Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 24


MIJIN MALAMA
08119237616
Uhm get ready…… Yanzu zamu fara凉26
Majeederh ta sake kallon Aliyu, she saw that he had changed from the way she knew him, duk da ba wani mugun sani ta yi masa ba, ta É—auke kai ganin yadda ya kafeta da idanunsa da suka janye, a hankali ta juya idanunta cike da hawaye ganin Khan’s family maza da mata yara da manya suna É—aga mata hannu. Jikinta na Æ™yarma da É“ari na rashin sabon tafiya ita É—aya ta Æ™arasa kujera ta zauna tare da kifa kanta a tsakanin cinyoyinta, wani rauni ya mamaye dukkan zuciyarta fargaba da tsoran abin da zata tarar a Æ™asar daba tata ba ya wanzu a zuciyar Majeederh Abdul’aziz Khan. Ya za ta yi a garin da babu uwa ba uba? Garin da ba wa ba Æ™ani? Garin da babu idon sanin? Garin da babu mai kwaÉ“arta? Ya za ta yi idan abu ya faru da ita wa kuma zata tunkara? Rashin sanin wanda zai bata amsar tambayoyinta ya sanya ta Æ™ara tura kanta wani mahaukacin kuka na kwace mata ta yi saurin rufe bakinta. “Assalamu alaiki” Wata murya ta sauka cikin kunnenta a hankali ta goge hawayen idanunta tas ta É—ago kanta bayan ta gyara zaman liÆ™ab É—in fuskarta. A hankali ya daidaita tsaiwar shi ya Æ™ara cewa “Assalamu alaiki” Su take ta amsa amma harshenta ya yi mata nauyi ta É—aga kanta suka haÉ—a idanu, yana tsaye ya rungume hannu É—aya a Æ™irjin fuskarsa maÆ™ale da face mars, ya Æ™ara zuba mata idanu ganin yadda take ta sauke ajjiyar zuciya ya ce “Ki duba number seat É—in ki” Sai a lokacin ta duba taga a number 35 take zaune number ta kuma 34 ne, ta langwaÉ“ar da kai alamar ban haÆ™uri kana ta tashi a hankali ta zaune a number dake window. Ya nemi waje ya zauna yana danna airplane mode a wayarsa tare da ware jarida ya shiga dubawa, yadda Majeederh ke sauke numfashi a wahale ya sanya ya juya ya kalleta tare da cewa “Are you okay?” Ta jinjina kanta.
“Are you sure?” Ta Æ™ara jinjina kanta ya bita da kallo kafin ya ce “Okey”
Sanarwar aka fara kowa ya shirya jirgi zai ta shi, a hankali ta jawo ballet ta É—aura a jikinta.
Jirgi ya fara juyawa a ƙasa tsayin wasu daƙiƙo zuwa mintuna, Majeederh ta rufe Idanunta tare da ƙanƙame jikinta waje guda, lokacin da jirgin ya yi katantanwa zai tashi ji tayi kanta yana sarawa amai na shirin zubo mata. A taushashe ya ce
“Sorry” tana cikin wannan yanayin jirgin Emirates Airplane ya É—aga da É—arorun É—alibai. Ta sauke ajjiyar zuciya ya É—auki ruwa ya miÆ™a mata ta girgiza kai, har lokacin bai ji maganarta ba.
“Please bear with the interruptions, is this your first time on a plane?”
“Uhm” ta furta a yanayin da ba zai iya haddace muryarta ba.
“I see, sorry” Ya mai da hankali zuwa ga jaridar dake hannunsa deep down na zuciyarsa he was thinking ko dai bata jin magana, kurma ko bebiyya? Only God knows… Majeederh ta rufe Idanu yayinda da dukkan wani farin cikinta ta barshi a jihar Kano, Æ™asar Nijeriya.
Aliyu ya zame idanunsa daga kan jirgin su Majeed wanda ya gama shigewa cikin gajimare, ji ya yi kamar da zuciyarsa ta tafi tare da nutsuwarsa ya sauke numfashi yana Æ™oÆ™arin buÉ—e murfin motar shi ya ji an ce. “Hi”
Ya tsaya ta buÉ—e motar ya juya idanunsa ya sauka akan Alpha wanda baya jin zai iya mance yanayin daya gansu shi da Majeederh. Bai ce masa komai, Alpha ya gyara zama ce ya ce
“Alpha Bello khan my name, Captain, It is the highest rang in Tactical troops organization”

“Good” Aliyu haydar ya ce murya kuma can Æ™asa, Alpha ya gyara tsaiwa ya ce “Sunanka Aliyu Sufyan Alhassan, É—an Jarida a matakin farko na fara aiki, Kayi karatu a Al’Æ™alam University, daga nan ka shige Cairo ka É—ora da karatu, a gida anso ka karanci É“angaren politics Democracy, kai kuma ka ce Law ka ke so, mahaifinka Alhaji Sufyan Alhassan shi ne Commissioner for education, ku biyu iyayenku suka haifa, yayanka Almustapha shi ne Manager a Bua campaign, mahaifiyarku tana ji daku sosai shi ya sa bata jure dukkan É“acin ranku, wannan dalilin ya sa bata takura ku akan maganar aure duk da akwai Æ´an mata a familynku amma kuna jin kun girmi ajin su” Alpha ya yi murmushin gefen baki ya zuba hannu a aljihu ya ce.
“Idan har a kwana É—aya zan iya sanin waye kai, to karantar zuciyarka ba zaiwa Alpha wahala ba, bayan kasanceweta soja ina aiki a hukamar fikira ta jiha ka kiyaye, kada ka fara abin da ba zaka iya ba, kada ka sanya zuciyarki cikin ramin da zata kasa fitowa, kada ka yi Æ™ullin da zaka saka cikin kejin kaza, kasan kaza uwar tune-tune ce, stay away from her, Ina nufin Majeederh Abdul’aziz Khan she’s my sister”
Bar Aliyu Sufyan Alhassan dake jingine da jikin lafiyayyiyar motarshi ya É—an miÆ™e hannunsa mai É—auke carnoner ya É—aga ya shafa kansa ya ce “Anzo wajan”
Ya dubi idanun Alpha dake kwance cikin nasa idanun kai tsaye ya gane me launin idanun yake nufi domin a yawan karatun English Novels da yake da literature daya karanta yasa fahimtar hakan bai masa wahala ba “Uhm”
Sai kuma ya ce “Me ya sa zaka nuna maitarka a fili? Kada ka manta nan fa ba filin yaÆ™i bane ko dajin sambisa Captain Alpha Bello khan, a tsare rayukan jama’a kafi Æ™arfi, amma ba zaka nunawa Babba lauya fahimtar waye mutum ba, by the way, who are you talking about? Stay away name? Please open your heart Æ™ilan na fahimta sosai”

“Ka janye jiki daga gare ta, baku dace ba?” Cewar Alpha. Cike da rainin hankali irin na Lauyoyi Aliyu ya ce “Wai wa kake magana? stop bitting around the bush, just go to the point” Ya faÉ—a da muryar marasa lafiya.
“Na hango soyayyar Majeederh a cikin Æ™wayar idanunka, shi ne nake maka gargaÉ—i kada ka sanya son abin da ba naka ba, ku dan muhimmancin rayuwarka ga wanda suka damu da kai” Alpha Said, ya na buÉ—e ido.
Aliyu ya ware idanunsa ya ce “Soyayya? Ni É—in? Kuma wai da sister naka? Goodness, to an faÉ—a maka halin Lauyoyi da Sojoji É—aya ne? A cikin gari muke fa ba wai barrack ba, balle ka ce zakai kishi akan kilaki, and ka yi kuskuren fahimta zatonka ya saÉ“a lissafinka”
Aliyu ya taka a hankali har gaban Captain Alpha ya ce “Yes Am in love, amma da Æ™awar Hawwy ba ita kanta ba, bani da tabbaci da zuciyata, ban yi kuma al’Æ™awari ba, domin shi kayana ne, zuciyata ba sansanin sojoji bane wanda a koda yaushe za a cillaku duk garin da aka so, zuciyata ba rigar sawa ba ce, balle a cire sanda aka so a kuma saka sanda aka so, Shi kuma so a makaho ne, baya ji baya gani baya kuma fahimta balle a gargaÉ—e shi, shi ne kamar dukiya ne wanda maganar mai shi kawai take ji, Ni bana soyayya domin So tsuntsune yana iya tashi daga kan wata ya koma kan wata, abun da zuciyar Barrister Aliyu Sufyan Alhassan ta sani shi ne _“KAUNA”_ irin ta har abada, Æ™auna wacce zan iya mutuwa akan ta, ban san sacrifice a cikin Ƙauna ba, Cikakken namiji shi ne mai faÉ—a domin cimma nasara, nasara bata tabbata sai da tarin Æ™alubale, Æ™alubale a rayuwa shi ke nuna yarda da Æ™addara, yadda da Æ™addara ke nuna yarda da Allah Ubangiji maÉ—aukakin sarki” Ya yi shiru yana sauke numfashi kafin ya daki kafaÉ—ar Captain Alpha ya ce “My friend, fight for your love”

“And you too Barrister Aliyu Sufyan Alhassan, kada ka manta ko a kasancewata Cousin zan iya yi maka illa”
Alpha ya sake faɗa a siga ta ya zama dole ka bar abinda zuciyarka ke so. Murmushi kawai Aliyu ya yi domin ƙoƙarin magana kawai yake yana faɗin hakan ya shiga mota, daidai nan Latifa ta ƙarasu ta ce

“Meke faruwa, kai da…..,”
Sauran maganar ta maÆ™ale ganin Captain Alpha tsaye jikinsa sai É“ari yake shi kaÉ—ai ta yi saurin nufar Aliyu ta ce “Yaushe ka zo?” “…. Not too long”
“Tafiya za ka yi?” Latifa ta sake tambaya ba tare daya kalleta ba ya ce
“In sha Allah” Ta ce “Ok then, Bye zan ki raka na ji jikin” Ya ware idanu akan Lafita ya ce “Ok love”
Ya yiwa motar key tare da yin reverse ya bar wajan da gudu.
Da sauri Alpha ya shiga ta sa motar har lokacin jikinsa É“ari yake yana jin Anti na kira amma ya yi banza. GabaÉ—aya Khan’s family suna can kan Aaliyyah dake ta faman kukan tafiyar Majeederh da Æ™yar suka lallaÉ“ata tare da shiga napep su kai gida.

New life
Airplane É—in Emirates ya sauka a filin sauka da tashin jirgi na Cairo International Airport, kasancewar tsakanin Nigeria da Egypt tafiyar 5 hours 25 minutes ce. Ya sanya su ka yi saukar dare, weather garin ta bambanta data Æ™asa Nigeria, Ruwan sama: 1 Laimar iska: 30 Iska 18km/h tun a step É—in farko na jirgin Æ™ofofin fatar jikinta suka buÉ—e suka shiga amsar saÆ™on sauyin yanayin da suka samu. A hankali Majeederh ta É—aga kanta sama tana ganin sararin samaniya sama É—aya ce kaf duniya, amma ta bambanta da saman data gani a taushashe ta ce “Majeederh a Misira”

Misira/ Egypt
Kasar Misra,ko Masar tana kudu maso gabashin Afrika, kuma tana kudu maso yammacin Asiya, É—aya daga cikin muhimman siffofin da take taÆ™ama da su shi ne na kasancewarta a kan mararraba ta kusa da nahiyar Turai. Sannan kuma tana matsayin Æ™asar da ta kasance mashiga tsakanin Afirka da nahiyar Asiya. Har ila yau kuma, ita ce ta haÉ—a hanyar safara ta cikin ruwa, tsakanin tekun Mediterrenean da tekun Indiya ta hanyar Bahar maliya. Harshen Æ™asar Larabci ne, Shugaban Æ™asar Abdul-Fatah El-sisi ya wadata Æ™asar shi da komai, kuÉ—in Æ™asar kuma Fam ne, ita ce Æ™asar da tafi ko wacce yawan Al’umma a cikin Æ™asashen Larabawa, ga babban birninta Al’Æ™ahira har ila yau gata a Æ™arshen kogin Nilu, wanda shi ne kogi mafi girma a duniya.

Majeederh ta buÉ—e ido jin ana tambayarta da larabci “Shin ko lafiya kike?” Majeederh ta kalli kyakkyawar farar budurar dake tsaye kusa da ita kafin ta ce.
“Lafiya lou” Budurwar ta ce “Ma sha Allah, Sunana Ƙhulud Arzaan daga Saudiyya na zo nan karatu tare da mijina Ajlaal” Ta yi mata bayanin cikin larabci. Majeederh ta sake murmushi ta cikin liÆ™ab É—in kafin ta ce “Ma sha Allah, Allahumma Barik”

“May i knw You?”
Cewar Ƙhulud Arzaan Majeederh ta ce “Me zai hana?” Ta gabatar mata da kanta ganin yarinyar nada nutsuwa, Ƙhulud Arzaan ta juya idanu ta ce “Ina mijinki?”
“Bani da aure” Majeederh ta faÉ—a a taÆ™aice, Ƙhulud Arzaan da bakinta baya shiru ta ce “Oh sorry, kuma Abbanki ya barki barin Æ™asarku zuwa wata babu muhrrami? Ba kyau hakan, shi namiji Garkuwa ne”
“Nawa Uban da kansa ya tursasani zuwa, ko da zan mutu a nan” Majeederh ta faÉ—a a zuciyarta tana Æ™ara karaya da lamarin mahaifinta. Daga nan gabaÉ—aya babbar mota ce ta sake kwasar su zuwa inda aka tana ta domin su, zuwa wayewar gari kuma za su fara shiga Al-Azhar University.
Tana kwance idanunta a sama tunanin rayuwarta da makomarta kawai take na yadda zata iya gabatar da rayuwa a Æ™asar Misira babu kowa nata, har dare ya tsala bacci ya kasa É—aukan idanunta a lokacin kuma ta mance da batun wanda suka haÉ—u a jirgi. Ta mirgina kaÉ—an tana riÆ™e mararta dake mata wani irin murÉ—awa tsigar jikinta sai tashi take tana zubewa kofofin gashin jikinta duk suka buÉ—e alamar a shirye suke da karÉ“ar abin da suke buÆ™ata. Ta Æ™anÆ™ame jikinta tare da jurewa waje guda tana jin gabaÉ—aya duniyar na yi mata zafi, al’amarin da take ji ya tsananta ta miÆ™e tare da tsugunawa tana girgiza kanta a raunace ta ce
“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Ubangiji ka kawo mini É—auki, Allah ka dubeni ka kare mini martaba da kimata har zuwa É—akin mijina idan ina da rabon yin aure idan bani da rabo Ubangiji ka tsare mini imanina ka kare mini budurcina har zuwa sanda raina da ruhina zai dawo gareka” Jikinta duk Æ™yarma da É“ari yake ji take kamar ana kwara mata wuta a fatarta mararta ta kumbura, Æ™irjinta ya Æ™ara girma fiye da Æ™ima tabbacin tana kan buÆ™atar namiji. Tana nan har ta ji kiran farko na sallar Subhi da sauri ta miÆ™e tsaye tare da shiga toilet ta sakarwa kanta shower tana sauke wani wahalallan numfashi, ta fito É—aure da towel duk a tsorace take na rashin sabo. Duguwar riga ta saka ta buÉ—e fridge ta É—auki fruits da ruwa da dabino kaÉ—an ta ci ta sha ruwa sosai kana ta É—auki niyyar azumi kamar yadda ta saba. Raka’atul fjr ta yi tana zaune Ƙhulud Arzaan ta shigo cikin kyakkyawar shiga ta ce “Zo mu je masallaci”
“A masallaci ake sallah?”
Ƙhulud Arzaan ta ce “Eh”
Ta faÉ—a ne kawai amma hankalinta duk yana kan fuskar Majeederh bata taÉ“a ganin zubi da tsarin halitta kamar na Majeederh Abdul’aziz Khan ba, har ta shirya cikin wata abaya ruwan huda idanun Ƙhulud Arzaan akanta ta sanya hijabi mai kyau kana ta saka LiÆ™ab sabo. A hanya Ƙhulud ta ce
“Kuma are you sure a Nigeria kike?” “In sha Allah” cewar Majeederh “You look familiar”
“Me??” Majeederh ta tambaya domin bata ji ba, Ƙhulud ta watsa hannun ta ce “Mafi mushkila”….. Suna shiga Al-Azhar University Majeederh ta cike komai da komai akai sa a department É—aya suke da Ƙhulud Arzaan, course É—in farko Majeederh ta É—auke komai da komai a kanta domin da gaske karatun ta zo ba wasa ba, burin mahaifinta zata cika har Æ™arfe biyar suna cikin makaranta.
Abbu ne tsaye a gaban wani mutum ya ce “Maganar gaskiya nake maka, gidana da nake ciki nake so a rushe komai a sauya sabo kafin bikin Æ´ata Ruma” Alhaji Bashir ya ce “Taya zaka biya?” Abbu ya ce “Ni nake da hanyar biya, mai Æ´a kamar Majeederh har a faÉ—a masa wani abu?” Alhaji Bashir ya yi dariya ya ce “Ƴarka jarinka, to yanzu dai gasky ko zan maka wannan kwangilar sai na Æ™ara maka kuÉ—i a Æ™alla dubu É—ari biyar akai shi ne ribata, idan kuma ni zaka bani auren yarinyar ma shikenan zai na yi maka haÉ—aÉ—É—en gida 200by 200 matsayin sadakinta kaga data dawo sai ayi maganar biki, ko kuma a É—aura auren idan ya so sai na bita can” Abbu ya yi shiru Alhaji Bashir ya ce “Think about that Malam Abdul’aziz, bayan gida har kyauta zan maka muddin zaka aura mini Majeederh” Abbu ya ce “To a nawa zaka iya bani?” Alhaji Bashir ya zaro takarda ya ce “FaÉ—i adadin miliyan nawa ka ke so, ni kuma take zan baka zaka tashi daga matsayin Malam ka koma Alhaji” Jikin Abbu na rawa ya ce “Na amince, na amince wallahi zan baka auren Majeederh…..27
Alhaji Bashir ya gyara tsaiwa yana shu’umin murmushi ya ce “Bana É—aukan asara ba kuma zan fara akan ka ba, ka yarda zaka bani auren yarinyarka Majeederh? Ni kuma na baka dukkan abin da ka ke so?” Abbu bai dugun tunanina ba ya ce “Na baka aurenta Æ´ata Majeederh halak makal, ko bayan bana raye” Alhji Bashir ya ce “Baka raye to waye zai tashi matsayin shaida?” Ya yi jim kafin ya ce “Allah da Manzonsa su ne shaidar hakan?” Alhaji Bashir ya haÉ—e fuska ya ce “Na san da haka, amma mutane huÉ—u shaidu nake so” Abbu ya shiga nazari idan ya ce a’a ya san tabbas zai dauma cikin wannan gidan nasa da baya samun ci-gaba, mafarkinsa na zama wani a duniya ba zai tabbata ba, hanya É—aya ce wacce ta kasance madafar shi shi ne “Majeederh” Abbu ya ce “Zuwa dare sai ka dawo ni kuma zan haÉ—a maka shaidun” Alhji Bashir ya ce “Never mind, Allah ya kaimu” Su kai sallama Alhji Bashir ya shiga mota ya tafi, Abbu kuma ya koma gida. Yana shiga ya samu Mami zaune ya nemi waje ya zauna tare da yin shiru yana mamakin abin da ya hana Majeederh kiransa gashi har anyi kwana biyu.
“Lafiya?” Ya sauke numfashi ya ce “Ina yaran? Aaliyyah, Raihana, Ruma?” Mami ta ce “Ruma ta tafi raka Imran, Aaliyyah da Raihana sun je gidan Widad” Abbu ya numfasa ya ce “Rumana ta dinga janye jikinta daga yaron nan”
“Wanne yaron?” Abbu ya tsareta da idanu babu alamar wasa ta yi saurin cewa “Naga aurenta zai yi shiyasa bana damuwa” Abbu ya ce “Kina da tabbacin haka? Baki san meke É“oye ba” Mami ta yi saurin cewa “Me ka ke nufi? Bayan shi ya ce yana son ta zai aureta?” Bai ce mata komai ya miÆ™e ya shiga duba gidansa lungu da saÆ™o deep down na zuciyarsa yana tunanin wa zai kira matsayin shaidu?…
Da daddare misalin Æ™arfe tara Latifa Omar na kwance idanunta a sama kewar rashin Aminiyyarta na damunta, ga rashin kiran Aliyu wayarsa ma gabaÉ—aya a kashe take, she so much loves you ya yi tasiri a zuciyarta sosai. Ta Æ™ara juyawa idanunta rufe a hankali ta sake jawo wayarta tare da danna kira a number da tayi saving da “Heart choice” Cikin sa a kiran farko ta ji an É—aga a marairaice cikin damuwa ta ce “Sweetheart” Almustapha ya yi shiru yana gyara zaman wayar a kunnenshi tare da juyawa ya kalli Aliyu dake kwance saman gadon asibiti ya yi mahaukacin ramewa “Hello”
Muryar Latifa ta sake dawo da shi hayyacinsa ya ce “Majeederh Abdul’aziz Khan, right?” Latifa ta zaro idanunta waje zuciyarta na bugawa, mene haÉ—in Aliyu da Majeederh? Ta yi shiru tuna muryar da ta ji kamar bata Aliyu ba, a hankali ta ce “No, Latifa Omar ke magana, Aliyu fa?” Ta yi saurin tambayar hakan cike da bin umarnin zuciya. Almustapha ya ce “Ok, mai wayar yana kwance asibiti” A ruÉ—e cikin tashin hankali idanunta har ya ciko da hawaye ta ce “Subuhanallahi! Wanne asibiti” Musty ya ce “Aminu Kano”
“Am on my way” kafin ta ajjiye wayar ya ce “Amma kamar dare ya yi, da kin bari zuwa safiya” Ta girgiza kai kamar yana ganinta ta ce “I can’t, ba zan iya bacci bangan shi please” Musty ya ce “Ok, daman daya farka ke ya kira, so na kira ki wayar a kashe shi ne ya ce a nemi Malama Majeederh kuna tare” Ya faÉ—i hakan yana gyara É“arnar da ya yi a baya. Daga haka ya yi hanging off.
Papa dake jin duka maganganun Musty da Latifa ya ce “Me ya sa kayi mata Æ™arya Almustapha Sufyan Alhassan?” Almustapha ya shafa kansa ya ce “Shi ne mafita Papa, zan so a É—aura auren shi da Latifa in prioud time. “He doesn’t like her” cewar Papa. Almustapha ya ce “Yanzu mene amfanin haka Papa? Duk jiya yake kira mana suna É—aya Majeederh, Hawwy, Hawwa’u, na tambaye shi me ya sa yake son Latifa bayan Majeederh ce a bakinsa?”
“Me ya ce?” In ji Papa.
“He refused to answers my question” Hajia ta juya kan Aliyu dake jin duk abin da suke faÉ—a amma idan ka ganshi zaka É—auka bacci yake, hannunsu dake danne da Æ™irjinsa kawai ke motsawa dalili bugawar da zuciyarsa ke yi.
“Me ya sa Zaki?” Ya buÉ—e gajiyayyun idanunsa da sukai jajur kamar ba zai magana ba har Hajia ta Æ™ara cewa “Meke faruwa ne?” Ya yi saurin riÆ™e hannun Hajia ya ce “Ban sani ba, Amma ina sonta a gefena” “Aurenta za ka yi?” Hajia ta tambaya tana riÆ™e nasa hannun.
“A duk sanda na ji ina son aurenta sai na ji na tsaneta, amma idan na cire batun auren sai na ji babu wacce nake son gani sai Majeederh, i want to see by my side, ko sunanta na ji zuciyata bugawa take don Allah ki taimaka mini Hajia please” Papa ya yi zuru yana ganin ikon Allah, wani abu mai kama da almara. Bai taÉ“a ganin hakan ba, ko a film na hausa, Indian movie ko series balle novels, ace wacce mutum ke son aura daban wacce kuma take zuciyarsa daban “Ikon Allah” Cewar Papa Hajia ta ce “Ikon gaske, Yanzu me ka keso” Cikin sauri Aliyu ya ce “Majeederh na keson gani Hajia please” Hajia ta zabga tagumi Idanunta jajur alama ta jima tana kuka domin tun jiya Aliyu bai san inda kansa yake ba sai yanzu, Papa ya sauke numfashi cike da jimamin al’amarin da kuma tausayin É—an nasa ya ce “Zan nema maka auren ita Majeederh a wajan Mahaifinta idan ka amince, kada ka sanwaltar da rayuwarka akan ta” Aliyu ya girgiza kai ya ce “Ba aurenta zan ba” Almustapha dake tsaye harÉ—e da hannu ya ce “Ok ita Teddy ce da za a ajjiye maka ita kai ta Kallonta? Me ya sa ka ke son kan ka har haka? Kana ganinta, But you don’t want to marry her? what kind of nonsense and stupidity is that??” Aliyu ya marairaice ya ce “Ka tausaya mini Yaya, ni kaÉ—ai na san halin da nake ciki idan kai baka rarrashi su Hajia ba waye zai taimaka mini?” Jikin Almustapha ya yi sanyi ya ce “Papa Hajiya help him don Allah kada wani abu ya same shi” Papa da ran shi ya fara É“aci ya ce “Ok kai ma da kake da hankali kenan ko? To ba zan É—auki wannan haukan ba, zan je na nema masa auren Latifa Omar Æ™ilan hakan zai sanya ya manta da batun Majeederh” Wani irin rikitaccen kuka Aliyu ya saka jikinsa sai rawa yake ya riÆ™e Hajia da Æ™arfi numfashinsa na sarÆ™ewa yana riÆ™e Æ™irjinsa, Almustapha ya shiga faÉ—in “Dr… Dr… Dr..” Likitoci suka haÉ—u akan Aliyu da Æ™yar suka dawo da numfashinsa tare da yi masa allurar bacci dake jininsa mai Æ™arfi ne sai bacci ya gagari idanunsa ya dinga surutai. Dr ya kalli su Papa ya ce “Alhaji zaku tafka babban kuskure idan zaku dinga yin abin da zai É“ata masa ran shi” Papa ya kasa magana sai kan shi da yake jinjinawa. Suna haka wayar hannun Almustapha ta fara ringing ganin sunan “Latifa Omar” ya sanya ya É—aga kiran “Ok” ya furta yana barin cikin É—akin, not too long suka dawo tare da Latifa da kanta ke Æ™asa sanye da hijabi ta yi sallama tare da durÆ™osawa ta ce “Ina yini ya mai jiki?” Hajia ta dinga kallon Latifa Omar frm head to toe a taÆ™aice ta ce “Alhmd” kana ta miÆ™e ta bar É—akin, Papa ma ya fita Almustapha ya ajjiye wayar Aliyu ya fice wajan ya rage daga Latifa Omar sai Aliyu dake kwance. A hankali ta miÆ™e ta zauna a gefen gadon ta ce “Nasan ba bacci ka ke ba, ya jikin?” Aliyu sai ya ji tamkar muryar Majeederh lokacin da take cewa _“ I don’t want to interfere”_ Da sauri ya buÉ—e idanunsa tare da sauke su akan Latifa Omar wacce a yanzu ta zame masa Majeederh Abdul’aziz Khan sak! Duk da bai san fuskarta ba amma zubin yadda idanunsa suka kalle masa Latifa sai yaga kawai Majeederh ce gabansa, ya mance drip a hannunsa ya tashi zaune yana kafeta da idanunsa wanda suka sauya Latifa na Æ™oÆ™arin magana ta ji gabaÉ—aya ya jawota ya riÆ™eta tsam a jikinsa ya Æ™anÆ™ameta yana sauke wata mahaukaciyar ajjiyar zuciya cikin magagin allura ya ce “Don’t leave me alone please, ban so kada ki barni please Hawwy” Ya riÆ™e ta yana cusa kansa a wuyanta, Latifa Omar tsoro ya kamata sbd babu wani namiji daya taÉ“a yi mata hakan a tsayin rayuwarta, gefe na zuciyarta kuma bata jin zata iya hana shi yin haka sbd Allah kaÉ—ai ya san irin son da takewa Aliyu. “Ba zan barka ba, ni É—in taka ce Allah da Manzonsa ma sun shaida hakan” Ta faÉ—a a sanyaye ta kuma rasa faÉ—uwar gaban na mene?..
_*5 Month later…*_
Majeederh ce ke ta fe a hankali kanta a Æ™asa hannunta riÆ™e da littafai yadda take tafiya zai tabbatarwa da mai Kallonta a mugun gajiye take, kusan haka É—in ne domin karatu ya yi mata yawa bata da lokacin komai da kowa sai karatu tsayin watanni biyar da zuwanta Egypt bata taÉ“a kiran number kowa a Nijeriya ba, haka kuma bata da Æ™awa idan ba Ƙhulud Arzaan ba, hakan ya sa da yawan student suke mata kallon mai masifar girman kai suka yi tunanin Æ´ar gidan wani ce a duniyar ma bawai a Nijeriya ba, Ilimin da Majeederh take da shi ya Æ™ara mata kwarjini a idanun malaman jami’ar da sauran É—alibai, ita kuma suka zaÉ“a matsayin shugaban É—alibai duk da ta ce bata so amma aka tilasta mata amsa, da yawan Student na zuwa ta Æ™ara musu haske, wasu kawai don su ji maganarta wasu kuma ko Allah zai sanya suga fuskarta suga mene dalilin rufe fuskar. A cikin watanni biyar harshenta ya juye sak cikakken Balarabiya ba zaka taÉ“a cewa ta san hausa ko English ba idan tana larabci, to ta je garin larabawa uwa uba É“angaren Arabic take karanta. Duk rashin son maganarta sai da ta saba da Ƙhulud Arzaan ba tare da sanin dalili ba, haka kawai take son yarinyar kamar Aaliyyah, Ƙhulud Arzaan ta taka rawa sosai wajan wayar da Majeederh ta jata har shopping ta kwasu mata abayas masu mahaukacin kyau tsada very expensive classic one and unique. LiÆ™ab É—in ma ta sauya mata irin na Larabawa da suke sawa, a cikin 5 Month É—in nan Majeederh a rame take bata gaba bata baya jia iyau kamar kazar matsiyata ramar kuma ta samu asali akan abinda ke hanata bacci kullum yake sanyata azumi wanda babu fashi ya zame mata jiki kullum. “Majeederh… Majeederh” Kiran ya dakatar da ita daga tafiyar da take Ƙhulud Arzaan ta Æ™arasu tana dariya ta ce “Shi ne kika taho ko?” Majeederh ta É—an saki numfashi ta ce “Kin tsaya gulma” Ƙhulud Arzaan ta ce “Gulmar ta yi mini amfani kam” Ita dai Majeederh bata ce komai ba sbd an kusa kiran sallar Magriba bata so ta yi mata a hanya Ƙhulud Arzaan ta ce “MusabaÆ™ar Alkur’ani za a yi, Ta duka Æ™asashen duniya na Muslunci” Majeederh ta waro idanu ta ce “Ma sha Allah, za mu ga manyan malamai mu tada haddarmu mu ma” Ƙhulud Arzaan ta ce “Au haba? Kin san me gabaÉ—aya ko wacce Æ™asa ta bada sunan wanda zai wakilce su, Æ™asar ku Nigeria kawai ta rage” Majeederh ta yi shiru tana tunani wa Nigeriya zata zaÉ“a? Allah ya sa ko waye ya dawo musu da martabar Æ™asar su. Kafin ta yi magana Ƙhulud Arzaan ta ce “Kuma Saudiya ta sallamawa Misira kamar yadda suka buÆ™ata ayi MusabaÆ™ar a nan Æ™asar, kuma hadda Granny ta a mutanen da zasu zama masu tantance Æ™asar da tayi nasara” Majeederh ta ce “Kullum ana bani labarin Granny Finally zan ga Granny” Ƙhulud tayi dariya sosai ta ce “Like serious, ba ruwanta idan kin ganta sam ba zaki ce ta haifi Sarki Sultan ba” Majeederh ta ware idanunta ta cikin liÆ™ab ta ce “Kai, ke jinin sarauta ce?” Ƙhulud Arzaan ta yi shiru domin bata son cewa Majeederh ita surukar gidan ce babanta kuma Æ™anin Sarki Sultan ne. Suna hira har suka Æ™arasa gidansu Majeederh ta yi part É—inta Ƙhulud Arzaan ta shige nata. Wanka Majeederh ta yi kana ta yi sallah sannan ta sha ruwa, tana mai yin watsi da maganar Ƙhulud Arzaan. A nutse ta jawo wayarta ta kunna cikin nutsuwa ta danna number Abbu, ringing É—in farko ya É—aga ta cikin wayar ta ji ya ce “Ko baki faÉ—a ba nasan Majeederh ce” Ta sauke numfashi ta ce “Asslaymu Alaika Ya Abbu” Ta faÉ—a a nutse.

“Ke ce Majeederh?” Ta faÉ—a a fili wanda ya jawo hankalin su Aaliyyah, sosai muryarta ta sauya ta zama ta Larabawa. “Ni ce Abbu” Abbu ya ce “Allahamdu lillahi shiru shiru har wata biyar?”

A nutse cikin tarin kamala ta ce.
“ليلة سعيدة ، أتمنى أن تكون بخير”
Ma’ana “Barka da dare, fatan kana lafiya” Abbu ya ce “Wallahi lafiya, kina lafiya ya karatu?” Cikin Larabci ta ce “Allhamdulillah” Ta tambayi kowa na gidan duk ya basu suka gaisa Aaliyyah hadda kuka wurjajjen. “Hawwa’u shiru ba kira ba saÆ™o?” Majeederh ta ce “Ka yi haÆ™uri Abbu” Ya ce “To na yi” Ta ce “Ma sha Allah” Jin shiru bata ce komai ba ya ce “Har yau dai gamo jiya iyau, ba wani abu” Sosai Majeederh ta ji babu daÉ—i ta ce “Zan tura maka kuÉ—i Abbu ta nita sai aje a cire” Abbu ya ce “Yawwa to nawa ne kuÉ—in? Daman an kusa bikin Ruma don ma anyi jinkiri ne” Majeederh ta Æ™ara yin shiru domin rashin son maganarta ya Æ™aru fiye da baya ta ce “Ƙilan su yi 200k fam ne ban san nawa za su tashi a Nigeria ba” Abbu ya ce “Dubu É—ari biyu ya yi kaÉ—an Majeederh ina laifin Miliyan É—aya” Majeederh ta zaro idanunta da suke farare tas ta ce “Miliyan? Abbu ina zan gan su wannan ma Albashin da gwamnatin Nijeriya ke bamu ne bana taÉ“a wa” Abbu ya ce “To babu damuwa amma duk wata idan aka baki kada ki taÉ“a ko ficika ko kwabo karki É“atar” Mamakin mahaifin nata ya cika mata zuciya ya kira sunanta ya ce “Majeederh babu ke ba namiji, ko aurenki mutum zai yi ki ce ke ba zaki aure ba ki ce kina da miji kawai, Majeederh wallahi wallahi duk sanda na ji labari ko na ganki da wani namiji to Allah ya isa ban yafe ba, karatu kawai zaki a tsayin shekaru takwas É—in nan……..

 

No comments