Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 25


Mijin Malama
0811923761628
Majeederh was listening to her father with great surprise, her heart was pounding, A ranta tana jin cewa ko mahaifin nata bai ce kada ta kula kowa ba, babu wani É—a namijin da zai ce yana son ta balle ya yi ji sha’awar aurenta, This is her destiny, and she answered with both hands as a complete Muslim. “Majeederh” Abbu ya kira sunanta cikin kakkausar murya ta kasa amsawa sbd taraddadin rashin sanin abin da zai biyu baya ya ce “Ni ne ubanki, mahaifinki jinina ke yawo a duka jijiyoyin jikinki, Æ™wayar haihuwata ita ce ta samar da ke, idan kina zaton a zuciyarki kiyi gaggawar cire zaton, wallahi tallahi nine mahaifinki Allah ya shaidawa, Manzonsa ya shaida, Mala’iku sun shaida haka…..,”
Majeederh ta katse Abbu jikinta na rawa ta ce “Na sani, na sani bani da wanda ya fika duka duniya Abbu don Allah ka yi haÆ™uri kada ka aibata ni” Abbu ya ce “Kin yarda da hakan?” Ta yi saurin É—aga kai sbd ba zata iya magana ba, Æ™irjinta ya yi mata nauyi. “Hawwa’u a matsayina na wanda ya haifenki wallahi wallahi idan kika kula wani namiji sau É—aya tak da sunan soyayya Allah ya isa ban yafe miki ba, karatu kawai na yarje miki kiyi tsayin shekaru takwas É—in nan” Maganar Abbunta ta sanya mata wata iriyar faÉ—uwar gaba mai tsanani da Æ™yar ta ce “Na yi maka al’Æ™awari Abbu, ka tayani da addu’a kuma ka yi mini alfarma É—aya don Allah Abbu”
“…. Alfarmar me?” Abbu asked. Ta yi saurin cewa “Abbu ka duba halin da nake ciki idan da hanyar da zaka iya mayar dani jinsin namiji don girman Allah Abbu ka taimka ka mayar dani namiji,ni ma zan fi nutsuwa zan fi yin karatun yadda ya dace”
Abbu ya ce “A’a ba shakka, ni kikewa hannunka mai sanda? Ni kike son nunawa ban isa ba, duk abinda É—a namiji zai kema zaki iya, daga yau yanzu ki daina kallon kanki matsayin mace ki fara ganin kanki tamkar É—a namiji, wanda zuwa nan gaba yake fatan zama babba a Æ™asar, ta hanyar zama Gwamna, shugaban Æ™asa, ko shugaban wani katafaren kamfanin, amma idan kina jin ban isa ba go ahead Hawwa’u kina da full right na yi duk mai kikeso haihuwa ce a haife dai mun haifa” Cikin hanzari Majeederh ta girgiza kai ta ce “Wallahi ka isa, ni ikonka ce ba zan sake cewa komai ba ka yafe mini na bi Allah na bika Abbuna” Ya yi shiru jin haka ya sa Majeederh runtse Idanunta zuciyarta na wani irin zafi da raÉ—aÉ—i. A takaice Abbu ya ce “Duk wata kina tura mini kuÉ—in Albashin nan, kada ki ciri ko kwabo idan kuÉ—i kike buÆ™ata ki nemi taimako wajan wani” A sanyaye ta ce “In sha Allah”
Kashe wayar ta yi tare tsorawa kanta idanu ta cikin madubi, ta jima tana kallon kanta kafin a fili ta ce “What should I do?” She don’t know What to expect and kept thinking about how her father would react to seeing her after so long, yanzu ma ya aka Æ™are balle ta ja lokaci, ta dafe kanta dake juyawa azumi ta kai babu komai a cikinta sai ruwa. _“Majeederh, pray ki faÉ—awa Allah komai”_ Wata zuciyar ta bata amsa. She breathed out, trying to calm herself nerves.
Tana zaune har aka kira sallar Issha amma bata motsa ta yi nisa cikin tunani domin ko kiran ma Allah bai nufeta da ji ba, ta zama kamar zararriyya. KafaÉ—arta da aka jijjiga da Æ™arfin gaske ya sa ta sauke wani wahalallan numfashi tana mai buÉ—e idanu a firgice ganin Ƙhulud Arzaan ya sa ta haÉ—e fuska sosai tana É—auke kai, Ƙhulud Arzaan ta ce “Ƙarfe 10 na dare ke kam kina zaune?” Majeederh ta kalli Ƙhulud Arzaan ba tare da ta ce komai ba “Ki zo ku gaisa da Kalb” Majeederh ta ce “Maimaita” Ƙhulud ta ce “Kalb ya ce na kira ki ku gaisa” Majeederh ta girgiza kai ta ce “Kafin wannan, kin ce wani abu?” Ƙhulud Arzaan ta dinga kallon Majeederh kana ta ce “Ƙarfe 10 kina zaune?” Zumbur Majeederh ta miÆ™e ta ce “Asstagafirullah Ya Allah” …. “Lafiya?”
“Ban yi sallar Issha ba” Ta faÉ—a a gigice kamar ta yi kisan kai. Ƙhulud ta nemi waje ta zauna tana mai cewa “Eh to da sauÆ™i, ai sallar Issha bata É“aci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce; da ba don kada na matsantawa al’ummata ba, dana umarce su da yin sallar Issha bayan sun farka daga bacci, Talatainin dare” Ita dai Majeederh bata ce komai ba, Ƙhulud Arzaan sai bin Majeederh da kallo take zuciyarta fal tunani har ta iddar da sallah kana ta fara azkar. Ganin Majeederh bata da niyyar ta shi yasa Ƙhulud Arzaan miÆ™ewa ta koma part É—inta, ta samu mijinta Ajlaal zaune yana danna waya hannunsa riÆ™e da Apple sbd yana Æ™aunar dangin kayan lambu, ta zube a saman cinyarsa idanunsa akan wayar ya ce.
“Meke damun rayuwar Yarima Ajlaal Sultan?” Ƙhulud ta kwaÉ“e fuska ta ce “Allah daga kai har Majeederh baku son ku gaisa” Ya yi kyakkyawan murmushi kawai yana girgiza Æ™afarsa alamar rarrashi can ya ce “Ga ni fa… Call her” Ta tura baki ta ce “Gashi nan sai sallah take Allah don kar tazo ne” Ya saka hannu ya zame hular kanta yana cusa hannunsa cikin sumarta bai ce komai ba. “Ka zo muke part É—in nata, ka ji Kalb my prince”
Ya waro dara daren idanunsa cikin murya irin ta masu mulki ya ce “Prince É—in Saudiyya da zo wajan wata? Ni Ajlaal? ” Ta yi shiru tana kallonsa ya ce “Uhm, shi ya sa kike ta zubar mini da Æ™wayaye a hanya Æ™asa Æ™asa, kin kasa riÆ™e ko Æ™wai É—aya balle Sultaan ya saka ran samun grandson?” Ta daki Æ™irjinsa dake buÉ—e cike da yalwataccen gashi kafin ta ce “Ajlaal wayo zaka mini, idan ka fara haka” Ya tsorawa lip’s É—inta idanu kana ya saki wayarsa a gadon ya ce
“Damn it…!”
“Me?” Ya miÆ™ewa gabaÉ—aya tana wutsil wutsil haka ya cillata gadon yana kashe hasken É—akin gabaÉ—aya muryarsa can ciki ya ce “Yarinya ina zama lafiya wajan aikina kika saka rigima ashe Allah ke sona da rahama”……. Cikin dare Majeederh ta kasa bacci sai juyi take saman gado tana riÆ™e cikinta a hankali take kiran sunan Allah, jin azabar ta yi yawa ya sa ta miÆ™e a haukace tana girgiza kanta tare da zubewa saman gwiwoyinta ta ce “Ya Allah ka É—auke mini abin da na ke ji har gaban abada wlh ban so, Ubangiji ka karkatar da halitta jikina zuwa ta jinsin maza” Ta yi shiru duk da sanyin ac amma zufa take jikinta na Æ™yarma da É“ari, ta zari hijabi tare da sakawa ta nufi wajan part É—in. Lokacin data fito yana zaune saman kujera a daidai corridor wanda zai mayar da kai part É—in Ƙhulud, daga shi sai wata Jersey fara tas faffaÉ—an Æ™irjinsa a bayyane, ya É—ora Æ™afarsa saman table hannunsa riÆ™e da system yana dannawa, lokaci zuwa lokaci yake yatsuna fuska yana É—aukan green tea tare da sha a hankali, sumar kan nan nashi har wuya, Prince Ajlaal Sultaan gabaÉ—aya mahaifinsa ya É—akko sak. Yana zaune ya ji motsi ya juya kansa ya hango mace durÆ™oshe ta cure waje guda tana yarfe hannu, taÉ“e baki ya yi tare da kwasar system nasa ya na jan tsaki….. Washegari dai wajan 11 ta shiga Al-Azhar University tun kafin ta nufi department É—in su taci karo da babban malaminsu. Cike da tsantsar ladabi ta gaisheka ya ce “Majeederh Abdul’aziz Khan?” Ta jinjina kai ya ce “Follow me” Yana tafe tana binsa kamar bata son takawa har ya isa office É—insa, manyan mutanen data gani a office É—in ya bata tsoro ta zauna gefe guda. Malamin ya yi gyaran murya ya ce “Majeederh ga jakadan Æ™asarku Nijeriya dake zaune a nan Misira, bayan zaman tattaunawa da manyan Æ™asar ku kama daga shugaban Æ™asar, gwamnan sauren jihohi da naku, shugaban malamai na Æ™asa dana jiharku daga Æ™arshe sun bada sunanki matsayin wacce zata wakilci Æ™asarku Nijeriya a gasar musabaÆ™ar Alkur’ani ta duk duniya” Majeederh ya zaro idanu waje ta shiga girgiza kai a raunace ta ce “Ba zan iya ba, ba zan iya ba ni ÆŠaliba ce”
Jakadan Nigeria ya ce “Zaki iya Majeederh, Malamin daya baki ilimi ya shaida hakan, mahaifinki ya shaida” Muryata na rawa ta ce “Duk duniya fa? Ba zan iya ba please a sauya wata” Ta faÉ—a a shagwaÉ“e Ajlaal Sultaan ya É—ago kansa dake naÉ—e da hirami ya É—an kalleta kana ya taÉ“e baki yaci gaba da abin da yake. “Ki nutsu wannan dama ce da ba kowa Allah ke bashi ba, abin alfahari ne ko da baki nasara ba ace kina cikin jerin ÆŠaliban da suka shiga, Nijeriya yanzu ke ya zubawa idanu, jikarki, unguwarku, Malaminki, mahaifinki ke ce hope É—in su, sun yarda dake don haka ki basu mamaki” Majeederh ta yi shiru ta ce “Ina tsoran rashin nasara” Wani dake zaune ya ce “Good, than sai ki miÆ™e ki tashi tsaye ki saka yaÆ™ini sai Ubangiji ya tabbatar, kuma sai nan da wata biyar za ayi kafin nan kin samu hurarwa” Ta Æ™ara yin shiru tabbas dama ce a gare ta ta bawa Abbu abin da yake buÆ™ata.
“Zan yi” Suka sauke ajjiyar zuciya kana suka sanya mata albarka ta miÆ™e a hankali ta fice Ajlaal ya É—an saci kallonta yana É—auke ido.
Tun daga ranar Majeederh bata da lokacin kanta, manyan malamai suka sanyata a gaba, karatu safe, rana, dare. Daman tuni haddar Alkur’ani sittin É—in suna zaune a kanta daram, Tajwid da mukarijin hurum ake tisa mata, da saita Æ™ira’a daman Ubangiji ya bata murya kamar haihuwar Larabawa. Ya zamana a tsaye bacci take sbd karatu, Ƙhulud Arzaan ganin Majeederh ya yi mata wahala idan tana bita da rigima Ajlaal baya ce mata kanzil. Majeederh ta goge harsu malaman mamaki kawai suke idan tana karatu, hakan ya Æ™ara sa musu hope mai girma akanta…

*5 Month later….. The day*
Ranar MusabaÆ™ar Alkur’ani ta Æ™asa ya tashi ranar watan tafiyar alhazzai, watan zul-hajj. Tun ana sati É—aya gabaÉ—aya ÆŠaliban ko wacce Æ™asa ta Muslunci suka sauka a Æ™asar Misira, daga nan kuma manyan mutane, shugaban Æ™asar ko wacce Æ™asa, da gwamnoni, hatta Sarkin Saudiyya Sarki Sultaan ya halaccin Misira ana kwana É—aya da shi da Mahaifiyarsa Zaytoon, hadda. Babban hall É—in ya cika da jama’a fal, Æ™abila da yare daban daban farar fata da É“aka, jami’an tsaro kamar me. Saura minti ashirin a fara ÆŠaliban duk suka shigo ko wanne da tambarin Æ™asar shi a jikinsa, kowa aka nuna masa wajan zama kana zama computer zata nuna sunanka da kuma Æ™asar da kake, gabaÉ—aya kuma ya kasance mata ke namiji É—aya ne daga Qatar. Majeederh kanta a Æ™asa sbd jiri da faÉ—uwar gaban dake riskarta na rashin sanin su waye a wajan. Zagaye biyar ne masu zafi, da kayi kuskure Computer zata tsayar da kai. Aka fara da Æ™asar Saudiyya ta tayi karatu yadda ya kamata, a zagaye na huÉ—u dana biyar ta samu matsala. Abun kamar abin mamaki Majeederh ce ta zamo ta Æ™arshe ma’ana Nigeria, Computer ta nuna mata farkon shafin suratul Yusuf, kana malamin ya ja.
Kanta a Æ™asa ba tayi kuskuren É—ago kan ba, lokacin da tayi Basmala shiru wajan ya É—auka ya zamana kamar ba a ji Æ™ira’ar kowa ba sai nata, sbd zaÆ™i da sautin muryarta daya zaga ko’ina na hall É—in, a tare Sarki Sultaan da Zaytoon suka É—ago kan su, tare da kallon inda Majeederh take zaune fuska rufe, Zaytoon ya dubi computer gaban Majeed taga ansa. _“Majeederh Abdul’aziz Khan, from Nigeria”_ Karatu take mai É—auke da zallar Æ™a’idoji na Kur’ani. Tunda ta fara karatun idanunsa akanta ya kafeta da wani irin rikitaccen kallo yana mamakin yadda a Æ™asar su Nigeria aka samu mai daÉ—in murya da ilimi kamar Majeederh. Tunda ta fara karatun babu gyara ko tuni, waÆ™afi, aya ko wasali har zuwa zagayen Æ™arshe. Computer ta nuna mata Suratul Maryam tsakiyar surah. Cikin rashin sa a ta É—ago kanta da nufin sauke numfashi nan take komai nata ya kunce dalilin ganin dubban jama’ar da suke gabanta tare da kallonta suna kuma saurarenta. Ai gabaÉ—aya neman duk haddar Alkur’anin dake kanta tayi ta rasa kaf, a tare kuma Aliyu-haydar, Captain Alpha, Prince Ajlaal Sultaan da wani matashi dake kusa da Gwamnan jihar Kano suka ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!….

No comments