Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 26


[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: _*Arewabooks@Nimcyluv*_
A É—an tsorace cikin yanayi na kiÉ—ima da gigicewa da wani irin firgice kuma Abbu yake kallon fuskar Gimbiya, cikin Æ™anÆ™anin lokaci kuma wata zazzafar zufa ta shiga yanko masa a dukkan jikinsa, a fili kuma a kausashe yana yarfe hannu babbar riga ya ce “Fulani” kalmar data ja hankalin Uncle Isma’il kenan zuwa ga É—an uwan nashi, a É—an hanzarce ya juya zuwa ga fuskar Gimbiya a kiÉ—ime shi ma ya furta “Fulani” Hakan kuma ya yi daidai da shigowar Aaliyyah da kuma Latifa, Aaliyyah ta zubawa Æ™yakÆ™yawar matar idanu wacce Khalil ya kwantar da ita saman gadon marasa lafiya, Dr ya kalli Khalil ya ce “Shall we?” Ya girgiza kai yana mai jingina da jinin bango, bashi da wani Æ™arfin halin duba Gimbiya sbd he’s shocked the same time confuse. Aaliyyah ta bi matar da kallo ganin kamar fuskar Majeederh aka cira aka sanya mata, bata san mahaifiyarta ba tana dai ganinta a photo lokaci zuwa lokaci, likitoci wajan huÉ—u ne suka shigar da Gimbiya emergency room aka bata gado kusa da room É—in Majeederh,wajan ya É—auki shiru kowa da tunanin da yake a ran shi, idan kuma kaga Khalil zaka tausaya masa time to time yake zubawa Dad Idanu ya yi ta kallonsa kamar bai san shi ba, can kuma sai ya É—auke kai yana saki wata É“oyayyiyar ajjiyar zuciya. Dad É—in ma, a irin halin da Khalil yake ciki a haka yake, deep down na zuciyarsa tsoro da fargaba ne fal ran shi, Why is she still alive?? Da gaske ita ce ko dai wata mai kama da ita ce? Ya akai ta kasance a a raye all this year’s? Mai yasa bai taÉ“a samun information na kasancewar a rayen ba? Ko Investigators É—in nasa ne suka yaudare shi?. Mai martaba Ajlaal Sultaan was totally confused, He was at a loss for words, his thoughts stopped and he didn’t understand anything, kallon komai yake kamar almara, bayan tsayin shekaru wajan 18 Gimbiya ce ta miÆ™e tsaye akan Æ™afafuwanta? Tunanin da Ajlaal yake shi ne abin da Zaytoon ke yi, Dr ya sake dawowa idanunsa akan Khalil da kansa ke sunkuye ya ce “Dr Khalil” Khalil ya É—ago kansa tare da kallon Dr bai ce komai ba, Dr ya ce “Jinin da za a sakawa matar ka?” Khalil ya É—an matse hannunsa sai kuma ya miÆ™e tsaye yana nuna Mai martaba wanda ke alamanta cewa ya amince a sanya mata jinin na Mai martaba Ajlaal Sultaan, kai tsaye kuma Khalil fita ya yi daga cikin emergency É—in ya nufi can waje gefen wasu bishiyoyi tare da zama ya KaÉ—aita da kowa, tunani daban daban yake “Who is she? Me ya sa ta suma da taga Dad? Ya akai ta san sunan Dad? Akwai wata alaÆ™a tsakanin su ne?” A hankali ya ji an ce “I knw her, na santa” A nutse Khalil ya kalli Dad ba tare da ya ce komai ba, Dad ya zauna kusa da Khalil yana É—ora hannunsa a kafaÉ—ar shi ya ce “Ita ce silar zamanka abin da ka zama, ita ce silar kawo hargitse da rashin fahimtar juna tsakanin ni da kai, ita ce silar daya sanya na rabo da kai a lokacin da kake tsananin buÆ™atar kulawa ta iyaye, duk abin da ya sameka ita ce sanadi, ita ce dalilin raba RUHI BIYU, ta cuce ni ta cutar da rayuwata ta kuma yi yunÆ™urin kashe ka da hannayenta, kuma tayi al’Æ™awarin rabani da kai, taso ganin bayanmu duka amma Jesus na tare damu”
A É—an makake kamar wani mashayi ya ce “Jesus? Yana tare da kai not me, da Allah subhanahu wata’ala na dogara” Dad ya jinjina kai yana son a yanzu Khalil ya yarda da shi hundred patient na yarda ba zai iya gujewa komai na shi ba, ya numfasa yana gyara murya cike da rauni ya ce “Son ban san me take so ba, am sure a yanzu ma ba zata barmu ba, ka É—auki matarka mu bar Æ™asar nan yanzu, Before she woke up from her coma” Khalil dai bai magana ba, kuma bai motsa ba, calmly Dad ya ce “Guess who she is?” Da wani irin masifar zafin nama, jinkima, izza, zafin kai da taurin zuciya Khalil ya miÆ™e tsaye kamar zai daki Dad É—insa ya ce.
“I don’t want, I didn’t ask you, I don’t want to hear anything” Cikin É“acin rai shi ma Dad yana jin nasa girman kan ya zabgawa Khalil mari ya ce “Ko kaÆ™i ko kaso dole ka bini, daga yanzu ka daina rayuwar Nigeria har abada zan kai ka idan babu wanda isa ya sani even your wife” Khalil ya yi wani irin murmushi ya ce “Oh really? Mu zuba mu gani taurin kai na yafi naka Mr President sir” Yana faÉ—in hakan yabar wajan zuciyarsa a cunkushe yana tunanin meke damun nasa, He always creates problems between them.
Babu wanda ya runtsa a ranar, daga Abbu, zuwa Mr President, Khalil da shi kansa Mai martaba Ajlaal Sultaan, Majeederh daban bata san meke faruwa ba. Washegari da safe suna zaune a room É—in gabaÉ—aya Dr ya shigo bankuna riÆ™e da files yana duba Majeederh, Khalil dake zaune kansa a Æ™asa wanda tun safe daya shigo bai cewa kowa komai ma even his wife Majeederh, kallonta yake kamar bai santa ba shi kansa he don’t know what comes over him yana jin fargaba da faÉ—uwar gaba wanda bai taÉ“a jin irinta ba tunda yake, ga ciwon Majeederh daya tsaya masa gana Gimbiya gefe guda kuma zancen General Alpha yana nan zaune daram a zuciyarsa, Dr dake tsaye ya yi Æ™yakÆ™yawan murmushi yana kallon Majeederh kana ya kalli Khalil ya ce “Perfect match” Alpha ya kalli Dr É—in bai ce komai, Dr ya miÆ™awa Khalil takadda ya ce “Your wife is two months and two weeks pregnant” Dr ya sake murmushi ya ce “Congratulations dear friend, Allah subhanahu wata’ala ya inganta ya raba lafiya” kamar saukar aradu haka General Alpha ya ji saukar maganar ta Dr, maganar cikin jikin Majeederh ya gigita shi ya sanya ya rasa nutsuwa da lissafin da yake É—auke da shi, bai yi tunanin ko da wasa Majeederh zata amincewa wani É—a namiji ba, wanin ma É—an cikinta, domin shi bashi da labarin Æ™addarar daya faÉ—a mata na haihuwar Baby Khalil, ya yi Æ™asa da kansa ganin jiri na neman yarda shi duk da cewa a zaune yake, Khalil ya kalli Dr da jajayen gajiyayyun idanunsa wanda suke É—auke da bacci a hankali cikin Æ™asa da murya ya ce “Thank you” Dr ya ce “My pleasure Dr Ibrahim” Majeederh tayi saurin kallon Khalil taga yaÆ™i kallonta, a sanyaye ta saka hannu ta shafa cikinta da matsanancin mamaki “pregnant?” Ta furta ta wani irin Æ™yakÆ™yawa kuma raunataccen yanayi, ta lumshe idanunta wasu hawaye suka shiga sakko mata tayi saurin juyawa, Maman Alpha bata yi mamakin cikin jikin na Majeederh ba, mmkinta É—aya jin har wata biyu da sati biyu wanda idan ta lissafa ya yi daidai da sanda ya É—auketa zuwa Qatar, wato tun kafin ta tare suka riga suka tare abin su da kansu, sosai kowa ya yi farin ciki Majeederh kunya ta hanata sakat, Yaya Bilkisu dai dariya kawai take tana girgiza kai yadda kuma zata sha tsiya wajan Innati kawai take tunawa, Dr ya ce “Allhamd jikinta da sauÆ™i mun rubuta mata magani Dr Khalil zai Æ™arasa abin da muka fara” Uncle Isma’il ya ce “Hakan na nufin an sallameta” Dr ya ce “Sure, In sha Allah” A hankali suka fice bayan Ajlaal Sultaan ya shaidawa kowa meeting wanda za a yi a gidan Uncle Isma’il É—in. Room É—in ya rage daga Majeederh sai Khalil jin shiru ya sanya Majeederh juyawa suka haÉ—a idanu da Khalil ta zuba masa idanu ganin duk ya sauya hankali ta miÆ™e zaune ta ce “Me ya sa zaka damu kan ka?” Ya É—an ware idanu ya girgiza kai ya ce “For?” Ta ce “I am sorry” Ya Æ™ara cewa “For?” Ta yi Æ™asa da murya ta ce “Akan Yaya Alpha” Ya zuba mata shanyayyun idanunsa ya yi murmushi ya ce “Frgt” Ta É—an langwaÉ“ar da kai ta ce “Ban yi haka da nufin komai ba, nasan da shi na zaÉ“eka, he’s my cousin, and he still be, kai kuma” Ta yi shiru yana kallonta sai sai ta ce “You’re my husband, enternal husband” Ta kama hannunsa ta É—ora a cikinta, ya yi saurin lumshe idanunsa jin É—umin cikin wanda gudan jininsa yake ciki daidai kunnen shi ta ce “The father of my children” Ya ware idanunsa kamar zai dry ya faÉ—aÉ—a fuskar shi da murmushi calmly ya ce “Me?” Ta buÉ—e ido ta ce “Me fa?” Ya lumshe idanunsa ya buÉ—e ya ce “The last words before wannan” Ta ce “You’re my husband” Ya girgiza kai ya ce “Laaah!!” Taya jim sai ta ce “Na zaÉ“eka na barshi” Ya yi dariya sosai wacce bata taÉ“a ganin ya yi ba, zallar kyansa ya bayyana da wani irin tarin kamala wacce kamar yanzu ta kula da ita, sosai ya yi sai kuma ya girgiza kai ta ce “What, me ne?” Ya girgiza kai ya ce “Babu” Ta haÉ—e fuska sosai ta ce “To meye na dariya?” Ya juyawa gabaÉ—aya tare da saka hannu ya yi squeezing bakinta a kunnenta yana sakar mata numfashi mai zafi ya ce “To yaushe kika zaÉ“an? Ina har suma ki kai?” Ta É“ata fuska ta ce “Eh, ni na zaÉ“eka ai ka sani” Ya ce “To” Ta ce “Ka manta ka ce baka so na? A latter? Ka ce first love É—inka kake so?” Ya jawota gabaÉ—aya yana shafa cikinta suka kalli juna ya yi ta kallonta ya ce “I like you” Ta ce “Why not love?” Ya goga hancinsa a wuyanta ya ce “Thank you, na gode sosai Madam, Allah ya yi miki Albarka” Ta ja hancinsa ta ce “Husband material, idan na mutu na bar zuri’a ta wajanka bani da doubting” Ya ware idanu ya ce “Kenan zatonki zaki rigani mutuwa?” Ta ce “Sosai” Ya kwaÉ“e fuska ya ce “I don’t think so, ko yanzu na mutu nrml ne?” Ta ce “Like how” Ya yi murmushi ya ce “Like yadda kika ji, ban jin zaki iya barina a raye domin jikina na bani na kusa baÆ™un….” Da sauri ta rufe masa baki sai kuma ta fashe da wani irin raunataccen kuka, hannu yasa sai jawota ta shiga dukan Æ™irjinsa, ya zuba mata Idanu idan ta kula kamar ruwa ne kwance a idanunsa, da sauri ya jawota ya rungumeta sosai zuciyarsa na harbawa muryarsa na rawa ya ce “Sorry” Ta É—ago kai zata kalle shi ya yi saurin É“oye fuskarsa a wuyanta, a hankali suka ji an ce “You both come out” Majeederh ta É—ago kai da tsananin mamaki take kallon wacce suke shegen kama da juna, a hankali ta ce “Ajlaal’s sister” Khalil tunda ya kalli matar sau É—aya ya yi saurin É—auke kansa, Gimbiya dake tsaye hannunta maÆ™ale da kanona ta zuba musu Idanu calmly ta ce “Out” Majeederh ta miÆ™e tsaye tana saka mayafin doguwar rigar jikinta, tare da sakkowa Æ™asa, Gimbiya idanunta akan Khalil ta nuna shi da hannu idanunta akan Majeederh ta ce “Shi yaron can ba zai fito?” Majeederh ta kalli sai kuma tayi shiru a hankali kuma ta fice daga cikin room, Gimbiya ta yi ta kallon Khalil, kallo na mamaki sai kuma ta juya tare da ficewa ya sauke numfashi da Æ™yar yana dafe kansa.
Parlon a cike yake gabaÉ—aya family, Germany, Saudiyya, Nigeria. Bayan addu’a Ajlaal ya numfasa a hankali ya ce “Nasan za ku yi mamaki ko? Tun a zuwan Majeederh Æ™asar Egypt nasan she’s the part of our family, banga fuskarta ba tafiyarta kawai na gani da idanunta na shaida hakan, hakan yasa na fara bibiyarta da zaton ku Æ´ar uwat ce da na yi missed sama da shekaru, mai sake gasgata cewa ita É—in jina na ce kuma tsatsona ba sai dana jin sautin muryarta, a ranar ban iya samun cikakken bacci ba, kamar yadda Zaytoon bata iya ba” Ya sauke É“oyayyiyar ajjiyar a fili, duka suka kalli Majeederh ita kuma kanta a Æ™asa ya ce “Bani da cikakkiyar lafiya, domin abubuwa da yawa sun mini iyaka da farin ciki, na saka a raina dole na je Nigeria kota halin yaya ne, duk kowa shamakin da rayuwa ta gindaya mana a tsakani, sanda naga fuskar Majeederh a gadon asibiti na kwana sbd tashin hankali, ita kanta kuma bata sani ba, shekarun baya a office É—inta na risketa tana ciwon ciki wannan ya bani damar ganinta ba tare saninta ba” Khalil ya yi saurin kallon Mai martaba Ajlaal Sultaan, sai kuma ya É—auke kai ya É—ora da cewa “Na koma Saudiyya cike da farin ciki, na koma ci alwashin sanin komai ta hanyar yin DNA test, sbd na samu gashin kan Majeederh wanda ya bani damar samun Æ™wararren likita daya ya yi mini bayanin shi kansa DNA test É—in da yadda yake, bai nuna mini cewa Æ´ar Hawwa’u bace, ban kuma san ya mu’amalarmu da ita yake ba, amma zahiri DNA test É—in ya nuna kawai alaÆ™a mai Æ™arfi tsakaninmu da Majeederh” Ya nuna Majeederh da hannu ya ce “Amma yanzu al’amarin ya juye, ganin mahaifin Khalil ya rusa tunanin da na yi ya kuma raba fahimta ta kashi kashi, hakan na nufin Khalil É—an Gimbiya ne, Mr President kuma mijinta ne” Da sauri Abbu ya miÆ™e tsaye jikinsa na rawa ya juya ya kalli Mr President ya kalli Gimbiya dake hakimce wacce izza da jinkimarta ya dawo sabo fil, ba walwala ko kaÉ—an a saman fuskar balle kaga wasa har ka kawo mata wargi, Abbu ya nuna Gimbiya idanunsa a waje cikin tashin hankali ya zaro photon aljihun shi sai kuma ya girgiza kai ya ce “She’s my wife, matata ce wlh ita ce ashe bata mutu ba, yaudarata Æ´an uwana sukai, Æ™arya Mr President ke yi wallahi she’s my wife she is still alive….

No comments