Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 40


0/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: “Zuleehart? Aure? Da yara kuma har uku? Wanne irin wasa ne wannan mara daÉ—in ji, you’re my neighbor not my daughter-in-law” Zuleehart ta Æ™araso ciki, kyawawan yaran suka biyo bayanta da sauri, Bilal, Dina, Waheed, Maman Alpha ta dinga kallon Bilal dake tsananin kama da General ta durÆ™usa kanta a Æ™asa hawaye na zuba a idanunta ta ce “I am sorry General, bani da zaÉ“i na gaji da zaman É“oye kai na, na gaji da rayuwa daga ni sai yarana, na gaji da zuwa gidan nan matsayin maÆ™ociya bayan ni surukar gidan ce, na gaji da É“oye Bilal i am tired of everything”. Uncle Isma’il
Ya ce “Kai na ya É—aure”
“Dame?” Uncle Bello ya furta idanunsa akan Bilal
“Bello kana ji fa? General ke da aure har da yara uku? Bayan duka mun san baya da shi sai yanzu?” Zuleehart ta girgiza kai while hawaye na sake zuba akan fuskarta ta ce
“Ask him Uncle, ba zan masa Æ™arya ba, bana da kowa a Æ™asar nan, dalilin shi nazo” Uncle Isma’il ya ce “Alpha” General dake kusa da Majeederh ya É—ago kansa ya zubawa Uncle duk ya yi zuru zuru
Uncle ya ce “Mene gaskiyar lamari? Da gaske matarka ce? Su É—in yaranka ne?” Yaya Bilkisu dai bata uhm bata uhm’uhm sai Innati ta ce “Bama sai ka tambaya ba, kana ganin tsageran yaron nan kasan jinin soja ne, shi kenan ka rungumi matarka ka sake kululu uban kowa ya huta” Sai kuma ta fashe da kuka wiwi ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Ubangiji kayi mana magani, tunda uwata tayi cikina ta haifa, nayi cikin wasu na haifa ban taÉ“a ganin masifa irin ta jiya ba” A taÆ™aice Abbu ya ce
“Innati, ki bari muji abu É—aya” Tayi saurin cewa
“Yanzu Audil azizu maganata ka mayar amshin shata?” Clamly ya ce “Kiyi haÆ™uri”
Girgiza Æ™afa kawai take, Uncle Isma’il ya sake kallon Alpha cikin kakkausar murya ya ce “Ina magana kana tsare ni da Idanu? Abinda Yarinyar kenan ke faÉ—a gaskiya ne?” General ya juya ya kalli Majeederh wacce kanta ke Æ™asa, tsoro yake ya furta “Eh” ta ce ya yaudareta ya mata kishiya ko taÆ™i accepting auren nashi, tunda ya auri Majeederh bai ga dalilin da zai sanya ya yi wasa da damar shi ba, Zuleehart kallon Alpha take wanda yaÆ™i yarda ya kalleta.
Kau! Uncle Bello ya saukewa Alpha wani gigitaccen mari, wanda ya sa ya É—an dafe fuskarsa, cikin faÉ—a da bala’i wanda ba a taÉ“a jin Uncle Bello ya yi ba ya ce
“To! Ban haifi É—an da zai raina mini É—an uwa ba, da har ana magana kanawa mutane kunnen uwar shegu, who are you? Dame kake taÆ™ama da gadara? Eh?”
“Bello” Uncle Isma’il ya kira sunan Æ™aninsa, yana É—aga masa hannu, alamar ya saurara abi komai a sannu, ya lura Shock da damuwa ne ya yiwa Alpha É—in yawa, a karo na uku ya sake cewa “Ya zama last time da zan tambayeka, who is she?” Kansa a Æ™asa ya ce “She’s nothing, but a human being” A gigice Zuleehart ke kallon shi da wani irin masifaffan tashin hankali, jikinta na rawa da É“ari ta kasa cewa komai . “Ba matarka bace?” Ya girgiza kai, Maman Alpha kallon Bilal kawai take koman shi iri É—aya ne da General. “BuÉ—e baki za ka yi kai bayani, ya akai ta ce matarka ce? Wannan yaran fa? Kamar da kuke da wannan fa?” Ya nuna Bilal. Alpha ya ce
“I know nothing, kama kuma tsarin Ubangiji ne, she’s not my wife!”
Da wani irin sauri Zuleehart ta kalli Alpha, tashin hankali, ruÉ—u, gigita, suka haÉ—e mata lokaci É—aya cikin kuka ta ce “General kasan me kake cewa? Kasan me bakin ka ke furtawa? Kana cikin hankalinka?” Cikin tsawa ya ce “Kin sanni ne? Wani ya turo ki? Sharri zaki mini? Kin taÉ“a jin labarin nayi hauka? Yaushe na aureki? Mene hujjarki na auren?” Tayi baya kamar zata kifa da sauri yaran sukai kanta a tare lokaci É—aya suka ce “Maaa!” Bilal yazo wajan General ya riÆ™e hannunsa ya ce “Abbie, Maaa Abbie” General ya runtse idanunsa can kuma ya dakawa Bilal wata gigitacciyar mahaukaciyar tsawa ya ce “Leave” Bilal ya fashe da kuka, Zuleehart hooking brain É—inta yayi na wani lokaci ta kasa yarda ko gasgata abubuwan da suke faruwa, yau ita General ke faÉ—awa haka? Ta rabu da iyayenta saboda da shi? Tayi sadaukarwa mai yawa dalilinsa? Tun baya hayyacinsa har yasan waye shi? Ya bata labari ta yarda dashi, ya mata tayin soyayya ta amince masa, har aure? Kenan ya yi haka ne saboda ya manta da Majeederh? Gudun kada depression ya kama shi? Ta durÆ™ushe cikin tashin hankali ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” Kuka take kamar ranta zai fita ta kalli General ta ce “Ka ji tsoron Allah, ka tuna akwai ranar mutuwa ka duba yaran dake tsakaninmu” Ya miÆ™e kamar zai daketa yana nunata da hannu ya ce “Kee! Stay away from my life, ban sanki ba, baki sanni ba idan burin ki haÉ—ani da matata ce you decieve yourself, yara kuma ban haÉ—a komai da su ba” Ta kalli Majeederh ita dai Majeederh duk wannan tashin hankalin baya kanta, damuwarta ta ya isheta. Zuleehart tayi murmushin takaici ta ce “Haka ku Hausawa kuke, manta abu baya muku wahala, cin mana, yaudara, da rashin Æ™ima da darajar aure da matayenku, kuna wasa da zuciyar mata” Ta share hawayenta tana riÆ™e hannun Dina ta ce
“Ban dawowa, duniya nan zaka gani, lokaci al’Æ™ali” Ta danne zuciyarta ta ce “Yadda ka sama silar zubar hawayena, In sha Allah sai Majeederh ta zama silar zubar naka hawayen, yadda kayi wasa da zuciyata In sha Allah haka Majeederh za tayi da taka, yadda ka raunata tawa haka taka zata tarwatse, In sha Allah, In sha Allah idan har bani da hak’Æ™i akan ka, Allah zai saka mini tare da zu’riata” Ta girgiza kai ta ce “Da yardar Allah ba zaka taÉ“a samun wacce zuciyarka ke so ba, da yardar Allah ba zaka taÉ“a samun farin ciki a soyayya ba, da izinin Ubangiji sai soyayya ta sanya ka wahala Allah ya É—anÉ—ana maka so da daÉ—in da zaÆ™in soyayyar wacce ba zaka taÉ“a samunta ba a rayuwarka” Tana faÉ—in haka taja hannun Bilal dake ta kuka ta É—auki Dina, Waheed ya riÆ™eta suka fice daga cikin gidan. Maman Alpha ta miÆ™e tare da yin waje itama at the same time.

Washegari suna zaune a parlour, lokacin ma dai tattaunawa suke dake kuma weekend ne, a hankali ta yi sallama ta shigo, suka kalleta Maman Alpha ta haÉ—e fuska, Latifa ta shigo tana tura wani tsohon mutum a wheelchair, suka dinga kallon mutumin Abbu kamar ya ganeshi sai kuma ya manta ina ya san shi. Maman Alpha ta ce “Mene ya kawo ki yau kuma? Maza tashi ki fita” Tana kuka ta ce “Don Allah ku saurareni, hakan zai sanya ku Æ™ara fita daga duhun da kuke ciki ta wani É“angaren” Maman Alpha za tayi magana Uncle Bello ya ce “Bari muji meke tafe da ita ko?” Latifa Omar ta ce “Banga laifinku ba, na cancanci ko wane irin hukunci, son zuciya da kwaÉ—ayi da kuma baÆ™in ciki ya jani zuwa cikin kabarina tun kafin lokacin mutuwata, ban kasance Æ™awa Aminiya ta gari ba, duk abinda ya samu Majeederh ni ce sila amma ba komai ya zama laifina ba” Ta kalli Abbu ta ce “Abbu ka tuna wannan? Wani Alhaji Bashir da kuka yi maganar auren Majeederh akan Deal? Zai baka kuÉ—i ka bashi auren Majeederh?” Su Uncle Isma’il gabaÉ—aya suka kalli Abbu shi kuma ya dinga kallon Alhaji Bashir, Latifa Omar ta ce “Shi ne wannan, ga nan ya karÉ“i nasa hisabin duniyar, ka hana shi auren Majeederh bayan ka amshi kuÉ—in shi, akan gurÉ“atacciyar zuciyarsa ya sace Majeederh tare da reping nata, hakan ya faru ba tare da saninta ba, domin an gusar mata da hankali” Tayi Æ™asa da kai ta ce “Maman Alpha idan kin tuna sanda bamu ga Majeederh ba tsayin sati har tace mana farkawa tayi ta ganta a asibiti to a lokacin akai reping nata, babana ya shirya hakan” GabaÉ—aya suka kasa magana, Yaya Bilkisu ta ce “Ke mene haÉ—in ki da shi? Bayan Malam Umaru babanki?” Ta ce “Ni Adopted child ce, nima Shegiya ce bana da uwa shi kansa bai san wacece babata ba, yana da yara sunfi 30 yayi amfani da arziÆ™in shi ya yaudari Æ´an mata da zawarawa da yawa, rabin yaran shi duka sikila ne kamar yadda Baby Khalil ya kasance sikila, Mijin Malama baya da alaÆ™a da baby khalil banda ta Kasancewar shi É—an uwa, suna kama ne da Dr Ibrahimul-khalil saboda kasancewar, shi da Majeederh are cousins, baby khalil is my younger brother” Abbu ya kasa motsi, bai taÉ“a baÆ™in cikin kasancewar shi uba irin yau ba, yana ina duka hakan ke faruwa ne? “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” A fili ya ce
“Nawa ne kuÉ—in” Latifa Omar ta ce “Ba kuÉ—in ake buÆ™ata ba yanzu, yafiyar Majeederh ni da mahaifina muke so, abubuwa sun mana yawa, duniya ta juya mana baya sai data bari muka gama jin daÉ—inta, naci amanar aure data mijina gashi yanzu nida haihuwa sai kallo amma yanke mini mahaifa, duka abubuwan dana shiryawa Majeederh ya dawo kai na, hatta aurenta da Khalil ni ce sanadi nayi zaton bashi da kowa, a gari kawai yake yana gantali, shi da gang team sai nayi zaton zata sha wahala idan ta aure shi, ashe bokana ya rufeni bai faÉ—a mini asalin waye Dr Ibrahimul-khalil mijin Malama ba” Innati ta miÆ™e tana dungure kan Latifa ta ce “Annamimiya, algunguma Æ´ar maza mai warin zina” Kuka kawai take, Alhaji Bashir baya motsi saboda paralyse shi kansa kuma sikila É—in ce da shi. “Na yafe miki, dake da shi, but it’s over between us” Latifa ta ce “Na sani, kinfi Æ™arfina kin mini nisa, don Allah don Annabi ki bani baby khalil na riÆ™e na dinga kallon yaro a gabana ko zan ji daÉ—i” Majeederh ta ce “Allah ya sauwaÆ™a, ki É—auka bashi da haÉ—i daku, zan ma nesanta shi daku” Maman Alpha ta ce “Ai yara kike so? Sanda kike ta zubar da kyautar da Ubangiji ya yi miki bakya tunanin zaki iya son haihuwa Nan gaba? Hoooo Æ™aaasa! An yafe muku tashi kuje” Fita sukai jiki a sanyaye Abbu ya dafe kansa dake juya masa.
A hankali Khalil ya juya kujerar da yake zaune, bluetooth a kunnen shi yana jin komai dake faruwa, domin a jiya sai daya sanya wata na’urar É—aukan sauti a gidan, ya kuma saita ta, idanunsa sukai jajur. John ya ce
“Mene amfanin É“oye kanka ne? Yana da kyau su san mijin malama is still alive” Khalil baiyi magana ba, sai jijiyoyin kansa da suka fito tare da yin É—oÉ—ar a saman goshinsa, idanunsa sukai jajir John na lura da yadda naman jikin Khalil ke rawa, gargasar jikinsa ta mimmiÆ™e tsaye tana zubewa. Har John zai yi shiru sai kuma ya ce “Mene amfanin zuwa Orphanage É—in nan kace zaka yi rayuwa cikin yaran da kake taimakawa?” Khalil ya miÆ™e tsaye yana dafe kansa John ya miÆ™e ya ce “Ko wajan Ummie ne ka….,” Bai Æ™arasa maganar ba yaji Khalil ya É—auke shi da mari ya damÆ™i wuyansa ya haÉ—e da jikin bango duka jikinsa rawa yake idanunsa sun firfito waje da Æ™arfi ya ce “Shut up!” Sai kuma ya saki John Khalil ya dafe kansa a gigice ya ce “My head” Daidai nan FaÉ—imatu ta shigo da basket kyakkyawar yarinya cikin kamilalliyar shiga, John ya ce “Wife stay right there” FaÉ—imatu ta kalli John wanda sunan shi tuni ya koma Othman Zannur. Ta ce “Dear Yaya Khalil na kawowa abinci fa” John ya ce “Wife i said ki tsaya nan ko” Ta tsaya tana kallon Khalil durÆ™ushe, John ya kama hannunta suka fice tare da rufe Æ™ofar, babban Orphanage ne, gidan marayun ya haÉ—u Khalil tun yana asalin bad boy É—insa ya gina, FaÉ—imatu a gidan ta tashi itama har zuwa lokacin da John ya aureta, yara ne sosai a gidan Khalil na mutuwar son su kamar rai haka kowa na Orphanage É—in. Khalil ya jima zaune kafin ya miÆ™e tsaye ya É—auki bottle water ya zubawa tsakiyar kansa, kamar ya kira Zaytoon ko Mai martaba Ajlaal haka yake ji, amma ya É—auki niyyar sai ya yiwa kowa hauka duk wanda ya shiga rayuwar Majeederh dame Æ™oÆ™arin raba shi da ita more especially GENERAL ALPHA BELLO KHAN. tsayin wata guda kenan kullum Khalil yana zuwa bedroom É—in Majeederh, sai asuba yake guduwa ya razana Uncle Bello hade da General, Majeederh kuma taÆ™i yarda ta tare, ta yarda zata rayu da ruhin Khalil tunda yana sanyata cikin farin ciki, kuma har yanzu a tunaninta a mafarki yake zuwar mata, tayi wani irin kyau haske da Æ™iba Maman Alpha har mamaki take, cin abicinta ya Æ™aru shi da kan shi Khalil ya fahimci haka, har wata guda ba wanda ya san labarin Khalil na raye! Even his mother, Aaliyyah bata Æ™asar ma bakiÉ—aya ita da Barrister Aliyu ya É—auketa sun barwa Latifa gidan.

Yau ma kamar kullum Khalil ya hauro ta katanga ya sanya fararen kaya voyel ne fari tas da shi, kai tsaye direction É—in da zai kai shi bedroom É—in Majeederh ya nufa, ya zuge glass É—in window ya diro, abinda bai taÉ“a gani ba ya gani, ya ganta kwance ta rungume Alhassan dake ta kuka zai sha tea cikin dare tana bashi kuma ya tarwatsa cup É—in saboda ya ji haushi, baccin da ya yi kenan bai sha ba, Khalil ya zubawa fuskar Alhassan idanu ganin wata mahaukaciyar kama da suke da yaron, nan da nan ya fara loosing control É—in shi, so da Æ™aunar yaron ya wanzu a zuciyarsa, ya Æ™arasa bakin gado ya zauna, a hankali ya kifa kansa tare pecking kumatun Alhassan yana buÉ—e idanu yaga yaron ya kafe shi da Idanu, sai kuma ya É—auke shi ya rungume yaron kamar yasan babansa ne ya Æ™anÆ™ame shi yana sauke ajiyar zuciya, sun jima haka kafin Khalil ya goya yaron abayan shi dake Alhassan É—an fitina ne irin babansa ya Æ™anÆ™ame shi, Khalil ya kama window É—in ya dira yana jin Alhassan yana kyalkyala dariya a haka ya fice da yaron goye a bayansa…
[

No comments