Breaking News

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 7

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

 

_The Prisoners E7_

*Daga alƙalamin Boss Bature*


~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

 

“ka na nufin ba su mutu ba suna a raye”? A Æ™agare ta jefa mashi tambayar, jinjina mata kai yai ba tare da ya furta mata kalma ba, bugun zuciyarta ne ya qaru a sukwane ta juya baya don ta samu damar Æ™are masu kallo, bargunan da ya lullu6e su da shi ya hana ta gan su da kyau, jikinta na 6ari ta Æ™ara sa gaban su ta zuÆ™unna tare da kai hannu ta É—age saman bargon, duk wani motsin ta akan idon Danish.

Wani irin farin ciki ne Ya lullu6eta haÆ™iÆ™a ta yi al’ajabin wannan iko na Allah, kamar zautacciya haka ta dinga É—aura kanta saman Æ™irjinsu haÉ—i da jogana kunnanta saitin zuciyar su don ta ji idan tana bugawa, daga kan Jamimah ta fara tana É—osa kunnanta bugun zuciyar jemimah ya daki dodon kunnan, nan ta ke ta fahimci cewa bacci su ke yi, Tambayoyi ta shiga jefawa kanta, Ta ya ya akai haka ta faru? Dama wanda ya mutu yana tashi? don ita dai a iya saninta idan an mutun ba adawowa, É—aura kunnanta ta yi saman Æ™irjin Azeeza lumshe idanuwanta ta yi wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, jin bugun zuciyar azeeza na har6awa, matsawa ta yi gaban Parveen tunkan ta É—aura kanta saman Æ™irjinta idanuwanta su ka sauka akan Æ™aramin bakinta ganin yana motsi yasa ta fahimci tana araye, Lamarin yai matuÆ™ar É—aure mata kai, ta ya akai su ka rayu! Kuma Danish da kanshi ya tabbatar masu cewa Heart attack ne yai silar mutuwarsu, duk da bata da Æ™oshin lafiya hakan bai hana smart brain É—inta aiki ba, Zurfin tunani ta shiga idan har su Jemaimah su ka iya jure abunda ya faru dasu ya kenan ta 6angaren Sauran Æ´an uwansu da su ka baro? Waro idanuwanta waje ta yi yayin da zuciyarta ka harbawa da sauri da sauri, a fujajen ta zabura ta miÆ™e kamar an zungure ta, ta juya ta nufi Danish dake a zaune Ya É—an lumshe idanuwanshi, Æ™oÆ™ari ya ke ya hana kanshi yin bacci gudun kada yaja masu matsala, zuÆ™unnawa tai agabanshi

“Danish taya akai su Jamima su ka rayu? Bayan kai da kanka ne ka faÉ—a mana cewa zuciyarsu ce ta buga” ware idanuwanshi yai akan fuskarta, tsananin tausayinta ne ya kama shi, damuwarta akan Æ´an uwanta, bata damu da kanta ba, Æ™arantar shekarunta yafi komai É—aure mashi kai, yadda harta iya jure waÉ—annan wahalhalun rayuwar wanda yayi imanin ko wani babban ba zai Iya jurarsu ba.

“Danish bana so ina magana kana share ni, ka faÉ—a min ta ya ya akai su ka rayu? A iya sanina idan mutun ya mutu baya tashi, Sai gashi su Azeeza sun tashi, ko dai ka yi amfani da sihirinka ne wurin dawo masu da rayuwarsu…”? A ruÉ—e tai maganar babu kwanciyar hankali atattare da ita, a hankali ya É—an motsa la66ansa.

“My Angel, u should stop talking about them, ba ki da lafiya u need a rest,” damÆ™ar wuyar best É—in jikin tai sosai ta fashe mashi da kuka tana faÉ—in”Danish ka faÉ—a min dama kasan suna araye shi ne ba ka bari mun goyo su Deeja mun taho da su ba? Me yasa ka yi mana Æ™aryar cewa zuciyarsu ce ta buga”? Tana magana tana ku ka, raunin gefen bakin ta tuni ya fara tsastsafo da jini.

Ranta yai mugun 6aci zuciyarta ta harzuÆ™a, A haukace ta miÆ™e tana faÉ—in”Zan koma na taho da su Deeeja, ban damu da in rasa raina ba,” a hanzarce ya miÆ™e jin abunda tace, ido cikin ido su ke kallon juna”Am sorry Angel i don’t mean to hurt u, kinsan bana Æ™arya, sannan bani da amsar da zan baki that’s why nayi shiru, hatta su Azeeza ban san suna araye ba, a daren jiya na yi Æ™oÆ™arin binne su cos bana son ku farka ku taras da gawawwakinsu, hakan zai fama ma ku ciwon da ke a cikin zuciyarku, nayi amfani da sihirina wurin tsaga Æ™asa har na fara sanyasu a ciki idona ya sauka akan yatsun Æ™afafuwansu dake motsi, i was shocked cos ban yi expecting din zasu rayu ba, kin ji yadda akai nasan suna a raye”

kamar ta so ta fahimce shi sai dai wani sashe na zuciyarta yaÆ™i aminta dashi, girgiza mashi kai tai”Ni dai zan koma kurkuku in É—auko su Deeja, Saboda ina ji araina cewa Suna araye”

Ya fahimci damuwace ke ƙoƙarin zautar da ita, Zaiyi wuya ta fahince shi, yasan halin kayansa da rigima ga kafiya da taurin kai, juyawa ta yi tare da nufar ƙofar fita daga kogon dutsen, da sauri Ya bi bayanta tare da ruƙo arm ɗinta ya janyota zuwa jikinshi, sosai ya matseta.

“Angel daji ne fa, ba mu a kusa da kurkukun Æ™addara, ta zarar awanni ce, A daren Jiya bayan mun fita ni ne na É—auko ku na dawo da ku nan duk don na sauÆ™aÆ™a maku wahala” daÆ™yar ya ke magana, damuwace Æ™arara akan fuskarsa, Æ™oÆ™arin raba Jikinta tayi daga nashi.

Zuciyarta ce ke azalzalarta sam bata fahimtar kalamansa, idanuwanta sun makance

“Ka sake ni Danish, nasan ko nace kaje ka É—auko min su Deeja ba za ka je ba, don haka ni zanje, saboda ina ji araina Æ´an uwana suna araye basu mutu ba gashi mun baro su a hannun Azzaluman mutanancan…..” cikin shessheÆ™ar kuka ta Æ™arasa maganar, duk yadda yaso ya hanata tafiya taÆ™iya, har kwatanta mata haÉ—arin da dajin gare shi amma ta kafe akan sai taje, sakinta yai idon shi akan bayanta, sam babu kuzari a jikinta ahaka ta fuce daga cikin kogon dutsen, Hasken ranane ya galle mata idonta da sauri ta lumshe su na É—an sakanni kafin ta ware su tana Æ™arewa Æ™urmin Dajin kallo, DaddaÉ—ar iskar dajin ce ta ratsa sassan jikinta ni’imtacciyar gaske, hatta sumar kanta sai kaÉ—awa take yi saboda Æ™arfin iskar, saboda taurin kai irin na Angel da kasada, Ahaka ta soma tafiya tana nufar cikin dajin ita ala dole saita gano inda kurkukun Æ™addara ya ke, tun kan aje ko’ina ta fara tsorata da ganin Æ™ananun halittun da ke yawo Saman bishiyoyi, duk da haka bata sare ba taci gaba da tafiya hada É—an saurinta da gudunta, ko takalma babu a Æ™afarta.

Tun bayan fitarta Danish Ya fito daga cikin kogon dutsen, ya goya hannayenshi saman faffaɗan ƙirjinshi Yana kallon bayanta, Ta yi matuƙar bashi mamaki, duk da ya fahimci babu hankali atattare da ita, in ba haka ba ta ya ya wanda ya tsira yake ƙoƙarin komawa ga halaka. Yarinta ce ke damunta da kuma son ƴan uwanta.

Tana cikin yin tafiyar nan, kukan namun dawa Ya dakatar da ita cak ta tsaya tana ƙarewa wurin da take atsaye kallo, ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Snake ɗin dake bin jikin bishiya yana ƙoƙarin saukowa ƙasa, zaro ido waje tai a gigice ta fasa ƙara tare da juyawa da gudun gaske tamkar zata tashi sama, majicin na ƙarasa saukowa yabi bayanta, tashin hankali duk ta bi ta rikice don ta fahimci ita yake bi, tun da uwarta ta haife ta bata ta6a yin tozali da maciji ido da ido ba sai yau da Allah ya haɗosu, Tarasa gane ta wace hanya zata bi ta koma cikin kogon dutsen.

Danish ta dinga Æ™walawa kira kamar maÆ™oshinta zai 6allo, sai da ta gama galabaita cikin rashin sa’a tai tuntu6e da dutse gaba É—aya ta tafi zata kife Æ™asa, Æ™iris ya rage ta kife Æ™asa a lokacin da ba ta yi tsammani ba taji Ya damÆ™o ta tare da kwantar da ita saman chest É—insa.

ƙanƙameshi tayi sosai ta fashe mashi da kuka tana zazzaga mashi masifa akan me zai barta ita kaɗai acikin daji? Idan ma don saboda ta yi mashi kafiya ne, bai ga ita yarinya bace, tun da fara mashi faɗa bai tanka mata ba, hannayen shi biyu suna tallabe da ita, sai da ta yi mai isarta, tukunna ta buɗe kumburarrun idanuwanta akan fuskarshi, tun daga kan tausasan red lips ɗinsa ta soma bi da kallo har izuwa ga dogon hancin sa kafin ta ɗauke idon nata ta ɗaura su kan sexy eyes ɗinshi masu matuƙar jan hankali.

Æ™oÆ™arin shagala su ke yi da kallon Juna, tunawa da Æ´an uwansu da su ka baro a kogon dutse ne yasa tayi saurin katse masu kallon Æ™urullan da suke bin juna dashi”Danish mu koma kada wani abu ya same su” girgiza mata kai yai in a smoky voice ya furta mata”ba abunda zai same su, ina sane dasu, na rufe kogon dutsen babu wani abun cutarwa da zai Iya tunkarar su”Sam hankalin bai kwanta da kalaman shi ba

“Danish ni dai mu koma,” ashagwa6e tayi mashi maganar, ita kanta batasan ta sanya shagwa6a ba’

“Zamu koma, but before that, Inaso ki raka ni cikin Dajin in nemo mana abunda zamu ci, ko kina so su farka suna Jin yunwa ne”?

Girgiza mashi kai tayi”a’a amma ni ba zan bi ka ba, Ka maida ni cikin kogon dutsen in ya so kai sai ka je nema mana abunda zamuci” kafe ta da ido yai, hakan yasa ta jefa mashi harara haÉ—i da murguÉ—a mashi baki, munin fuskarta bai hana shi ganin kyanta ba, musamman da ta yi mashi abunda ke jan hankalin shi gareta, Harara da murguÉ—e abun A jinin ta ya ke.

“Idan ba za ki bi ni ba, Ga hanya nan ki koma kogon dutsen ni kin ga tafiyana” yai maganar tare da nufar Cikin dajin, da ido tabi bayanshi da kallo, ranta a 6ace yasan ba zata iya kai kanta ba shiyasa yace ta koma, Tunawa da macijin da ya biyota ne yasa ta zabura da gudu tabi bayanshi, Yana cikin tafiya yaji ta zura hannunta cikin nashi, Æ™ayataccen murmushine ya bayyana akan fuskarshi.

Ta yi tsammanin Iya abincin da zasu ci ne zasu nemo, ba ta san plan Ya shirya mata ba, Yanayin Iskar dajin ba Æ™aramin ni’ima ta saukar masu ba, Suna tafiya suna kallon Juna, wani irin Sanyi ne ke ratsa zukatan su, dakatawa tai dayin tafiyar ta É—an kalli fuskarshi”Na gaji Danish Æ™afata ciwo ta ke yi min” ba tare da ya amsa mata ba, ya juya mata bayan shi, ta gane me yake nufi, da sauri ta haye Saman bayan Ya miÆ™e É—auke da ita, ba Æ™aramin daÉ—i taji ba, shin me yafi ranta gata ga garkuwar kurkuku, ta Æ™anÆ™ameshi sosai, lumshe idanuwanta tayi sai faman shaÆ™ar mashi fatar wuyan shi take yi, bai sauke ta a ko’ina ba sai abakin wani tabkeken ruwa mai gudana, Ta jikin dutse ruwan ya ke gangarowa tsaftatacce fari Æ™al dashi.

“Mun Æ™araso,” Jin abunda yace ne yasa ta É—ago da kanta, tana Æ™arewa wurin kallo, nan ta ke ta ji tana sha’awar shan ruwan, ZuÆ™unnawa yai ta sauko daga saman bayan nashi, a jere suka tsaya suna bin ruwan da kallo, ga dukkan alamu ya burgesu .

“Danish Æ™ishi na ke ji, nasan kaima kana ji, mu sha sai mu É—ebi wani mu kai ma su Parveen ko”? Ba tare da ya juyo ya kalli fuskarta ba ya soma magana”Wanka nake so nayi maki, saboda kinyi muni, jikin ki yayi datti”

Har saida gabanta ya faÉ—i jin abunda yace, juyowa yai da fuskarshi ya kalleta tare da kashe mata ido É—aya

“za ki iya cire kayan ko in taimaka maki ne”? gabanta ne ya dinga faÉ—uwa sai ta ga kamar ya canza mata, babu alamun wasa akan fuskar shi yai maganar.

Ganin yana matsowa kusa da ita, yasa ta juya da niyar ta gudu, ko ta ku ɗaya bata kai ga yi ba taji Ya damƙi ƙugunta, ƙarfi ba ɗaya ba, Duk yadda taso ta kubce mashi ta kasa, matseta yai a ƙirjin shi, A hankali Yai amfani da hannun shi ɗaya wurin zame rigar Jikin shi, tare da wandon kakinsa na Giant, ya rage daga shi sai short fari, saman gungurumeman dutsen dake agefen ruwan, ya jefar da uniform ɗinshi.

kamar jinjira haka ya ɗauke ta, kaitsaye Ya nufi Cikin ruwan da ke gangarowa, ba yadda ta iya dashi, Tana kuka tana fadin bataso ya ƙyale ya rabu da ita, ahaka yayi mata wanka tass ya wanketa Kamar yayi amfani da sabulu ita kanta tayi mamikin yadda Jinin jikinta ke fita, Farar fatarta sol ta dawo har wani salƙi takeyi da ɗaukar ido, hatta uniform ɗin da ke ajikinta sun wanku sosai sun manne ma fatarta,

kwantar da kanta yai saman broad chest É—inshi, Ya cusa yatsun hannunshi cikin sumar kanta yana cuccuÉ—ata da ruwa, Jinin da ya danÆ™are mata a cikin kan ya dinga fita, gashin kanta ya dawo ainihin launin shi dark brown mai kyan gaske, ba Æ™aramin taimakonta yai ba da yayi mata wanka, Ita kanta tasan bazata iya wanke najasar dake a jikinta ba, Æ™anÆ™ame jikinshi tayi sosai la66anta na kerma take faÉ—in”sanyi Danish san yi ni ke ji, tamkar ana Æ™ara gudun ruwan sun jiÆ™e sharkaf acikinsa, sai da ya kammala tsaftace mata jikinta tukunna ya É—aukota saman kafaÉ—arshi ya dawo da ita Gefen dutsen da ya É—aura uniform É—inshi.

Tun da ya sauke ta ta faÉ—a ma faffaÉ—an Æ™irjinshi, ta zagayo da hannayenta saman bayanshi, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, idanuwanta a lumshe, ita kaÉ—ai tasan daÉ—in da ta ke ji, da farko taji haushi da ya yi mata wanka, amma yanzu ta fahimci Dalilin dayasa ya tursasa mata yin wanka, jikinta yayi mata daÉ—i wata irin ni’ima ke sauka, tamkar an yaye mata damuwar dake acikin zuciyarta, sun natsu suna sauraron bugun zuciyar junansu, irin yanayin da yafi son kasancewa tare da ita, yana son Angel dinsa fiye da yadda yake son kanshi, a shirye yake daya sadaukar da ranshi indai akanta ne”

Fatar wuyanta ya ƙurawa ido fara sol sai ƴan tabannin da ba arasa ba, na gurjewar da tayi, ɗaura tafin hannayensa yai asaman bayan nata,

“My Angel!” a kasalance ya furta sunanta shiru bata amsa mashi ba

“Are you feeling sleepy?” kamar yayi magana da bango shiru taÆ™i buÉ—e ba ki ta yi magana, Æ™oÆ™arin rabata yayi daga Æ™irjinsa, sai dai taÆ™i bari ya É—ago da ita, ta yi tighting É—in shi tamkar zata koma cikin shi, baiwar Allah, Dama abuÆ™ace take da ta samu inda zata sassauta raÉ—aÉ—in da ke acikin zuciyarta, abubuwan da suka faruwa a rayuwarta ta soma tariyowa tun daga lokacin da ta mallaki hankalin ta, har zuwa rayuwarta a hannun fulanin Daji da kuma faÉ—owarta gidan kurkukun Æ™addara, Zafafan hawayene suka wanke fuskarta, jin shessheÆ™ar kukanta ne yasa shi rikicewa ya shiga ambaton sunanta adabarbarce, daÆ™yar ya iya 6an6arota daga Æ™irjinshi, eyes dinshi akan fuskarta ta runtse idonta

“My Angel I don’t want you to dwell on what happened before, I know it hurts you, but please forget about the past. I don’t like to see you cry.

tun da ya soma lallashinta bata buÉ—e idanuwanta ba, tsawon mintuna kafin a hankali ta É—ago da kanta tare da jingina bayanta jikin dutse.

Matsawa yayi jikin ƙaton dutsen ya miƙa hannu ya ruƙo uniform ɗin shi, A tsanake Ya sanyasu a jikin shi

“Zaki Iya jirana anan”? girgiza mashi kai tayi”tsoro nake ji, ka maida ni cikin Æ´an uwana” yaso ta amince ko dan ya samu ya shiga cikin Dajin Ya nemo masu abunda zasu ci, kwantar mata da hankalinta yai”Yanzu zan dawo, bana so Æ´an uwanmu su tashi da yunwa pls ki jirani anan, ba abunda zai same ki, kada kije ko’ina” bai jira amsarta ba, ya 6ace ma ganinta.

Tunawa da cewa ita fa yanzu mai ƴanci ce yasa ta ɗan saki murmushi, har ta fara tunanin irin mugun kisan da za ta yi ma waɗanda su ka sadaukar da su, badajimawa ba ta soma Jin motsin tafiyar mutun a firgice ta buɗe idanuwanta lokaci ɗaya ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya ganin Danish ne ya dawo hannun shi a ruƙe da Zomayen Daji da ya yo masu farautarsu, ya ruƙe ƙafafuwansu da hannu ɗaya, yayin da ɗayan hannun ke aruƙe da gorar ruwan, mamaki ne ya kamata ganin zomaye, miƙa mata gorar ruwan yai da sauri tasa hannu ta kar6a, Acike take da ruwa, jera kafaɗa su ka yi suna tafiya suna satar kallon juna, abunda ya ɗaure mata kai yadda Danish yasan komai dangane da Daji mutumin da bai ta6a fita daga cikin kurkuku ba, Yanzu tadaina yi mashi kallon solo6iyo, A Namijinsa ta ke kallon shi.

Lokacin da su ka Æ™araso Gaban Kogon dutsen, Atare su ka shiga Ciki, Ya ajiye zomayen saman korayen ciyayin da ke shimfiÉ—e Æ™asa, ya É—ago da ido ya kalle ta, zanje na haÉ—o itace yanzu zan dawo, Ta amsa mashi da toh,’

Bayan tafiyarshi ta ajiye gorar ruwan Æ™asa, kafin ta nufi shimfiÉ—ar su, ba ta yi mamakin ganin ba su farka ba saboda ta riga ta gane aikin Danishi, gaban akwatin kayansu ta zuÆ™unna ta buÉ—e ta curo tsoffin uniform É—inta, Cikin Æ™anÆ™anin lokaci ta canza na jikinta da suka jiÆ™e ta shanya su daga wajen dutsen, dawowa tayi cikin kogon Agaban shimfiÉ—ar ta zuÆ™unna tana Æ™are masu kallo, idanuwanta akan Jemimah da Azeeza, daÉ—i kamar zai kasheta, a Æ™agare ta ke da su farka su ga wurin da Allah ya kawosu tasan zasu sha mamaki da al’ajabi kuma zasu ji daÉ—in cika masu alÆ™awarin da ta yi.

Sam ba ta ji motsin shigowarshi ba, har sai da yai mata gyaran murya tukunna ta waiwayo su ka haÉ—a ido da shi

In zo in tayaka”? girgiza mata kai yai” a’a bana so ki wahala” miÆ™ewa tayi tare da zuwa gabanshi ta zuÆ™unna tana Æ™are mashi kallo, hankalin shi ya koma akan itacen da ya ke jerawa bayan ya kammala ya É—auki duwatsun jiya da yai amfani wurin rura wuta, duk wani motsin shi akan idonta har ce mata yai “kije ki huta mana, ba kince kina jin sanyi ba? Ki É—auko bargo” maÆ™e mashi kafaÉ—a tai alamar ba za ta je ba.

Bawan Allah shiya zauna zaman gasa masu naman, sai maiƙo yake yi kamar an soya shi da mai, Kitsan jikin zomayen ne ke narkewa, bayan ya kammala ya ɗaura gasasshen naman da ya tsira Jikin icce saman faffaɗan ganyan da ya shimfiɗa a ƙasa.

“Danish” É—agowa yai tare da kallonta, bakomai ya gani acikin idanuwanta ba face Tsantsar tausayin shi

“Kada ki damu kanki am ok, idan zan shekara inayi maku bauta ba zan gaji ba” kalamanshi sun Æ™ara sanya mata Æ™aunarshi acikin zuciyarta.
“A ina ka samu wannan gorar ruwa”? Tai maganar tana nuna ta da yatsa

“A cikin Daji ba abunda ba zaki Iya samu ba, Hada kan mutun” murmushin gefen fuska ta saki, ga dukkan alamu zasu fara kafa nasu tarihin soyayyar tun acikin Daji.

ÆŠagowa yai da lumsassun idanuwanshi ya É—aura su kan fuskarta

“Can you eat by yourself? Or do I need to feed you?”

Girgiza mashi kai tai” ka wahala sosai, ni ya kamata in baka da hannuna” ya ji daÉ—in maganarta har ya buÉ—e baki da niyar mayar mata da martanin maganarta, kwatsam! muryar Jemimah ta katsesu da wani irin sautin mai amo take kwaÉ—awa Angel kira amatuÆ™ar gigice take fadin”Genie wayyo Allah Genie Zafi Jikina Æ™aiÆ™ayi nake ji” Ahanzarce Danish da Angel suka miÆ™e da sauri suka nufi shimfiÉ—arsu atare suka zuÆ™unna agabansu, Hannu biyu Angel ta sanya ta É—auko ta zuwa saman jikinta, ta Æ™anÆ™ameta, Duk tabi ta furgice sai kuka takeyi masu tana harba Æ™afafuwanta, Sautin kukanta ne ya farfaÉ—o da sauran Æ´an uwan nasu, Batul ce ta fara miÆ™ewa kamar fatalwa idanuwanta luhu luhu sun kaÉ—a jawur, baiwar Allah har faÉ—awa tayi sai uban haske, gashin kanta kuwa a hargitse yake, BuÉ—e idonta keda wuya ta sauke su akan na Danish dake kallonta, Muryarshi na É—an rawa ya furta sunanta”Ba..tul” É—auke idonta tayi daga kan fuskarshi ta mayar dasu Kan kogon dutsen da suke aciki saÆ™o da lungu tabi da kallo, kukan farin cikine ya kubce mata, Da sauri Danish ya ruÆ™o hannunta acikin nashi ya kwanto da kanta saman Æ™irjinshi, sosai ta Æ™anÆ™ameshi tana cigaba da yin kukan.

Farkawa Gabriel yai zumbur ya miÆ™e yana ambaton sunan Azeeza, da ita ya kwanta acikin ranshi, sai tsuma yake yi yana fitar da huci, Cikin shessheÆ™ar Kuka Angel tace dashi”She’s still alive! Azeezar mu bata mutu ba, suna araye,”

Karaf maganarta ta sauka akan kunnan sauran ƴan uwan su da suka farka, a zazzaune suka miƙe Tun daga kan Javed, Naufal da Hannah mutun uku ne basu motsa ba, parveen Azeeza da Haris, ga dukkan alamu sun farka daga bacci sai dai sun kasa motsawa, Jikinsu ba ƙoshin lafiya, ko yatsan su sun gaza ɗagawa.

Hankulansu gaba É—aya ya koma kan su, kowan nan su fuskarshi akumbure take suntum, babu walwala ko annuri, dagaske Azeezana bata mutu ba? Gabriel ne yai tambayar yayin da idonshi ke fitar da hawaye, Danish ne ya bashi amsar tambayarshi, Tsabar farin Cikine ya bayyana akan fuskarshi, Rumfa yai ma azeeza da Æ™irjinshi motsa la66anta da take yi ne ya tabbatar mashi da cewa tana araye sungumarta yai tare da É—aurata saman laps É—inshi, Danish Ya miÆ™a mashi gorar ruwa don ya bata tasha, Yatsun hannun shi na kerma ya kar6a ya kafa mata abaki, ruwan yana wucewa ta maÆ™oshinta sai dai ta gaza buÉ—e idonta, Farin Ciki duk ya cikasu, Naufal ne ya É—auki Parveen Baiwar Allah anji jiki, miÆ™a mashi gorar ruwan Gabriel yai ya kar6a yabawa parveen kamar zata haÉ—a da gorar duka ta shanye, Sai lokacin Danish Ya raba jikin shi daga na Batul Ya rarrafa zuwa gaban Haris dake kwance kamar matacce ya É—aura hannayenshi biyu wurin É—ago dashi ya kwantar da kansa saman kafaÉ—arshi, Cikin sanyin murya ya ke ambaton sunanshi”Haris! Haris!” shiru bai amsa mashi ba, jikin shi yai zafi sosai babu alamun lafiya atattare dashi, É—aura tafin hannun shi yai saman Æ™irjinshi bugun zuciyar haris a hargitse yake fita, hakan ba Æ™aramin tada mashi hankali yai ba, Yana fargabar wani abu ya same shi.
“ÆŠan uwana Rabin raina nasan kana jin muryata pls kada ka bari damuwa tayi maka illa, ina atare da kai” jin muryar Danish acikin kunnanshi yasa shi Æ™oÆ™arin motsa la66ansa sam sautin yaÆ™i fita, Fahimtar hakan yasa danish matsar da kunnanshi saitin bakin Haris

“Deeja ta mutu! Na rasa Deeja Danish! Bazan iya rayuwa ba tare da ita ba, zuciyata nauyi take yi min, ka taimaka ma rayuwata” a hargitse yake magana, tsananin tausayin shi ne ya kama Danish, dama sai da ranshi ya bashi cewar akan Deeja ne ya shiga mawuyacin halin nan.

“Haris ka kwantar da hankalin ka, ba mu da tabbacin suna araye ko sun mutu, tun da har su Azeeza suka farka bayan munyi tunanin sun mutu ina saran suma za’a iya samun masu rai acikin su” cikin jin Æ™unar rai Haris ya furta”Danish idan har hakane deejana tana araye azzuluman mutanancan zasu Iya kashe min ita, mun barsu fa a kurkuku, Danish ka koma ka É—auko min ita, idan baso kake na mutu ba’ sosai ya sanya mashi kuka, Rarrashin shi ya dinga yi yana lalla6a shi duk don ya samu ciwon nashi ya lafa.

Waɗanda suka fi jin jiki a cikinsu Jemimah ce da Azeeza sai Haris, Ita parveen tunda taji ta ajikin Naufal ta wartsake, har tana iya ambaton yunwa take ji, Jemimah kuwa taƙi daina yi masu kuka, Sautin kukanta ya karaɗe kogon dutsen kamar ana zare ranta, Hankalin Angel duk yabi ya tashi, Ta rasa ya zatayi da ita, Cikin muryar kuka take yiwa Danish magana akan yazo yataimaka mata, Har ƙwara Azeeza tun da ta ƙanƙame Gabriel bata ƙara motsawa ba, ta lafe mashi idanuwanta arufe suke gam.

Sun rasa ya za su yi dasu, kukan jamima ba ƙaramin tsuma zuciyarsu yake yi ba, taji jiki baiwar Allah, Sunga ƙoƙarinta da har ta iya yin kukan, azabar raɗaɗin gabanta ne ya addabeta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, fuskarta jaga jaga da hawaye, yarinyar da bata wuci shekara goma da watanni ba, ta rasa budurcinta, su kansu sunyi mamakin da ta iya rayuwa, lokacin mutuwarta ne baiyi ba, Tana kuka suna kuka, Babu wanda bai zubar mata da ƙwalla ba in ka cire Danish, kwantar da Haris yai saman shimfiɗar, jikinshi na tsuma ya nufi Angel Ya sanya hannu biyu ya kar6i jemimah daga hannunta, fucewa yai da ita daga Cikin kogon dutsen basu san Inda ya nufa da ita ba.

Tsawon mintuna sai gashi ya dawo rungume da ita a ƙirjinshi, ajiyar zuciya suka sauke Jin tayi shiru tadaina kukan, Akwatin kayansu ya buɗe ya ɗauko mata rigar sanyi, cikin waɗanɗa tsohuwa ta yi masu kyautarsu, Ya sanya mata a jikinta, ga dukkan alamu wanka ya yi mata, bayan ya kammala sanya mata rigar, ya curo mata hula ya zura mata akanta, ya kuma ɗauko Mayafin kayansu, Sai kallon shi suke yi, Danish ya basu mamaki, Asaman bayanta ya yafa mata mayafin ya miƙe tsaye yana lallashinta kamar yadda akeyi wa jarirai, jemimah ta natsu sai faman lumshe idanuwanta takeyi, Jikinta ya lafa sosai ta daina jin raɗaɗi ciwo nata, juyowa yai tare da nufar Angel ya miƙa mata jemimah,

“Zan tafi da Azeeza ki basu naman su fara ci” amsa mashi tayi da toh, ta kar6i jemimah tare da rungume ta a Æ™irjinta, bayan Ya É—auki Azeeza Ya fuce da ita, janyo masu naman tayi zuwa gabansu, duk da halin da suke aciki hakan bai hanasu Cin naman ba, Saboda matsiyaciyar yunwar da suke ji, Mutun É—ayane ya kasa cin naman, ko da Javed Ya tallabo shi ya zaunar dashi Yana tura mashi abaki, Amayar dashi ya dinga Yi, ruwa kaÉ—ai ya iya sha, sun damu da rashin lafiyar Haris Ya galabaita sosai, Jemimah dai ta É—anci naman Angel ce take bata abaki, har yanzu bata buÉ—e idanuwanta ba, balle ta san a ina suke.

Shigowa cikin Kogon Danish yai Hannunshi ɗauke da Azeeza, Ya wanke ta tass jikinta sai kakarwa yakeyi, tunkafin ya ƙaraso Gabriel Ya buɗe akwatin kayansu ya ɗauko mata rigar sanyi tare da mayafi, Bayan Danish Ya miƙa mashi ita, Ya sanya mata rigar asaman uniform ɗinta, Ya ɗaura mata mayafi saman kanta, kafin ya kwantar da ita saman ƙirjin shi, Abaki ya dinga gutsuro namanta yana tura mata abaki daƙyar take iya taune shi, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba, duk fa wannan budurin da sukeyi Azeeza da Jamimah da Parveen basu san cewa sun bar kurkukun ƙaddara ba, Saboda basa acikin hayyacin su.

Danish bai samu damar cin nashi naman ba, Jira yai sai da suka kammala ɗaya bayan ɗaya ya raka su zuwa bakin ruwan nan suna yin wanka, da taimakon shi Haris ya samu yayi wanka jikin shi ya ɗanyi mashi daɗi, bayan sun kammala Ya ƙara haɗo wasu itacen Ya kunna masu wuta Kogon dutsen ya ɗumama sosai Sanyin da su ke ji ya washe, sun cinye namansu duka, Kaɗan Danish ya samu yaci, kamar masu zaman makoki haka su ka zauna kewaye da wutar da ke ci, Suna kallon junan su kowa da abunda ya ke saƙawa aran shi, jemimah tuni bacci ya ɗauketa kamar jinjira haka Angel ta matseta a ƙirjinta, haka azeezama bacci ne ya ɗauke ta, tana kwance saman jikin gabriel, Haris ya langwa6a kanshi saman kafaɗar Danish, Batul ta ɗaura kanta saman kafadar Angel, Parveen tana a kwance saman ƙirjin naufal, da hannu biyu ya tallabeta, haka zalika Hannah tana arungume jikin Javed, sun natsu suna sauraron kukan namun dawan dake hargowa acikin Dajin, ba zaka ta6a fahimtar yanayin da su ke a ciki ba, kowa da abunda yake saƙawa aranshi.

*OBIE STATE*

In Abuja

*Boss Bature✍️ Mu haÉ—u gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun Æ™addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuÉ—in*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number É—ina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

No comments