Breaking News

Garkuwa 18

*GARKUWAR FULANI*Ta kai hannun ta, kusa da bakinta kenan
Wani ƙaton gadamgare ya faɗo jikinta.
Wani irin tsalle tayi tare da rauza ihu, ta faɗa jikin Aysha tuni tayi fatali da akoshin gasassun zabbin nan ya ɓare ƙasa kirib.



A firgeci Ummiy ta yunƙuro tare da nufar inda suke, wanda hakan yasa tayi fatali da akoshin da akasawa Bappa zabbuwar da kuma take wanda aka zuba mata a plet ɗin ya ɓare cikin lallausan yashin garin.

Ita kuwa Junainah gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi, fizge-fizge takeyi tana ƙwaƙumar Shatu.
Sabida ita ji takeyi kamar dai har yanzu ƙadangaren yana jikinta.
Cikin kiÉ—ima Shatu ta ruggume ta, tare da cewa.
“Ke Junainah ki bar ihun Æ™adangaren ma ya razana da ihun da kika kurma ya sauÆ™a ya tafi.”
Jin hakane yasa ta tashi zaune tare da zazzaro ido,
Rafi’a kuwa dariya tasa tare da cewa.
“Kai Junainah yaseen kin cucemu, kallifa yadda kikayi fatali da akoshin nan”.
Cikin sanyi Shatu tace.
“Haba wannan abu dai Allah yayi ba raban mu bane, Ni dama can haka nan in naga naman sai inji zuciyata ya tsinke ashe ba rabanmu bane, da muncima da mun harar dashi.

Ita kuwa Ummiy jan hannun Junainah tayi kana ta zauna kusa da Shatu.
A hankali ta jingina kanta da kafaÉ—an Shatu,
Rafi’a kuwa miÆ™ewa tayi ta shiga kitchin É—in su.
Abincin data dafa musu ta kawo musu.
Ta ajiye gefe, sannan ta É—auko tsintsiyar kwakwa ta share ta kwashi naman kab ta maidashi cikin babban akoshin, ta rufe, sannan taje ta wonke hannunta kana tazo ta zauna suka fara cin abincin.

A can cikin fadar masarautar JoÉ—a kuwa.
Jin jiri na É—ibanshi ga duhu dake rufe mishi ganine ya sashi, tafiya a hankali tare da dafa jikin gini.
A haka har ya isa bakin Jakuzin,
A hankali ya zare al’kyabbar jikinshi, ya wurgar dashi can gefe,
kana ya tura ƙofar ya Jakuzin ya shiga,
tsayuwa yayi tsakiyarshi, hannun na rawa ya buÉ—e shawan ruwan É—umi.
Wani irin numfarfashi wahala ya sauke lokacin da yaji ruwan É—umi yana ratsa raÉ—i-raÉ—in azabobbun bulalin da yasha.
Wasu irin hawaye masu masifar zafine yaji suna tsastsafo mishi cikin jijiyoyin kekyawan idanunshi, sai dai basu kai ga damar samun zobowa ba.
Wani irin tsuma duk illahirin sashin jikinshi ya fara,
zafin ruwan yakeji har cikin ƙoƙon ranshi,
wani irin karkarwa haƙoranshi sukeyi har suna dukan juna, kat-kat.
Kanshi ya sunkuyar tare da buɗe idanunshi a hankali, ruwan dake gangarowa daga jikinshi yana bin ƙasa in da zai gangara yake kallo,
sabida zakace jinine ba ruwaba,
Sabida yana wonke mishi jinin jikinshi.
Haka ya tsaya a ƙasan ruwan ɗumin har saida yaga jinin ya daina zuba kamar da fari.
Sannan yasa hannunshi ya ɗauki daddaɗan sabulun wankan shi, ya fara murza sabulun taki wani sashi na jikinsa, wani irin wahaltaccen ƙara yayi lokacin da sabulun ya ratsa inda ya farfashe a jikinsa, cikin rauni yace.
“Wayyo Allah na! Wayyo Mamey na zan mutu, zafi zai kasheni tun kafin cikar burina.”
Ci gaba yayi da murza sabulun tare daci gaba da cewa.
“Wayyo Umaymah wayyo Ummi”.
Sai kuma ya taune lips É—inshi kana ya rumtse idanunshi yayi ta murza sabulun tako ina yanayi ruwan É—umi na dukanshi.
A haka yayi wonka ya wonke duk wani jini dake jikinshi yayi fes.
Al’wala yayi, kana ya fito cikin Glass É—in sannan ya É—auki wanni tattausan baby towel fari Æ™al ya É—aura a Æ™irjinshi ya sauÆ™o har zuwa guiwansa.
Hannunshi yasa ya murza farin boxes dake jikinsa wanda ɗazu yake jiƙe da jini yanzu kuma yayi fari tas.
Murza boxes É—in yayi har Æ™asa, kana ya É—aurashi kan al’kyabbar jikinshi da ya cire,
Cikin Woshing mashine yasasu,
Kana ya fara yin taku a hankali ya iso gaban drower’n glass É—in dake cikin bathroom É—in.
Wani tattausan gajeren wondo fari tas mai ratsin sky blue ya saka, gajeren wondon yazo mishi har guiwarsa, kuma mai É—an faÉ—ine,
Wata tattaunawar riga mai guntun hannu wacce itama farace da ratsin Sky blue, ya saka, kana ya zaro wata ɓakar tattausar jallabiya doguwa har ƙasa tazo mishi daya zurata,
Wani hulan taɓa kaji Hadisi ya kifa kan suman kanshi dake da ɗan damshin ruwan ɗumin.

A hankali yake taku sabida zuwa yanzu wani fitinenne zazzafan zazzaɓi yakeji.
Jiki na rawa ya fito, bisa sallayarshi dake shimfiÉ—e a wata Æ´ar kusurwa yaje ya hau.
Yana hawa kan sallayar ya fuskanci gabas, yaji zuciyarshi tayi wasai, baya tuna komai, baya kuma jin ciwon komai a jiki da zuciyarshi sabida kushi’i da tawakkali da kyutata ibada baya jin komai sai hasken farin cikin ibada.
Kabbara ya tada tare da niyar sallan la’asar daya mannata bisa laruri ya makarar dashi.

A falonshi kuwa, hankalin Haroon ya tashi yana nan tsaye bakin ƙofa yana ta magiyar ya buɗe mishi,
bai saniba shi yana can har cikin bathroom É—in shi.
Yana nan tsaye, mai Martaba LamiÉ—o da Galadima suka iso tare da Sarkin ShaÉ—i.
Cikin sanyi yacewa LamiÉ—o.
“Ya shiga ciki kuma ya rufe Æ™odar ta ciki, inata kiranshi baya amsawa.

Murmushi LamiÉ—o yayi kana, yacewa Galadima.
“Muje”.
Kusan a tare suka fito falon.
Suka zauna, kana ya kira Abba, yace yazo yasa ɗanshi ya buɗe musu ƙofar.

Jin hakane yasa Abba tahowa da sauri.

A can babban falon kuma. Cikin damuwa Jamil ya labartawa Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya abinda ya faru.
Ga mamakinsu sai sukaga Jakadiyarsu tayi wani ƙayataccen dariya cikin sakekkiyar murya tace.
“Alhamdulillah wannan shine abinda muka daÉ—e muna jira tsowon shekaru da dama.
Kuma jinyarsa abune mai sauÆ™in”.
Cikin ruÉ—ani Jalal yace.
“Ummi kuka daÉ—e kuna jira kuma?”.
Kai ta jinjina mishi, kana ta miƙe ta nufi kitchin dan harhaɗa aikin da akasata.

A nan Abba yazo ya samesu.
Jalal na ganinshi ya kauda kanshi.
Hakama Jamil Imran kuma bayanshi yabi suka nufi side É—in Jabeer É—in.

A falo ya samu iyayen nashi,
Cikin girmamawa ya rusuna yayi Lamiɗo Barka da yammaci kana ya matso kusa da baƙin ƙofar Bedroom ɗin Jabeer cikin ɗaga sauti yace.
“Muhammad! Muhammad Jabeer! Jabeer!! Jabeeey!!! Ka taso maza kazo ka buÉ—e min Æ™ofar nan ina jiran ka”.

Jabeer kuma da yanzu yake raka’ar Æ™arshe, sam hankalinshi baya ga jin kiran Abbanshi domin a yanzu yana gaban Ubangijinmu ne.

Haroon kuwa wayar dake kunnenshi ya gyara riƙewa cikin shaƙiyancinsa yace.
“Uhumm Umaymah ke dai kicewa Sarki Jalaluddin da Sarki Abubakar baban Daddy na, suyiwa masarauta JoÉ—o gudumowar suturu. Domin yau dai ran Æ´an maza ya É“aci, nasan sai ya yayyage kab wani abu mai yaguwa a masarautarsu”.
Cikin wani irin farin cikin wannan labarin da Umaymah taji tayi kekkyawan dariya tare da cewa.
“Haroon yayan naka kakeyiwa tsiyako?”.
Cikin tura baki yace.
“Allah ko Umaymah kecema kike sawa Jabeer yana rainani wai yayana”.
Da sauri tace.
“To ba yayanka É—in bane?”.
Cikin yamutsa fuska yace.
“Yayan kwana arba’in, shiyasa yake min kallon kobo biyu da sisi, sabida yana jin kuna ce mishi yayana, wani lokacin har cemin yaro yakeyi dan tsabar son girma da manyance, Ni mamaki da yake bani kawai sai in zuba mishi ido in naga yana min faÉ—a kamar wani É—an cikinsa”.
Murmushi Umaymah tayi kana, tace.
“Gobe zuwa jibi in sha Allah ina nan zuwa Masarauta JoÉ—o, sabida zanzo in lallashi É—ana nasan yayi zazzafan fushi tunda yaÆ™i kula Dr Aliyu ma”.
Daga nan sukayi sallama.

Shi kuwa Sheykh Jabeer saida ya isar da sallameshi yayi addu’o’in shi
Kafin ya tashi a hankali ya nufi bakin ƙofar sabida zuwa yanzu zanan bulalin sunyi tsami ga zazzaɓi daya mishi rubdugu.
A hankali ya murɗa key ɗin ƙofar ya buɗe ta, kana ya juya ya koma kan gadonshi, sabida rawa da jikinshi keyi na zazzafan zazzaɓi da wahala.

Yana konciya ya lumshe idonshi tare da fara karanta Suratul Khaf kasancewar yau yammacin jumma’a ne.

Su kuwa a falo suna jin sautin buɗe ƙofar, suka zubawa ƙofar ido ganin shiru bai fitobane yasa.

Galadima da Haroon suka nufi cikin É—akin.
Jim kaÉ—an da shigarsu Galadima ya fito da sauri ya kira sarkin ShaÉ—i, da LamiÉ—o kana da Abba.

A tare suka nufi cikin É—akin, suna shiga Haroon ya fito.
Babban Falon ya koma ya nufa yana kiran Jakadiyarsu da sunan da suke kiranta.
“Ummi! Ummi!!”.
Da sauri ta fito kitchen ɗin riƙe da filas da kofuna, sai kuma wani ɗan kwarya mai kyau ruwan ciki na tururi.

Da sauri ta miƙa mishi tare da cewa.
“Yauwa Haroona gashi kai musu da sauri”.
To yace kana ya amsa ya juya ya koma, can cikin É—akin Jabeer É—in.

Zaune suke gaba ɗayansu, shi kuma yana konce ya duƙunƙune cikin wani jibgegen blanket mai masifar kyau da taushi.
Sai karkarwa yakeyi tamkar mazari,
Cikin sanyi LamiÉ—o ya É—an janye borgon tare da cewa.
“Jabeer!”.
Duk da azaban zafin da yake ciki, bai hanashi buÉ—e idonshi ba, wani irin mugun kallo ya watsawa LamiÉ—o,
murmushi sukayi baki É—ayansu kana cikin lallami Galadima yasa hannunshi ya kamo nashi cikin sanyi yace.
“Jabeer tashi ko? Tashi kasha mgni”.
A kufule yace.
“Bazan shaba ku barni in mutu tunda hakan shine fatanku”.
Da sauri Abba ya kauda kai tare da yin wani faffaÉ—an murmushi kana, ya juyo ya kalleshi cikin bada umarni yace.
“Muhammad tashi. Maza tashi kasha mgni”.
Kanshi ya ɗan gyaɗa kana a hankali ya fara yunƙirin tashi zaune.
Ganin hakane Haroon yayi saurin taimaka mishi ya tashi zaune.
Idonshi ya rumtse sabida ji yake kamar har cikin ƙasusuwan jikinshi ake tsikara da bakin allurai gashi duk inda hudar gashi yake a jikinsa sai ya ɗan tasa kamar wurin da cinaka ya ciza.
Cikin tarin kula da wani mashahurin farin ciki, LamiÉ—o da kanshi ya amshi haÉ—in maganin da sarkin ShaÉ—i yayi mishi a wani ma dai-dai cin kofi.

Hannunshi yasa ya amshi kofin kana ya kaishi bakinshi,
fuska ya kwaɓe sabida gafin mgnin da yaji a jikinshi.
Cikin bada umarni Abba yace.
“Ka shanye duka”.
Ido ya rumtse kana ya kafa kanshi ya shanye shi tas.
Miƙa musu kofin yayi, kana ya amshi wani kofin da Abbansu ke miƙa mishi,
Shima shanye shi yayi tas.
Yana miƙa wa Lamiɗo kofin.
Ya fara wani irin gyatsa mai ƙarfi, gyatsan a jere a jere.
Cikin sanyi Haroon yace.
“Sanno my broz”.
Ina babu halin amsawa dan gyatsan ya tsananta, wani irin zufane ya keto mishi daga tsakiyar kai har kan babbar yatsarshi.
Wani irin murÉ—ane ya fara É—ibanshi tamkar zai tsinke mishi Æ´aÆ´an hanji.
Cikin wani irin zabura ya fara wani irin yunƙiri.
Sai gashi yanata kela wani irin baƙin amai akan tattausan blanket ɗin nan.
Murmushi Sarkin ShaÉ—i yayi tare da kallon aman da kyau kana ya juya ya kalli LamiÉ—o da Abba yace.
“Da dafin kunamai yake tsuma bulalinshi, ga nan dafin yake amayarwa.”
Murmushi Galadima yayi tare da cewa.
“Uhumm kaji mugun banza ko”.
Shi kuwa Abba ido ya zubawa Jabeer ganin yadda yaketa kela amai, fuskarshi nan tayi jazir, jijiyar kan goshinsa nan ta tashi ta miƙe samɓal.
Haroon kuwa tallafeshi yayi yanata ce mishi sannu.

Sai dai yayi kusan 30 minutes yana kwara amai kafin ya koma ya jingina da jikin Haroon yanata wasu irin zafafan numfarfashi tare da lumshe idonsa.
Da sauri LamiÉ—o yasa hannunshi ya tattare blanket É—in ba tare da aman ya É“ata ko maiba.
Ya dunƙuleshi ya miƙa wa sarkin Shaɗi.

Da sauri Sarkin Shaɗi ya miƙa Abba wani butan duma.
Sannan ya amshi borgon.
Shi kuwa LamiÉ—o Haroon ya kalla tare da cewa.
“Cire mishi wannan rigar”.
Da sauri Haroon yace to kana ya fara kiciniyar cirewa mishi jallabiyar.
Duk da yana galabaice saida ya É—an ja tsaki tare da ture hannun Haroon cikin muryar dake baiyana a wahalce yake yace.
“Bana so ku barmin rigata”.
Hannunshi Abba ya buge tare da cewa.
“Bakinka bazai mutu bako”.
Shiru yayi yana gani Haroon ya cire mishi rigar
cikin murmushin da ganin jarumta da ƙarfin hali irin na Jabeer Galadima yace.
“Cire wannan ta cikinma”.
Ba musu ya bari Haroon ya cire mishi rigar,
Wani irin zaro ido Haroon yayi gani duk jikinshi yayi shatin zanen irin manyan kunama nan”.
LamiÉ—o da Galadima da Sarkin ShaÉ—i kuwa murmushi sukayi tare da haÉ—a baki wurin cewa.
“Uhum dafin ya gama fita, cikin jininshi.”
Abba kuwa hannun ya haɗa ya miƙa wa Lamiɗo dake mishi alamun zai zuba mishi abu a hannun.
Wani haÉ—in mgnin ya zuba mishi cikin tafin hannunshi.
Murzawa yayi kana, ya shafa a duk jikin Jabeer.

Wani irin sassanyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da lumshe idonshi.
sabida wani irin sanyin da yaji yana ratsashi har cikin ƙasusuwan jikinshi.
Tuni wani bacci mai fitinenne daÉ—i ya kwasheshi.

Nan suka gama yi mishi komai.
Kana suka fita,
Dr Aliyu kuwa da Ya Hashim suka shigo bisa umarni LamiÉ—o.

Drip and injections Dr Aliyu ya ɗaura mishi tare dasa ruwan alluran a cikin ƙarin ruwan da akeyi mishi.

Ganin sun gama yi mishi komai ne, suka fita suka tafi.
Suka bar Haroon kaɗai. Dan in ruwan ya ƙare ya cire mishi.

A falo kuwa Ya Hashim nayi musu bayanin ya samu bacci jikin da sauƙin duk sai suka tashi suka nufi masallaci.
Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya aka bari a wurin.
Sum jin shiru ba motsin Haroon yasa suka tafi sashin Juwairiyya dan bawa hadimanta umarnin shiga kitchen.

Bayan awa ɗaya kuwa ruwan ya ƙare ya cire mishi.
Ganin yana bacci ne yasa ya shiga wonka.

A can cikin gidan kuwa. Sashin Gimbiya Saudatu zaune take a bisa bakin gadonta ita da Laminu É—an ta na biyu video da yayi a Rugar Bani na zabgar Jabeer yake nuna mata, cike da tsantsar jin daÉ—i, sai dariyar mugunta sukeyi.
Babban É—an ta Ya Hashim ne, zaune can gefensu, ya zuba musu ido, yana nazartansu, to sukuma me sukeji a zuÆ™atansu, akan Jabeer da sauran Æ´an uwansa shin duk wannan Æ™iyeyyar ta mecece”.
Muryar Baba Nasiru suka jiyo a falon yana sallama.
Da sauri Gimbiya Saudatu ta miƙa tsaye tare da kamo hannun Laminu tace.
“Zo taho muje gacan Æ™aramin Babanku”.
Da sauri suka nufi hanyar fita, wani irin kallo yayiwa Ya Hashim tare da jan tsaki cikin faÉ—a tace.
“Banza mara zuciya, wanda bai san masoyansa da maÆ™iyansa, ai dai duk abinda nakeyi a kankane”.
Tana faÉ—in hakan suka fice.
Jiki a mace yabi bayansu, Allah ya sani baya son cutar da Jabeer da sukeyi.
A falon ya samesu zaune harda Baba Bashiru sunata sheƙa dariyar mugunta.
Gefe can ya zauna ya zuba musu ido. Bayan sun É—an tsagaita dariyar ne,
Baba Nasira ya nisa tare da cewa.
“Allah kenan maji roÆ™on bawa, gashi ya amsa min addu’o’in da nai a safiyar yau É—in nan,
Yadda na wuni da baÆ™in ciki, shi kuma zai kwana da azaba”.
Cikin sauri Gimbiya Saudatu tace.
“Ai Ni nafi kowa farin cikin wannan dukan Kawo wuÆ™a da akayi wa wannan hegen yaro mai jajayen kunnu, yaro sai hegen baki da rashin tsoro duk barazanar da akeyi mishi baya kashe bakinsa.
Musamman ni kam ina mgna kafinma in sauÆ™e numfashin ya bani amsa ga shegen azanci. ÆŠan is abun buga cincim yau dai babu wannan bakin ai”.
Cikin dariyar ƙeta Laminu yace.
“Ai wlh Umma ni so nayi a kashe hege a can, mu binneshi a waccar Æ™aramar Rugar mu dawo salum salum abinmu”.
Cikin murtuke fuska Baba Basiru ya kallesu tare da cewa.
“Ai Ni yau ko mutuwa yayi ban huce baÆ™in cikin dana shaÆ™a ba lokacin da naga ya fito É—akin sirri da LamiÉ—o har yanzu in na tuna zuciyata bugawa takeyi, to wai ma meye hakan ke nufi.
Da farin É—an uwanmu da aka bawa Galadima ya rasu dare É—aya, ana biyu aka bawa wancan hegen yaro mai nisan kwana Jafar É—in sarautar.
Wannan abu shi yafi komai tada mana hankali, tunda dama duk cikinmu yaran LamiÉ—o babu wanda ya ba koda sarautar fadanci ce sai Yaya Muhammad, to kuma dan ya rasu sai a maida sarautar kam jikoki a tsallake Æ´aÆ´an duka.”
Cikin tafasar zuciya Laminu yace.
“Yo waya ma sani ko sune suka kashe mana Babanmu dan mulkin ya koma hannunsu, ku kuma kuka barsu”.
Da sauri Baba Nasiru yace.
“Muka barsu kuma, ai Allah ne zai barshi ba mu in bamu É—auki mataki ba, Allah ya nuna ikonaa yanzu shi Jafar É—in kallon me akeyi mishi?”.
Da sauri Gimbiya Saudatu tace.
“Mahaukaci tuburan”.
Dariya sukayi kana cikin rashin gamsuwa Laminu yace.
“To kuma duk da haka ai ba’a dawo da sarautar kanmu ba sai, aka bawa É—an tsohon sarkin wannan bappan naku mai farin gemu.
Bayan nan kuwa duk bawa kowa mulkin komai ba, dan sakacinku an É—auki mulkin Garkuwa an bashi.”
Cikin sanyi Ya Hashim ya harari ƙanin nashi tare da cewa.
“Laminu kafa ji tsoron Allah ka tsarkake zuciyarka, ka raba kanka da wannan zalumci da kafurar zuciya”.
Cikin zafi Gimbiya Saudatu tace.
“Rufe min baki, samodaran banza sako tumaki É“allo jakai,”.
Cikin sanyi yace.
“Umma badake nakeyi ba da”.
Cikin mgnar in-ina Baba Nasiru yace.
“Tafi daga nan damu kakeyi mana, ka fake da Laminu, maza tashi ka bamu wuri”.
Miƙewa yayi ya fita ya bar musu wurin ya nufi sashinsa wurin iyalanshi.

Su kuwa nan sukaci gaba da sabgogin gabansu.
Nan Gimbiya Saudatu ke cewa.
“Sai gobe da sassafe zanje in salon hegen balaraben nan”.
Dariya Laminu yayi tare da cewa.
“Yau da yaga haza, yaga zai zanu sai cewa yayi, wai shi ba bafulatani bane, a kirashi dama duk Æ™abilar da akaga dama”.
Playing video yayi ya miƙa wa su Baba Basiru tare da cewa.
“Jaridar safi ta gobe da safe da wannan labarin zai fito a shafin forko nako wanne kamfanin jarida,
Kana wannan abun shine hirar da BBC Hausa da kanshi zasuyi karin kumallo dashi. Sai wannan lbri da video da hotuna sun bazu tako ina, dan ina jirane sai jaridu sun fidda shi kafin in watsashi kafafen yaÉ—a labarai na duniyar gizo-gizo”.
Cikin tsananin jin daÉ—i suka jinjina wa basirar Laminu.

A can sashin Gimbiya Aminatu kuwa, kekyawar tsohuwar bafullatana ƴar kimanin shekaru 61 sosai hankalin ta ya tashi jin labarin abinda ya samu jikanta mafi soyuwa a gareta. Cikin rawan jiki ta miƙe tare da juyawa zata nufi Side ɗin ta.
Da sauri LamiÉ—o yayi gyaran muryar dake mata nunin ta zauna ta nitsu.
Cikin tashin hankali ta koma ta zauna tare da cewa.
“Allah Rane zanje in duba halin da yake cikine”.
Cikin ƙasaita da bada umarni yace.
“Koma ki zauna ki nitsu kin ga magriba ta Æ™ara to. Bawai zan hanaki zuwa bane, ki bari ayi sallan magriba da isha’i sai ki aika Jakadiya ta dubo miki in idonshi biyu sai kije”.
Ba don ta soba ta amince da hakan.

Hajia Mama kuwa, tana jin lbrin abinda ya faru daga bakin Abba, kai tsaye daga sashinsa sashin Jabeer É—in ta nufa.
A falo ta samu Haroon kadai zaune cikin shigar kakanan kaya. Cikin tashin hankali da kiÉ—ima da firgici ta nufi hanyar side É—in. Jabeer É—in ido na zubda hawaye.
Da sauri Haroon ya miƙa tsaye cikin sanyi yace.
“Mama ya samu bacci ne, kuma Dr Aliyu yace kada a tadashi, jikin da sauÆ™i ma sosai ki kontar da hankalinki”.
Ina hankalinta bai konta da hakanba, saima ƙara kutsa kai cikin falon side ɗin shi takeyi.
Cikin sanyi ta tsaya jin Haroon na ce mata.
“Dan Allah Mama kiyi haÆ™uri, Allah kuwa jikin da sauÆ™in, Abba da LamiÉ—o da kansu suka kula dashi, yanzu haka bacci yakeyi.”
Cikin tashin hankali murya na rawa tace.
“Haroon hankali na ya tashi sosai, ina tsoron kada a cutar min dashi kamar yadda akayiwa Jafar.”
Hannunta ya kamo kana yaja suka dawo falo, cikin sanyi yace.
“In Sha Allah babu wani abinda zai sameshi, in Allah ya yarda an gama samun nasara a kansu, yanzu warakace ke kusantosu, in sha Allah duk sarÆ™aÆ™iyan dake sarÆ™afe cikin masarautarku da mutanen cikinta zai worwore, za kuma ayi walÆ™iya kowa zai ga kowa!”.
Wani irin lumshe ido tayi tare da cewa.
“Allah yasa haka”.
Cikin kontar mata da hankali yace.
“Amin Amin. Umaymah ma tace tana nan tafe”.
Cikin tarin mamaki da baiyana tsantsar jin daÉ—in ta tace.
“Alhamdulillah kai naji daÉ—in wannan mgnar ko ba komai in tazo ai zan samu wacce zan tattauna damuwar raina, sabida hirar waya bata wadatar wa”.
Murmushi yayi tare da nuna mata hanyar fita cikin tsokana yace.
“Wato kun san É—an naku ragone shiyasa duk kuka tashi hankulanku.”
Cikin share hawayenta tace.
“Haroon yayanka nefa”.
Tura baki yayi tare da cewa.
“To naji Hajia Mama je kiyi salla lokacin salla yayi, kinji an fara kiran salla”.
Da haka ta fita.

Shi kuwa Haroon a hankali ya nufi cikin É—akin, kamar yadda yabar Ya Jafar zaune a tsakiyar gado yasa Jabeer a gaba, yana karatu tare da gyara mishi rufuwar shi.
Haka ya sameshi yanzuma,
Kuma har zuwa yanzu idonshi bai daina zubda hawaye ba.
Kana ganin fuskarshi zaka hango zazzafan so da ƙanan da tausayin ƙanin nashi cikin ƙwayar idonshi.
A hankali Haroon ya matsosu.
Cikin sanyi yakai hannunshi ya kamo hannun Ya Jafar É—in.
Kanshi ya É—ago ya zuba mishi ido.
Murya cike da rauni Haroon yace.
“Ya Jafar tashi kazo muje masallaci lokacin salla yayi. Muje muyi salla muyiwa Sheykh Jabeer Addu’o’in samun lfy”.
Kanshi ya gyaɗa sabida in dai abu na ibadane to bai kasance jiɓeɓɓe a kanshi ba.
Sunkuyo wa, yayi ya sumɓaci goshin Jabeer kana, ya sauƙo kan gadon.
ƙofar Bathroom Haroon ya nuna mishi da yatsa.
Shiga yayi bayan ya fitone, shima Haroon ya shiga ya sabunta al’wala kana, suka fita.

A babban falon suka samu, Aunty Juwairiyya da Jakadiyarsu suna shirya musu abinci bisa dinning table.

Cikin kula Aunty Juwairiyya ta kalli Haroon murya a sanyaye tace.
“Haroon ya jikin nashi dai?”.
ÆŠan tsayawa yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah gsky zama muce ya worke, sabida ya amayarda duk wani dafin dake jikin bilalin yanzu naga shatin kunaman ma duk sun É“ace a jikinshi, ya zama sai shatin bulalin”.
Murmushi Jakadiyarsu tayi tare da cewa.
“Suma nanda kwana uku in sha Allah babu tabonsu a jikinshi. Na gaya muku ai jinyar ShaÉ—i ba abu mai wuya bane a masarautar JoÉ—a, yanzu da asibiti aka kaishi, koda ko Æ™asar waje za’a fiddashi a Æ™alla sai anyi watanni uku ana jinyarshi, in yanada nisan kwana ya worke da kyar in kuma kwananshi sun Æ™are ya cika a can. Amman yanzu yana tashi bacci zaiji sauÆ™in sosai”.
Cikin mamaki suka zuba mata ido.
Jalal da Jamil da yanzu suka shigone suka haÉ—a bakin wurin cewa.
“To wai Ummiy meyasa naga kamar farin cikin, abun kikeyi keda ko ruwan sama bakya son ya taÉ“a lfyarmu mu bare É—an gatanki”.
Kanta ta É—an jijjiga tare da cewa.
“Abune mai duhu shekarun ku baiyi yawan da zaku gane haskenba, su kansu magautan Jabeer duk basu san Æ™arfin iko da sani da shaharar wannan masarautar akan al’adun ShaÉ—i bane,.”
Jafar ne yayi gaba bayan ya duba agogon hannunshi ganin hakane duk suka bi bayanshi.

A can Rugar Bani kuwa, bayan anyi sallan bamgrib, anyi Isha’i.

Shatu, Rafi’a, Ummey, da kuma Bappa sai Autar gidan Junainah dake konce gefen Ummey duk sunyi shiru.
Suna jin Bappa yana basu lbrin yadda komai ya faru a wurin gasar cikin sanyi yaci gaba da cewa.
“Tabbas akwai abinda Allah yake nufi da wannan bawan, haƙƙun nasan Allah bazai bari a zalumceshi haka nan banzaba, inaji a jikina akwai wani babban al’amari mai girgiza zuÆ™atan mutane da zai faru a nan gaba”.
Cikin sanyin murya Rafi’a tace.
“Bappa meye sunan jikan sarkin ne?”.
Cikin sanyi Bappa yace.
“An faÉ—a amman na mance sunan”.
Sallamar da wani yaro yayine ya sasu maida hankalinsu kanshi, bayan ya rusuna ya gaisa Bappa ne yace.
“Bappa ana sallama da Shatu wai tazo”.
A hankali Shatu dake zubda hawaye ta juyo ta kalleshi. Bappa kuwa cikin girma yace.
“Waye ne?”.
Wani irin azabebben ajiyan zuciya Shatu ta sauƙe jin yaron yace.
“…!

 

No comments