Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 35


No Edited
Zamu fara page biyu kullum, biyu a arewabooks É—aya a WhatsApp group邏……. MIJIN MALAMA it’s a paid book Subscribe before you read….. Via WhatsApp for more information 08119237616Zame hannunsa ya yi yana É—an kame fuskarsa a hankali kamar bai son magana ya ce “Remove the vail” Ta yi saurin É—ago kanta zata kallesa amma ta kasa ya yi mata wani irin bala’in kwarjini, ta kasa cewa komai ta kasa aikata abin da ta yi niyya. Ajlaal ya tsuke tamau yau sai ya ga abinda ya turewa buzu naÉ—i. Bakinta na rawa ta ce “Baa…ba…baaaa!” Ta kasa furta abinda tayi niyya kaifin idanunsa sosai ya tasirin a kanta a hannun ta ce “Am sorry i can’t do that” Ta faÉ—a tana Æ™oÆ™arin barin bakin bedroom É—in nasa, wanda ta turje taÆ™i yarda ta shiga domin ta san sirrinsa ne. “Fita” Ya nuna mata hanyar fita tun kafin ta nufi hanyar ai kamar zata kifa duk da girman jan ajinta haka tayi waje, zata gilma ta gabansa ya sanya hannunsa mai taushi ya fizgota ta dawo gabansa, kai tsaye kuma fuskarta ya nufa da hannunsa He tried to lift the mask off her face. Duk jikin Majeederh rawa yake nan da nan ta ruÉ—e ta marairaice ita bata taÉ“a ganin rashin kunya haka ba, daman larabawa ba wani ta ido gare su, gashi ba zata iya yi masa rashin kunya ba, ta rirriÆ™e shi ta ce “Please don’t”
“Ohh!” Ya furta yana riÆ™e hannunta gam, sai ka rantse ba Mai martaba bane, ganin da gaske yake ya sa ta ce “Please Mai martaba” Nan ma ya yi mata banza aikowa ta daddage ta sakar masa cizo a hannu da sauri ya saketa yana faÉ—in “Auchhhii” Ta re da É—an lumshe idanu sai kuma ya buÉ—e, suna haÉ—a idanu ya zaro mata manyan idanunsa ta kwasa da gudu ta nufi Æ™ofa ya yi saurin shafa kansa tare da nufar bedroom É—insa. Tun kafin ya Æ™arasa ya ji muryar Ƙhulud na faÉ—in “Ya na ganki tsaye?” Ita dai Majeederh ba ta yi magana ba, Ƙhulud ta É—an yi shiru sai kuma ta ce “To wannan hakin kamar kin yi tsere na zaki fa?” Sai a lokacin Majeederh ta É—an sauke numfashi tana kame kanta ta ce “Zan ta fi”
“Baki isa ba, sai mun yi lunch tare, Mai martaba bai faÉ—a miki ba?” Ganin Majeederh ta Æ™i cewa komai ya sa Ƙhulud kallonta frm head to toe,She wants to understand Majeederh’s situation but she can’t understand anything. Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce “Ba dai miskilancin naki kika gwadawa mijina ba?” Majeederh ta harareta ta ce “The train at six o’clock in the evening will drop me off, I don’t want to miss the train” Ƙhulud ta ce “Ki rasa mana, sai a Æ™ara neman wani” Kafin Majeederh ta ce komai Ƙhulud’s ta shige haÉ—aÉ—É—an Bedroom É—in Mai martaba Ajlaal Sultaan, komai na bedroom É—in white colour ne, the furniture, bedsheet, Curtain, everything da ake zubawa a bedroom ba É—akin Ajlaal fari ne, ga wani irin Æ™amshi mai sanyi dake tashi. Ƙhulud tayi tsaye tana kallonsa ya fito daga toilet yana tsane ruwa akansa ta ce “Ba dai wanka kayi ba?” Shi dai bai ce komai ba, har ya nemi saman kujerar dake kusa da tafkekekn royal bed É—insa ya lumshe idanunsa tare da riÆ™e kansa da hannu bibbiyu, Fulani Ƙhulud ta Æ™arasa kusa da shi tare da zama a hankali ta leÆ™a fuskarshi suka haÉ—a idanunsa taga idanunsa jajur “Takawa lafiya kake?” Ya yi shiru sai kallonta da yake tasan kuma ba magana zai yi ba ta Æ™ara da cewa “Kun gaisa da Malama Majeederh?” Sai a lokacin ya É—auke yana miÆ™ewa tsaye tare da nufar wajan mirror ta ce “Ran Takawa ya daÉ—e ina ta magana?” A hankali cikin kasala ya ce “Wa fa?” Ta ce “Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, baka ganta ba?” Yana nufa wajan clothes É—insa ya ce “Gaskiya, bamu ga kowa ba nan ta zo?” Ta ce “Wai da gaske naga har tsakiyar parlour fa ta shigo, daman Majeederh É“oyewa ta yi haka last time kuka mini fa ku baku san zumunci?” Shi dai bai ce komai ba ta ce “Ina nan saka kaya kawai ka fito” jin haka yasa ya fasa É—aukar Jallabiyar da zai saka ya dawo kusa da ita ya zauna yana É—an turÉ“une fuska ya ce “Haka zamu zauna” Ta gwalo ido ta ce “Ba kaya?” Ya jinjina mata kai kafin tayi magana ya sunkuceta sai zuwa other bedroom É—in nasa dana zare idanu ta ce “Ajlaal cikina ya tsofa please ka rufa mini asiri” Ya direta yana binta da wani irin kallo kallo É—aya tayi masa tasan ba zai ji roÆ™an ba ya ce “Me?”
“Nothing” Nan da nan Mai martaba Ajlaal Sultaan ya sanya Ƙhulud yin baccin dole ya shirya cikin wata golden É—in Alkyabba mai masifar kyau da É—aukan idanu yana fidda Æ™amshin LONG BOARD. Wayarsa daya daÉ—e bai É—auka ba ya É—auka tare da kiran wani Digits, a nutse cikin izza da gadara ya ce “Follow her” Yana faÉ—in hakan ya kashe kiran ya juya ya tsorawa fuskar matarsa Ƙhulud da kallo sai kuma ya É—an shafa kai ya ce “Harnarn”…….. Majeederh ce tsaye tana kallon kanta a madubi ganin irin sauyin da tayi, tana mamakin yadda take zama tamkar wahainiya, yau Æ™irjinta ya cika sosai gobe kuma taga ya koma yadda yake, duk da irin ciwon idanun dake damunta wanda ta same shi sanadin nacin karatu a Egypt, bai hana nuna asalin zubi da tsarin halittar Æ™wayar Idanunta, duk inda ake neman cikakkiyar mace wayayyiya, mai hankali nutsuwa sanin ya kamata, educated one za a sanyata a ciki, duk inda ake neman mai ma tsarin diri na É—aukan hankalin É—a namiji nan take dole ka sanya Majeederh, takai ta cika bata buÆ™atar a rayuwar yanzu wanda ya shige ta ganta a É—akin mijinta, when? Sai kawai ta É—an yi murmushin takaici a fili ta ce “Bani da rabo ba” Ta sauke liÆ™ab É—in tare da jan trolley É—inta zuwa waje, ta shiga mota suka nufi airport, tana zuwa ta samu an fara shiga saura few minutes ya rage jirgin ya tashi, ta shiga ta zauna a mazauninta tana mai sauke numfashi bata jin daÉ—in komai, dauriya kawai take da nuna jarumtarta a fili. Tunda ta shigo Jirgin idanunsa yake kanta, bai É—auka zai sake ganinta sbd tun a hall É—in musabaÆ™ar ya nemeta ya rasa, muryarta kawai tabar masa wacce take masa amsa kuwwa a cikin kunne! Duk wani juyi da harabar daÆ™iÆ™o zuwa sakanni, da juyewarsu zuwa mintuna har kawo su zama awa guda basa taÉ“a tafiya ba tare da amon muryarta ba da bugun zuciyarsa, jin muryar a cikin lokaci É—aya ta wargatsa masa lissafin shekarun da ya yi na bayyana ta mantar da shi ainahin abinda ya kawo shi Saudiyya. Ganin kamar zata buÉ—e idanu ya sanya ya É—auke kai yana mai da dubansa ga Hammad dake masa magana Æ™asa Æ™asa amma baya ji, tunaninsa ya yi Æ™aura daga masarrafar dake sarrafa nutsuwarsa ta Æ™waÆ™walwa… Hammad ya ce “Meke damunka wai?” Ya haÉ—e fuska ya ce “Da aka yi me?” Hammad ya yi shiru sai kuma ya ce “Tun jiya da muka bar hall É—in nan naga sauyi a tare da kai, babu shiru kasa muka shirya dawowa Naija wai meke faruwa?”
Abuturab ya É—ago kansa baki É—aya ya zubawa Hammad ya ce “Stop Interrupt!” Hammad ya ce “Oh tambayar ya kake shi ne Æ™atsalandan?” Abuturab ya haÉ—e fuska ya ce “Ban so”
“To Ubana, wallahi sai na tambaya ai kasan ba ishasshiyar lafiya gareka ba, yanzu idan ka mace mini a nan ai na shiga uku wajan Maysoon” Annurin fuskar Abuturab ya É—auke nan da nan, ya kasa cewa komai a hankali kuma ya juya ya Æ™ara kallon direction É—in da take zaune, yana mmkin yadda tunda ta zauna ba tayi motsin kirki ba. Ana haka jirgin ya fara juyawa a Æ™asan kwalta kafin a hankali ya shila sama cikin sararin samaniya…. Mai martaba Ajlaal Sultaan ya sauke numfashi yana jin zufa na karyo masa all over himself, ya Æ™ara fitar da wani irin É“oyayyan nunfashi a nutse ya É—aga kai ya dubi yadda jirgin ke nutsuwa cikin gajimare can Æ™asan maÆ™oshi ya ce “Nigeria” faÉ—in kalamar Nigeria sai ya ji nan da nan ransa ya É“aci kansa a shiga sarawa da sauri ya ce “Palace please”
Misalin 10:7 jirkinsu ya sauka a airport É—in Malam Aminu Kano, a hankali suka dinga fitowa, can ta ta fara tako steps É—in jirgin hannunta É—auke da trolley, idanunta rufe tana shaÆ™ar iskar dake kaÉ—awa, idanunta kuma ta buÉ—e sosai a harabar wajan bayan ta fito daga can wajan da akai iyaka da jirgi mmki ya ishe ta babu wanda ya zo da sunan tafiya da ita, Ya Allah wacce irin rayuwa take ciki me ya sa kowa ya juya mata baya a dangi sbd kawai ba tayi aure ba? Ta duba haÉ—aÉ—É—an agogon hannunta taga dare ya yi ta nufi tafiya daga bayanta ta ji an ce “Hawwa’u” Ta yi cak ba tare data juya ya Æ™ara so cikin nutsuwarsa ya tsaya gabanta yana zuba mata Idanu ya ce “Ba sai saukarki kenan ba?” Ta É—an kallesa tana kame kanta fuska haÉ—e duk da ba ganinta yake ba ta ce “In sha Allah” Aliyu ya shafa kai ya ce “Oh wlcm, na yi dropping Papa ne zai je Brazil” Ta jinjina kanta ya ce
“Can i help you? By dropping off?” Ta É—an yi shiru sai kuma taja trolley nata zuwa gaba ya yi saurin shan gabanta ya ce “Please Malama Majeederh, it’s my responsibility to do that” A É—an taÆ™aice ta ce “No thank you” Ya marairaice ya ce “Don Allah, ki yi mini alfarmar nan” Bata da wani option daya shige shiga motar ta shi…. Tunda ya fara driving ta rufe Idanunta ta samu kanta da faÉ—uwar gaba sun jima suna tafiya ta ji ya tsaya bai daÉ—e ba ya dawo hannunsa riÆ™e da leader alamar takeaway.
“Sorry, Yunwa nake ji sosai kamar n ci babu tun safe da na ci abinci a wani restaurant” Sai a lokacin ta masa Æ´ar duguwar magana ta hanyar faÉ—in “Restaurant? Da aurenka? Akwai adalci ga Latifa anya?” Aliyu ya dai kalleta sai kawai ya girgiza ya ce “Bata jin daÉ—i, shi ne nayi takeaway” Ta ce “Allah ya sauwaÆ™a” Parking Aliyu ya yi a Æ™ofar gidansa bayan ya kashe motar ya fito yana zube hannu a aljihu wani irin baiwar kyau Ubangiji ya zubawa Aliyu, domin ko Ajlaal sai dai ya nuna mana hasken fata da suma mai yawa da kuma launin idanu, gashi da wani irin haÆ™uri da kawaici amma idan ransa ya É“aci kamar Mahaukaci haka yake yana da Æ™ulafuci da saka abu a rai. Ya ce “Kamar an rufe gidan ko?” Ta yi masa shiru yana mmkin yadda Majeederh ke feeling kanta da yawa, tsayin shekaru bai taÉ“a ganin munafukar fuskar da ake rufewa ba. Jin shiru ta É—ago kai suka haÉ—a idanu ta kame fuska tana jan jakarta zuwa hanyar gate domin tuni gatekeeper ya buÉ—e tana jinsa yana magana amma ta yi shiru a gareta haramci ne babba da É—aukar Æ™aton zunubi ga yin magana da namiji baligi sai ya zama dole. Tana shiga cikin gidan taga Abbu tsaye a Balcony ta zube har Æ™asa ta gaishesa ya amsa a wannan karan ta yi mamaki da ya ce mata “Congratulations” Ta nufi cikin gidan tana shiga Aaliyah ta rungumeta tana ihun murnar ganinta, Majeederh ta cire liÆ™ab É—inta bayan ta tsuguna ta ce “Barka da dare Mami” “Yawwa” Ta ce tana binta da ido, Raihana ta ce “Allah mai iko! Ana ta shiga rigar Muslunci ana ci da addini” Aaliyah ta kalleta ta ce “Idan fitsari banza ne kaza ma ta yi mana” Raihana ta watsa mata harara tana cewa.
“Ji saÆ™arya, ana maganar kan giwa wake jiyo Æ™amshin zomo? Mai da wuÆ™ar ni ba tsararki ba ce” Aaliyyah ta riÆ™e haÉ“a ta ce “Hooo Æ™aasa, to aini walkice daidai da Æ™ugun ko wanne lalatacce, kuma Majeederh kuturwa uwa ce zama da ita dole murucin kan dutse bai fito ba sai daya shirya” Raihana taja tsaki ta ce “To ai ga sararin subuhana É—in nan, sai a zuba muga idan za a kwashe daidai, ba girin girin ba ta yi mai” Majeederh dai ikon Allah kawai take kallo domin ita bata ma iya karin magana da habaici ba shi yasa ta rasa fahimtar me suke cewa, Mami na zaune watching all of them. Aaliyyah ta saki dariya ta ce “Ai gurbin idon ba idanun bane, ni masallacin kurawa ce bawa kare limanci daidai yake da datse iskar dake shaÆ™a, kiyi a hankali domin na kawo kai nasan fari na san baÆ™i kada ki ja nayi miki wankin babban bargo, domin naga fahimtar ki daidai yake da fahimtar yaron goye, bana son kuma ya kasance duk kun far bakinki kiyi haihuwar guzuma” Raihana ta ce “Me kike nufi da haihuwar Guzuma? An faÉ—a an Æ™ara faÉ—a idan Majeederh tayi zuciya gobe muji loud speaker Liman na sanar da É—aurin aurenta, waye bai san cewa Majeederh ba auren ne a gabanta ba? Office É—in data buÉ—e na mene? Gari gari da take zuwa da sunan kaiwa marayu taimako bayan Æ™arya ne na mene? Ke yarinya wahainiyarki ta kiyayi ramata, ta dauwama ba tayi aure ba har Mahadi ya bayyana” Aaliyyah idanunta a cicciko da hawaye ta ce “Bar gaigaye za kici tumu ne, Æ™addara zane gwara ita tata Æ™addarar ya fito sarari mun gani, kuma komai ya yi farko zai yi Æ™arshe” Ruma ce ta fito daga É—aki ta ce “Kaza uwar tune tune mene ya faru kuma?” Kafin Aaliyah tayi magana Abbu ya shigo gabaÉ—aya suka nutsu ya dinga binsu da kallo kafin ya ce “Kun kyauta, ko wacce ta fice mini daga cikin gida” Raihana ta ce “Abbu ka yi haÆ™uri baya nan fa, gidan shiru tsoro nake ji” A fusace ya ce “Ya kashe ki, kuzo ku fi ce mini” Jiki na rawa suka É—auki mayafi da handbags É—in su ya ce “Shashai, ku dinga faÉ—a kamar ba jini É—aya ba zan yi maganin ko wannenku kada É—an banzan yada dake dawo mini gida” Ya juya kan Aaliyyah ya ce “Dage, basu girmeki ba?” Ta ce “Kayi haÆ™uri Abbu Anti Jeederh sukewa gorin aure hadda sharri” Ya kalleta ya ce “To kashin awakai, ita Majeederh Ubangiji bai bata baki bane? Sai ke rasai? Ba ita ta sake musu ba da tana cin ubansu tun farko za ayi haka?” Mami ta dinga kallon Abbu sai bata ce komai ba, ya dawo kanta ya ce “Asabe kin kyauta,na kuma gode” Ya kalli Majeederh ya ce “Da safe ki same ni”….. Washegari da safe bayan Majeederh ta shirya cikin wata tsadaddiyyar Abaya Marron irin turkies Abaya É—in nan ta samu Abbu a parlourn shi yana zaune ya yi shiru bayan sun gaisa ta ce “Abbu gani” Ya ce “Hawwa’u, Hawwa’u, Hawwa’u” Ya yi pointing nata ya ce “Sau nawa na kira sunanki?” Ta ce “Uku Abbu” Ya jinjina kai ya ce “To wallahi Allah na gaji da ganinki a gidan nan” Da wani irin Shock take kallon Mahaifinta tashin hankali ya bayyana akan fuskarta tsoro da wasa fargabar Abinda zai biyo baya ya wanzu a zuciyarta Abbu ya ce “Shekararki 31 a duniya kina gantali,duk sha’aninki suna gidan mijinsu harda yara uku wasu huÉ—u amma ke kina yawon neman abin duniya? Yaran da aka tsuguna aka haifa akan idanunki duk suna É—akin mazajan su banda ke, kina jerawa da Majaufiarki kamar sa’arki? Ka kaf Family ke É—aya ya rage idan kika É—auke Aaliyyah da Sona? Wallahi wallahi idan ina ganinki a gidan nan zuciyata zafi take daurewa kawai nake idan kuma na ci-gaba da ganinki tabbas zuciyata bugawa za ta yi sbd baÆ™in cikin ki……

Littafina na kuÉ—i ne, biya ki karanta cikin kwanciyar hankali da salama da fitar da hakÆ™ina…….

No comments