Breaking News

Garkuwa 19

By
*GARKUWAR FULANI*”Ya Salmanu ne yake kirantan, yace tayi haƙuri tayi sauri ta fito.”
Cikin sanyin jiki Shatu ta manna kanta jikin kafaɗar Rafi’a.
Shi kuwa Bappa, gyaran murya yayi tare da cewa yaron.
“To je kace mishi tana zuwa.”



Jin haka yasa yaron ya juya ya fita.

Miƙa Bappa yayi kana ya kalli Shatu murya a sake yace.
“Shatu tashi kije, kiji dame yake nemanki”.
Cikin sanyi tace.
“To”. Kana a hankali ta miƙe dan cika umarnin Bappa.
Rafi’a kuwa, miƙewa tayi ta shiga cikin ɗaki, gyara musu wurin konciya tayi, sannan tazo ta shigar da Junainah kana ta cewa Ummey su shiga, jiki a saɓule Ummey ta miƙe suka shiga.
Bappa kuwa turakanshi ya shiga.

A can ƙofar gidan kuwa.
Bisa ɗan dakalin ƙofar gidan nasu, suka zauna.
Tunda suka zauna tayi shiru, kanta na sunkuye tana wasa da ƴan yatsunta, kana hawaye na ɗigowa kan tafin hannunta.
Shi ma Ya Salmanu shiru yayi, tamkar bazaiyi mgna ba.
Farin wata kuwa ya fito ras ya haska ko ina, alamun yau watan ya kai kwana tara ko goma.
Kanshi ya ɗan juyo ya ɗan kalleta cikin tsananin tausayawa ya fidda numfashi mai zafi tare da cewa.
“Shatu!”. Shiru bata amsa mishiba sai dai ɗago kanta tayi tana kallonshi hawaye na kwaranya, wani irin murmushi yayi cikin sanyi da harshen fillanci yace.
“Bazan hanaki kukaba, Shatu, sabida koni kaina nakan zubda zafafan hawaye a duk sanda na tuna yayuna ƙannena makusantana, abo kaina da aka kashe, wanda basujiba basu ganiba.
Nakanji zuciyata na tafasa, tafasar da nakejin bazai taɓa gushewa ba sai na ɗauki fansa.”
Cikin rawan murya tace.
“Ya Salmanu fansa kuma?”.
Kanshi ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Uhum fansar dai, tunda hukuma da gwamnatin da masarautun gargajiya basu ɗauki mataki kan abinda akeyi mana ba. To mu zamu ɗaukarwa kanmu.”
A hankali tace.
“Ta yaya ɗin bayan duk an kashe matasa majiya ƙarfin. Cikin kaso goma na mutanen Rugar Bani an kashe kaso 6 huɗune suka rage. Me amfanin ramuwa, wlh da zan faɗa aji da mun bar musu garinsu kawai mu koma wani wurin”.
Gyara zaman shi yayi ya fuskanceta da kyau cikin sanyi yace.
“Ko wani ɗan adam ina ya shiga dumuwa, ire iransa ke shige mishi ya magance matsalar.
Yanzu da ɗan jarida ɗaya aka kashe zakiga zakiji yadda ƙungiyoyin yan jaridu zasu magantu, sai ya zama babu wani rahoton da zasu buga sai na kashe ɗayansu da akayi.
Hakama da za’a kashe police officer ɗaya zakiji yadda hukumar zatayi ta bincike da ɗaukar mataki har sai sun gano wayene sun kuma ɗauki mataki.
Da za’a ƙona kamfani ɗaya ire irensa kamfanoni sama da dubu zasu iya shiga fadan.
Hakama in da za’a taɓa ɗan kasuwa to zakiji yadda duk yan kasuwa zasuyi ta kumfar baki.
Da za’a kashe manomi ɗaya to zakiji yadda gungun manoma zasuyi rubdugu kan mgnar.
Da za’a taɓa bafaden wata masarauta zakiji duk masarautun ƙasarnan sun amsa.

Haka abin yake. Duniyar ta zama waka sani? waya sanka? Mu kuwa Fulani bamu san kowa ba bayan Allah da Manzonsa, bamu da wani namu a siyasance.
To tunda haka abin yake, muma da wannan salon zamuyi amfani.
Muna nan munata raba goron gaiyata wa duk al’ummar fulanin makiyaya a duk inda suke a cikin duk faɗin duniyar nan, in dai sunada damar zuwa to su zo!.
Su kawo mana agaji, wlh in sha Allah da izinin ubangiji sai mun yaƙi kafuran Bonon sai mun kashe dodon tsafinsu Bonon mun hallakashi a doron ƙasa,
Shatu mun kai matakin da wallahi babu mahaluƙin da zai dakatar damu.
Sai mun kauda Shirka da waɗannan mushirkan a wannan yankin.”
Ido ta rumtse wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata.
Cikin muryar dake nuna ƙunar ranta tace.
“Ya Salmanu wane mataki ake ɗauka kan neman su ya Giɗi kuma?”.
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
“Yana cikin matakin shiga cikin ƙabilar mu yaƙesu, mu kuma bincika ko sun ɓoye su Giɗi a cikin garin nasu”.
Ajiyan zuciya taja tare da cewa.
“Allah ya taimaka”.
Amin Amin.
Murmushi yayi kana yace.
“Kinji batun gasar da akayi ko da nasarar dake tinkarar rayuwarki ko?”.
Cikin sanyi tace.
“Kaiya ya Salmanu ina kake da tabbacin nasara mutumin da bamu san irin fansar da zai ɗaukaba, naso ace kaine kai wannan nasarar da nafi kowa farin ciki”.
Murmushi mai ciwo yayi a ranshi kana yace.
“Nan ɗin ma muna zaton farin ciki, duk da akwai tarin ƙalubale, mu dai in mun samu wani ya ci Ba’ana a gasar Shaɗi kin san yayi al’washin zai bar ƙasar nan gaba ɗaya ko?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Uhum in bai sauya salon ba dai”.
Cikin jin daɗi yace.
“Ba zai sauya saloba, dole zai bar ƙasar sai dai shiri zaije ya ƙara, kafin ya dawo kuma, an aura min ke, shi kuma jikan sarki.
Muyi musu mubaya’a, mun yarda su masarauta Joɗo fulani ne”.
Cikin tsananin jin daɗi tace.
“Allah ya tabbatar da haka ya Salmanu yasa kuma a samo su Ya Gaini cikin Bonon don Ni dai nafi zaton can suka kaisu.
In anyi gasar an cishi, ya bar kasar, a ɗaura aurenmu a ranar”.
Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe idanunta alamun jin kunya,
Shi kuwa Salmanu murmushi yayi tare da cewa.
“Iye yan Matana an girma, me ma za’ayi mana?”.
Cikin kunya tace.
“Ban saniba”.
Murmushi yayi kana yace.
“Ni ai bazan manceba tunda yanzu burin mu na kusa da cika, ayi mana aure, nima haka ne tsarina ana watsewa gasar suna tafiya, za’a ɗaura mana aure.
Kinga gashi dama na samu aiki a babban birninmu.
Sai mu tafi can abinmu ko Wannan mugun saurayin naki ya dawo bazai samemu ba”.
Murmushi tayi shi kuwa ido ya zuba mata yana jin tarin farin ciki.

*DAN ALLAH DA MANZONSA DA DARAJAR IYAYENKI DA SUKA HAIFEKI SUKA BAKI TARBIYYA, KADA KI FITARMIN DA LITTAFINA DAN AL’FARMA ANNABI DA AL’ƘUR’ANI, KU DENA FITAR MIN DA LITTAFI DAN ALLAH Especially ku ƴan SPG na roƙeku da Allah

Da sauri ta gimtse dariyarta, cikin sanyi da tsoro ganinshi tamkar gilmawar walƙiya sai gashi a gabansu.
Wani irin azabebben tsorone ya rufe Salmanu amman sai ya dake, cikin ƙarfin hali da kalato jarumta ya kame jikinshi dake rawa.
Cikin ɗan rawan murya yace.
“Me haka, zuwa babu sallama?”.
Wani mugun kallo ya watsa mishi tare da cewa.
“Kiyaye bakinka idan maza suna wuri.”
Cikin dakiya Salmanu yace.
“Ina mazan!? Ai ni banga wani na miji a nanba sai mata maza. Ai namiji shi zai iya sa namiji ɗan uwanshi zubda hawaye ko tsuma da faɗuwa, a dai yanzu ai babu wani namiji a Rugar Bani da kewaye sama da Jarumin da bulalar SHAƊI bata sashi zubda hawaye ba Sheykh nake nufi”.
Wani irin zabura Ba’ana yayi ya nufi kansa alamun zai shaƙeshi.
Da sauri ya tsaya jin Shatu ta saki ihu tare da cewa.
“Bana so ya Ba’ana in dai kana son farin ciki na, to kada ka dakeshi ko ka cutar dashi da komai”.
Wani irin kallo ya mata mai cike da tuhuma da razana da kuma karaya,
Ita kuwa Shatu cikin rawan murya tace.
“Ya Salmanu ka tafi, bana so kaje ka bar koya min komai”.
Cikin sauƙe ajiyan zuciya na tsoro.
Salmanu ya juya ya tafi.

Shi kuwa Ba’ana, zama yayi inda Salmanu ya tashi, cikin taraddadin ko dai Shatu bata sonshi ne, ya nuna mata gefenshi.

A hankali ta zauna, shiru tayi tana sauƙe shessheƙan kuka.
Cikin ƙuna da baƙin cikin rashin sa wancan ɗan birni mai fata kamar ta jariri kukanne ya sakar mishi fargaba,
cikin sanyi yace.
“Mata!”.
Bata kalleshi ba kuma bata dena shessheƙan ba.
Kiranta ya kuma yi a karo na uku.
“Mata!”.
Cikin disashewar muryar tace.
“Na’am”.
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau a hankali yace.
“Mata bakya so nane!?”.
A bazata tambayarshi tazo mata,
ta ina kuma ta yaya zatace mishi bata sonshi, bayan tasan abin da yayi mata shekarun baya, dama fansar shi ta soshine kuma ta aureshi, da wanne bakin zatace mishi bata sonshi.
wasu zafafan hawaye masu ɗumi ta zubda.
Haƙiƙa ya Ba’ana mugune amman a iya saninta a kanta ya zama mugun, tunda sai wanda ya nuna baya sonta dashine yakewa mugunta,
Babbar matsalarshi mushirkine kuma baya salla.
Cikin rawan murya da kuka tace.
“A a Ya Ba’ana Ni bance bana sonka ba”.
Da sauri yace.
“Uhhmmm to meyasa bakya ganin laifin Salmanu akan duk abinda yake min, ko dai shi kikeso ne Mata!?”.
Da sauri ta jujjuya mishi kai sabida sanin ko jinkirin bashi amsa tayi zai iya yiwa Salmanu illa.
Cikin rawan murya tace.
“Bana son ka cutar da shine sabida, shi ya janye batun soyayyarsa gareni. Ka kuma sani karatu yake koya min amatsayinshi na wanda ya samu karantarwa a wata jami’a,
Yana sona da al’khairi kai kuma kana ƙinshi, ko dai ka manta ka ce min zaka so duk wanda yake sona da al’khairi yake kuma taimaka min”.
Jiki a mace ya gyaɗa mata kai,
sai kuma ya rumtse idanunshi da yakejin suna cikowa da hawaye yace.
“Lokuta da dama sai inga kamar bakya farin cikin ganina, a madadin farin ciki sai inga tsorona cikin ƙwayar idonki.”
Juyowa tayi gareshi da kyau cikin kuka tace.
“Ba kai ke bani tsoroba, abinda kakeyi ne yake sani tsoronka, ya Ba’ana ka bar wannan asirce-asircen babu kyau shirka ne, wanda yake ɗaya daga cikin manyan zunuban da Ubangiji ya haramtawa mumini yin tsafi haramun ne”.
Kanshi ya jingina da jikin gini yana kallonta tamkar yau ya fara ganinta,
A hankali ya fara mgna cikin muryar da bata taɓa jin rauninta a muryarsa ba yace.
“Mata ina sonki, wallahi Allah kenan rantsuwar musulmai, ina sonki, son da ni kaina bansan adadinshi ba,
Duk abinda nakeyi a kanki nefa, Shatu ki min uzuri, na roƙeki kiyi min ɗa’ar riƙe tukuicin abinda nai miki a baya,
Ki soni koda rabin yadda nake sonki ne.
Kiji tausayina Shatu ina jin tsoron kada ƙaddara ta rabamu,”.
Kekkyawar fuskarshi ta zubawa ido, tana gani. Irin kyan da Allah yayi mishi sai dai sam babu kyan hali ya zama kyan ɗan maciji.
Cikin sanyi tace.
“Ya Ba’ana tsoro kuma?”.
Kai ya gyaɗa mata cikin sanyi yace.
“Eh sabida muddin aka rabamu, zan zamewa fulani babban ƙalubale a rayuwarsa, kuma duk wanda yayi sanadin rabuwata da ke, wallahi zaiga toskun rayuwar duniya, zaiyi dana sani, zan zama mugun zahiri. Na san ke Kum bakya son hakan.
Yau kuma fargaba na, yafi na baya yawaita da wannan jikan sarki ya iya daurewa azabar bulalina baiyi ƙollaba.”
Wani irin ajiyan zuciya taja tare da cewa.
“Babu komai ya Ba’ana Ni dai ina tayi mana addu’an ALLAH yayi mana zaɓi mafi al’khairi a rayuwata, ya kuma shige min gaba a dukkan motsina”.
Ido ya zuba mata babu ko ƙebtawa, cikin sanyi yace.
“Nine mafa al’khairinki Mata”.
Da sauri tace.
“Baka saniba”.
A zafafe yace.
“Na sani mana”.
Cikin tsoro tace.
“Kai masanin gaibu ne kenan?”.
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Ehh kusan haka tunda nayi duba a kanki”.
A hankali tace.
“Wa’iyazubillah. Duba ba gsky bane, zai iya maka ƙarya”.
Hannu ya ɗaga mata da sauri kana ya nuna mata hanyar shiga gida.
A hankali ta tashi tsaye cikin sanyi tace.
“Allah ya baka haƙuri ya shiryeka”.
Ta ƙarishe mgnar tana ƙoƙarin yin kuka.
Da sauri ya juyo cikin sanyi yace.
“Kada kiyi kukan mata, nayi haƙuri.
yanzu na fasa jiran Sai kin gama karatu ayi mana aure.
Duk randa wancan malamin ya dawo ya rama gasar Shaɗinsa. Za’a ɗaura auren mu a ranar, domin
Koda duk bulalin duniyar nan zai zabgeni dasu wlh bazaici nasara a kainaba domin idona ba idon da zai zubda hawaye a kanki bane bilali ɗaya nake tsoro kuma babu wanda yasan inda suke.
In kuwa aka samu wani akasin dama bazai samuba, to zan bar ƙasar nan zan koma ƙasar Cameroon can babban birnin Yahunde, inbi cikin Rugar wasu fulanin.
Sai dai ko bana nan duk wanda ya aureki ya auri ajalinsa.”
Bata iya tanka mishiba, a haka ya juya ya tafi.

Kana ita kuma ta koma cikin gida.

A cikin masarautar Joɗa kuwa.

Sai da akayi sallan isha kafin.
Su Haroon suka dawo gida.
Suna tafe,
Abba da Lamiɗo da Galadima, da Dr Aliyu da kuma Sarkin Shaɗi.
Suna biye dasu a baya.

Kai tsaye wucewa sukayi har bedroom ɗin Jabeer har yanzu bacci yakeyi.
Sai dai tunda lokacin salla yayi yaketa jin baccin ba daɗi sai dai kuma Allah bai bashi ikon farkawa ba.
Dubashi sukayi tare da ƙara shafa mishi wasu magunguna kana suka fita suka tafi.

Hakama Gimbiya Aminatu tazo itama har ɗaki sai dai samunshi yana bacci yasa ta tafi.

Bayan fitanta ba daɗe Barrister Kamal da ɗan sa Sulaiman sukazo.
Suma har ciki suka shiga suka dubashi.
Kana suka tafi.

A ranan a daren gaba ɗaya mutanen masarautar kowa yaji lbrin abinda ya faru.

A falon su Jafar duk sukaci abinci.
Ganin dare ya tsalane yasa Juwairiyya jan hannun Jafar suka tafi.
Jalal, Jamil, Ya Hashim kuma sukayi musu saida safe kowa ya tafi side ɗin shi.

Jakadiyarsu kuwa itama ta nufi sashinta,
Ya zama dagashi sai Haroon.

Sha biyu da rabi dai-dai na dare.
Haroon zaune kan wata doguwar kujera irin ta sarakuna dake cikin ɗakin.
Waya yakeyi da Jannart,
yana konce ne dagashi sai boxes.
Waya sukeyi irin ta mosoyan da shaƙuwarsu tayi yawa,
Wani irin miƙa yayi wanda gaba ɗaya gabban jikinshi suka amsa.
Cikin tarin kasala da masifeffen shauƙi yace.
“Wash Allah na”.
Cikin kashe murya da ta ingizo Bukatarsa tace.
“Ohhh sorry Ya Haroon meya faru gaya min me yasameka”.
Cikin sakaliyar murya yace.
“Haroon yunwa yakeji”.
Sam bata fahimci inda batunshi ya dosaba haka yasa cikin haɗa fuska tace,
“Ya Haroon ka dawo gida, shi Hamma Jabeer ba matace dashi ba, bare ya kula da cikinku, na kuma san in kuna Side ɗinsa ba wani zuwa wurin Aunty Juwairiyya zakuyiba, kuma itama fama takeyi da mijinta.
Ni gsky ka dawo Tsinako nasan Umaymah zata kular min da kai da kyau, ko kuma kazo Masarautarmu Leddi julɓe, nida Sitti mu kula da kai”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Masarauta Joɗo fa masarautace mai daraja, da karrama baƙo baki san asalin tarihin inda masarautar tasamu suna Joɗa bako.
Baby kada ki damu kular da muke samu ko sarki mai mata huɗu da kwarkawara biyar baya samu.
Tako wani sashi na gidan abinci hadimai ke kawowa Side ɗin Sheykh a ƙalla wani lokacin kusan abinci kala goma muke riska, kinsan fulani ba marowata bane.
Kawai matsalar wannan yunwar rashinki ne, a kusa yasa nake jina ina tashi sama kamar doki”.
Cikin kunya da kauda zancen tace.
“Ya jikin Hamma Jabeer shugaban tuzuran ƙasar mu?”.
A hankali ya juyo kanshi ya kalli bisa makeken gadon da Jabeer ke kai.
Da sauri ya katse kiran bayan yace mata.
“Ina zuwa”.
Kan gadon ya nufa, jabeer ɗin yana ƙoƙarin tashi zaune.
Hannunshi daya miƙa zai taimaka mishi, ya buge cikin haɗe fuska yace.
“Yanzu ƙarfe nawa?”.
Wayarshi dake hannunshi ya duba cikin zuba mishi ido yace.
“Ƙarfe ɗaya dai-dai”.
Cikin tsuke fuskarsa tamkar zaiyi kuka yace.
“Shine ka barni ina bacci kamar kafurin da bashi da addini.
Anyi sallan bamgrib baka tasheniba, anyi Isha’i baka tasheniba, daga wannan masifeffen bacci mara daɗi mai cike da mafarkai marasa daɗin da nasan rashin yin salla a lokacin sane ya jazamin su.
Iya wunin yau duk so kuke kuyi min asarar lokuta masu muhimmanci da daraja, kun sani na makara la’asar da magriba hakama isha.”
Ya ƙarishe mgnar yana miƙewa tsaye,
Tare daci gaba da cewa.
“Da fari ansa ni na tsaya gaban jama’a da baiyana surata,
Aka ɗora min da duka kana, akasa na makara sallan la’asar,
Yanzu kuma mangriba da isha’inma kun barni ina baccin asara na makara, sabida baka san darajar yin salla a cikin jam’i da kuma yin ta cikin lokacin ta ba ko?”.
Cikin taɓe baki Haroon yace.
“Kasan ai ni ba musulmi bane, ban san komaiba”.
Harara ya dannawa Haroon tare da cewa.
“Kai ka gayawa kanka, Ni bana kafurta mutum, abinda na sani dai kai tsarin yahudu da nasarane,
To bari kaji, Ni bani da laifin komai sabida bacci nakeyi, mai bacci kuma al’ƙalami ya sauƙa kansa har sai ya farka.
Kai dake ganina ina bacci lokacin salla yayi idonka biyu baka tasheniba haƙƙin a kanka ya rataya.”
Ya ƙarishe mgnar yana shiga bathroom tare da cewa.
“Ka cire idonka a kaina banza mai kallo kamar mayun wancan garin mugayen”.
Murmushi Haroon yayi tare da komawa ya zauna bisa kujerar.

Shi kuwa Sheykh Jabeer wonka ya kumayi da ruwan ɗumi,
kana ya kimtsa cikin irin suturun da yake ta’ammali dasu, in yana gida.
kana ya ɗaura wata farar jallabiya kai.
Sannan ya fito bayan ya shafa mai ya fesa turare.

Yana fita ya fara ramuwar sallan daya wuceshi yana bacci.

Haroon kuwa falo ya fita abincin da yasan zai iya ci ya kawo mishin

A ƙalla awa ɗaya yayi kafin ya tashi kan sallayan
Gaban gadonshin ya dawo ya zauna bisa tattausan carpet ɗin da ke shimfiɗe a wurin mai kalar Sky blue and white.
Sosai yaji daɗin jikinshi, sai dai har yanzu yana jin raɗaɗin bulalin.
Tea kawai ya iya sha.
Kana a hankali yace wa Haroon.
“Canza min beshit ɗin nan da blanket ɗin.”
Hararanshi Haroon yayi tare da cewa.
“Zan koma, yaseen na gaji da mulkinka da sarautar da kake ji dashi. Ji yadda ka medani tamkar wani bawanka ko hadimin gidanku, kuma duk abinda zanyi maka sai ka cini gyara, mutum ba’a iya mishi sai masifa kake min kamar dai nine nace a zaneka”.
Ya ƙarishe mgnar yana miƙewa tsaye tare da gimtse dariyarshi, sabida ganin kallon da Jabeer ke mishi.
A haka dai ya sauya komai na gadon kafin suka, hau suka konta.
Tsaki Jabeer yaja tare da cewa.
“Ni dama ka tafi wancan ɗakin sabida zancen gsky kasan ni bana son takura.
Sabida zaka hanani sakewa yadda nakeso”.
Cikin gajiya Haroon yace.
“Allah babu inda zan fita inje”.
Da haka dai Haroon yayi bacci.
Shi kuwa Sheykh Jabeer karatu yayi tayi har biyu da rabi tayi kana, ya buɗe tafin hannunshi yayi addu’o’in bacci.
Falaƙi 3 Nasi 3 ƙulhuwa 3 Ayatulkursi’u 1 kana amarrasulu 1 tofa a tafin hannunshi ya shafa a jikinshi.
Kana ya kuma yi. Haka ya tofa a tafin hannunshi ya shafa a jikin Haroon Wanda tuni ya ɓingire,
Shi kuwa Jabeer wannan al’adar rayuwarsa ce daya saba, kan Jalal da Jamil sabida suma haka suke bingirewa, shikeyi tofi ya shafa musu.

Washe gari Lamiɗo baiyi zaton Jabeer zai samu fitowa masallaci ba,
Shiyasa limamin dake jansu salla in baya nan ya fito ya jasu salla,
yayinda Jabeer ke cikin sahun forko.

Wannan yasa mutane sukayi zaton ciwon ne yayi tsamari bai samu ya fitoba.
Ana idar da salla kuma ya fito yayi cikin gida sabida.
Fushi yakeyi da wannan tsohon ya sani in ya tsaya kuma zai dameshi da wata falsafarshi da zaici karo da addini.

Ƙarfe takwas dai-dai. Barrister Kamal da Ya Jafar, da kuma Baba Basiru ne zaune dashi a falon shi.

Suna zaune anan Jalal ya shigo cikin yanayin damuwa yace.
“Hamma Jabeer, Umma na falo tazo dubaka da jiki.”
Cikin yamutsa fuska yace.
“Wacece hakan?”.
Cikin fusata Baba Basiru yace.
“Ashe uwarka ma bazaka santa ba, ina dai baka san wacece Umma ba”.
Wani irin kallon ido cikin ido Sheykh yayiwa Baba Basiru,
sai kuma ya ɗora ƙafarshi ɗaya kan ɗaya, cikin ƙasaita ya kalli Jalal tare da cewa.
“Mene Umman!?”. Ya sani sarari Gimbiya Saudatu ake cewa Ummu .
Gyara tsayuwa Jalal yayi tare da gyara zaman belt ɗin ƙugunshi yace.
“Matar tsohon Galadima marigayi, Baba Muhammad ce Ummar Gimbiya Saudatu.”
Da sauri Baba Basiru yayiwa Jalal daƙuwa tare da cewa.
“Kan uwarka hegen yaro ɗan shila”.
Shi kuwa Jabeer ƙafarshi ya fara kaɗawa.
Barrister Kamal kuwa ido ya zubawa Fuskarta Jabeer da Jalal. Cikin sanyi da tausasan laffuza yace.
“Jabeer tashi muje ka gaisa da ita tunda ta taso tazo har nan dubaka da jiki”.
Kanshi ya gyaɗawa Barrister Kamal ɗin wanda suke cewa Baba Kamal wanda yake mahaifin Sulaiman, sa’an Jabeer.
Da hannu yayiwa Jalal alamun yaje yace, yana zuwa.
Shi kam Baba Basiru bayan Jalal yabi.
A babban falon suka zauna shida Gimbiya Saudatu da Laminu da kuma Baba Nasiru.

Jalal, Jamil, Haroon, Jafar, kuwa duk suna can Dinning area kan dinning table sunayin breakfast.

A jere suka fito falon shida Barrister Kamal.

Suna isowa tsakiyar falon.
Cikin wani irin taku mai cike da ƙasaita da rashin tsoro.
Ya kalli Gimbiya Saudatu dake zaune bisa kujerar zamanshi.
Yatsunshi biyu ya haɗa ya kaɗa mata tare da mata alamun tashi min kan kujera.
Cikin wani irin kallo mai nuna tsantsar fushi da tsana da zazzafan ƙiyayya ta fara mgna cikin ɗaga sauti tace.
“Hegen yaro mai idanun mujiya, Ni kakeyiwa wannan iskancin dan kan uwar..!”.
Kasa ƙarisa zagin da tayi nufin yi tayi jin yana cewa.
“Kan uwarki ko? Ki ƙara sa mana kikaga ikon wanda ya hana mata gemu ya baiwa maza!
Maza tashi min kan kujerar zama tunda ba wancan jiɓeɓɓen tsohon akun bane seyota”.

Wani irin zabura Baba Nasiru yayi tare da ɗaga hannu zai kifeshi da mari, kamar a mafarki yaji an riƙe mishi hannunshi da sauri ya juyo.
Ido ya zaro cike da mamakin ganin wanda ya riƙe mishi hannunshi cikin tafasar zuciya da ƙuna yace.
“J…..”

 

Cikin wani zare ido na masifa yace.
“Jalal ni ka riƙe wa hannu”.
Shima idon ya zare tare da cewa.
“Ba iya rikeshi kaɗai zanyi ba, in dai zai taɓa lfyar ɗan uwana a gaban idona, datseshi zanyi gaba ɗaya in wurgar”. Ya ƙarishe mgnar da ƙarfi tare da yarfa hannunshi.
Wani irin asirtaccen murmushi Barrister Kamal, yayi tare da kallon ɗan shi Sulaiman hannunshi ya dunƙule ya jinjina wa Sulaiman ɗin.
Kana suka koma suka zauna bisa kujera.
Shi kuwa Jabeer hannun ya nunawa Gimbiya Saudatu alamun ta tashi.
Mirtsitsi tayi tare da gyara zamanta.
Wani irin firgitacen tsawan da Jalal ya danna matane yasa, ta miƙe tsaye ba tare datasan ta miƙa ɗin ba.

Cikin ƙasaita Jabeer ya baza tattausar al’kyabbar jikinshi,
Kana ya matso ya zauna bisa kujerar ƙafarshi ɗaya ya ɗora bisa ɗaya.
Gyara hiramin kanshi yayi tare dayin gyaran murya kana ya kalli ƙannen mahaifin nashi kauda kanshi yayi ganin yadda suke wani irin cika da batse sun cika sunyi tamtsan da fushi.

Ita kuwa Gimbiya Saudatu zama tayi a kujerar dake kallon tashi
kujerar.
Itama ɗaura ƙafa ɗaya tayi kan ɗaya.
Cikin iya tijara ta watso sabbin jaridu gabanshi.
Jaridar bankaɗa da kuma kamfanin jaridar hantsi wato leƙa gidan kuwa.
Murmushin muguntan tayi tare da cewa.
“Ga sakamakon sa insa da kayi dani jiya, na yau kuma shima yana nan tafe.
Nayi maka murna darajar labarin ya kai matsayin da shine a shafin forko na jaridun”.
Da sauri Jalal ya sunkuyo yasa hannunshi ya ɗauki jaridar banƙaɗa.
Jiki na tsuma ya ɗago ya kalli Gimbiya Saudatu cikin tashin hankali yace.
“Wannan ƙarya ne, da babu jahilin da zai yarda dashi, wlh bazaku taɓa cin nasara ba.”
Hankali a tashe ya miƙawa Haroon jaridar tare da cewa.
“Ya Haroon gani zancen banzan da aka rubuta kan hotunan Hamma.”
Da sauri Haroon dake sauƙowa kan stpes ɗin sauƙowa falon daga dinning area,
ya ƙaraso. Hannuyasa ya amshi jaridar.
Wani irin azabebben zufane ya fara keto mishin ganin abinda aka rubuta a jikin jaridar.

Jin jikinshi na rawane ya sashi zama kusa da Sulaiman.

Ummi kuwa dake tsaye a dinning area tana haɗawa.
Jafar abin da zaici, gaba ɗaya ido ta zubo musu cikin taraddadin me aka rubuta.

Ita kuwa Gimbiya Saudatu wata iriyar shaƙiyiyar dariya tayi tare da cewa.
“Ya haka dai ƴan kanzagi, ku bawa shi uban gidan naku, jaridar yage me aka rubuta, daga nan sai inga bakinshi da baya mutuwa da bada amsa ko zai iya cewa wani abu.”
Baba Nasiru da Baba Basiru, ma fuska cike da farin ciki suka zauna.
Laminu kuwa miƙewa tsaye yayi tsakiyar faffaɗan falon cikin ɗaga sauti yace.
“To tunda bazaka iya bashi ba, bani ni in karanta mishi.”
Yana ƙarishe mgnar yasa hannunshi ya amshi jaridar.
Cikin ɗaga sauti ya fara karanta rubutun dake rubuce a ƙasan hoton da gefe da gefenshi.

“Abun kunya, ya baiyana jikan sarki Nuruddeen Bubayero ɗaga Habibullah,
Yayiwa ɗiyar Fulani fyaɗen da yasa.
Hanun Sarki Lamiɗo ya kama hannun Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero wanda yake limamin masalacin ƙofar sarki ya miƙa shi ga hukumar addini musulunci.
Gashi anayi mishi bulalin haddi kamar dai yadda Musulunci ya wajabta.

Wani irin murmushi Jabeer yayi, hannunshi yasa ya shafa tattausan gemunshi.
Cikin rashin karaya ya kalli Haroon cikin nitsuwa yace.
“Ɗan wannan abun ne kuke zaton zai kashe wannan bakin nawa da yake rayuwa da ambaton Allah!?
Shin ko kun mance tsawon shekaru da dama ana fataucin rufe bakin Ya Jafar, shima har yau baku samu nasarar hanashi ambaton Allah ba,
Duk sharrinku ya zame mushi al’khairi, tunda baya wani motsi ba tare daya kira sunan Allah ba, ikirarin ku na ya zauce, ya tabbata kune zautattun”.
Sai kuma ya ɗan kalli Gimbiya Saudatu, murmusawa yayi tare da cewa.
“Baki nafa bazai mutuba sai in nufashina ya bar jikina, batun shiga ɗakin sirri kuma, nifa wannan abin da kuketa haƙilo a kai ba wani baƙon abun bane a wurina.
sarauta a cikin jin jikina yake.”
Sai ya kuma juyo ya kalli Haroon da jikinsa yayi la’asar da lamarin su, miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Haroon wai ɗan wannan makircin nasune ya kashema jiki.
To kontar da hankalinka. Ni nan Muhammad Jabeer ƙi gudune sa gudu.
Tun kan suyi tunanin yin abu a kaina na nazarci abun.”
Juyowa yayi ya kalli Baba Nasiru cikin tsareshi da ido yace.
“Kaje duk inda ake saida jarudu ka bada farashin one million akan ko wanne jarida kaga in za’a fito maka da wannan jaridar, in bada wannan ƙwaya ɗayar kaga dai itama kuma gata a gabana.”
Cikin tarin mamaki suka zuba mishi ido.
Shi kuwa gaban Laminu ya isa cikin isa ya miƙa mishi hannunshi tare da cewa.
“Bani shi nan”.
Cikin tsananin tsoro da firgici ƙarara. Jiki na rawa Laminu ya miƙa mishi. Sabida kwarjin Jabeer ya mishi nauyi a idonshi ya kuma san artabu dashi ba daɗi.

Ita kuwa Gimbiya Saudatu wani murmushi tayi mai cike da taraddadi da al’hini da nazarin yadda zataga bayan wannan yaron mai bakin tsiya.
Jaridar gabanta ta miƙa mishi.
Kanshi ya girgiza tare da kaɗa mata yatsarshi manuniya cikin rashin tsoro da ƙasaita yace.
“Ba kifa kai matsayin da zaki nuna min wani abin da idanuna basu rigaya sun ganiba ko basu san dashiba domin ke a makance kike rayuwarki, Ni kuwa nan da kike gani idona buɗe suke ras.
Ita wannan itace tayi bayanin abinda ya faru na gsky a Rugar itace tai bayanin cewa bulalin shaɗi akayi min bana Haddiba to sai me kuma!?”.
Shiru sukayi gaba ɗayansu.
Kowa da abinda yake nazarta a ranshi sai bugawar da zuciyoyinsu keyi.
Buɗa al’kyabbar jikinshi yayi tare da kuma haɗe ta cikin fillanci yace.
“In kun gama ihun ku ficemin daga Side ɗina Dan ba haɗamu akayi ba. Kuma ku sani (MOH ALLAH WUJI FURƊATA).”
Yana faɗin haka ya juya ya nufi falonshi.

Ita kam Gimbiya Saudatu ta cika tayi maƙil.
Baba Nasiru da Baba Basiru kuwa,
A kufule suma suka fita.
Haroon kuwa ido ya zuba musu.
Barrister Kamal kuwa murmushi yayi mai tarin ma’anoni kana shima ya fita Sulaiman na biye dashi.

A hanyarsu ta komawa side ɗinsu ne, Gimbiya Saudatu ta kalli Laminu cikin takaici tace
“Banza kawai me tsoron zuci me dan ya matso kusa dakaii ka wani firgita ka razana har ɓari jikinka keyi ka miƙa mishi jaridar, da zamu iya kaita a tallata”.
Wani irin wawan ajiyan zuciya Laminu yayi tare da cewa.
“Uhummmm Umma kenan wato, fa duk wannan kumfar bakin da kikeyi abinda yasa kike yinta da jin daɗin yinta, dan wancan Jabeer ɗin bai taɓa kifa miki bari bane shiyasa.
Wallahi Allah da ya taɓa marinki da waɗannan hannayenshi da kike ganin taushinsu kamar na jarirai shakka babu, wlh suma zakiyi sai an yayyafa miki ruwa”.
Cikin kufula Baba Basiru yace.
“Kai tafi daga nan banza mai zuciyar mata, ji abinda kake cewa kan mari ɗaya tak daya taɓa yi maka”.
Wani irin kallo Laminu yayi musu kab lokacin da suka shiga falon Gimbiya Saudatu.
Cikin rumtse idonshi sabida tuno marin da Jabeer ya kifa mishi randa yayi gangancin zai zageshi.
Da sauri ya buɗe idanunshi cikin kara yace.
“Yesss sabida baku ya shararawa mari ɗayanba shiyasa.
Kuna sanefa mari ɗayan da yayi min. A take kunnena ya rinƙa zubda jinin da Ni dai har yau bansan ta inda ya ɓulɓuloba, wlh Allah lokacin daya mareni kusan suma nayi, har yau in na tuno marin sai inji kunnena yayi gummmmm”.
Cikin zafi Gimbiya Saudatu ta yunƙuro zata surfawa ɗan nata masifa, sai ta kuma komawa ta zauna jin Baba Nasiru na cewa.
“Uhummm Dafa gskyar Laminu, in dai Jabeer ya ɗauki hannun mahaifinshi to tabbas, suna da zafin hannu mai ban tsoro,
In dai ya gado hannun Ya Habibullah to fa duk abinda suka mara wlh in dai dabbace sai dai a matso mata da wuƙa, in kuwa mutum ne to, tabbas zai sha azaba mai raraɗi.
In jifa ne ma sukayi ma basa saɓawa saiti sai sun samu abin harinsu, in kuma tsuntsune ko ƙananan halittu tofa in suka harba sai lahira.”
Sai kuma ya ɗan tsaya ya kallesu cikin dakiya yace.
“Munada buƙatar sabon shiri, akanshi, zamuyi mgnin bakinshin nan da baya mutuwa”.
Cikin takaici Gimbiya Saudatu tace.
“A duk cikin ababen da ake dangantawa dasu babu, abinda yafi cimin rai kamar meda, zoo ɗin masarautar sade ɗin Jabeer.
Wlh duk sanda najiyo kukan Ɗawisun Masarautar da sauran tsuntsaye nakiji kamar in je in samisu shinkafar tsuntsaye suci su mace kab ɗinsu kowa ma ya huta.”
Barrister Kamal dne dake,
Jinsu ta window ɗin falon.
Ya jinjina kai tare da jan hannun Sulaiman suka tafi yana mai cewa.
“Uhum naku burin dai baza taɓa cikaba in sha Allah”.
Su kuwa nan sukaci gaba da tattaunawa yadda shirunsu a kanshi zai kaya.

Jakadiyarsu kuwa saida taga fitansu ta sauƙe ajiyan zuciya.
Jafar kuwa saida yaga Barrister Kamal ya fita kafin jikinsa ya dena rawa da karkarwa.

Shi kuwa Haroon da sauri yabi bayan Jabeer cikin sauƙe nannauyan numfashi yace.
“Wato kai bakinka bazai mutu bako.”
Cikin kufula ya juyo ya kalli Haroon jin ya yace mishi irin
Abinda kullum Abba yake cemishi.
A hatsale yace.
“Eh bakina bazai mutuba ba kuma zan bar ko wanne taƙadirinba, duk wanda yace dani tak zai samu amsa dai-dai da zancensa.
Wannan zarerriyar matarfa ta kiyayeni, kadafa ta fusatani, tam!”.
Ya ƙarishe mgnar da taune lips ɗinshi.
Cikin sanyi Haroon yace.
“Nifa tsorona ɗaya Jabeer kada su cutar da kai, so dan Allah duk abinda zasuyi maka kosu Jalal da ya Jafar kada ka tanka musu.
Yanzu wannan sharrin ya zamuyi dashi?”.
Wani irin kallo yayiwa Haroon cikin sauƙe numfashin yace.
“Tuni na magance ta, na saye jaridun, tun kafin a fiddasu, shima dan ya ɗauka ne tun kafin inji inje wurin.
Kuma gashi shima a hannun yanzu sai dai su nemo wani sharrin. Kuma batun basu amsa, da sun gane sun dena sako Mahaifiyata a duk abinda zasuyi min da Ni dai ko kallo basu isheni ba.”
Cikin sauƙe numfashin Haroon yace.
“To Alhamdulillah Allah ya kare gaba”.
Amin yace tare da zama bisa kujerarshi ta musamman wacce take kyautace ga Sheikh Abdulkarim. Tab ɗin shi ya ɗauka ya fara wasu yan dube-duben.

Anan falonshi suka zauna, shida Haroon.
Jin muryar Gimbiya Aminatu na ratso falon ne yasa Haroon yin murmushi cikin sabo da tsohuwar yace.
“Yauwa Gimbiyar Lamiɗo kizo kiyiwa wannan jikan naki faɗa”.
Murmushi tayi mai ƙayatarwa,
a hankali ta ƙara so cikin falon ita ɗaya hadimanta suka tsaya a can babban falo da abincin data kawo mishi.
A hankali tayi taku zuwa gabanshi gefenshi ta zauna,
cikin sanyi ya kalleta.
Ita kuwa cikin kulawa tace.
“Jabeer, ya jikin naka”.
Cikin harshen fillanci yace.
“Da sauƙi”.
Yadda ya bata amsa a taƙaicene yasa ta kalli Haroon tace.
“Yaci wani abu kuwa?”.
Da sauri yace mata ehh.
Cikin kula tace.
“Me yaci!?.”
Murmushi yayi cikin tsokana yace.
“To da sanyin safiyar nan dai an sanshi magantuwa”.
Dariya ta ɗan yi tare da cewa.
“Taso kuzo kaci abinci”.
Kanshi ya girgiza mata tare da cewa.
“Bana buƙatar komai, kawai ki gayawa wannan dottijon mijin naki da sufanshi baya gaya mishi dai-dai ya gargaɗi Gimbiya Saudatu ta dena zuwa min side ɗina.
In kuwa taƙi wata ran zan bar Jalal yayi mata ɗan karen duka”.
Murmushi tayi tare da cewa
“To naji taso muje kaci wani abun”.
Dai-dai lokacin Lamiɗo da Galadima suka shigo.
Ɗanzagi da dogari kuma suka tsaya a can bakin ƙofar shigowa falon.

Bayan sun zauna ne Lamiɗo yace.
“Ya ƙarfin jikin?”.
Rai a ɓace yace.
“Ai baka da case da raina da lfyata, ko in samu sauƙi ko kada in samu ba matsalarka bace, tun da gani kake iyayena sun haifa maka nine dan ka bawa wasu ƙattin daji su dakani”.
Murmushi Lamiɗo yayi cikin tsokana yace.
“To wai in ban basu kaiba wa kake son in basu?”.
A hatsale yace.
“Ka basu kanka mana, me zai hana kai ka tuɓe gwanjinka a zaneka, dan masifar rainin wayo sai ka nunani, duk da tarin jikokinka da suke wurin.”
Murmushi Galadima yayi tare da cewa.
“Yanzu dai jikin da sauƙi gashi, har zanar ta maidaka mataɗaci, ka fara shiri nan bada dadewa ba za mu koma ka rama”.
Da sauri ya ɗago kanshi daga kallon Tab ɗinshi ya zuba musu tare da nuna kanshi.
Ido suka zuba mishi. Shi kuwa cikin tsuke fuskarsa tamkar zaiyi ruwan jini yace.
“Ni! Ni!! Ni!!! Muhammad Jabeer Kuma a wancan garin, me zanje inyi a can, wannan garin ko a mafarki bana fatan Allah ya gwada minshi, dan Wallahi Allah kenan duk duniya babu garin da na tsana sama da wannan garin.
Na tsani garin bana ko son jin makamacin sunan garin. Da garin da mutanen garin gaba ɗaya basa cikin jadawalin jerin mutanen da zuciyata zata sosu har gaban abadan me na samu a wannan garin banda tozarci da ɓaƙar azaba.”
Murmushi Lamido yayi kana cikin son jikan nashi ya dafa kafaɗarshi tare da cewa.
“A makon-nan ma kuwa zaka koma wannan garin da izinin Allah”.
Mgnar Lamiɗo ta ƙarshe da yace da izinin Allah ne yasashi yin shiru.
Haka suka ƙaraci mgnarsu bai kuma ɗago kanshi ya kallesu bama bare ya kulasu.

Bayan sun tafine.
Ummi da Gimbiya Aminatu suka samu suka sashi ya ɗanci abinci.

Zuwa azahar kuwa sai ga Sarkin Musulmi Jalaluddin da Sitti.

A sashin Gimbiya Aminatu Sitti ta sauƙa shi kuwa Jalaluddin a sashin amininshi Lamiɗo ya sauƙa.
Saida akayi sallan la’asar kafin suka isa sashin, Jabeer.
Sosai suka nuna mishi kulawa da gata,
Inda yaketa son huce haushin da yakeji a kansu tunda sune dai suka sashi yin wannan abun a bisa dole.
Hajia Mama kuwa daɗi kamar ta goya Sittin dan kulawa da so.

Sai washe gari. Suka koma Laddi julɓe sunan jihar da nanne asalin tushen masarautar sarkin Musulmai yake.

Mama kam hankalinta ya konta ganin jikin Jabeer yayi sauƙin sosai.

Batul kuwa babu nacin da batayiba ta samu ta ganshi ido da ido abin yaci tura.

A haka kwanaki sukayi ta tafiya, ana bawa Jabeer kula tamusamman.

Yayinda Sarkin Shaɗi kuwa yake ta tsuma bilalin Shaɗin masarautar Joɗa wanda a ƙalla tsawon kusan shekaru ɗari biyu da wani abu. Suna binne cikin ramin tsuminsu
Wanda da dafin macijin gadin masarautar ake tsumashi.

Umaymah kuwa tana shirin zuwa duba jikin ɗan ƴar uwar tata ɗa mafi soyuwa a gareta sama da ƴaƴan data haifa a cikinta ma.

Yau kwana biyar da faruwan abun.
Sosai jikinshi yayi ras.

Yaune kuma Umaymah ke tahowa jirgin yamma zata biyo.

Shi kuwa Jabeer zuwa yanzu ko mgnar kowarshi wannan garin ba’ayi sabida irin ɓacin rai da yake baiyana a fuskar shi, in an mishi mgnar zuwa garin.

Allah ya sani yana jin ya tsani wannan gari tsana mai tsanani.
Yana masifar jin kunyar komawa na wannan garin da a tsakiyarshi akashi cire suturarshi ya zauna dagashi sai boxes.

Yakanji kamar ya faɗi ya mutu in ya tuna garin.

Ƙarfe biyar dai-dai motocin da suka ɗauko Umaymah suka iso cikin harabar masarautar.

Dai-dai lokacin kuma Hajia Mama da Batul suna gab da shiga sashin Jabeer,
A tsakiyar falon sukayi kiciɓis dashi. Yana sanye cikin tufafin da sune suturarshi, al’kyabbar ruwan madarace, sai kayan dake cikin al’kyabbar su kuwa ruwan bonbitane, yayi wani irin masifar kyau, sai ƙamshi yake bazawa tako ina.
Fuskarshi ta fito ras cikin hiraminshi ruwan madara,
Wani irin ƙyalli da sheƙin kyau yakeyi.
Duk da ba murmushi a kan fuskarsa amman ana iya gano tsantsar farin cikin da yake ciki.
A hankali yake taku, Ya Jafar na biye dashi a baya,
Cikin tarin kula da nuna soyayyarsa Hajia Mama tace.
“Masha Allah, Ɗan Umaymah yayi kyau, ga farin ciki ya wadaci kekyawan fuskarnan taka”.
Kanshi ya ɗan kauda ya kalli Ya Jafar daketa jan hannunshi su fita, cikin nitsuwa yace.
“Sun isoma”.
Cikin jin daɗi tace.
“Eh haka dai Jamil ya gaya min”.
Ta ƙarishe mgnar tana juya baya tare da Batul da cikin sanyi tace.
“Ya Jabeer ya jikin?”.
Cikin jan gajeren tsaki yace.
“Lfyata lau”.
Murmushi tayi sabida jin zazzaƙar muryar shi.

A tare suka fito su Mama na gaba shida Jafar suna baya.

Suna fitowa harabar Side ɗin shi.
Motarshi da Sheykh Abdulkareem yasa aka taho mishi da ita wacce bai taɓa hawantaba, asalima gani yake tamkar almozzaranci ne,
sai yau ya bawa Haroon key ɗin ta yace a ɗauko mishi Umaymahnshi, shi bazai je ɗaukotaba sabida.
Lamiɗo yace bazai fitaba.
A hankali ya tsaya ganin hancin motarshi ƙirar Mercendes benz maybach Exelero wacce ta kai kimanin $8 million dollars.

Da sauri ya ƙarasa jikin motor. Hajia Mama na biye dashi.
Yana isa inda suke yasa tattausan hannunshi ya buɗe marfin motar.
Karo na forko da naga murmushi a fuskarshi, cikin tarin shaƙuwa da kulawa yace.
“Marhababuki ya Umaymah, ta faddal”.
Wani irin murmushi Umaymah tayi cikin tsantsar so tasa hannu ta kamo hannunshi daya nuna mata alamun ta fito.
Wani irin yalwataccen murmushi mai nuna tsantsar jin daɗi ya kumayi lokacin da yaji tasa hannunta tsakiyar kanshi.
Da sauri ya rusuna a bakin motar cikin sanyi ya manna kanshi da guiwowinta dake zuro woje,
kanshi ta shafa tare da cewa.
“Allah yayi maka al’barka ya kare mana kai da kariyarsa mai tarin yawa ya iya maka abinda idonka baya gani”.
Amin Amin, su Haroon da Jalal, Jamil, Hibba, ƙanwar Haroon, da kuma Imran, Sulaiman, Aunty Juwairiyya dake kusa da Umaymah.
suka amsa tare da murmushi a fuskokinsu.
Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya tashi kana ya buta hanya ta fito.
Tana fitowa Hajia Mama ta ƙara so gareta cikin tarin baiyana jin daɗi ta ruggume Umaymah tare da cewa.
“Ta ɗanki kawai kikeyi, mu har mun kusa mu bushe a tsaye”.
Murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
“Afwan ya Aunty kin san in Jabeer na yana wuri bana ji da ganin kowa sai shi”.
Haroon ne ya taɓe baki tare da cewa.
“Uhumm ai mun saba ganin wariyar launin fata”.
Hannunta tasa ta ɗan zunguri Haroon tare da cewa.
“Kishi”.
Jamil ne ya ɗan kallesu lokacin da suka ɗunguma suka nufi Sade ɗin Jabeer cikin tura baki yace.
“Allah ko Mama kada ki bari Umaymah ta sauƙa a sade ɗin Hamma in dai ba sade ɗinmu zata sauƙaba Muda muke ƙanana sai ta sharemu saishi.
Tunda hakane ta sauƙa side ɗinkin”.
Cikin dariya Umaymah ta juyo da sauri ta kalleshi tare da cewa.
“To Jamil harda kai, wato kaima ɗan team ɗin Haroon ne ko?
To sha kuriminka Aunty bazata shiga tsakanin uwa da ɗaba, ko Hajia Mama?”.
Ta ƙarishe mgnar tana kallon Hajia Mama daketa murmushi cikin jin daɗin tace.
“Haka kuma ɗa bazai shiga tsakanin ya da ƙanwaba,
Gaba ɗaya Jabeer ya kwace mana ke”.
Murmushi mai kama da dariya sukayi gaba ɗayansu lokacin da suka shiga cikin falon.

Shi dai Jabeer sai murmushi yakeyi.
Ya Jafar kuwa in yaga Jabeer na murmushi sai shima ya ɗanyi murmushi.
Aunty Juwairiyya ce ta ɗan kalli Batul dake gaida Umaymah sakin fuska tace.
“Matar ƙani yau tun safe ban jikiba”.
Wani irin murmushin jin daɗi tayi Allah yasani in Aunty Juwairiyya tace mata matar ƙani tana jin daɗi.
Cikin happy tace.
“Yau a kitchen na wuni inayiwa Umaymah girkinsu na larabawa”.
Murmushi Juwairiyya tayi tare da cewa.
“Yo ai na rigaki, dama girkin bare bari kikayi mata”.
Kanta ta ɗan juya takalli Sheykh Jabeer dake zaune kusa da Umaymah, in zaiyi mata mgna sai ya juya harce zuwa larabci.
A ranta take addu’o’in Allah ya nuna mata ranar da zata zauna kusa dashi haka a matsayin abar sonshi.
Tattausan Lips ɗin shi masu kama da kunnen fure ta kalla.
sunan jazir sai sheƙi sukeyi a cikin tattausan sajenshi da gemun tamkar an shafa musu mai.
Allah ya sani randa ta samu lips ɗin nan a matsayin mallakinta, tabbas sai ta kusan haɗiyesu.

Hajia Mama da kanta da ita da Aunty Juwairiyya ne suka rinƙa kawowa Umaymah abubuwan motsa baki yaran yar uwarta na zagaye da ita, Hibba ce yar autarta ta ƴar kimanin shekaru 16 kalli Jabeer cikin cikin sanyi tace.
“Hamma Jabeer Aunty Jazrah tace in gausheka, wai yaushe zamuje”.
Kanshi ya juyo ya ɗan kalli Hibba cikin son yarinyar yace.
“Hibba auta yaushe kikeso muje”.
Da sauri tace, sai na tambayi Aunty Jazrah”.
Murmushi yayi kana ya kalli Aunty Juwairiyya yace.
“A shigar mata da kayanta, a ƙara gyara mata masauƙinta, yafi fadar Jalaluddin kyau”.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Shi kuwa Sheykh Jabeer kamar ba shi yayi mgmar ba.
Ita kuwa Umaymah da Hajia Mama hararanshi suka ɗanyi tare da cewa.
“Ai babu fadar da zatafi fadar shi kam, shinefa gatanka”.
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
“A a kam Allah ne gatana, shi kuma da yake son ayi ta ɗimata”.
Juwairiyya kanta tayi mamakin sakewar Jabeer sosai
Duk wanda ya ganshi zaiga tarin farin ciki tare dashi.

Nan dai suka zauna akayi ta hira.

Saida aka kira magriba ne, duk suka miƙe sukaje sukayi al’wala.

Batul kuwa tafi kowa farin cikin, zuwan Umaymah ko ba komai ta samu ganin Jabeer yadda take so.

Bayan an idar da sallan isha’i ne suka dawo masalacin.
A nan bisa dinnin area. Suka zauna nan sukaci abinci.

Koda suka gama ne, sunata hira a falon harda Jakadiyarsu.
Jabeer ne da yanzu ya fito falonshi cikin nitsuwa yace.
“Kai dan Allah ku barta ta huta mana”.
Sai ya kuma ɗan kalli Umaymah tare da cewa.
“Umaymah muje ki gaisa da Lamiɗo, ya kirani yanzu yanata min ihu a kunne wai yaji kin iso tunda yamma kuma ban kai mishi keba”.
Da sauri ta miƙe tare da cewa.
“To muje”.
Hibba ce ta tashi da nufin binsu sai kuma ta zauna, jin Jabeer nace mata.
“Zauna Hibba saida safe kuje da Jalal.”
Sai ya kuma kalli Jakadiyarsu cikin taushin murya yace.
“Ummi muje”.
Itama da sauri ta miƙa.

A tare suka fito yana gaba Umaymah na binshi,
Jakadiyarsu na bayansu.
Suna tafe cikin jin daɗi ko ina yayi lib sai sanyin korayen ciyawi da furannin da dogayen bishiyoyin gwanda da ayaba da sukayiwa ko ina ƙawanya.

Suna isa ƙofar Gimbiya Aminatu da sauri.
Sallama ya basu hanya, wanda a ƙa’ida sai ya shiga ya nemawa mutun izinin shiga kafin ka shigo.
So amman Jabeer baida hijabi da sashin kakanin nashi,
shiyasa kai tsaye suka wuce.
Shiru babban falon babu kowa.
Haka yasa suka wuce sashin Lamiɗo, a hankali yayi sallama,
Cikin murmushin Lamiɗo ya amsa sallamar tare da cewa.
“Bismillah, ku shigo”.
Kusan a tare suka kutsa kai cikin tamfatsen falon nashi.

Wani irin kallo sukayiwa juna,
Ganin…!

 

 

No comments