Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 22


MIJIN MALAMA
0811923761624
Latifa ta kalli Majeederh ta ce “Amma ba zaki gudu ba kowa? Ki bar gidan kawai idan a kaga babu ke dole a haÆ™ura” Majeederh ta shanye mamakin da Latifa Omar ta bata, she just staring at her kafin ta girgiza ta ce “Kina nufin na gudu na bar gidanmu? Sbd buÆ™atar mahaifina?” Latifa ta ce “Yes, that’s what i mean, idan kika ta fi after a month or a year sai ki dawo nasan babu abin da zai ce, sai murnar ganinki Majeederh” Tunda ta fara Maganar Majeederh ke jin zafin zuciyarta na Æ™aruwa ta ce “Anya ke Æ™awar arziÆ™i ce?” Latifa ta ce “Haba Majeederh? Is just a suggestion bawai dole sai kin aikata hakan ba, kawai gani na yi kina cikin takura na mahaifinki by the way ga rashin saurayi da baki da shi balle mijin aure”
“Kuma É—an Æ™aramin tunaninki ya baki na gudu? Kina gidan iyayenki,ni ki bani shawarar na yafi yawon duniya? Na taÉ“a ce miki Abbu ya takura ni?” Latifa ta yi shiru, Majeederh ta haÉ—e fuska babu alamar her heart stopped beating, ta ce “Ban so, a gaban saurayinki kin zauna kina zayyana masa Abbu faÉ—a zai mini idan ban amshi form, mene nashi? Ko halin ubana kike faÉ—awa wani? Ba ruwana da wanda kuke tare ki daina faÉ—a masa wace ni ko ya nake” Latifa da mmkin maganar Majeederh ta ce “Ba dai wata manufa kika juya zancan ba?” “Ban ji daÉ—i ba” Majeederh said quietly. Kana a raunace ta ce “Na yarda ni macace mai tarin buÆ™atu, ina sane da abin da ke yawo akaina, amma Latifa ban taÉ“a cewa ki bani ko biyar ba, na yarda Allah ke yi, na riÆ™e aikina da albashina nake komai, na taimaki mahaifina, kun fimu wadata amma Allhamdu lillahi, ina da wadatar zuci kuma yanzu na fahimci maganar Abbuna, to ki daina tunani komai mahaifina ya yi zan iya barin gidan nan, ya zama first and last time da zaki bani wannan shawarar” Ta faÉ—a cikin daÉ—in zuciya tare da miÆ™ewa zata bar wajan, Latifa Omar ta riÆ™eta ta ce “Ki yi haÆ™uri Majeederh, i don’t mean to hurt you, ba zan sake ba” Ta jinjina mata kai alamar babu komai ta ce “And yana da kyau ki kwanta ki huta, naga bacci da ciwon kai a idanunki sosai” Majeederh ta harÉ—e hannu a Æ™irji tana kallon Latifa Omar kamar me nazartar wani abu kafin ta É—auke kai tana duba littafin hannunta ta ce “Ok Dr Latifa Omar.”
“You need as much beauty sleep as you can get.” Latifa ta faÉ—a tana dry ganin yadda Majeederh har yanzu ranta ke a haÉ—e alamar dai sam bata ji daÉ—in shawarar data bata ba, kuma ita ma É—in ta fahimta Majeederh doesn’t deserve that, Ta gyara zama ta ce “Amma bakya tunanin farinki ya yi yawa? Shi yasa ake zaton wani abu daga gareki, ni a tunanina ki zauna yau na miki make up a shafa miki baÆ™i a fuska kiyi duhu wa’allah sai kiga an dace idan muka je wajan kamon Widad” Majeederh ta ajjiye littafin hannunta ta yi shiru alamar tunani speaking calmly ta ce “bleaching?” Latifa ta ce “Wanne irin bleaching ni Æ´ar nan, kin taÉ“a ganin farin mutum na bleaching?? Kawai baÆ™i zan shafa miki a fuska” Majeederh bata sake magana ba, ta shiga ta yi wanka ta fito É—aure da towel wani irin kallo Latifa ke binta da shi, zata iya cewa tunda suke bata taÉ“a ganin Majeederh haka, tafi ganin ta gama shiryawa tana saka kaya ko tana zaune, ko aiki, ko kuma dai tana karatu domin ko bacci bata fiye samu taga tana yi ba. Ita da kanta zata iya cewa Majeederh ba Mutum ba ce, in her whole life bata taÉ“a ganin mace mai kyau da tsarin halitta kamar Malama Majeederh Abdul’aziz Khan ba. “kallon fa?”
“No, na fara missing ne” Bata ce komai ba harta gama zaro abaya zata saka, Latifa ta ce “Yau É—aya sai kin kafa mana tarihi a Æ™asarmu Nigeria da jiharmu Kano” wata atamfa ta É—akko tun wacce matar Uncle Isma’il ta bata, É—inkin riga da skirt, atamfar Golden ce mai blue sai É—aukan idanu take, daman tun tuni Latifa ta kwaso kayan make up. Majeederh bata san meke damunta ba, amma zuciyarta ta amince da buÆ™atar Latifa Omar, ta zauna akan stool Latifa ta shiga yi mata kwalliyya ita dai idanunta rufe ta tafi wani tunani nada ban, wanda sam bai dace da ma’aunin iliminta ba. harta É—aura mata head bata buÉ—e Idanunta ba, Latifa ta ce “Wow, wallahi kin yi kyau kalli kanki fa” slowly kamar mai tsoran ganin kanta ta buÉ—e Idanunta, tare da kafe kanta da kallo ta cikin madubin, gabaÉ—aya ta tashi daka baÆ™a, fuskarta sai azababben maiÆ™o take na baÆ™in kwallin da Latifa ta shafe fuskar da shi tas, sai fararen Idanunta wanda aka shafa musu kwalli ga wanin jambaki tun na iyaye da kakanni da aka lafta mata a lips É—inta, ko ita É—in É“aka ce da wahala a nan a samu mai irin baÆ™in ta, amma har zuciyarta ta ji hankalinta ya kwanta da ganinta a haka fiye da ganinta a fara, sai taga baÆ™in ya mata kyau ta juya ta kalli Latifa ta ce “To ba zan iya baka Black gabaÉ—aya ba?” Latifa ta ce “how? BaÆ™in mutum zai iya bleaching ya dawo fari, fari kuma no way sai haÆ™uri” Ta yi jim ta ce “What about my hands? Legs, da wuya”
Latifa ta ce “Ki saka Safa, Æ™afa da hannu, wuyanki kuma ki rufe da mayafi” haka ta yi ta É—auki babban mayafi ta rufe jikinta ruf sai baÆ™ar fuska kamar bayan tukunya a waje tana da Æ™yalli. Ba kowa a gidan suka rufe jawo gidan tare da ficewa, yammaci ne kusan duk samarin unguwar na nan, suka dinga bin Majeederh da kwallo suna mmkin inda Latifa ta samu mahaukaciya domin duk mutum mai hankali ba zai taÉ“a irin kwalliyyar da Jiddatul-khairy ta yi ba, ganin kallon na yawa kuma Latifa bata son su fasa zuwa gidan bikin a haka sai ta tsare napep ta masa kwatancen gidan Uncle Isma’il….. Compound na gidan ya zama kamar hall event yadda aka tsara akai komai, ga manyan mutane Æ™awayen amarya da sauran family. Bugawar kiÉ—an ya yi daidai da bugawar zuciyarta, ta sako Æ™afa a hankali kanta Æ™asa musamman da taga mutane kamar furanni sbd tsabar kyau da iya matching colour na dress, Hajiya Luba ce ta shige Majeederh tana sauri ganin Latifa ya sa ta tsaya ta ce “A’a zuwan yaushe Latifa? Ina babar taki?” Latifa ta ce “Yanzu na zo, wallahi bata jin daÉ—i ta ce ayi muku Allah ya sanya alheri” Hajiya Luba ta ce “Allah sari, Allah ya bada lafiya Majeederh bata zo ba ko?” Latifa ta ce “A’a, gata nan tare muke” Baki sake Hajiya Luba take bin wacce aka ce Majeederh ce da kallo with shocked ta ce “Malama Majeederh tamu nake magana, wannan ai na É—auka wata mata ce mai taÉ“in hankali dake kusa damu” Latifa ta zare idanunta ta ce “Wallahi Malama Majeederh ce Anty, kalli cikin Idanunta zaki yarda” Hajiya Luba ta riÆ™e haÉ“a ta ce “Jama’a mun shiga uku, Majeederh lafiyarki É—aya kuuwa? Kinga kalli kanki” Ta Æ™are haÉ—e rai ta ce “Shawarar wace a cikin ku? Yin kwalliyyar?” Da sauri Latifa ta nuna Majeederh ta ce “Ita ce”
Sosai ran Anti ya É“aci ta ce “Tsaya a nan ina zuwa” Tana barin wajan sai ga amarya Widad da friends É—inta suka gaisa da Latifa tana ta mata complain bata zo da wuri ba, gashi Anti Jeederh ita ko zuwa ba ta yi ba. Ta juya ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, wacece wannan waye ya Æ™ara barin wannan mahaukaciyar ta shigo?” Majeederh ta runtse Idanunta ganin yadda ake haÉ—ata da mahaukaciya bata ji ba bata gani ba, kafin Latifa Omar ta yi magana ta sulale da sauri tabar wajan. Tun daga nesa wasu tawagar maza suke dariya É—aya hadda É—akko waya yana danna vedio yana cewa “Lallai bikin Widad da Mansur ya yi albarka, hadda su mahaukaciya a wajan?” Ta Æ™arawa tafiyarta sauri harta shigewa bayan Æ™ofa ta shiga gidan Uncle Isma’il tana dafe Æ™irjinta. Her heart broke, she hugged her knees even righter. She felt warm tears running down her cheeks, nothing hurts like they words, ta wulaÆ™anta kanta akan neman mijin aure sai gashi buÆ™ata bata biya ba mazan ma kallon mahaukaciya ce suke bata, a wancan karan ance Aljana yanzu kuma suna kiranta da mahaukaciya. Ba abinda ke bata tsoro ganin hatta Aaliyyah da suke ciki guda bata ganeta ba. Ta Æ™ara Æ™anÆ™ame jikinta waje guda.
Hannunsa duk biyun ya sa ya rufe kunnenshi wanda sautin kiÉ—an ke neman fasa masa dodon kunnen, a hankali ya juya yana buÉ—e idanunsa cikin sauri kuma ya sakko daga kan gadon yana jan tsaki, gabaÉ—aya Æ™addara ce ta kawo shi gidan Uncle Isma’il ya É—auka a gidan Uncle Bello za su yi Shirman abun nan, gashi daga dawowarsa garin ba a bar kunnenshi ya wuta ba, idanunsa sun Æ™anÆ™ance sbd bacci ya buÉ—e Æ™ofar ya fito daga shi sai wani 3gauter, tunda ya fito ta tsora masa idanunta da suke É—auke da jiÆ™aƙƙun hawaye tana mamakin yaushe ya dawo shi kuma? Harya gama watannin kenan, yana zuwa ya fice ta gefen Æ™ofar kai tsaye kuma wajan M.c É—in ya nufa “Hi” M.c ya ce “Hi” Ya kame fuska sosai ya ce “Kwashe kayanka kabar wajan nan yanzu, duk wanda ya yi magana ka ce Alpha Bello khan ya saka ka ok” Yana faÉ—in hakan ya juya, Ruma ce ta fara magana ta ce “Kai Dj ya haka? Yanzu fa abokan ango za su zo, kawai sai ka shiga kwashe kaya” M.c bai magana ba sai Dj ne ya ce “Wa nine ya ce mu kashe yanzu” Ruma ta ce “Kan uba waye?” Ya ce “To gashi nan dai, amma kamar Soja yanayin jikinsa” M.c ya ce “Sunansa Alpha Bello khan” Da sauri Ruma ta rufe baki tana zare idanu daidai nan Widad ta zo tana complain me ya sa ta ji shiru, Ruma ta faÉ—a mata Alpha is back, wani irin rushewa da kuka ta yi shikenan ta shiga uku, yanzu dinner É—in gobe hanata zai yi ta dinga kuka, Anty ta zuwa ta ce “What did i miss?” Sahar ta ce “Captain ya dawo, Alpha” Anty ta ce “Na gode Allah, ya dawo a daidai”…. Majeederh na zaune ta ji an saka hannu tare da miÆ™ar da ita tsaye da sauri ta buÉ—e ido ganinsa tsaye a gabanta ya harÉ—e hannu a Æ™irji yasa ta haÉ—iye sauran hawayen, ya dinga kallonta frm head to toe ya girgiza kai ya ce “Follow me” Ya juya zuwa bedroom É—in daya fito, a hankali ta tura Æ™ofar ta shiga yana zaune hannunsa riÆ™e da waya yana magana a hankali ya nuna mata toilet “Clean your face, now” Za ta yi magana ya haÉ—e dole ta shige, ya daÉ—e zaune kafin ta buÉ—e Æ™ofa ta fito a hankali take takawa zata bar bedroom É—in ta ji ya ce “Come, Jiddatul-khairy” Ta juya tare da zubewa a Æ™asa ya ce “Meke faruwa?” Ta girgiza kai, ya ajjiye wayar tare da juyawa gareta bakiÉ—aya ya saka hannu ya tallafo haÉ“arta ta yi saurin ja baya zai Æ™ara ta É“ata ta marairaice fuska cikin shagwaÉ“a wanda daman ita halittace a jikinta ta ce “Don Allah Yaa Alpha kar ka sake ta É“ani” ta faÉ—a har zuciyarta domin daya ta É“ata ji tayi kamar an watsa mata wani abu, tsigar jikinta ya miÆ™e, ya nuna mata Æ™ofa ya ce “Out” ta fice da sauri…. Bayan gama bikin Widad aka zauna family meeting amma rawar bata sauya zani ba, har su Uncle Isma’il suka zare hannunsu daga kan al’amarin Abbu, har lokacin Alpha bai san meke faruwa ba, shi ne babban É—an Uncle Bello, daman jininsa bai haÉ—u da Mami ba shi ya sa bai damu da zuwa gidan Abbu ba, Ranar monday aka gama komai na batun tafiyar Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, daman tana yin dashi kuma ita ce É—aukan Æ™arshe aka bata kuÉ—i ta siyi kayan sawa sabbi da taimakon Latifa, sosai ta yi mamakin yawan Abayas É—in data tambaya sukai mata shiru kawai, ta siyawa Abbu buhun shinkafa, katan na tafiya dana makaroni, ta siya musu masara ta Tuwo, ta bawa Aaliyah kuÉ—i ta ce ta riÆ™e a hannunta kana ta bawa Abbu ya dinga murna yana cewa “To gashi É—an Æ™aramin albashi ya yi rana, ina ga idan ta fara aiki a Misira ai shi Allhamdu lillahi, Majeederh ta wanke masa zuciya” Kanta a Æ™asa, a daren ta shiga sallama da Æ´an-uwa Innati kuka sosai, Majeederh na zaune a gaban Anty tana mata faÉ—a suka ji an shigo É—akin ganin yadda yake huci kamar an maciji yasa Anty jin tsoro ta É—auka ko wani abun ya faru domin tasa duk wani soja kullum cikin shiri yake ta ce “Alpha lafiya??” Idanunsa jajur bai kalleta ba, ya saka hannu ya damÆ™i hannun Majeederh tare da janta zuwa É—aya bedroom É—in yana shiga ya juya ya sakawa É—akin sakata tare da harÉ—e hannu a Æ™irji ya shiga takawa zuwa inda take tsaye…..

No comments