Breaking News

Tsutsar Nama 10


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒆𝒏_




.......Oho mu bama musan sunayi ba, dan lokacin da suke nasu bidiri ni inama can office ɗin MD na kai masa aikin daya saka ni. Kamar kullum yau ma a kwai mask a fuskata, sannan dogon hijjabi ne har yana jan ƙasa na saka. Dama dai shigar tawa kenan. Idan har ka ganni babu hijjab to abaya ce na saka kuwa. Amma gyale dai a jikina zan iya rantsuwar tunda ma mallaki hankalina na san kaina ban taɓa sakawa ba. To bamma da shi sam, sai ƴan madaidaita da nakanyi rolling idan zan saka abaya. Duk da yanda na suturta jikina bai hana MD zuramin idanu ba, dan shi indai kallone ya iya shi na masifa ma da UBANGIJI ya hanemu yi. Ni dai miƙa masa takardar nayi na maida hankalina akan wayata.

       “Wow! Kai Samraah sannu da ƙoƙari. Shiyyasa duk girman gidan nan ke na fara hangowa dan nasan bazanyi zaɓen tumin dare ba, saboda nai matuƙar yarda da basirar ki, kina da saurin ɗaukar abu wlhy. Sosai komai yayi, sai fatan ALLAH ya kaimu ranar kuma. Yanzu zuwa anjima sai kizo ki amsa kiyi printing nashi ko. Ki kuma je ki zama cikin shiri na musamman, dan wannan ranar muna fata ta zama ta musamman a garemu. Dan ALLAH kada ki saka dogon hijjabin nan tamkar matar limamin anguwa. Ki yi shiga ta ƴammatan zamani dan kin san irin manyan mutanen nan sunfi son komai na wayewa su balle shi matashi dake a ganiyar samartaka. Inda son samu ne ma ki saka sabbin kaya, ki samu makeup artist ta tsantsara miki irin kwalliyar nan taku ta zamani Please”.

       Yanda kuka san television haka nai galala ina kallonsa. To amma kun san tsiyar mutuniyar taku. Sai ban musa masa ba nayi murmushi kawai da faɗin, “In sha ALLAHU Sir”. Yako ji daɗi, dan tuni ya washe baki da jera min godiya. Niko sai nayi dariya kawai a raina. Kuga ɗan banza yana son iskantani kawai. Yo in ba son iskantawa ba taya zai ce nai irin wannan shiri dan kawai burge wani sakarai can da ban san ma a wace alƙibla yake ba, ta musulinci ko ta masu kaɗa ganguna. Humyim bai san halin ƴar Abdul-wahab ba ne ba, amma zan sanar da shi sannu a hankali. Office na koma na cigaba da harkokina. Bayan azhar kuma muka haɗu da Mansoor. Dan nifa da kuke gani na duk rintsi bazaka ganni office ɗinsa ba in ba a dalilin aiki ba. Dan tun farko daya fara nuna buƙatar hakan ta hanyar kirana wai nazo na samesa office na dakatar da hakan. Nama nuna masa anan fa aiki mukazo, ya kamata mu ajiye batun alaƙa gefe muyi abinda ke a gabanmu kamar yanda muka rayu a makaranta. Idan mun fita anan sai mu dawo da batun alaƙar. Mansoor mutum ne mai sauƙin kai da fahimtar abubuwa, sai in kana kallonsa daga nesa ne zaka fassarashi da girman kai. Ya fahimceni harma ya nuna jin daɗinsa da hakan. Bawai dan ina zarginsa da wani mugun haline nayi hakan ba. A'a nayine domin kare mutuncina da martabata ta ɗiya mace. Sannan kuma hakan da nayi zai ƙara bani kariya daga hare-haren irinsu MD da basu iya ɓoye maitarsu a fili ga ƴaƴan mitane.

       “Amarsu ta ango”. Daya faɗa ya sani ɗauke kai gefe ina murmushi. Shima ƙaramar dariya yayi yana dawowa ta inda na maida kan nawa. Ƙaramar harara na sakar masa ina sake ɗauke kaina. Ya ce, “Tab irin wannan harara haka amarya ai sai kisa na zube ƙasa wlhy. Kinga adana min ita sai nan da ƴan watanni kawai,  kinga inma suma nayi dai ƙya farfaɗo dani da kanki babu wanda yaji ko ya gani ko?”.

    Dariya ya bani, amma kasancewar ba'a ganin bakin nawa sai nayi murmushi kawai na sake ɗauke kaina.

      

     ★ Alƙawarin ALLAH ya cika. Iyayen Mansoor dai sun kawo kuɗi gidanmu a ranar juma'a. Ranar ni naga baƙin halin Mum muraran. Dan zage-zage ta dinga yi da yima Abba masifa wai an munafunceta. Ashe bai gaya mata ba sai ganin su kawu Musa yasa ta fara tambayarsa abinda ya kawosu. Shine ya sanar mata iyayen wanda yake nemana ne sukace zasu zo yau. Takaici ya sakata zuba masa ido kawai, amma ta kasa cewa komai. Dai-dai isowar baƙi kuma sai ga abinci Yaya Musaddiq na shigo da shi da ruwa da lemo batare da tasan daga ina aka dafo shi ba. Shiko Yaya Musaddiq sanin halinta da yay ne ya sashi saka matar ogansa ta dafa abincin. To ranar dai munga tujara. Dan nima da ban san mike faruwa ba ina a wajen aiki ina dawowa na samu rabona. Baby kuwa banda kuka babu abinda take yi. Ni dai ko uffan bance musu ba, a wajen Yaya Musaddiq kuma naji komai yanda ya kasance. Iyayen Mansoor sun kawo 300k, amma su Kawu Musa sun barma Abba 200k su sun ɗauki 100k na ɓangaren uba. Hakan da sukai baimun ba. Dan kamata yay su su ɗauki 50k Abba 50k aba Yaya Musaddiq 200k dan nasan dai shine mai mun wahalar ba kowa ba. Ban dai ce masa komai ba muka ci gaba da hira. Dan banama sha'awar shiga gidan. Ko hijjabi na ma da zan saka a gobe idan ALLAH ya kaimu domin zuwa taron can anan ɗakin Yaya na gogesa. Sai kusan sha ɗaya na shiga. Baby kawai na samu a falon zaune. Bance da ita komai ba na kama hanyar shigewa ɗakinmu.

     Ji nai kawai an sakar min duka ta baya tare da damƙo hijjab ɗina. Da ƙyar naja numfashi saboda an shaƙe min wuya. Nai saurin riƙe hijjab ɗin ta gaba na yaga shi sannan na juyo ina sauke numfashi da ƙyar. Baby ce tsaye tana faman huci kamar mai shirin dambe. Na mata kallon sama da ƙasa kafin cikin mamaki na ce, “Lafiya kuwa baiwar ALLAH zaki shaƙeni kamar wadda ta ci miki bashi? Are you okay?”.

         “A haukace nake dan uwarki. Kuma kaɗan ma na miki, wataran idan na shaƙeki har sai kin daina numfashi zan ƙyaleki. Dan haka ina mai gargaɗinki in har kina son ranki ki fita a sabgar Mansoor wlhy. Ki kuma bar ganin ya kawo kuɗi da sunan na aurenki, wlhy sai dai in bana raye hakan zata kasance. Dan yanda ban samesa ba kema baki isa samunsa ba jaka kawai ƴan karoro a gidan mutane mai ƙwacewa yaran gida samari su mayya”.

       Murmushi kawai na saki mai faɗi dan wlhy ni dariya ma ta bani da tausayi. Bance mata komai ba nai shigewata ɗaki na barta tana ɗuran zagi kamar ba dare ba. Zuwa can kuma naji kamar maganar Abba sama-sama ita kuma tana kuka. Baki kawai na taɓe na gyara kwanciya dan so nake nai barci sosai kodan abinda zan tunkara a gobe in ALLAH ya kai mu. Sai dai duk da haka kamar kullum sai da na tashi nai ƙiyamullaili dan ya riga ya zame min jiki tashin a kullum, sai dai idan banda lafiya, amma ko prioud nake saina farka....


     *_DAMA ACE....._*


            (Dama ace) kalmace mai harshen damo. Zaɓa mata gurbi a nawa labarin shine cigaba da nutsuwar saurarensa. Kamar kullum yau ma sai da nai duk ayyukan gidan kasancewar nasan yau ɗin Mum a cike take da haushina. Hatta shi Abban ban san a wane matsayi ya ɗauki auren nawa ba. Dan daya dawo da ga sallar asuba na gaishesa sama-sama ya amsa min ya shige ɗaki abinsa. Ga Baby a gefe da marasa kunyar ƙannenta su Bibaa da Nabil. Shiri na nayi kamar yanda na saba, dan baƙin dogon hijjabin jikina har jan ƙasa ma yake. Ban biye ta maganar MD ba, na kawo kuma face mask na saka kamar yanda na saba shima baƙi, na ɗaura sirrin farin eyeglasses ɗina da har ana iya ganin ƙwayar idona fes. Sai ƙamshi dake fita a jikina mai daɗin tsiya na humra da turare. Yaya shike sayamin turare da duk wani nau'in kayan kwalliya na mata. Hatta kayan ciki da suturu shine ke saya min. Hakan yasa banjin ƙyashin duk sanda salary na ya shigo account na tura masa su gaba ɗaya a account ɗinsa batare dana cire ko sisi ba a ciki. To idan na ajiye mizanyi da shi. Duk wani abinda nake buƙata baya gazawa wajen saya min. Idan abin yayi ya shigo zaka sameni a layin farko cikin masu sakashi. Da harda Baby yake saya, amma ta ce masa yama bar wahala bata so. Koda ta faɗa ɗin bai daina saya ba. Sai da yaga bata sakawa sannan ya daina. Hakan kuma baya hanashi bata kuɗi akan ta saya abinda take so. Wannan kam sukan amshe ita da uwarta kuma baza'a sayi abin kirki ba kuɗin zai gantale. Hatta da data sakara Yaya sakamin yake da credit, sai daga baya ne ma Mansoor ya amshesa wannan. Dan haka Yayanmu kallon uba nake masa ba yayaba wlhy, dan ya share mana kukan maraici tuni sai dai na kewar iyaye da bazai taɓa gushewa ba ga ƴaƴansu. Amma ta ɓangaren rayuwa komai Alhamdullah.

       Kamar yanda Yaya Musaddiq yay alƙawari shine ya ɗaukan a mashin ɗinsa da yasha wanki sai ɗaukar ido yake. Office ya kaini inda su Mansoor ke jirana dan da motar office zamu fita. Ba sauran abokan aikina ba hatta da Mansoor ƙuri yay kawai yana kallona cikin nuna mamakin ganin hijjab dana zuba har yana sharar ƙasa. Amma sai yay murmushi tare da kashe min ido ɗaya alamar yaji daɗin hakan da nayi. Nima murmushin nayi kawai na ɗauke kaina ina mai gaishesu. Duk suka amsa min da kulawa. Sai Davido ne ke magana akan shigar tawa. Ban tanka masa ba na shige mota abina na zauna batare da na yarda na kalla inda MD yake ba ko sau ɗaya, dan gaisuwa ma kaina a gefe nai masa. Naci sa'a dama sun gama loda komai dama ni suke jira. Kulsoom ma na ciki ita. Kusa da ita na zauna muka gaisa, sai gasu suma sun shigo. Da farko Mansoor na kula kusa dani yaso zama. Amma ganin yanda na koma jikin window muka saka bags ɗinmu a tsakkiya yasa shi haƙura ya zauna kujerar gabanmu, sai lokacin na ɗan saci kallon MD, yay kicin-kicin da fuska sai mazurai yake. Ƙasa nai da kai ina kwasar dariya, ɗan son banza an shirya ganin banza. To bata samu ba ai, sai a tafi wata tashar.......✍️





_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments