Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 22


[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: Khalil ne ya fara fitowa ya bar cikin bathroom É—in, ta jima tsaye tunani fal ranta ganin har yanzu ko tari baiyi ba balle ya ce mata wani abu, lokacin data kammala sabon wankan daya sanyata na dole ta fito É—aure da towel, ta bi bedroom É—in da kallo ganin baya ciki sai Æ™amshin mayataccen turaren shi na Boadicea The Victorious wanda ke ratsa zuciyarta a hankali yana sanyata cikin shauÆ™in son turaren as always, tayi shiru sai kuma ta nufi gaban mirror ta zubawa kanta Idanu, ganin yadda ta sauya hankalinta bai wani gama kwanciya da kyau ba, a kullum idan ta tuna bayan ita Khalil nada wata matar sai hankalinta ya tashi komai ya fita daga ranta, kalman kuma Latifa na mata amsa kuwwa a kunne, na batun sharing miji da wata, kenan sai ya tsoma bakinsa a na wata yake sawa a nata? Ta rufe Idanunta tana addu’ar neman sassauci akan Abinda take ji wajan Ubangiji, a hankali ta fara duba sauyin da tayi,ta Æ™ara wani irin kyau mai fisga da jan hankalin namiji, ga wani irin fari da fatar jikinta ya Æ™ara sai glowing take, tayi Æ™iba da kauri irin ta cikar É—aki. Ta goge idanunta daya cika da hawaye tare da neman waje ta zauna a ranta tana cewa “Ko mai ba zan shafa ba, balle kwalacca É—in da kake shin-shine a kanta kaje can Æ™edarar matarka ta shafa maka” Tunawa da Æ™ila yana can rungume da ita ya sanya ta haÉ—e kai da guiwa tare da fashewa da wani irin raunataccen kuka…
Khalil na tsaye a bakin Æ™ofa ya jingina, hannunsa harÉ—e da Æ™irjinsa, ya zubawa Debeka Idanu wacce ke kuka kamar ranta zai fita, ya fi minti 5 tsaye yana jinta bai ce komai ba, bai kuma hanata kukan ba, She regretted not listening to her father that very day, had she listened to him, she wouldn’t have met Abraham that very day, da ace ta gane maganar Dad É—inta sanda yake cewa ya zaÉ“a mata mijin aure maybe da tayi farin ciki, tsautsayi ya kaita har taga Abraham, wanda ya riga ya zama destiny É—inta. She was already depressed, and most times, she feel like attempting sucide but she couldn’t. She was tired, and frustrated for real. Ganin kukan ba mai Æ™arewa bane ya sanya walking slowly Khalil ya Æ™arasa shiga cikin bedroom É—in nata tare da zama kusa da ita a hankali yana sauke numfashi kamar an yi masa dole ya ce “What?”
Ta kalle shi da jajayen idanunta ta ce “What! Shi ne abin da zaka ce mini Abraham? Kana ganin na cancanta da abinda kake mini? Na sadaukar da abubuwa da yawa saboda kai amma ko inuwata bata isheka kallo ba, You left me,ka barni ni É—aya” wasu hawayen suka sake sakko mata ta ce “Duk girman part É—in matarka wanda yafi nawa komai amma bai muku ba, sai kun sakko down stairs a tsakiyar main parlour za ku yi soyayya? Har a sutale maka wando?” Khalil ya gwalo idanu waje da Æ™yar ta ce “YES, har maganata kaji ka nuna kamar baka san dani ba, ko zuciyata ce za ta yi bindiga ta yi gutsi-gutsi baka da hasara, ka nuna mini ka kasance da matarka not me after all i’m virgin ba ragowar wani a tare dani” Khalil ya haÉ—e fuska da kyau tare da saka hannu ya juyo da ita ya ce “Kuma wace ba virgin ba? Ragowar wani?” Kai tsaye ta ce “Ur wife, tsohuwar matarka wacce mutuwar zuciya ya sameta ta auri É—an cikinta…,” A tsawa ce ya ce “Debeka!” Ya faÉ—a da Æ™arfi yana matse kafaÉ—arta idanunsa na juyewa ya ce “Ya zama first and last da zan Æ™ara jin wannan maganar, kuma ni na yi dis-virgining É—in Jee, Madam ragowata ce bata wani ba, kuma sau nawa kina attempting lalata ni Allah ne kawai ya tsare ni?” Debaka ta saki baki tana kallonsa,then wiped the tears which streamed down her cheeks with a thumb ta ce “Gori zaka mini? Ai ban lalataka É—in ba, kuma saboda ina son ka nayi hakan” Khalil ya girgiza kai ya ce “Ohho dai Allah ne ya taÆ™aita mini wahala, kuma Madam da kike gani zata iya bada ranta akan nawa ke fa?” Debaka ta ce “Amma ka san I’ve sacrificed alot saboda kai?” Ya yi Æ™asa da murya ya ce “Sanda nazo bedroom naki na yi 2days kin ji tayi complain? Kuma da kike cewa na rungumeta yanzu ni Ibrahim-Khalil idan ban rungume matata ba wa zan rungume? Ko satar kwana kike so in miki?” Debaka ta ce “I can relate, thank you” Shi fa baya son tashin hankali ya ce “To ba zan É—auki tashin hankali ba, na zo na ce miki hi naga ya kike” Ya miÆ™e rai É“ace ya bar part É—in bakiÉ—aya daman a shirye yake don haka yana fita, Wani Sojan driver ne ya budewa Kspider bayan mota Æ™irar Mercedes-Benz S-Class white colour, driver ya rufe bayan motar ya koma mazauninsa tun kafin su isa gate aka buÉ—e dake daga parking lot zuwa gate akwai tazara sosai, a nutse driver ya fita daga cikin gidan a bakin Æ™ofa kuma ya tsaya yana tambayar Khalil ina zasu nufa? Kafin Khalil ya bada amsa idanunsa ya sauka akan Lafita dake sakkowa daga napep ya zuge glass É—in motar ya kalli gatekeeper clamly ya ce “Kar a barta ta shiga” Da sauri yana Æ™amewa ya ce “Yes sir” Driver ya ja da sauri suka bar wajan. Latifa ta dinga kallon tafkeken gidan da aka ce nan aka kawo Majeederh, bata taÉ“a ganin gida mai kyau da tsarin shi ba, kamar a Æ™asar turawa nan ma ba ko wanne gida ba, gashi gidan fari tas sai É—aukan idanu yake a unguwar, ita sam bata gama yarda gidan bane da shi ne yadda mai wannan jibgegiyar motar ya fito zai iya tsayawa ya ce ta shigo, domin ta tabbatar babu mai fita sai mai gidan, idan haka ne kuma mai gidan shi ne Khalil, ta nufi wajan shiga ta Æ™aramar Æ™ofa tafi minti goma sha biyar tana bugawa ba a buÉ—e ba, can aka buÉ—e Sojan ya ce “Hajiya wa kazo gani?” Ta ce “Nan ne gidan Khalil?” Ya ce “Sure” Ta ce “Ohk buÉ—e mini” Ya haÉ—e fuska ya ce “Wajan wa?” Ta ce “Mrs Khalil, Majeederh” A taÆ™aice ya furta “You’re not welcomed” Cike da masifa ta ce “Meye wani welcomed, kasan yadda muke da ita kuwa?” Ya yi mata banza ta É—auki wayarta da nufin kiran Majeederh ya ji taÆ™i shiga, ta kira ya fi sau shurun masaÆ™i amma amsa É—aya ne, bata sani ba tuni Khalil ya dannawa numberta blocked a wayar matar shi, ta dinga ruwan bala’i sai ta shiga Soja da ba imani ne da shi ba ya zaro bindiga ai da gudu ta bawa wandon ta iska, hawaye na zuba daga cikin idanunta ta rasa komai, abubuwa da yawa sun lalace mata, idan ba Majeederh ce ta bata shawara ba bata taÉ“a ganin daidai, a haka ta tari napep zuwa gida tana tafe tana goge hawayen idanunta, ta kara regretting abubuwan data aikata babu mamaki hisabin hakan ta fara amsa, domin ba zaka shuka dawa ka girbe shinkafa ba, ta fahimci Majeederh ta riga ta gama mata nisa, nisa na har gaban abada mijin data Æ™wallafa rai da shi gashi sam bai damu da ita ba, ta rasa aikinta uban da take taÆ™amar shi ya haifeta gashi ance bashi bane, ita bata da confidence É—in tarar Majeederh ta faÉ—a mata cewa, ita ce silar duk abubuwan daya faru da ita,she destroyed her life because of her selfishness, Maybe idan ta samu yafiyarta wani abun ya zo mata da sauÆ™i ta samu Barrister Aliyu ya fasa auren a fili ta ce “What should I do?” Da sauri ta ce “Northern_hibiscuss” Ta É—auki wayarta ta shiga I.G daman already tana following account É—in kai tsaye ta tura requesting na message ta ce “Asslam Malama, i need your attention it’s very urgent, ban kasance Æ™awar arziÆ™i ba ki saurari maganar da zan faÉ—a miki plx” Ta tura bayan nan ta sauka daga network É—in hankali tashe ta nufi gida, tana sauka daga napep Barrister Aliyu na fitowa daga cikin gidan shi zai je can gida wajan Hajia sarai ya ganta ta tsaya wajan Aaliyyah data fito ya share ya tsaya daidai wajan yana sauke glass É—in motar ya kalli Aaliyyah dake tsananin kama da Majeederh ya ce “Fita zakiyi ne?” Ta ce “Eh Yaa Aliyu” Ya jinjina kai ya ce “Oh shigo na rage miki hanya” Ta kalli Latifa sai kuma ta ce “No thank you” Ya haÉ—e fuska ya ce “Come in” Ganin yadda ya yi yasa ta shiga gaban motar daya jima da buÉ—e mata, ya matsa sosai tayi saurin yin baya ya kalleta sai kuma ya É—auke kai yana rufe Æ™ofar, Latifa tayi kamar statue baki sake tana kallon ikon Allah, kamar zautacciyya kuma ta shige cikin gidan tana fashewa da wani irin kuka. Sun É—auki hanya sosai Barrister Aliyu ya ce “So how are you Leeyerh?” Aaliyyah tayi dariya ta ce “Leeyerh kuma Yaa Aliyu” ya juya ya kalleta sai ya É—auke kai ya ce “Sunan ya yi tsayi, to cut the name short kenan dear” Ta jinjina kai ta ce “Ohh” Ya ce “Ya school? Wanne level kike ne?” Ta ce “Zaka mai dani yarinya Yaa Aliyu, am a graduate” Ya kalleta da kyau from head to toe haske kawai da manyanta haÉ—i da fararen idanu Majeederh zata fita sai kuma Æ™aramin baki ya ce “Kenan babba ce kenan?” Ta ce “Sosai” Ya yi murmushi kawai yana yin roundabout ya ce “To i congratulate you, sai aure” Ta yi shiru ya ce “Ko ba zakiyi ba?” Ta É—an yi murmushi ta ce “With time” Ya ce “Malam Bahaushe kenan, ina Yaya Nuran?” Ta zare idanu ta ce “Ka san muna tare ne?” Sai kuma ta ce “He left me, saboda abin da ya samu Anti Jeederh ya ce gidan babu tarbiyya” Barrister Aliyu dai bai ce komai ba deep down ya tausayawa mata, ganin ya É—auke hanya ta ce “Ina zaka ba nan zanje ba?” Ya ce “Zaki gidanmu ne, wajan Hajiata”. Da wani irin Expression His Excellency yake bin wanda ke saman kyakkyawar kujerar dake a parlour, ya nemi waje ya zauna yana cewa “You?” Khalil daya harÉ—e Æ™afarsa saman table É—in dake kusa da shi ya yi wa Abuturab wani jahilan kallo ba tare da ya ce komai ba, His Excellency ya ce “Who are you? Who gave you permission to enter my house?” Khalil ya yi wani miskilin murmushi yana Æ™arewa inda aka kira gida da kallo ya yi baya laying on the couch, tare da É—ora É—aya Æ™afar ta shi, cike da nutsuwa ba wani tashin hankali ya ce “Mijin Malama” His Excellency ya ce “You! Me kazo yi nan?” Khalil ya rufe Idanu can ya buÉ—e ya ce “Kai baka kai na zo wajanka ba, na zo na yi maka warning ne” Ya ce “Warning?” Khalil ya girgiza kai ya ce “Firstly; I Ibrahimul-khalil Denial David, mijin Malama na har abada, da gaban abada idan akwai, ka fita daga sabgar matata, domin ita ce suffata kuma zaka yi regretting mayar mini da mata Æ´ar Shaye-shaye, idan ka yi haka don na tsaneta to ka tafka babbar hasara, ko kai na za a saka gabas bazan iya sakinta ko rabuwa da ita ba” Ya girgiza kai ya ce “Baka da ce da zama shugaba ba, ina da wani kyakkyawan labari” Ya zaro wayar shi tare da kunna all maganganun da sukai da Majeederh amma an yi edited an cire muryar Jee, Khalil ya ce “Bom!” Da sauri Abuturab ya miÆ™a hannu zai É—auki wayar Khalil ya damÆ™e yatsun hannun Abuturab a cikin nasa, zufa ta shiga yankowa His Excellency all over himself, yatsun suka fara wata Æ™ara alamun karyewa suke duka biyar É—in, Khalil ya yi Æ™asa da murya ya ce “Ka sa an dake ni, an É—auke ni zuwa prison duk na maka shiru, to baka gabana ne ok, yanzu ka taÉ“a wacce zaka gane waye Ibrahimul-khalil, waye Mijin Malama a lokacin Abraham bad boy ka daka, banda am not interested da siyasa wlh da akan idanunka zan tsaya takara na Gwamna kuma na ci dole ni bana faÉ—uwa nasara a jikina yake, amma zan maka sanadin kujerar wacce ba dan Allah kake kanta ba, ka cutar da al’umma da yawa na san abin da baka sani ba” Abuturab ya miÆ™a hannu zai danna kiran securities Khalil ya cilla masa wata daily news paper yana sakin hannunsa, His Excellency ya É—auki news paper É—in, tittle É—in farko yaga an saka ”The president’s son” Ya kalli Khalil ya duba sauran rubutun, Photon Khalil ne dana Germany’s president an rubuta.
_“ƘyakÆ™yawan labari ga al’ummar duniya bakiÉ—aya, Musulmi da Kirista, bayan haÉ—in kan da ake samu tsakanin mabanbanta addinai guda biyu a kullum, ga wani babban Albishir babban É—an gidan shugaban Æ™asar Jamani wato Abraham Denial David, wanda a yanzu ya koma Dr Ibrahimul-khalil Denial David a sanadin musuluntar da ya yi, ya angwance da babbar Malamar addinin Musuluncin nan dake garin Kano Nigeria mai suna Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, kimanin wasu satuttuka kenan da yin auren, a yanzu kuma ya sake aure na biyu da Æ´ar addinin su kuma Æ´a É—aya tilo wajan Chancellor na Germany a jam’iyyar su Mr President, mai suna Debeka Akilan, wannan ya zama izinin ga mabanbanta addinai guda biyun da basa son haÉ—a jinsin su aure, ya Æ™aro yawaitar Mutanen da suka musuluntarsa tunda ba a taÉ“a tunanin wani daga jinin Mr President zai musulunta ba, al’amarin daya kawo yawaitar surutai a Æ™asar ta Germany”_
A Æ™asa aka sanya photon Majeederh da Khalil wanda yake rungume da ita an yi shi ne kuma ranar dinner a lokacin da yake mata raÉ—ar shi fa yunwa yake ji, zata bar wajan yi saurin rungumota jikinsa, Abuturab duka zufa ya wanke masa fuska Khalil ya yi murmushi ya ce “Ban san da wannan news É—in ba, a hanya na siya, ban dogara da Dad É—ina ba, ka leÆ™a kaga Escorts da sojojin da suke nan, kada ka jawo asarar rayuka” His Excellency ya yi murmushi ya ce “Liar, za ka yi Æ™arya da identity na wasu” Khalil ya zaro wayarsa babba ya danna, kai tsaye kuma facetime ne, fuskar President ta bayyana yana zaune saman kujera a hakimce, ya zubawa É—an nasa idanu cike da so a hankali ya ce “Son ya akai?” Khalil ya kwaÉ“e fuska yana langwaÉ“ar da kai ya ce “Dad, I’m just missing you” President ya ce “Zan tura jet yanzu ya kawo mini kai Germany da Daughters-in-law” Khalil ya rufe ido ya ce “I’ll come not now, Dad ina son manyan sojojin Germany, a yi musu izinin na harbi, hukumar kula da manyan laifuka, jami’an fikira na Æ™asa, sojojin sama, na Æ™asa na ruwa, shugaban Æ™asar Naija, shugaban sojoji na Æ™asa dana Æ´an sandan Nigeria su san da zuwan su” Dad ya yi murmushi ya ce “Guda nawa kake so, kai da waye?” Khalil ya juyawa Dad camera zuwa fuskar Abuturab, Abuturab ya kasa kallon Dad jikinsa rawa yake sosai, batu da shugaban Æ™asa kuma ma na Germany ai babba ne, kusan ya fi ko wanne shugaban Æ™asa Æ™arfin iko daga shi sai na Russia “Who is he?” Ya ce “Wai Gwamnan Kano” Dad ya ce “Ohh” Khalil ya ce “I’ll catch you later Dad” Har zai kashe sai ya ce “But Dad, kace zaka ma Madam gift shiru” Dad ya yi murmushi don ya gane wace Madam É—in ya ce “Ina sane” Ya katse kiran, Khalil ya miÆ™e tsaye yana zaga parlon ya ce “babu wanda nasararsa ta yawaita a duniya face sai ya kasance mai gujewa jin daÉ—in da ke zuwa da fargabar samun lahirarsa, Shin meyasa ka ke gajen haÆ™uri? Ashe ba ka ga yanda Allah ya ke ciyar da tsuntsaye ba? Ya ciyar da dabbobin da ke dawa, kuma ya warkar da marasa lafiyar cikinsu ba tare da magani ba, shin ba za ka yarda, kuma ka haÆ™ura da kwaÉ—ayi ba, kwaÉ—ayin duniya mai É—auke hankali mai saka nadama da kuka? Allah ne ya ciyar da abinda ba a sani ba, kuma ya ciyar da wanda aka sani, lallai shi ne zai ciyar da kai idan ya so, ba da Æ™arfi, dabara ko iyawarka ba” Yana faÉ—in haka ya fice, Abuturab ya bisa da kallo yana mamakin yaushe ya musulunta har ya iya yiwa wani wa’azi? Kuma duka ya faÉ—a ne cikin harshen Turanci domin till now bai iya cikakkiyar Hausa ba… Sai bayan Isha ya shiga gida yau gabaÉ—aya ya zaga companies É—insa, ya kwashi sabbin ma’aikata ya duba komai, don a haka a gajiye yake sosai, Debaka dake Main parlour tayi saurin miÆ™ewa tsaye tana nufar shi, kafin ta rungumesa ya yi mata side hug yana kissing goshinta ya ce “Thank you dear” Ta ce “Yau ka yi late” A hankali ya ce “Sure” ledar hannunsa ya bata guda É—aya, basu rasa komai ba a cikin gidan ga kuma maids nan kaca-kaca amma khalil mutum ne mai son kyautatawa iyali, part É—insa ya shige ya yi wanka sosai ya shirya cikin Lingerie night wear white colour, Æ™afarsa cikin D&D couples slippers, sai zabga Æ™amshi yake, ya nufi part É—in Jee ya sameta zaune a saman gado ko parlourn na bedroom bata fita balle na main part É—inta uwa uba na gidan, tana sanye da Falling rose pattern nightdress, sai sumar kanta dake É—aure da blue É—in ribbon har baya, ga wani Æ™amshin kwalacca dake tashi ya haÉ—u da turarenta na MORESQUE Midnight, ta lula duniyar tunani sosai ta ji ya zunguri Æ™afarta tayi saurin sauke ajjiyar zuciya tana ganinsa kuma ta yi Æ™asa da kanta idanunta ya yi rau rau zaton ta fushi yake, muryarta na rawa ta ce “Sannu da zuwa” Bai amsata ba sai hannunsa daya miÆ™a mata ta kalli hannunsa sai kuma ta miÆ™a nata, ya haÉ—e a nasa alamar musabaha ya ce “Salamu Alaiyki” Ta jima tana mmki shi haka yanayin gaisuwar nasa yake? A hankali ta ce “Wslm, wlcm” Ganin taÆ™i kallonsa ya riÆ™e hannun ya kalli fuskarta sai kuma ya kalli plate É—in gabanta yaga dafaffiyar madara ce mai kauri aka zuba honey a ciki, sai kuma hot milk cake fall plate ta É—ago kai suka kalli juna ganin hawaye ya ce “Baki da lafiya ne?” Kamar jira take ta haÉ—e kai da guiwa ta fashe masa da kuka tana buga Æ™afa, ai Khalil tuni ya manta komai ya tashi da sauri ya miÆ™ar da ita tsaye ya ce “Mene?” Ya faÉ—a a hankali kuka kawai take ya jawota jikinsa ya rungumeta sosai yana patting bayanta, daidai kunnenta ya ce “It’s ok, I’m here for you Madam” Ta ce “I’m sorry” Ya riÆ™o fuskarta ya ce “For?” Ta ce “Na abinda ya faru” Ya yi murmushi yana girgiza kai ya ce “It’s ok” Ta ce “A’a ka yi fushi” Ya girgiza kai nan ma ya ce “Banyi ba” Tana maÆ™ale jikinsa hannunta na shafa kwantaccen sajansa ta ce “You left, ka je wajan matarka” Sai kuma ta sake rushewa da kuka, a hankali ya ce “I am sorry, bana iya fushi da ke” Ta ce “Gashi ka je wajanta” Ya lumshe idanunsa ya ce “Stop kukannan ban so, ai kin san ban taÉ“a miki Æ™arya ba so bana nan ne” Ta jinjina kai ya sumbaci kumatun ta, kana ya juya ya É—auke plate É—in cake ya fara ci, ta zare idanu ta nufe shi ta ce “Ni dai ka bani abuna” Ya zagaya yana ci yana dariya, suka shiga zagaye parlon ganin ya kusa cinyewa ya sa ta fashewa da kuka ya yi saurin ajjiye plate É—in yana rungumeta sosai while yana sake dariya ya ce “Sorry” Ya kamo fuskarta yana É—ora bakinsa a nata ya ce “Haa” Ta buÉ—e ya juye mata sauran cake É—in daya tauna, ta lumshe idanunta tana jin kamar ma ya fi daÉ—i daga cikin bakin nasa, tana gama ci ta sakar masa cizo a tongue zata É—auke bakin ya riÆ™e ta, ganin gumin dake tsastsafowa daga goshinsa yasa ta fahimci cizon ya ratsa shi, sai jikinta ya yi sanyi a hankali kuma ta kama harshen nasa daidai tsinin ta sakar masa wata Æ™yakÆ™yawar sumbata a hankali a kuma sanyaye ciki yanayi na shauÆ™i da buÆ™atar mace zuwa ga mijinta ta shiga tsotsar wajan, while hannayenta kuma na gaban rigarsa ta fara É“alle botirs É—in, bai jira ta kammala ba ya saka hannu a igiyar gaban rigar nata, ya sutale ta faÉ—i Æ™asa yau bai farka ba saboda ba mai zif bace, kasancewar babu bra a jikinta ya sanya yana cire rigar tayi saurin sakin bakin nasa ta rungume shi tana É“oye Æ™irjinta, a hankali ta saka hannu a naked back skin É—insa tana shafawa while tana kissing brest É—insa da yake babba, daidai kunnenta ya ce “Something new?” Ta É—aga kai ta kalle shi hawaye fal idanunta sun yi caÉ“a-caÉ“a a fuskarta ya tallafo fuskar da kyau yana É—ora nashi akai ya yi kissing lip’s É—inta kaÉ—an but a hot kisses, Khalil is the best kisser haka Jee take ji Kspider ya Æ™ware wajan kiss, calmly ya ce “What?” Bata bashi amsa ba sai ta É“oge da waÆ™a mai cike da kai saÆ™o ta shiga rerawa tana cewa. _“Ehh; Ai duniya ta shige duk saninmu tsoro nake kar aje a rabamu, ni na fisu muttuwa ta raba mu zaman amana mugasgata wannan”_
Tunda ta fara yake binta da kallon bakinnan nata, tana yi shi kuma yana zagaye lip’s É—inta da yatsar shi, a hankalce yake fahimta da kuma noticing kalaman sai kuma ya saki murmushi kafin a hankali ya haÉ—e bakinsu waje guda tare da É—aga ta sama zuwa kan mirror ya saka hannu yana zare ribbon É—in kanta…

 

No comments