Breaking News

Rainon Soja 3

 

              Free page 3_______________________

        MAMAN TEDDY

           Marubuciyar

           My Lady boss

           Walijaam


           Siyasata

           Yar maula 

           Kwaryar sama

           The virgin maid

           Gidan Ƙwarata

           The Sexy Boss

                Yar aiki 

          Bafullatanan Ruga

          X world duniyar shahara

           Mr romantic

           Dijama 

           Kwarton manya

           Yar tsakar gida

           Zuma da maɗaci

           Sadaka yalla

           Yar waye

           Taɓarah

________________________

"Da sauran su💃🏻 a yanzu kuma gata ɗauke muku da sabo mai ɗauke da sabon Salo na musamman wato Rainon soja , niko da kaina nace za'a sha duka😹soja da raino ai abun ba'a magana 🤣labarin sai wanda y karanta shi kar ki bari ayi babu ke Hajjaju...labari ne mai tafe da rikirkirteccen Al'amura wanda da fari sai kunce ya abun yake , Gaban yafi farkon🕊️dadi tun a yanzu ina sauraren comments din ku da masu fatan alheri na gode sosai . Sannan masu buƙatar daga farko don Allah kuna rinƙa tambaya ne a wasu groups da kuke ciki , idan kuka biyo Ni ayyukan da hidimomin nawa suna da yawa , bana samun damar turawa ta private 🙏🏻.  Gare ku masu buƙatar fara payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake ; Regular group ₦500 

Vip group ₦1000

SPC payment ₦1500

Via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 Vtu transfer number 09061466409 Yan Niger zaku turo da katin Airtel 500f . 


Duk wanda nayi ma tallah a shafi na ku bishi kuyi kasuwanci dasu ina da cikakken Aminci dasu da ba babu cuta inshallah. Sannan masu buƙatar na tallah masu hajar su ƙofa a buɗe take 💃🏻 .


                     •••••


Takowa yayi yana Fuskantar Mami da itama shi take kallo yana ƙara gyara zaman yarinyar dake bisa wuyan sa , Yes Mami zan Aje aikin soja na naɗan wani lokaci, zan raini Ma'eesha har ta girma , zata taso ne a hannu na Wato RAINON SOJA...................!


Rainon soja ”! 

Tabbas ya tabbata Aliyu baka da Hankali , ko ka tarkata ka fitar mun da yarinyar nan daga cikin gida ko kuma yanzu kaga ɗanyar hukunci daga gare Ni . Tayi maganan tana rufe idanun ta babu alamar rahama a tare da ita , don ta lura sai tayi masa zafi-zafi sannan zata iya tanƙwara zuciyar sa .  Muryar Daddy ne ya katse su wanda tun da suka fara maganganun nasu tun da fari yana daga Saman up stairs da yake saukowa yana sauraren su " Cikin Muryar sa ta manya General Saleh Yelwa ya fara da cewa " Haidar ”! Ali Haidar har yanzu kafiyar nan naka bata rabu da kai ba ko? Duk da ita ce ai ka biyo, yayi maganan yana kallon Mami da take zabga mawa Aliyu Harara, Yanzu ba zamu hanaka abun da kayi niyya ba Haidar, tun tasowar ku nan gidan Daddyn ku gida ne mai cike da yanci kowa abun da yake so yake yin sa . Amma ka sani muna da iko da kai da dole idan munce abu sai kayi shi koda bai maka ba , ai mu muka kawo ka duniya baka kai ka haifo mu ba .


“Daddy...”!


“Saurara mun ,yi mun shiru sau na gama magana ta sannan kayi naka , General ya katse yaron nasa yana takowa zuwa tsakiyar falon.  Baka da hankali har yanzu kan ka Rawa yake yi Haidar ka fara mantawa da Waye Ni , Saboda tsaban sarganci kawai kaga yarinya a jeji kasa hannu ka ɗauko ta ,kuma kana maganan zaka bar aikin soja? Naga dalilin da zai dakatar da kai daga aikin nan.  Ni bai dame mu ba ka riƙe ƴa ko ka kaita duk inda zaka kai ta,amma mu dai ka sani Soja kaman kayi shi kuma yanda ka fara babu tsayawa . Sannan fitowa daga Barack da kayi yau sai ka fuskanci hukuncin daga gare Ni”. 


Kallon Daddy Mami tayi don ita har ga Allah bata son duk abin da zai ɓata ran Aliyu , Sannan kuma tasan Genaral Saleh Yelwa da magana ɗaya idan yayi ta sai anyi shi.  Cikin sauri ta kalli Daddy tana furta“A'a janar ka rabu dashi kasan idan ya koma can ma horon da zai fuskanta sai yafi ta nan. Aliyu maza koma ka mayar da wannan yarinyar ko ka bani ita na miƙa mawa police a shigar da case akan lamarin ta ” .


“No mami”. Wannan ba abu bane wanda zai yiwu, nace Miki duka moton fa sun ƙone itama Allah....... Alright na Fahimta. Mami tayi maganan a ƙufule cike da jin Haushin taurin kai irin na yaron nata , Daddy na wuce Office shi zan turo Babba yazo ya fara amsan hukuncin sa ” . Tana gama faɗin haka ta juya tana ficewa daga falon,yayin da General Saleh Yelwa shima ya fara ficewa daga falon ne Muryar Aliyu ya katse sa. “Daddy na shirya amsan ko wacce hukunci daga gare ku , amma ban shirya amincewa a rabani da wannan yarinyar ba , a gaban idona naga gawan iyayen ta , bata da kowa ,ko gidan marayu aka kai ta baxasu bata kulawa ba . Meye amfanin arziƙin mu da ba zamu iya daukar nauyin wannan yarinyar ba? Mu zamu iya kulawa da ita....Eh ƙwarai zata samu kular soja”! Daddy ya furta yana katse Haidar tare da cigaba da cewa “ ban damu ba don ka raine ta amma ka sani Soja shine cikar burina akan ka , So nake ku zama kamar Ni, koma nace fiye da Ni. A yanzu ina da matsayin Genaral kai kuma so nake naga ka zama Marshal a kaf Nigeria mutane uku ne suka taɓa iya riƙe matsayin Marshal a aikin soja don haka haidar ko kai ko Yayan ka Khaleel dole ina buƙatar ganin wanin ku ya zama Marshal, ba General nake so ku kai ba ”. 


Jub-jub-jub-jub . Babba ya shigo falon wani irin ƙaton basamuden soja ne , ɓaki ƙirin har bula yake yi na baƙi fuskar sa a murtiƙe wannan ko a hanya ka gan shi sai ka face ba zaka tsaya ba🤣 . Ka hora mun shi ta hanyar bashi training exercise mai wahala daga nan sai ya koma NDA . Ok general. Babba ya furta yana ƙame mawa Daddy . Yayin da shi kuma ya juya yana barin falon .


Kallon babba Aliyu yayi kana yace “Babba please Bara na ba Ma'eesha wani abun da zata ci , kaga bata ci komai ba kuma alamu sun....cike da murya ta Basawa Babba yace “Yi sauri”. Nufar fridge Ali yayi cikin sauri yana Buɗewa tare da fiddo da nutri mulki yasan wannan don jidderh ake ajiyewa, Saurin Ɗaukar Glass cup yayi yana cewa “ Mu tafi ” . Bayan gidan suka nufa can ƙarshe inda aka saba hora su duk idan sunyi laifi. A hankali ya sauke ma'eesha yana kallon kyaƙyƙyawar fuskar ta,kana ya fara kokarin aje ta ƙasan wani bishiya mai ƙasa ƙasa don wurin kaman gerdina yake . Buɗe baki Ma'eesha tayi tana fara tsala ihu tare da riƙo hannun Ali haidar tana juyar da kan ta tare da kokarin riko hannun shi irin na yara . Don duka kallon baƙi take yi ma sauran Sojojin.  Ganin yanda Aliyu ya ruɗe yasa Babba dan tsagaitawa yana jiran ya rarrashe ta sannan ya bashi horon kaman yanda General yace dashi.  Ɗaukar Ma'eesha yayi yana Girgiza ta tare da Buɗe nutri milk din yana fara bata ba bu magana don shi ba gwanin surutu bane ,sai dai yayi mamakin yanda ya iya kula da yarinyar ma haka.  Shiru kaji tayi tana amsan madaran tana sha , kusan mintuna Goma kana ta ture bakin ta da kan ta alamun ya ishe ta . Farin hankie yasa yana goge mata bakin ta ,kana ya kalli babba yana cewa " ina jiran ka. Sauke yarinyar ka aje ta can gyefe.  


Wani irin kallo Aliyu yayi masa kana cike da haɗe gira ya furta " Naka ka bani horo inda zan aje yarinya wannan Ni ya shafa Yallaɓai ". 


Girgiza kai Babba yayi kana ya kalli ma'eesha wanda tausayin yarinyar ya kama shi ,duk da bangare ɗaya na Zuciyar sa yaji zafin kalaman Aliyu. Kallon sa yayi yana cewa "Sit-up zaka yi na awanni biyu daganan sai ka koma Barack . Ɗauke kai Ali yayi yana Maida Ma'eesha wuyan sa tare da fara yin Sit-up ɗin wanda hakan yayi mugun ba da yawa sojojin wurin mamaki . Shi fa yanzu ne ya fara Aikin sojan amma a haka yake sit up da yarinya a wuyar sa babu alamun ya gaji sai dai kawai gumi da sauko masa.  Kusan mintuna arba'in ya ɗauka bai huta ko ya tsaya ba ,don yasan yana tsayawa to farko zai dawo , sannan ƙila ma ya amshi wani horon da yafi wannan wuya.  Idanun sa sun yi jaaah don yanzu ƙafafun sa sunyi zafi kaman basa jikin sa haka yake jin su ,amma da yake yaro ne namiji sam bai yi yunƙurin dakatawa ba.  Hannun Ma'eesha yaji tana wasa da suman kan shi tana gwalon gwalon gwarancin ta na yara , Wannan yasa shi ɗago kai yana zuba mata Lulun idanun sa tare da sakin mata murmushi . Itako sai ta sake Wangale masa baki . A haka ya kammala bai ma san lokacin yayi ba sai da babba ya dakatar dashi sannan . Saɓa Ma'eesha yayi yana ficewa daga cikin gidan tare da komawa NDA a ƙasa .

**


Kai tsaye wurin ƙwanan su ya nufa inda kowa yake da gadon sa kaman zaman hostel . Areef ne cikin sauri ya dirko daga gadon sa yana aje littafin hannun sa tare da bin Ali haidar da kallo yana kuma kallon Ma'eesha da a halin yanzu idanun ta a rufe suke alamu tayi barci. Haidar Wacece Wannan?. Miƙa masa Ma'eesha yayi cike da rashin son magana Aliyu yace “ Ƙwantar da ita Bara naje wurin Major Jibril na sanar masa da dawo wa ta ” . Aliyu kana cikin matsala Major a fusace yake me yasa baka dawo tare da Lawal ba?. Banza Aliyu yayi ma Areef yana ƙoƙarin raɓa sa don ya kwantar da Ma'eesha ne Areef ya kuma riƙo hannun sa yana ƙoƙarin yi masa magana ne Aliyu ya harzuƙa wani irin asharrrr ya danna masa da sai da Sauran mates din nasu dake wurin suka kakkale su . Juyawa Aliyu yayi idanun sa sunyi jah cike da masifa da jaraba ya furta " Ya akayi ne ? Da me wani magana ne ,munafukan banza”! Shiru babu wanda ya tanka sa don sun lura a fusace yake , duk da Wasu dariya suke yi ma Areef ƙasa ƙasa , don yana wulaƙantuwa wurin Aliyu amma kullum yana nan nace dashi.  A gadon Areef ya kwantar da ma'eesha yana juyawa tare da ficewa daga Wurin . 


“Kaman yanda Areef ya faɗa masa hakan ya faru don ya wahala da horo iri² a wurin Major tun yanayi yana dauriya sai da idanun shi suka fara zubda ƙwallah duk ƙarfin zuciyar sa sannan Major yasa akayi masa ligi-ligi ƙafafun sa sun sha duka da sanda . Da kyar yake iya tafiya don yanzu har 8:pm yayi . 


Tun da ya shiga inda suke yake jin sauti kaman na kiɗa tare da ɗan kukan Yarinyar, Muryoyin abokanan sa sojojin yara yana tashi a hankali kaman masu bitan karatu wai nan waƙa suke yi ma ma'eesha😹 . Yana jan ƙafan sa da suka kumbura ga nauyi da jikin sa yayi ya isa inda suke . Gani yayi su kusan shida duka sun zagaye Yarinyar kowa nayi mata Wasa ,Areef na riƙe da ita , Sai Ibrahim dake aikin ƙarƙada Wani roba wai duka don tayi shiru , Sai wasu sun su dake mata waƙar baby girl . Ganin yanda ya shigo yasa su duka jikin su sanyi . Gadon sa ya nufa yana faɗawa ta rigingine kansa na kallon sama . Tun da ya shigo ma'eesha ta gan shi sai ta dakata da ƙananan kukan nata tana gwalon gwalon gwarancin ta . Murmushi Areef yayi yana kallon ta tare da nuna mata inda Aliyu ke kwance yana furta “ Uncle” . Uncle ya dawo. Hannu Ibrahim yasa yana amsan ma'eesha kana ya nufo inda Aliyu ke kwance. Da gudu ta saki zullo tana kuɓcewa daga hannun Ibrahim tare da faɗawa jikin Aliyu tana kwanciya bisa ƙirjin sa tana yin lamo . Sauke Ajiyar zuciya Aliyu yayi tare da ɗaura hannun sa bisa suman kan ta yana shafa mata a..................!



*Littafin Rainon soja na kudine regular group ₦500 vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 .*

*Ga masu buƙatar a tallah masu hajar su zasu iya mun magana sannan kar ku manta wurin yi mun share zuwa masoya baki ɗaya ngd*

No comments