Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 34


Na’ima Shu’aibu Sulaiman fidelity bank….. Kindly send your evidence via 08119237616 Book 1 and 2 1k.

Naso yin typing É—in ya fi haka yau Sadakar Bakwan rasuwar da akai mini Mu haÉ—u weekend a arewabooks.*_Huhuu! To bance komai ba, amma ya kuke yaÆ™in neman MIJIN MALAMA Don’t you know cewa na kuÉ—i ne? Mata masu fama da Jinkirin aure wannan littafin sadaukarwa ne a gareku邏….. A daina shelar neman Mijin Malama tunda akwai Mazan da yawa Allah kaÉ—ai yasan waye mijin Madam come and Subscribe before you read, meye wata Æ´ar 1k da zata muku wahala?…….. Chat me via WhatsApp 08119237616_*

Kasa bata amsa tayi saboda tashin hankali, ganin kowa ya yi shiru ya sa ta ce “Finally, ni ma na zama matar aure Allah na gode maka bisa wannan tarin Ni’imar da kayi mini, na Æ™ara yadda wani jinkirin alheri ni Anti, gashi yanzu Ubangiji ya bani nagartaccen miji” Majeederh ta yi murmushi tana goge hawayen farin ciki, duk wani zafi da Æ™unci ya kau a ranta, tabon dake cinta a zuciya ya hanata sukuni gabaÉ—aya ta neme shi ta rasa. Aurenta da Yayanta Alpha ya zama abu na farko wanda ba zata taÉ“a iya mantawa fashi ba.
Anti ta juya ta kalli Aaliyyah da Sona ta ce “We need privacy, ku je waje yanzu zan fito” Aaliyyah ta yi waje, Sona ma ta bi bayanta. Anti ta kalli Majeederh tana murmushi wanda bai kai zuciya ba ta ce “To Amarya” Kunyar Anti ta kamata, ta É—an yi Æ™asa da kanta a hankali Anti kamar kazar da Æ™wai ya fashewa ta ce “Ki je ki yi sallah, wanka,cin abinci we need to talk ok” Majeederh ta miÆ™e tsaye da sauri ta dafe gefen kanta “Sorry kan ne dai?” Anti ta tambaya tana riÆ™e kan nata, jijiyoyin kan duk sun fito sai har bawa suke idanunta jajir, ta Æ™ara yin murmushin Æ™arfin hali ta ce
“Abbu ma zai farin ciki ko Anti? Zai yi farin ciki yaga aurena, ni kuma zan aurar da Aaliyyerh” GabaÉ—aya Anti tunanin dake sarrafa Æ™waÆ™walwarta ne ya tsaya da aiki ta tsaya ta dinga kallon Majeederh da Æ™yar ta iya cewa “Ki je ina jiranki Majeederh” Ta nufi bathroom da Æ™yar ta yi wanka tare da sallolin dake kanta, Anti ta kawo mata wata atamfa Valisco milk da yafin blue a jiki, É—inkin duguwar riga Ashap. Majeederh ta dinga kallon kayan domin bata saba saka irin su ba, tina cewa ko wacce amarya irin kayan da take sakawa kenan sai bata ce komai ba, ta shirya tsaf tayi wani irin masifaffen kyau, kamar irin Fulanin Usul É—in nan ko na Daji ko kuma irin Half-caste É—in nan jinsan larabawa da yankin Niger na Agadas ko Sudawa. Idanunta zuru-zuru tayi muguwar rama kamar kuÉ—in guzuri, fuskarta kamar tafin hannu. “Anti na kira number Yaya a kashe fa? Zan yi masa godiya da aurena da ya yi” Anti ta kasa bata amsa ta juya da sauri tare da ficewa daga bathroom É—in ta nufi part É—in Uncle Isma’il lokacin yana zaune saman kujera yana waya, tana zuwa ta rushewa Uncle Isma’il da kuka tsabar firgici ya saki wayar hannun sa tare da miÆ™ewa jikinsa na rawa ya ce “Subuhanallah! Ƴar Aljanna ke dawa?” Anti ta dinga kuka jikinta har rawa yake kai kace Uncle Isma’il ne ya rasu, ko kuma an aiko mata da mutuwar mahaifinta daga Gombe.
Cikin kuka ta ce “Mun shiga Uku YallaÉ“ai, mun shiga uku Abban Jawaad” Uncle Isma’il ya ce “Ba mu shiga uku ba da izinin Allah, Ubangiji na tare damu” Ya saka hannu ya É—agota yana riÆ™e fuskarta ya ce “Majeederh ko?” Ta kasa magana sai kuka Uncle Isma’il ya rasa yadda zai rarrashi matar tasa ya kamo ya rungume ya ce “Haba bansan fulani da raguwar zuciya ba, haba jinin Gwambawa haba Æ´ar Bafullatanar matata uwar Æ´aÆ´ana kukanki azaba ne a zuciyata” Ya yi murmushi cikin dauriya ya ce “Akanki bulala nawa na shanye? Gwambawa sun gana mini azaba a haka na shanye shaÉ—in na aureki, mene ya kawo haka? Kinga juriya ce da yadda da Allah da Æ™arfin addu’a, ki zama jaruma kamar yadda na zama jarumi a soyayyarki ki yi haÆ™uri don Allah uwar Jawaad da Sona, garkuwar Du’a haba matar Isma’il amarya kuma uwar gida, idan baki jure ba ina zaki samu Æ™arfin qiwwar rarrashin Majeederh” Ya goge hawayen da suke bin idanunta tana shassheÆ™a ta ce “Na rasa yadda zan yi babu kalaman ban haÆ™uri ga Majeederh, wannan yaron ya cucemu he disappointed us” Uncle Isma’il ya ce “Da wannan salon yaudarar taki da kika sace zuciyar Isma’ila da shi zaki rarrasheta, komai na rayuwa yin Allah ne ba namu ba, bama da ikon hana komai ko faruwar shi take heart please” MiÆ™ewa tayi tana gyara É—aurin zaninta ta nufi part É—in da Majeederh take ciki. A zaune ta sameta idanunta rufe Æ™irjinta na É—agawa kamar wacce asthma É—in ta take shirin tashi, kafin ta Æ™arasa ta nufi wajan freezer ruwa ta É—auka mai sanyi ta tsiyaya a kofi ta ce “Drink”
“Azumi nake” Majeederh ta bata amsa, Anti ta ce “Ai kowa zaki karya azumin me?” Ta yi Æ™asa da kai ta ce “Nuna godiya ga Ubangiji” cewarta.
Anti ta nemi waje ta zauna tana bin bedroom É—in da kallo a hankali ta ce “Hawwa’u!”
“Na’am Anti” Ta amsa gabanta na faÉ—uwa haka kurum. Anti ta ce “Mece Æ™addara?” Da mamaki Majeederh ta kalli Anti sai kuma ta ce “Jarrabawa ce da Ubangiji yake jarabtar bawansa domin gwada imaninsa, shi ya sa aka ce yarda da Æ™addara shi ne cikin imanin ko wanne musulmi” Anti ta sauke ajjiyar zuciya ta ce
“Allahamdulillah” Wajan ya yi shiru can dai Anti ta Æ™ara kiran sunan Majeederh a wannan karam kasa amsawa tayi ta ce “Hawwa’u mace da ciki da ciki ta mutu, miji ya rasu ya bar matarsa da yaransa, uwa ta rasu tabar miji da yaranta, iyaye sun rasu sun bar yara, GabaÉ—aya hakan tsarin waye? TSARIN ALLAH, Ubangiji ke da ikon Æ™addara kuma shi ne wanda masarrafar rayuwarmu ke hannunsa, ya haliccemu domin bauta masa dayin biyya da iyaye duk mutumin da ya cika haka bazai taÉ“a tuzarta ba, Æ™addara shuÉ—aÉ—É—iyya ce, ba za’a taÉ“a hana zuciya Æ™untata ba, domin baka da ikon yin haka amma akwai mataki na kare kai, Majeederh ki yarda Allah ke tsara duk abinda zai faru, Mu so wanda ya ke son mu shi ne soyayya, mu so Mutum ya so me shi ne dacewa a soyayya, mun so abu babu damuwa maybe abin ya dace aso shi saboda nagartar da yake da ita, rasa abinda zuciyar mu ke so, bashi yake nufin rasa rayuwarmu ba, watakila rabonmu na ta wani wajan yana jiranmu, idan soyayya na gudunm Æ™auna ta har abada tana can wata duniya idanu rufe tana nemanmu, faÉ—uwa a soyayya nuni na cewa hakan ba alheri bane a ranmu, ba laifi bane don munyi kuka idan an yaudaremu, babbar asara ce ka komawa wanda ya guje ka ko ya yaudareka, hakan na alÆ™inta mana mun rasa wani abu a baya inma mu rayuwa inma mutum mu rayu da sanin Ubangiji ke zana komai cikin tsaftaccen allon lauhil mahfuz, yi kuka Majeederh akan farin ciki kada ki yi kuka akan baÆ™in ciki….” Anti ta yi shiru kana a hankali cikin rauni tausayi da fargaba ta ce “Ba a É—aura aurenki da Alpha ba, domin ya gudu bisa ra’ayinsa na Æ™in auren wanda Ubangiji ne kaÉ—ai ya san dalili” Da wani irin Expression Majeederh take kallon Anti, kallon da sai da hantar cikinta ta motsa, gabanta ta faÉ—i domin bata taÉ“a ganin rikiÉ—ewar idanu lokaci É—aya irin na Majeederh ba, Æ™arar tsayawar abu a wuyan Majeederh yasa Anti taÉ“ata ta ce “Majeederh ki yi haÆ™uri ki yi haÆ™uri, ban san yaushe ne hakan ta faru ba, ban san mene ya sauyawa Alpha ra’ayi ba, amma nasan yana son ki ina ganin hakan acikin idanunsa, rabonki yana wani tsagin rabo mai girma rabon da zai bawa kowa mamaki,ki yi haÆ™uri da rayuwa Majeederh” Maimakon kuka sai taga Majeederh ta saki Murmushi, murmushi mai kyau wanda bata taÉ“a ganin irinsa a fuskarta ba, irin wanda dashi gwara kayi kuka irin sa yafi kuka ciwo a zuciya hakan na nufin Mutum yana cikin halin da kuka ya yi masa kaÉ—an. Ta miÆ™e tsaye ta ce “Zani gida”
“Majeederh are you okay?” Ta ce “In sha Allah” A hankali ta ce “Kiyi haÆ™uri ki miÆ™a lamuranki ga Ubangiji please” Ta Æ™ara yin murmushi ta ce “Ba komai, bani hijabi da liÆ™ab É—in Sona” Ba zata iya tsayar da ita ba, akan Idanunta ta saka hijabin da liÆ™ab É—in tare da amsar kuÉ—in napep wajan Anti ganin haka yasa Anti Æ™walawa Aaliyyah kira ta ce “Maza jeki ku tafi akwai matsala” Jefa Æ™afafuwanta kawai take without knowing ina take takawa, da gudu kuma Aaliyyah ta cimmata ta tsare mai napep ta ce masa Lodge Road….. Misalin 8 na dare wani irin ciwon kai ya kama Majeederh har bata iya gani sosai ga jiri da Æ™yar ta miÆ™e ta nufi part É—in Abbu da yake kiranta tana zuwa ta zube a Æ™asa wajan Æ™afafuwansa ta kasa cewa komai. Ya dubeta ya ce “Kin kyauta”
Da sauri ta kalle shi tana son tambayar mai tayi sai kuma tayi sbd nauyin da harshenta ya yi mata wanda ya tilasta mata kame bakin. Ya gyara zama da kyau ya ce “Kin tuzartani cikin dangi Majeederh,kin kunyatani kin cin mutuncin shekaruna, akan namiji? Yanzu me gari ya waya? Kin barwa kanki abin gori kin bar mini nima koma babu komai tarihi zai kafo akan Alpha ya gudu saboda baya Æ™aunar aurenki” Ya girgiza kai ya ce “Majeederh kin yarda ni mahaifin ne?” Da sauri ta ce “Wallahi Abbu ban taÉ“a kokwanto hakan ba” Ya miÆ™e tsaye tare da É—akko Alkur’ani mai girma daman yana da alwala ya É—ora hannunsa akan Alqur’ani izzu sittin ya ce “Wallahi wallahi Allah Majeederh ni ne ubanki mahaifinki, wanda jinina ke yawo a jijiyoyinki, na rantse da Allah ni ne mahaifinki ni Alhaji Abdul’aziz Khan” Ta dinga girgiza kai babu hawaye ko É—aya a Idanunta ta ce “Don Allah Abbu ka bari” Ya kalleta ya ce “Amma ni ina tunanin kamar an sauya mini É—iyata, kamar ke É—in ba Majeederh ta bace”A rikice ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, Ya Allah wallahi bana gane komai ko fahimta” Ya zauna ya ce “Kin kasa bani abinda nake so nake buri Majeederh, na rasa yadda zan yi dake kin kasa rufa mini asiri, Hawwa’u aure fa ba dole bane tunda zaki iya riÆ™e kanki, kuma ni na san jinkiri ne kawai kika mijinki nan zuwa ki taimaka mini, ni mahaifinki ne” Majeederh ta ce “Ka yafe mini, ba sake cewa ina son kowa ba shi na don Yayana ne ai kaga ma bai aurenin ba shikenan sai na fara neman aiki” Abbu ya saki kuka wiwi yana cewa “FaÉ—a kawai kike Majeederh ki je kawai nama haÆ™ura kiyi aurenki kawai kuma na yafe” A rikice, rikicewar da ko sanda aka faÉ—a mata Alpha ya gudu ya fasa aurenta ba ta yi ba ta riÆ™e Æ™afar Abbu ta ce
“Nayi asara Abbu, rayuwata ta halaka na shiga uku akaina kake zubar da hawaye mai yasa zaka ja mini azabar Ubangiji Abbu Innalillahi wa’inna ilahir raji’un Abbu kuka kake a kaina??” Ganin yadda halinta ya tashi Æ™arara yasa ya Æ™ara rushewa da kuka tashin hankali ya bayyana akan Majeederh amma ko É—ison hawaye babu a fuskarta zuciyarta ta Æ™afe ta ce “Na tuba, wallahi na tuba gobe zan nemi aiki zan fara nayi maka al’Æ™awarin wadataka da abinda kake so iya kacin iyawata, za ka yi alfahari dani Addu’arka da albarka ka nake nema kawai” Ya share waye ya ce “Da gaske zaki aikin?” Ta ce “Na yi alÆ™awari” Ya sauke É“oyayyiyar ajjiyar zuciya ya ce “Kin cika Æ´a, na gode Æ™warai Allah ya yi miki Albarka” Ta miÆ™e da Æ™yar zata fita ya ce “Ga mata nan da yawa na garari duka babu aure, shi fa auren nan lokaci ne kiyi ta azumi” A wannan lokacin bata fahimtar komai, dishi dishi take gani ga jiri ga kuma haki da Æ™yar ta lalubi hanya ta nufi part É—in tana ta faÉ—i wanwarsa a tsakiyar É—akin babu numfashi….. Bayan kwana bakwai da faruwar komai Latifa na driving fitowar su kenan daga B.u.k sun shiga duba wani ita da Majeederh, ganin ta É—auke hanya ya sanya Majeederh É—ago kai a hankali tare da zubawa titin idanun sai dai bata ce komai ba, ta maida idanunta ta rufe mamakinta kuma bai shige ganin yadda Latifa take wani Mahaukacin driving ba. A hankali ta ce “Kee” Murmushi kawai Latifa ta yi cikin sauri ta ce “Ina da hankali ba kashe mu zan ba, nasan adadin giyar dana saka ban shige limit ba” Ta juya ta kalli Majeederh suka haÉ—a idanu ta É—aga mata gira ta ce
“Afuwa Malamarmu zan shiga Tahir Quest Palace ne” A gajarce Majeederh ta ce “Hotel?” Latifa ta ce “Eh, Abu zan amsa ai” Majeederh ta yi shiru tana tunani me zai sanya ita kowa ta shiga hotel? Ai hakan babban zunubi ne, kayi ta ganin kartin maza ba zata iya wannan mummunan saÉ“on ba. Bata ce komai suna zuwa gate É—in shiga Majeederh ta ce “Wait”
“Like how? Kamarya na tsaya?” Ta ya motsa fuska ta cikin liÆ™ab ta ce “Amai nake ji” Jin hakan yasa Latifa tsayawa Majeederh ta fito da Æ™afafuwanta daga cikin motar tana fitowa ta ce “Shiga,ki saman nan” Girgiza kai kawai Latifa ta yi taja motar a 150 ta shige cikin Hotel…. Tana tsaye bakin Hotel É—in ta ji an ce “Malama Majeederh me kike a nan?” Da sauri ta É—ago kanta ganin É—an unguwarsu yasa tayi saurin jan jikinta baya daidai nan mai napep ya tsaya ta shiga, saurayin ya dinga mamakin ganinta a bakin hotel. Har sama da awa guda Latifa bata fito ba, can sai ga motar ta ganin babu Majeederh ya sanya ta kirata a waya ta ce “Kina ina ne?” A taÆ™aice ta ce “Gida”
“Gida kuma? Au tafiya ki kai” Ta ce “Kamar uzurinki babba ne, ni kuma ina jina Uncomfortable a wajan” Kafin ta yi magana Majeederh ta kashe wayar. Lokacin da Latifa ta isa gida ta samu Aliyu tsaye a balcony sanye da wata farar singlet sai gajeren wando hannunsa riÆ™e da coke yana sha, kallo É—aya ya yi mata ya É—auke kai, ta Æ™arasa inda yake tana murmushi ta ce “Sweetheart harka dawo?” Bai ce komai ba. Ta saka hannu ta karÉ“e coke É—in hannunsa tana sha ta ce “Am sorry”
“For…?” Aliyu ya tambaya yana zuba mata narkakkun idanunsa. A hankali ta ce “Da daÉ—ewa, na raka Majeederh meeting ne a Tahir Quest Palace” Ya dinga kallonta sai kuma ya ce “Ohk” ta zauna a cinyarsa ta ce “Me kake yi kai É—aya?” Ya haÉ—e fuska sosai ya ce “ÆŠaga ni” Ta É—aga shi ya dinga kallonta up to toe kana ya ce “Exlty, tun jiya kayan nan ke jinki kenan baki wanka ba?” Ta yi shiru ya miÆ™e tsaye tare bi ta gefenta ya shige ciki, yana zuwa ya haura sama not too long ya fito cikin tattausan voyel fari tas sumarsa kwance luf hannunsa zube cikin Aljihu ganinsa haka ta ce “Ina zaka?” Ya dinga kallon parlourn kamar na mahaukata sai warin yawu yake, Aliyu ya rasa me ma zai ce can ya ce “Ki tabbatar kin gyara gidan nan, Hajia na hanya” Yana faÉ—in hakan ya fice, ya É—auki good 20 minutes kafin ya shigo yana fitowa daga mota ya nufi cikin gida, yadda yabar parlourn tun jiya haka yake ya ajiye takeaway É—in hannunsa cikin É“acin rai ya nufi bedroom É—inta yana toshe hanci, ganinta ya yi durÆ™oshe jini na zuba ta Æ™asanta a rikice ya nufeta yana faÉ—in “Wife lafiya badai cikin ne ya sake zubewa ba?” Cikin mawuyacin hali ta ce “Aliyu shikenan yanzu ma mun rasa shi, na rasa babyna Aliyu cikin ya zube” GabaÉ—aya Aliyu ya rikice tashi Æ™addarar kenan ya ce “Taya kika san ya zube? Wife kada ki tarwatsa mini zuciya” Da Æ™yar ta ce “Wallahi ya zube” Bai magana ba ya sunkuceta zuwa mota, suna zuwa likita ya tabbatar ya zube Aliyu har kuka ya yi domin wannan shi ne karo na uku…. Majeederh na zaune tana shigar da bayananta domin ta samu offer a B.u.k za tana koyarwa, da kuma gidan t.v akan yiwa mata wa’azi musamman da Ramadan ke gabatuwa. Mami ce ta fito fuskarta É—auke da murmushi ta ce “Yawwa Majeederh shirya yanzu ki je gidan Amani Æ´ar wajan Hajiya Nusaiberh haihu tayi kuma babu wanda zai zauna mata” Majeederh ta kalli Mami ta ce “Mami kuma ni zan zauna mata? Ina cewa ko Aaliyyah ta girmi yarinuaty? Ina Hajja? Kakar Amani É—in?” Mami ta ce “Hajja tana Gombe, yayyun Amani kuma duka aure ne da su Kinga ai ba a ce suzo ba suna gidan mazajen su, Su Raihana ma haka, za a Turo Hajja na ce kawai ta zauna ke kyaci tunda kina zaune gida ke ba aure ba, ki je kiyi mata arba’in É—an wanki da abincinta dana mijinta” Majeederh ta kasa cewa komai ga biyya da take da ita bisa dole ta shirya ta nufi Badalawa…. Daddare Majeederh ta gama abinci tsaf tana zaune a parlour Amani ta ce “Allah sarki ashe Alpha guduwa ya yi wai za a Æ™aÆ™aba masa ke kuma baya so? Haka Raihana ta ce mini, ni dai don Allah ba ruwanki da mijina daya dawo ki shige bedroom kawai haka kurum yadda mata suke kwantai ki aure mini miji na shiga uku” Majeederh dai ta yi shiru Amani ta ce “Kema dai Æ™uruciya ke damunki ina ke ina Alpha? Yaran zamani kenan” Majeederh ta miÆ™e zuciyarta a Æ™un ta ce wai Æ™anwar Æ™anwarta take faÉ—a mata haka? Maybe Æ´ar cikinta da auren wuri ta yi…..Majeederh ta fara koyarwa a B.u.k kuÉ—i take samu sosai ta zama feminist É—in dole, a cikin shekarar Abbu ya je makka arziÆ™i ya ci uban nada, tsakanin Majeederh da kuÉ—i siyan suttura itama ba da yawa ba gudun kada Abbu ya ce ta kashe kuÉ—in….

After 3yrs*
Lokacin Majeederh nada shekaru 31 cif a duniya a lokacin ta Æ™ara cin ta Æ™ara cin gasar Alkur’ani ta duniya, Nigeria ta Æ™ara É—aukan award, kuÉ—in data samu ba zai faÉ—o ba, wannan karan a Saudiyya akai murmushi kwance a fuskarta ta tarawa Abbu dukiya tana tsaye riÆ™e da Award idanunta ya sauka akan wani Matashin ko magidanci da yake ta kallonta Without blinking his eyes sai ta ji ta tsargu ta shafa fuskarta ta jita a rufe ta sauke numfashi, tana Æ™oÆ™arin barin hall É—in musabaÆ™ar ta ji an ce “Tagawa lafiya Meke faruwa?” Ta sauri ta juya idanunta ya sauka akan kyakkyawar fuskarsa sai ya motsata yake kamar yaro ga wata ilhama dake kwance a kanta, ta Æ™ara ware idanu a ranta ta ce “Ƙhulud’s husband, Ajlaal?” GabaÉ—aya fadawa suka rufe shi ruf ganin sai zufa ce ke yanko masa jikinsa na wani irin É“ari “Sannu Tagawa, Allah ya Æ™arawa sarki lafiya” A ranta take Mamakin yaushe Ajlaal ya zama sarki? Kuma ta san sarkin Makka ai bai mutu ba, tana tsaye a wajan aka shigar dashi wata Æ™aramar mota mai azabar kyau aka nufi Palace da shi. Ta É—an taÉ“e baki ta nufi mota zuwa masauki domin a gobe zata koma Æ™asarta Nigeria tabar Saudiyya É—in, Majeederh ta zama kamar namiji sbd jajir cewa Æ™oÆ™ari da neman na kai, sai dai ba ruwanta da kowa magana sai ya zame dole ga bala’in ji da take a lokacin kuma gabaÉ—aya dangi kowa ya shiga yar bata da habaici babu aure sai gantali Anti ce kawai ke bata baki Uncle Isma’il ma ganin laifinta yake aka juya mata baya ko taro ta daina shiga……

Titin Government house cike yake da abun hawa an tara uban go-slow manyan mototci da Æ™anana, masu napep da barura hankalin kowa a tashe yake sbd ranar data Æ™walle, an kuma rasa abinda ya haddasa go-slow É—in… Abbu ya gyara zamansa a bayan mota yana jan tsaki ya ce “Nigeria ba zata sauya ba” Driver ya ce “Wallahi Alhaji kamar faÉ—a ake a tsakiyar titin ma” Abbu ya Æ™ara jan tsaki ya ce “Fita if there’s any way sai ka bi” Driver ya fita, cikin sauri yake kutsawa har ya Æ™arasu tsakiyar titin. Wata baÆ™ar mota ce lafiyayyiya daka gani ba a jima da siyanta ba, ita ta tare kan titin, sai wasu Æ´an matasa wajan su goma tsaye a wajan sun saka wani a tsakiya wanda bakinsa ya fashe jini na zuba, sai a lokacin ya Æ™ara lura da sauran motocin da sukai blocked hanyar…. “Fouk You” Wani ya furta daga cikin samarin daga shi sai gajeren wando ko riga babu jikinsa kansa babu ko gashi sbd tabbatacce ne shi Ya nuna guy É—in da suke doka ya ce “Kai dan ubanka sa’an ubanka ne ni? How dare you talk to me like that? He?” Taj ya saki dariya ya ce.
“You’re just wasting your time, ka ci uban É—an Shegiya muga waye ya tsaya masa a Nigeria, Legas ma babu wanda ya isa damu balle Kano”

“Exlty, We are Nigerians, we will decide, we will say whether it is heard or not, there is no one behind us….. Tell them” John Ya faÉ—a yana murza gun É—in hannunsa. Taj ya Æ™ara sakin dariya ya ce ya ce “Speak louder John, ba wani shege” Joshua ya ce “Mahaukata ne ku, wallahi kun saÉ“a ba haka bad boy ya ce ba, a karya masa Æ™afar daba da hannun hango a zubar titi” Driver ya zare idanu. A na kana wani police ya zo ya ce “who are you? Waye uban a garin nan? Dalla ku matsa akan titi…..,”
“What if we refuse?heeee?” GabaÉ—aya Gang team É—in suka juya idanunsa ya sauka akan shi, fitowarsa kenan daga cikin mota, Matashin saurayi mai ji da Æ™uruciya. Police É—in ya ce “I’ll report, za ku yi prison for life” Guy É—in daya fito daga motar yana wata iriyar tafiya majestic har ya Æ™arasa gaban police É—in a taÆ™aice ya ce. “Ohhh” Ya faÉ—a yana hura masa yahaÆ™in Cigarettes… Police ransa ya É“aci ya É—aga hannu zai nuna shi da yatsa cikin zafin nama guy É—in ya kama hannu tare da murÉ—ewa nan take hannun ya kare…….Kuka Abbu yake wiwi hannunsa dafe da Alkur’ani ya ce “Wallahi wallahi Majeederh ni ne ubanki, mahaifinki ni na haifeka jinina ke yawo a jijiyoyin jikinki, Majeederh ina tunanin ke aka sauya mini kin tuzartani kin É“ata mini suna a dangin kina roÆ™an Soyayyar namiji? Ni na cancanci haka?” Majeederh ta ce “Ka yafe mini, zan yi aikin ba zan Æ™ara ba kuma ba ai bai aurenin ba he left me”…… Shekarunta 31 cif tun ranar ba wanda ya Æ™ara cewa yana sonta balle aure, a haka ta Æ™ara zama Gwarzuwar Alkur’ani wacce aka gabatar a Saudiyya…..

Sun cike titi babu wajan da mota zata shige, sun haddasa go-slow na ban mamaki wasu ne da basu da maraba da Æ´an fashi wajan su goma a tsakiyar titin sun saka wani a tsakiya suna duka.

” Kai dan ubanka sa’an ubanka ne ni? How dare you talk to me like that? He?” ” Wanda suke doka ya ce “Me nayi muku?” Taj ya ce “You’re just wasting your time, ka ci uban É—an Shegiya muga waye ya tsaya masa a Nigeria Bama kano ba, Lagos ma babu wanda ya isa damu balle Kano”

Joshua ya ce “Mahaukata ne ku, wallahi kun saÉ“a ba haka bad boy ya ce ba, a karya masa Æ™afar daba da hannun hango a zubar titi” Wani police ne ya ce “Ku titin iyayenke ne? Zaku jawa kanku dilla ko kwashe motocin ku, ku bawa jama’a waje.

Daga bayansa aka ce “What if we refuse?heeee?” GabaÉ—aya Gang team suka kalli Bad boy wanda ya fito daga mota, police É—in ya É—aga hannu zai nuna Bad boy kafin ya yi pointing É—insa ya kama hannu tare da karya shi nan take….

https://arewabooks.com/chapter?id=64ac50ef324ef73a495e70b9″This is the first and last da za ki yi pointing nawa da finger, Dog!” Guy É—in ya furta hakan a tsawa ce, mai da police É—in ma ce ta hanyar faÉ—in “Za Ki yi” Saboda rashin cikakkiyar hausa maganar ta shi ma a gurÉ“ace take. Sosai Police yake jin azaba nan take hannun ya kumbura zufa na yanko masa ya ce “This is not fair, su waye ku? You came and blocked the road and prevented the vehicles from entering”….“Your Father” Guy É—in ya faÉ—a. Yana ware kuma dara-daren idanunsa akan ÆŠan sandan, Kyakkyawan saurayi ne mai Æ™arancin shekaru domin baifi 16yrs ba, kulawa da kwanciyar da jin daÉ—in rayuwa haÉ—i da samun duk wani abun da yake so ya sanya jikinsa wani irin mahaukacin buÉ—ewa, domin gabaÉ—aya cikin Gang team É—in yafi kowa girman jiki, tsayi da kauri jikinsa a murÉ—e yake ga wasu six-pack da suka bayyana musamman saman Æ™irjinsa, baÆ™i ne shi sosai irin baÆ™in Æ´an America É—in kana ganinsa kaga Ba’amurke baÆ™ar fatarshi mai kyau da sheÆ™i irin baÆ™in da yafi farar fata kyau da É—an kan idanu. GabaÉ—aya jikinsa zanen tattoo ne daga wuya har zuwa Æ™irjinsa da hannaye ga wata Æ™atuwar sarÆ™a mai tabon Cross a jiki. Sumar kansa a murmurÉ—e kamar indomie wacce ta Æ™ara fito da kayan fuskarsa da jajeyen laÉ“É“ansa…. he is outstandingly handsome and robust, very masculine. Cikakken namiji mai iko da tsayawa akan ra’ayinsa. Police É—in ya nuna kansa ya ce “Ni ka ke zagi?”
“An zage ka titin na ubanka ne?” Taj ya faÉ—a yana nufar kan Police É—in ganin haka yasa ya yi saurin yin baya tare da barin wajan. Taj ya ja tsaki ya juya ya kalli Guy É—in daya karyawa police É—in Hannu ya ce
“Abraham let’s go” Da wani irin kallo wanda aka kira da Abraham É—in yake bin Taj da shi cikin warning ya ce “Sai na ci Babarka, duk sanda ka sake ce mini Abraham” Ya faÉ—a cikin harshen turanci. Da sauri drivern Abbu ya juya zuwa wajan mota yana isa jiki na rawa ya ce “YallaÉ“ai wallahi Æ´an fashi ne, mun shiga uku” Abbu ya É—ago kai ya dubi driver a hankali ya ce “No! Ba Æ´an fashi ne, Æ´an fashi da rana??” Driver ya ce “Kwarankwatsa su ne, hadda bindiga irin ta film na gani fa? Innalillahi mun shiga uku” Abbu ya ajjiye Jaridar hannunsa domin meeting ne da shi na gaggawa akan wata contract da zai yi signing akan papers É—in. Ganin haka ya sa Driver buÉ—ewa Abbu Æ™ofa ya fito yana tattare babbar riga cikin sauri kana ganinsa kaga manyan Alhazawan nan masu tashe da kuÉ—i, ya dinga ratsa mototci yana shigewa har ya isa tsakiyar Gang team É—in. Abraham na tsaye hannunsa riÆ™e da Cigarette yana busawa tare fitar da yaÆ™inta zuwa sama. Taj ya ce
“Guy’s let’s go, go go” Abraham na Æ™oÆ™arin shiga mota ya ji an damÆ™i wuyansa ta baya, abinda tunda uwarsa da haife shi ba a taÉ“a yi masa ba, kasa juyawa ya yi saboda tsananin mamaki kafin a ankare ya ji an fizgoshi tare da sauke masa wasu tagwayen maruka. GabaÉ—aya Gang team É—in, Taj, Joshua, John… Da sauran sukai kan Abbu kowa yana fito da bindiga Jikin Abraham har wani tsuma yake naman wajan na wata kakkarwa idanunsa sukai jajur Yatsun Abbu suka fito raÉ—au a saman kyakkyawar fatarsa. Da wata murya ya daka musu tsawa ya ce “Noo!!!!! Don’t shoot him” John ya ce “But why? Marinka ya yi, He slapped you, waye shi a Kano? Ubansa ma ubansa zamu ci dan kaza kazanshi” Abraham dai kallon Abbu yake without blinking his eyes. “Ni ne zan hukunta shi, Ba a taÉ“a mini haka ba in my whole life” Abraham ya basu amsa. Cikin sauri kuma ya Æ™waci bindiga a hannun Taj zai bugawa Abbu kan bindigar ya ji Abbu ya ce “Wato kune irin gagararrun da muke da su a kano ko? Haihuwar kan titi wanda baku san girma da darajar kowa ba? Shegu gayyar tsiya, gayyar na ayya” Cak Abraham ya tsayar da hannunsa dab da fuskar Abbu ya runtse rinannun idanunsa. Ganin ya tsaya Gang team É—in suka haÉ—a baki wajan faÉ—in “Bad boy Shoot, Shoottt him” Ko motsawa bai yi ba balle ya yi Æ™oÆ™arin harbin Abbu, murmushi Abbu ya yi ya ce “Idan kai É—an halak ne harbeni, É—an daba masu kwacan wayoyi sisi babu a aljihu maimakonsa ku nemi aikin yi kun bige da sata da bashi da makami, me ake da talauci shi yake saku irin wannan Allah wadaran naka ya lalace” Wani acikin jama’ar wajan ya ce “A’a Alhaji É—a ai na kowa ne, ka yi musu fatan shirya idan da rabo watarana sai kaga sun zama wasu a Nigeria bana jihar nan ba” Abbu ya girgiza kai ya ce “Goodness! Ai basu da rabon shiriya irinsu da haihuwar su gwara É“arin su, basu da wani muhimmaci talakawan banza, maybe na shan wiwi da sigari basu da shi” Yadda jikin Abraham ke É“ari kaÉ—ai zai bawa mutum tabbacin maganganun sun shige su, duk da ba komai yake fahimta ba cikin yaren Hausar.
“Useless” Abbu ya Æ™ara furtawa yana tofar da yawu. Kafin su Taj su lura Abraham ya shigo dukan kansa da Æ™asan bindigar nan nan da nan jini ya fara zubar masa. Ganin hakan ya sa John nufar Abbu Gadan-gadan zai harbe shi kafin ya Æ™arasa Abraham ya cimmasa yana zuwa ya dunÆ™ule ya naushi John a ciki yana huci kamar zaki ko kumurcin maciji cikin Æ™ara ji ya ce “I said no!”
“Bad boy akan wannan tsohon ka ke cutar da kan ka?” A fusace ya sake juyawa kan Taj ya ce “Abu É—aya ka Æ™ara cewa zan kashe ka, I’ll kill you Taj” Yana faÉ—in haka ya Æ™waci key É—in motar shi hannun Joshua motar da tafi ko wacce mugun kyau ya nufa yana zuwa ya buÉ—e tare da shiga ya jata da wani irin sauri kamar zai tashi sama haka yabar wajan, ganin irin gudun da yake saka Gang team É—in suka shiga mota tare da marawa Bad boy baya, Abbu ya ja tsaki tare komawa a hankali masu tsaron kan hanyar suka dinga bawa mutane hannu suna shigewa “Ƴan iskan yara gantalallu” Abbu ya faÉ—a bayan driver ya shige da shi zuwa hanyar su da Murtala Muhd way…. Gudu kawai Abraham yake idanunsa yana zuwa kan corner da zai You-turn danja ta tsayar da shi, a hankali ya É—ora kansa akan string motar zuciyarsa kamar tayi tsalle ta fito sbd wani irin baÆ™in ciki da takaici da yake ji, This is the second time he finds himself in this situation, bai damu da jinin da yake zuba daga kansa ba burinsa kawai ya tuna inda ya taÉ“a jin muryar, tabbas ya san muryar Abbu but where? Ba a taÉ“a riÆ™e wuyan rigarsa ba balle wani ya yi attempting marinsa, bai kuma san dalilin daya sanya ya kasa yin komai akan Dattijon ba, da alama he’s special da wani da wallahi sai ya kuntile hannu idanunsa har wani ruwa ne ke kwanciya sbd tsabar zuciya da taurin rai…. Knocking Glasses É—in motarshi ya ji ana yi a fusace ya É—ago zai zabga ashar idanunsa ya sauka akan wata yarinyar wacce take duÆ™un-duÆ™un ya ja siririn tsaki ganin yadda fuskar yarinyar take duk majina, idanunsa ya É—auke tare da rufe shi yana jin komai ya duniyar ya fice masa a rai, ya yi dana sanin dawowa Æ™asar bakiÉ—aya. Ci-gaba da knocking kawai tayi ya zuge Glasses É—in zuwa Æ™asa da sauri ta ce “Ka taimaka mini dana abinci saboda Allah YallaÉ“ai” Bai san meta ce ba, amma ya ji sunan Allah sarai sai ya ci gaba da kallonta, nan da nan zuciyar tausayin sa ta motsa musamman akan É—iya mace yana da tausayin mata Æ™warai tashin hankalinsa yaga mace na kuka, ya É—auke yana kwaso kuÉ—i ya watsa mata ta Æ™ofa da sauri kuma ya ja motar ya yi gaba… Tun daga Æ™ofar gate É—in gidan yake danna horn kafin gatekeeper ya fito ya yi saurin fitowa kansa a Æ™asa domin baya jira bai yarda kuma a jira shi ba, ya nufi Æ™aramar Æ™ofar shiga tare barin motar a buÉ—e a waje, cikin sassarfa cike da kuzari duk da jiri na É—aukarsa haka ya nufi cikin gidan ya tsaya a Æ™ofar farko yana danna password Æ™ofar ya buÉ—e, a Main parlour ya tsaya cikin zafin nama kamar Mahaukaci ya shiga É—aukan duk abinda hannunsa ya je kai yana doka shi da Æ™asa… Daga saman upstairs aka ce “Grandson!” Abraham bai tsaya daga abinda yake ba, ganin zai jiwa kansa ciwo ya sa David ya shiga sakkowa daga steps É—in benen da sauri yana zuwa ya kama hannun Abraham ya ce “Waye? Kai da wa?” YaÆ™i cewa komai sai huci da yake jikinsa na rawa David ya san Abraham ba zai taÉ“a magana ba, hakan yasa ya ja hannunsa zuwa saman kujera ya damÆ™a masa wani cup ya ce “Drink”
Bai tsaya tantance mene ba ya amsa tare da kafawa a baki ya shanye tas, David ya ƙara zuba masa wata ya shanye daga nan ya miƙe ya nufi wani part not too ya dawo hannunsa riƙe da first-aid box ya gyara masa wajan.

“Who is he?” David ya tambaya, cikin mayen daya fara É—aukar shi ya ce “I don’t know, but i knw him na san muryar” David ya ce “Where?” Ya yi shiru… Ganin yana cikin maye kuma zai fi É—aukar magana ya sa ya ce “Look Grandson, na ce ko da wasa bana son ganin jini a jikinka gwara ka fitarwa da wani jini da a fitar maka, ka ci mutuncin wanda ya ci naka, ka taka wanda ka ke so, kai É—aya nake da shi a gefena You’re my grandson exit? Babanka yabarka, baka da Mother baka da kowa a duniya sai ni, ni ne Grandfather naka, idan kuÉ—i na maganin komai a duniya to duk irin bala’in daka É—auko zan ji da shi, ni ne shugaban church ni ne Pasto bayan haka kafi kowa sanin matsayina a Æ™asar nan bana country ba, ina da kuÉ—i mai kuÉ—i shi ke da magana, a top 5 na masu kuÉ—in Nigeria zan shiga ciki, Mahaifinka Daniel zai shiga…..,” “Stop calling his name, i hate him he’s not my father” Abraham ya faÉ—i hakan idanunsa na lumshewa ya shiga surutan maye yana faÉ—in
“She left me, Mamina Grandpa, Mamina Mamina” Sai kuma jikinsa ya shiga jijjiga. Grandpa ya yi shiru kafin ya ce “Mamin nan taka maybe she’s no more bata ra….,” Tasss! Ya ji saukar Glasses ya miÆ™e da sauri yana riÆ™e Abraham ya ce “Am so sorry Dear, Maminka na nan I’ll find out where she’s hiding to” Da Æ™yar bacci ya É—auke Abraham bakinsa É—auke da sunan “Mamin, JEENA” Ganin ya yi bacci yasa Grandpa kiran Taj a waya ta prvt line nasa yana É—agawa ya ce “What’s happened?” In brief Taj ya faÉ—a masa komai Ya ce “Ka nemi mai Zane ya yi drawing na mutumin ka kawo mini nan gida” Taj ya ce “Bad boy fa? Ai zai fi yin zanen yadda ake so” Grandpa ya ce “It’s secret”….
Saudiya. Majeederh na zaune saman kujera gabanta É—auke da laptop tana duba abubuwan da zatai a B.u.k idan ta koma Nigeria, komai nata maturel ne nutsuwa ga wani irin jan aji da kamon kai bata sakewa kowa fuska, har office ya buÉ—e wanda za a dinga samunta kai tsaye a ranakun weekend, ba ruwanta da batun tama sakawa ranta ba zatai ba tunda babu wanda ya Æ™ara tunkararta tana jin surutai na yawo a unguwa harda Social media ba ga family taÆ™i yin aure sai yawo… Door bell ta ji ta yi Æ™ara a hankali ta É—an zame hannunta daga keyboard É—in laptop É—in, tare da É—an yi shiru tana tunanin who is there by this time? Bata da appointment da kowa amma waye kuma? A hankali ta miÆ™e tana saka sunglasses É—in ta na medical kana ta Æ™arasa jikin Æ™ofar ta ce “Who’s there?” Aka amsa da “Messenger” “Ok came in” Ta faÉ—a a gajarce, tana kowa tayi saurin saka hijabi da liÆ™ab kana ta buÉ—e Æ™ofar, da mamaki ta dinga kallon mutumin ganin uniform É—in masarauta a jikinsa da alamar Bafade ne shi yana ganinta ya zube a Æ™asa yana kwarara mata gaisuwa, ita dai bata ce komai ba ya miÆ™e mata wata envelope ya ce “SaÆ™o ne daga Palace ranki ya daÉ—e Gwarzuwar Nigeria” Da hannu ta nuna masa ya ajjiye nan Æ™asa ya ajjiye bayan ya tafi ta durÆ™osa ta É—auka envelope É—in tana komawa cikin bedroom É—in, a hankali ta ware iya haÉ—uwa Envelope ta haÉ—u wani irin zaibar rubutu ne manne a jiki an rubuta.

_Your Highness Ajlaal Sultaan_
Invite
_Malama Majeederh Abdul’aziz Khan_

Ta duba date yau kenan sai kuma time 4 na yamma, ta dinga juya Envelope É—in Ajlaal mijin Ƙhulud Arzaan kenan? za taga Ƙhulud farin ciki ya wanzu a zuciyarta duk da fargabar kiran ya É—arso a zuciyarta…. 3:45 Daidai ta fito cikin wata Abaya dark blue tayi rolling kanta da vail sai liÆ™ab da wani sirrin Glasses a Idanunta hannunta riÆ™e da hand bag da wayarta, tafiya take cikin tarin nutsuwarta kamala da sanin ya kamata, harta isa motar da ake jiranta tana zuwa driver ya buÉ—e zata shiga gaba ya ce “Ranki ya daÉ—e baya, ni driver ne” Ta É—an girgiza masa kai kamar ba za tayi magana ba sai ta ce “Ina so gaban” Ta shiga ta zauna cikin sauri taja motar sai Palace…. Ƙhulud Arzaan na tsaye cikin shigar larabawa ga tsohon ciki a jikinta wanda shi ne karo na farko da zata haihu, fuskarta É—auke da murmushi Majeederh na yin sallamawa Ƙhulud ta fasa ihu tare da nufar Majeederh, cak ta tsaya idanunta na gizo mata wani abu sai kuma ta nufeta suka rungume juna sosai sukai farin ciki bayan shekaru nawa sun sake haÉ—uwa, Ƙhulud ta ce “Ina mijinki fa?” Majeederh ta É—an yi shiru sai kuma ta ce “Ban yi aure ba” Cikin wasa Ƙhulud ta ce “Kina jiran haÉ—aÉ—É—an namiji ko?” Murmushi kawai ta yi sai kuma ta ce “Kamar labari littafi? Kawai Allah bai kawo ba” Ƙhulud ta ce “Ubangiji ya kawo na gaban kwatance amma na yi mamaki na É—auka ma kin haihu wlh” Majeederh ta yi shiru Ƙhulud ta ce “Mu je wajan Granny Zaytoon” Suka miÆ™e wani plat suka nufa mai kyau da tsari. Zaytoon na zaune saman ladduma gabanta cike da kayan itatuwa ana mata firfita suna shiga Zaytoon ta sauke wani irin kyakkyawan murmushi tana tafa hannu ta ce “Lale lale da babbar Malama” GabaÉ—aya Hadiman suka fita Majeederh ta zube gaban Granny tana gaisheta ta amsa da “Ma sha Allah, Allahamdulillah Sannu kin ji ina sake tayaki murna” Ita dai kanta a Æ™asa, Granny ta dinga kallonta ko zata cire liÆ™ab É—in fuskarta amma taÆ™i itama kuma bata ce ta cire ba sbd she don’t want interfere a rayuwar Majeederh. Majeederh ta É—ago kai idanunta ya sauka akan wata matashiyar mata mai wani kyau kamar ba mutum ba, ta dinga kallon matar sai kuma ta ce “Ina yini?” Granny ta juya ta kalli matar da Majeederh ke gaisarwa wacce take zaune saman wheelchair Granny ta ce “Wai Gimbiya kike gaidawa? Allah sarki Hawwa’u ai bata da lafiya bata magana bata tafiya hannunta kawai ke motsawa” Cikin tausayawa Majeederh ta ce “Allah sarki, Allah ya bata lafiya” Granny ta ce “Ƙarasa wajanta mana, takwararki ce sunanta Hawwa’u yadda take kallon naki kamar ta sanki bayan ko Nigeria bata taÉ“a zuwa ba” Majeederh ta Æ™arasa gaban matar ta durÆ™osa ta ce “Sannu Allah ya baki lafiya” Ga mamakinsu sai su kaga tayi murmushi harda hawaye ta riÆ™e hannun Majeederh Æ™am! Sun jima kafin ta ce “Naga saÆ™on kira” Ƙhulud ta ce “Ohh Takawa ke kiranki” Gabanta ya faÉ—i ta ce “Mai martaba Sultaan?” Ƙhulud ta ce “Tsohon zance tuni muka ture shi mijina ke kan karaga ai, Mai martaba Ajlaal Sultaan ke kiranki” Ta yi shiru bata ce komai ba Granny ta ce “Fulani rakata mana, yana part É—insa ai ya bar fada tuni sai miskilanci yake ji jiya da yau” Ƙhulud ta ce “A’a jinin sarauta ke yawo a jikinsa fa, ba wani miskilanci” Tana faÉ—in hakan ta miÆ™e tsaye Majeederh ta miÆ™e Æ™irjinta sai bugawa yake a haka suka Æ™arasa wani irin Æ™yakÆ™yawan plat mai É—aukar kyau ga matso tsaran Æ™ofa nan birjik suna ganin Fulani suka zube Ƙhulud ta yi murmushi tare shigewa Majeederh ta bi bayanta, suna shiga Ƙhulud ta yi sallamawa yana zaune hakimce idanunsa rufe yana cikin wata Jallabiya mai kama da Alkyabba, ya É—ora hirami a saman kansa ga gefensa fuskarsa suma ta sakko kamar ka taÉ“a shi jini ya fito, bai amsa gaisuwar Ƙhulud ba, bai kuma buÉ—e idanunsa ba, Ƙhulud ta miÆ™e ta ce “Ina zuwa Majeederh” Majeederh kamar ta saka kuka ta cikin liÆ™ab É—in, amma ta kasa ko motsi. Wajan ya yi shiru ita ba tayi magana ba shi ma bai ce komai ba, bashi da niyyar cewa komai É—in, shafewar seconds kafin Majeederh ta ce “Barka da hutawa Takawa” muryarta na rawa domin ba Æ™aramin kwarjini ya yi mata ba, tana jin kanta Uncomfortable a gabansa musamman da taga kamar bai taÉ“a sanin wani Abu Annuri ba a saman fuskarsa. Ta É—auka bai ji ba ta Æ™ara maimaita gaisuwar nan ma shiru tana É—ago idanunta da niyyar ganin ko baya wajan cikin rashin sa a idanunsu ya sarke cikin na juna, Ajlaal Sultaan ya kafeta da narkakkun idanunsa can kuma ya taÉ“e baki kana ya janye idanunsa a hankali ta ce “Gani” Ya jima kafin ya ce “Ke wa?” Tama É—auka ba zai magana ba sai ta ji ya ce hakan. “Ance kana kirana” Bai ce komai ba ganin tana Æ™oÆ™arin wulaÆ™anta kanta gabansa duk da tarin nata kimar ya sa ta miÆ™e tare nufar hanyar fita, sai da ta je bakin Æ™ofa ta ji an ce “Wait” Bata É—auka da ita yake ba duka jikinta rawa yake Allah ya gani bata taÉ“a ganin mutum nai haibar Ajlaal ba zata fita ta ji an É—ora hannu akan hannunta dake jikin Handle da sauri ta juya ta ganshi tsaye kamar ya haÉ—iyeta gabaÉ—aya ya yi mata rumfa da Æ™aton jikinsa rawar jikinta ya tsananta haka ma bakinta Æ™irjinta na É—agawa tunda uwarta ta haifeta bata taÉ“a yin kusanci da namiji kamar yadda sukai da Ajlaal ba, hannunsa ya murza akan nata kana jata zuwa cikin bedroom É—insa ba parlour ba……

No comments