannan matar shine duk wani abu damuke buqata da ranmu da zuciyarmu,

Omar jeden Yana kallanmu daga nesa amatsayin matsiyata wainda ya take ya wuce nesa ba kusa Dan haka nakeson nuna masa Munfi karfinsa da gaske shi din a tafin hannunmu yake Dan kuwa idan ban zubar da jinin 'dansa ba bazan taba Ji ko samun nutsuwan zuciya ba.."



Lameenu dakejin zuciyarsa har wani rawa da tsallen tashin hankali takeyi sbd Jin inama zasu samu ganin matar da Gano komai a ranar da hannunsa zai cike aikinsa dabai qarasa ba Dan kuwa barin 'dan Omar a duniya kaman aikine da Basu samu cikawaba Wanda bazai taba samun nutsuwa ba idan ba cike aikin yayi ba daidai.


Cikin sauti me tattareda radadi da son samun abinda zuciya keso Dad Lameenu yace


"Ko nawa zaa kashe a kashe acika wannan aikin Daya gagara cikuwa shekara da shekaru,

Duk Wanda yasan wani abu gameda me aikin gidan Omar a nemesa aji nasa bayanin a Kuma kawar dashi bayan karban bayanan Dan basason barin sheda ko Daya datasan meyake faruwa Da abinda ma zai farun.


BB da Shima daya kawar da rayuka sunkai nawa akan wannan binciken Jin yayi zuciyarsa ta sake daukan zafi Dan rashin sauki ko kadan Dan haka Koda zasu tada kauyuka da rayuka nawa wannan Karan Se sun Nemo inda matar Nan take sunji me aka haifawa Omar din da inda abinda aka haifa din yake.


Kudi masu yawan gaske Dad Lameenu ya kira Haroon ya bawa BB da yaransa akan aikin Nemo matar wadda Shima Haroon yake tsananin so da buqatan a Gani din duk da Yana Jin shakkar abinda zai iya biyowa bayan samun me aikin da Kuma samun Abinda Dad Omar ya Haifa, duk da haka Shima Yana Nan Yana bincikensa sosai a boye sbd zaiso yasamo information da zai taimaki Dad dinsa Dan ya yaba masa Koda so Daya ne Kuma yayi alkawarin Yana samun Information koman kankantarsa zai sanarwa Dad din.


Bayan bawa lameenu kudin sanar dashi yayi duk information da zaa samu Shima ya sanar dashi ko yayane.


"Angama Barrister" BB ya fada Yana ficewa daga palon Haroon din zuciyarsa cikeda rashin Imani da Jin ya dauki sabon caji Baji ba Gani yayiwa kansa alkawarin Nemo matar Nan duk inda take a cikin Jos da zagayenta.



*****Anyi Hakan da kwana biyu Haroon ya tattara ya tafi Nasarawa sbd gaba Daya Dad ko kallan daraja Baya masa sbd tsananin bacin Ran dasuke ciki akansa Dan haka ya sake shiga damuwa sosai da rashin walwala duk da Bai bari Mum dinsa da Dan uwansa dashi kadai suke communicating a Nigeria sai siddeeq da duk motsin Haroon Yana sane dashi Yana sanarwa Jamaal Dan kuwa kwata kwata Jamaal Bai yadda dasu Dad din akan Dan uwansa ba.


Duk tsananin damuwa da kadaici da rashin mutuntawa ko daraja da Haroon din yake cikinsu Jamaal Yana sane da komai sbd Yana sane ya saka Haroon daukan siddeeq Aiki ya zama Dan hannun damarsa batareda su Dad sunsan asalin waye Siddeeq dinba hakama Haroon kansa baisan ma siddeeq din yanada alaqa haryanxu da Jamaal ba sbd kwata kwata abinda ya sani dashi kadai Jamaal ke magana a Nigeria Dan ko mum Atee duk nacinta ta gaji ta barsa Dan ko kwana zatayi tana kiransa Bata samunsa.


Koda ya karbi aikin project dinnan zuciyarsa cikin shakku da fargaba take sosai tareda tsananin tsoro Dan baisanma ta inda zai fara gudanar da wannan aikin da Dad ya basa damar karshe akansa ba,

Baisan Yaya zai fara ba gashi baisan ta Ina zai fara rokon taimakawan Jamaal ba Dan yasan Jamaal din bazai taba Saka hannu a aikinsu Dad ba Dan haka yake cikin damuwanda tini tafara taba ayyukansa da rayuwarsa Dan kuwa komaima kaman ya Dena ganewa daidai.


Tareda siddeeq suka sauka Nasarawa har babban hotel din da Aka kama masa motar data daukesa ta Kaisa.


Siddeeq ne yakai masa kayansa har dakinsa ya jere masa kafin ya fito ya nufi nasa dakin dayake kusa da nasa Shima ya jere kayansa ya fada toilet sbd zasuyi kwanakin da basusan yaushe ne ranar tafiyansu ba tukuna.


Shi kansa Haroon wankan yayi Yana fitowa ya shirya cikin kaya marasa nauyi yayi Sallah kafin ya kunna wayarsa sai alokacin ya kira Dad ya sanar masa sun iso.


Babu wani yabawa Dad din ya sake maimaita masa mahimmanci da tsananin buri dasuke dashi Akan aikin Nan tareda tabbatar masa da idan aka samu matsala to babusa Babu shi.


Wannan kalman itace kalma mafi Munin data girgiza zuciyarsa ta qarasa tarwatsa duk wani Dan sauran dubaru Dan kokarin Daya rage masa Dan haka ya sake shiga damuwa da tashin hankali me tsananin gaske gashi bayajin zai iya ajiye aikin Dan kaman nauyi ne Daya rataya akansa hakama bayajin Dad din ze barsa ya ajiye din Dan.


Jin yayi ciwonsa na tsananin ciwon Kai da depression na dawo masa sosai Dan kuwa take yafara Jin kaman kansa ze juye Baya gane komai,


Wayarsa ya kashe tareda wurgi da ita Yana silalewa qasa hannuwansa riqe da kansa Dake Neman bugawa tareda bugun zuciyarsa.


Maganinsa yafara rarrafawa Dan nemowa yasha amma kwata kwata Baya Gani daidai saima juyawa dayaji kaman anayi dashi,

Hannuwansa Dake wani Irin rawa sosai suna kakkarwa ya dago Yana kalla sunai masa bibbiyu.


Sake rarrafawa yakeyi Yana faduwa Yana tashi harya Isa gaban mirror inda siddeeq ya ajiye masa maganinsa kafin yakai hannunsa ya dauka ya Fadi akan mirror din kayan Dake Kai suka zube qasa Wanda sautin ya Isa har dakin siddeeq Dake maqale da nasa da sauri ya fito ya shigo dakin Yana ganin Halinda yake ciki da sauri ya qaraso Yana daukan maganin ya Bude roban ya Ciro Daya ya Saka masa a Baki tareda dauko ruwan Roba a fridge ya basa.


Yana shanye magana ko mintina uku beyiba sai gashi ya fara dawowa daidai Yana hada zufa idanuwansa nayin jajir.


Boyayyar ajiyan zuciya me zafi siddeeq ya sauke Yana kallan Haroon dan kuwa da Baya kusa wani abin ya samesa baisan me zaicewa JEEY ba.


Miqewa Haroon din yayi da kansa Yana kasa kallan siddeeq ya Bude Baki ahankali ya furta


"Thank you"


Kujera ya nufa ya zauna ahankali har lokacin zufa yake tsiyayowa ya dauki tissue Dake gabansa aje Yana Dan gogewa kadan.

#MAMUH#



*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

_Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments