Breaking News

Ameenatou 4


 *_AMEENATOU_*

_Mamuhgee_

#ZafafaBiyar

#Arewabooks@Mamuhgee




4

Hankalin Omar tashi yayi mummunan yi rashin Jin motsin mamman da lameenu Dan haka ya fara sarewa Dan kuwa idan har an kashe mamman da lameenu anyi musu mummunan raunin da seelahs zasu bace gaba Daya Dan Suma ba tsira zasuyiba.


Jamilu da Shima yafara gabalaita bazai iya taresu ba ya juyo inda su mamman din suke zai ambaci sunan lameenu kawai lameenun ya daga wuqarsa Dake wani irin daukan ido a duhun ya kutsata gabaki Daya a cikin jamilun take jamilun ya dago jajayen idanuwansa da sukai jajir ya Kalli fuskar lameenu,


Shima lameenu jamilun ya kalla tareda zaro wuqar ta sake kutsata a gefen cikinsa tareda cirowa jinin jamilun na gangara a hannunsa har qafafunsa,

Jajir idanuwansa sukayi wasu irin hawaye masu tsananin zafi suna cika a cikinsu dukkanin jikinsa rawa yakeyi hakama.


Mamman ma tasa wuqar ya Ciro ya daga sama tareda warawa da qarfi zai kutsata gefen cikin Omar kasim da acikin duhun idanuwansa suka sauka akan abinda yake Shirin faruwa yayi saurin karawa da niyar ture mamman din sedai tini wuqar ta kutsa gefen cikinsa ta shige gaba Daya.


Kafin ya zare wuqarsa acikin matune ukun wani ya sake sokawa kasim wuqar daga bayansa take mamman yayi saurin cire tasa wuqar Yana ja da Baya sbd juyowar Omar Yana ambatar sunan kasim da karfi.


Ihun Omar da sunan kasim dayake kira ya Saka aka juyo hayaniyarsu kafin su lameenu suyi kan Omar tini mutane suka yo runfar kowa suka juya kan fadansu kan wainda suka kawo musu farmakin suka illata su sosai Dan haka Koda aka taho da fitilu masu yawa ana duba mummunan lamarin dayayi Munin da Babu me iya kalla Dan kuwa jini ne na kowa da kowa da aka zubar Amma na kasim da jamilu da suka mutu a take shine yake gangara kwance a qasa hakama Omar yaji rauni sosai.


Su kansu mamman yajiwa kansa rauni sosai sbd fita daga zargi duk da a duniyarsu duk Wanda yasan seelahs yasan bazasu taba illata junansuba koda kalmomin bakinsu ba kuwa bare irin wannan mummunan kisan Gillan rashin tausayi da Imani tareda  tashin hankali.


Acikin wainda suka kawo musu farmakin Daya Shima take ya rasu sbd raunikan Daya samu dagasu mamman da lameenu sauran biyun ma sunji raunin sosai Dayan har idonsa Daya ta tsiyaye.


Duk tsananin halinda Omar ke ciki kuka yakeyi sosai kaman ransa zai fita da ganin gawar kasim a gabansa da jamilu,

Su kansu mamman da lameenu kuka sukeyi suna ambatar sunan Yan uwansu cikin tashin hankali da dacin zuciya.


Fada ne ya sake kaurewa akan gawawwakin uku sbd zinariyar dasuka bari take aka fara kokawa ana fidda makamai ana ihu batareda ko gawar an dauke daga gurin ba.


Hankalin lameenu Dan mamman tashi yayi suka Kalli juna Dan kuwa bazasu yarda ba bayan uban sukan bayan da akwai aminansu Yan uwansu na alkawarin har mutuwa duk akan wannan zinariyar Kuma suxo su rasata.


Omar gabaki Daya ya fita hayyacinsa sbd tsananin tashin hankali da girgizan wannan balain Dayake shedawa na mutuwar Rabin jikinsu biyu a lokaci Daya Kuma kisan rashin Imani.


Dayasan samun zinari zaiyi sanadin ran yan uwansu daya raki Allah ya hanasu samunta har karshen rayuwarsu.


Fada sosai kaman yaqi ya kaure a take gurin inda har an sake illata wasu mutum biyu an cinnawa rumfar wuta.


Omar da sauri duk rauninsa ya miqe ya dauki jakar zinariyarsu da shi kadai yasa inda suka ajiyeta ya daure a jikinsa tareda Jan gawar kasim ya fara fitarwa su mamman suka kamo ta jamilu suka fito da ita har lokacin kuka Omar keyi sosai Yana kallan gawarsu Yana juya ta yanda zaiyi rayuwa ba kasim hakama yanda zaije ya sanar da mahaifiyar kasim din kasim ya rasu ya barta hakama mahaifiyar jamilu.


Irin kukan dayake yi ne sosai ya Saka da yawa dakatawa daga tashin hankalin manyan Ashalawa din suka iso gurin ana haskawa da fitilu ana ganin Munin lamarin.


Akan gawar su kasim aka tsaya tareda wainda suka mutu duk akan fadan.


Gefe Akai dasu aka rufe Saida safe zaa musu sallah a rufe.


Omar kuwa dole dashi suka tafi Dan basa kariya idan ba Hakan ba Shima kafin safiyar ba samunsa zaayi ba Dan haka Suma su mamman duk tashin hankalin da suke ciki na yanda komai zai kasance Bai hanasu bawa Omar din kulawa ba daga raunikansa ba.


A rayuwar Omar bai taba tinanin zasu samu kansu a irin wannan mummunan yanayin ba duk yawonsu da hadarukan da suka Saba shiga,

Sun dauka zasu samu kyakkyawar rayuwar da iyayensu Basu samu ba Ashe zasuyi mutuwar kaskanci ne wadda iyayensu su Kam basuyiba sunyita ta rufin asiri daidai gwargwado sbd su a cikin rijiyar zinarin suke mutuwa.


Zazzabi ne take me karfin gaske ya rufesa Babu inda Baya kakkarwa a jikinsa gashi jikinsa har lokacin jini na zubar masa.


Mamman ne ya Kalli lameenu

Shima lameenun shi ya kalla kafin suka fara kokarin cigaba da tattalinsa suna basa kulawa da share masa jinin fuskarsa suna  kukan rashinsu jamilu.


Duk da antaho dasu Omar din bangaren manya kafin safe fadan Ashalawa din be kwanta ba saima qara girma yakeyi Daman lokuta da dama karamin fada ko fada kadan sai a tayarda fadan da fitinarsa zatai babbar illa ga kowa sai anyi rashin rayukan da dama shiyasa koyaushe zinariyarsu Bata karewa habbaka takeyi.


Fatinar Bata lafaba ko kadan take ta zama babba Ashalawa ta dauki hayaniya,

Koda asuba tayi sallah kawai Akai turawan sukace tafiya zasuyi sbd tashin hankalin dayaketa sake rikicewa.


Tini sukai waya helicopter zai taho ya daukesu ya fidda su dajin.


Babban tashin hankalin Daya Saka mamman da lameenu kusan Yanke jiki a gaban manyan Ashalawa da turawan da zasu siye danyar zinarin shine Sanar dasu gabaki Daya tarin danyar zinarin kasim ya bawa Omar tin a daren jiyan da Akai rubuce rubuce komai sunan Omar aka Sanya sbd Omar shine zai riqe musu dukiyarsu dashi dashi din Dan haka gaba dayanta ta Omar ce gashi kaf acikinsu ukun da suka samu me yawan gasken ta kasim din tafi ta kowa yawa hakama ta Omar din Dan haka lissafinta ma da aka hada din hankali bazai taba daukaba.


Wani mummunan hayaqin tashin hankali ne mamman yaji Yana fita kunnuwansa Yana gurbata numfashinsa dake fita da daqyar.


Lameenu kuwa manyan idanuwansa ya fiddo waje suna sauyawa zuwa jajir hannuwansa na daukan rawar tashin hankali yayi saurin qanqame hannuwan Yana kasa boye firgicinsa duk yanda yaso.


Juyawa yayi ya Kalli inda mamman yake zuciyarsa na dauka wani irin radadin zafi da 'dacin baqin cikin da Bai taba sanin da akwaisa ba.


Akan Omar dukkaninsu suka mayar da kallansu lokaci Daya zuciyoyinsu naci da wata irin wutan tafasar zuci.


Me kenan?

Omar sukaiwa kisan su kasim din kenan tinda shine yafi kowa arziki a Ashalawa kenan yanzu ko me?

Me Hakan ke nufi da cewan kasim ya bawa Omar taskar arzikinsa gaba Daya?


Lameenu a tasa zuciyar kuwa abu Daya ya sani shine tinda suka riga suka kawar dasu kasim akan zinariyar to kowama yayi musu shamaki da ita inda suka aika su jamilu can zasu aika koma waye,

Sun Riga sun fara aikinda Babu tsayawa sai sun mallaketa,

Omar bazai taba hanasu mallakarta ba Dan zai musu zarran da bazasu taba kamosa ba har abada Kila,

Tayaya zasu kallesa a samansu su suna qasansa bayan sune sukai dirty work din Daya basa Arzikin dukiyar.


Sake kallan juna sukai shida mamman har lokacin Babu Wanda zuciyarsa ba tafasa takeyi cikin tashin hankali da tsoron tabbatuwar abinda aka fada din ba.


Omar kuwa har lokacin Yana cikin halin rashin lfy Daya rufesa da kukan rashinsu kasim Daya kasa dawo dashi daidai.


Zinariyar kuwa baa tsaya komaiba aka ware ta Omar da kasim aka ware masa abarsa shine zai kula da mahaifiyar kasim Daman tamkar itace ta haifesa yake.


Ta jamilu kuwa batareda tinanin komai ba ko bin tsarin Daya kamata ba haka aka Kara rabe musu su uku,mamman da lameenu Da Omar din Wanda yace ya yafe musu aka barmusu su biyun.


Kason da suka samu ba qaramin kaso bane da zai ishesu Gina rayuwarsu cikin wadata sosai da Kwanciyar hankali tareda samarwa Kai suna da wani matsayin ma Amma duk wannan Bai saukar da mummunan nauyin Daya Riga ya danne zuciyarsu ba data rikide a dare Daya Takoma wata sabuwa daban da kadan Baya isarta.


Gabaki Daya baqin cikin duniya ba basusan dandanonsa ba shine dabaibaiye da zuciyoyinsu akan mahaukaciyar arzikin da suke kallan Omar dashi Wanda basajin zai taba sauka matiqar ba sune suka kasance mallakinta ba Kokuma rabinta ma.


Tafiya zaayi da Omar sbd baturen dayayi musu alkawarin Basu irin rayuwar da suke so shi da kasim kafin rasuwar kasim din Dan haka ana rufe su kasim tashin hankalin Omar ya qaru sbd Kai tsaye su mamman sukace ba zasu bisu ba su zasu zauna anan su sake samun zinariya kafin su biyosa.


Su biyar din basu taba rabuwaba tinda suke a rayuwarsu sai wannan ranar da biyunsu suka bar duniya gaba Daya sai Kuma yanzu da zaa tafi da Omar abarsu Badan sunso ba sai Dan ana son nuna musu fin karfi.


Mr Jaden da tin farko Allah ya Saka masa kasim arai sosai fiyeda kowa a Ashalawa sbd ladabinsa da nutsuwarsa data fita daban haka kawai yaji bazai iya barin Omar ba a Nan bayan rasuwar kasim Dan yariga yayi musu alkawari hakama zuciyarsa Bata yardar masa barin Omar a tsakanin mamman da lameenu ba Dan haka baiyi tsaiko a tafiyar tasu ba duk yanda Omar ke cikin tsananin tashin hankalin rabuwa dasu mamman Amma Shima yanason cika burinsu shi da kasim na rayuwar Kwanciyar hankali da nutsuwa tareda wadatar ilimi Dan haka yabi Mr Jaden din tinda su mamman din zasu biyo Daga Baya.



Mamman da lameenu tamkar tsokar jininsu ce ake yanka ana rabasu da ita sukeji a lokacinda suke kallo Omar zai tafi da tarin arzikin da suke ganin sunada cikakkiyar haqqi akanta tinda sune sukai aikin kawar da me ita din Dan haka kukansu da baqin cikinsu na tafiyar akan Hakan ne sedai zuciyoyinsu ne kadai ke kika Banda idanuwansu da suka bushe Babu komai Dake cikinsu bayan radadin Jan bacin Rai suna kallo har Mr Jaden Dake riqe da hannun Omar ya jasa suka nufi filin da helicopter din dazai daukesu yazo ya daukesu suka bar dajin Ashalawa.

##MAMUH#

#TOOTOOHOT

#JAMAAL JEEY SEELAH

#AMEENATOU SEELAH

#ZAFIN KAI

#LOVE

#DEEP

#ROM



*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

 _Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments