Breaking News

Rainon Soja 4

 *🕊️RAINON SOJA🕊️*

*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story .*

      Free page 4





________________________

        MAMAN TEDDY

           Marubuciyar

           My Lady boss

           Walijaam

           Siyasata

           Yar maula 

           Kwaryar sama

           The virgin maid

           Gidan Ƙwarata

           The Sexy Boss

                Yar aiki 

          Bafullatanan Ruga

          X world duniyar shahara

           Mr romantic

           Dijama 

           Kwarton manya

           Yar tsakar gida

           Zuma da maɗaci

           Sadaka yalla

           Yar waye

           Taɓarah

________________________

"Da sauran su💃🏻 a yanzu kuma gata ɗauke muku da sabo mai ɗauke da sabon Salo na musamman wato Rainon soja , niko da kaina nace za'a sha duka😹soja da raino ai abun ba'a magana 🤣labarin sai wanda y karanta shi kar ki bari ayi babu ke Hajjaju...labari ne mai tafe da rikirkirteccen Al'amura wanda da fari sai kunce ya abun yake , Gaban yafi farkon🕊️dadi tun a yanzu ina sauraren comments din ku da masu fatan alheri na gode sosai . Sannan masu buƙatar daga farko don Allah kuna rinƙa tambaya ne a wasu groups da kuke ciki , idan kuka biyo Ni ayyukan da hidimomin nawa suna da yawa , bana samun damar turawa ta private 🙏🏻.  Gare ku masu buƙatar fara payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake ; Regular group ₦500 

Vip group ₦1000

SPC payment ₦1500

Via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 Vtu transfer number 09061466409 Yan Niger zaku turo da katin Airtel 500f . 



                     •••••


Tun da ya shigo ma'eesha ta gan shi sai ta dakata da ƙananan kukan nata tana gwalon gwalon gwarancin ta . Murmushi Areef yayi yana kallon ta tare da nuna mata inda Aliyu ke kwance yana furta “ Uncle” . Uncle ya dawo. Hannu Ibrahim yasa yana amsan ma'eesha kana ya nufo inda Aliyu ke kwance. Da gudu ta saki zullo tana kuɓcewa daga hannun Ibrahim tare da faɗawa jikin Aliyu tana kwanciya bisa ƙirjin sa tana yin lamo . Sauke Ajiyar zuciya Aliyu yayi tare da ɗaura hannun sa bisa suman kan ta yana shafa mata a Hankali. Girgiza ta yake yana ɗan jijjigata da jikin sa , kana ya lumshe Lulun idanun sa ba tare da yace da sauran abokanan nasa komai ba . 


Kallon Ibrahim Areef yayi kana ya maida kallon sa ga Aliyu da har a wannan lokacin idanun sa suke a lumshe tamkar mai tunanin wani Abu koma muce babu shakka wani abun yake tunanawa . Sauke Ajiyar zuciya Ibrahim yayi yana zama Gyefen mattress din Aliyu , “Haidar”! Ya ambaci sunan shi tare da mai da kallon sa sosai bisa kan Fuskar Aliyu wanda a yanzu ba tare da ya ware idanun nasa ba sai motsa laɓɓan sa da yayi yana cewa “ Ya akayi?”.


“Ali ka taimaka kayi mana bayani wai wannan yarinyar Wacece? A ina ka same ta , a yanzu shirun nan naka bata da wani amfani idan har ba zaka faɗa mana komai gami da yarinyar nan ba to Meye amfanin mu na zama abokai kuma aminan juna?” ... Muryar Areef ya katse su wanda yake maganan cike da nuna damuwar sa , don shi babu abun da yake shan wuya dashi gami da Aliyu Haidar irin Miskilancin sa da kuma Ƙafiyar sa. “Hummmm...” wani Gwauron numfashi Ali ya sauke kana ya ware idanun sa yana zuba su a bisa fuskokin su . Ganin yanda idanun Areef suka yi ƙwal³ tamkar zai saka masa kuka yasa Aliyu sakin Murmushin nan nasa Wanda idan yayi shi yake ƙara zama Arrogant, faffaɗan Hushiryar sa dake saman tsakanina fararen haƙoran sa na bayyana, wani sihirtaccen ƙyawun shi na fitowa . “To Meye na damuwa Abokai? Zan faɗa maku Wacece Ma'eesha, amma ku ɗan dakata na rarrashe ta tayi barci tukuna....Me ne kuka bata taci bayan fita na?”. Ya ƙare maganan yana ɗago Ma'eesha da a yanzu idanun ta suke a rufe tayi barci sai sauke numfashi take a hankali alamun tana cikin Lafiya. 


Ibrahim ne yace “ Mun bata tea ne , sai Ragowar Talia ce da Adam ya girka muka bata ” . Manyan idanun Aliyu ne suka fito waje jin an ba yarinyar da a ganin sa a yanzu bai fi ta iya shan Golden moon ko cerelac da sauran abincin yara ba.  A dai dai yanzu ma Golden moon yake ganin yafi kamata a bata ,wai amma sun bata talia . 


“Talia fa kace? Talian kuka Bama wannan yarinyar ƙarama ta ina zata iya cin sa?”. Ali tama fi cin shi fiye da tea din da muka bata , Alamu ya nuna tana cin sa sosai   . Bin su yayi da kallo kamin ya Lumshe idanun sa yana furta “ Ohk na fahimta ” .

“Yanzu Aliyu faɗa mana Wacece Ma'eesha?”....Areef yayi maganan yana dafa Aliyu, Kallon sa Aliyu yayi yana kai hannun sa tare da ɗago Ma'eesha yana ƙara Rungume ta tare da haɗata da ƙirjin sa yana jingina da gadon nasa . A hankali ya fara labarta masu yanda ya tsinci ma'eesha da kuma duk abun da ya faru bayan nan , zuwan sa gida da kuma Dawowar sa . 


Yanzu Mami taƙi amsar ma'eesha? But why mum ....Katse Areef Ali yayi da cewa“ Saboda muma dukan mu bata raine mu ba , Sojojin gidan suka raine mu duka , a yanzu ma tace bazata raini Ma'eesha ba , a ganina marainiya ce kuma bata da gatar da ya wuce Ni. Girgiza kai Areef yayi yayin da Ibrahim ya matsa kusa da Ali yana cewa“ kayi hakuri haidar bamu fahimce ka ba da fari” . “Bakomai Aboki” . 


Yanzu Zuwa gobe ka bani Ma'eesha na kaita wurin mummy na nasan ita zata riƙe mana ita har ta girma.


“Daaammm”. Ƙirjin Haidar ya buga da ƙarfi jin Furucin Areef na ya kai ma mummyn sa Ma'eesha  .“No Ni da hannu na zan raini Ma'eesha, bana buƙatar kowa ya rainon mun ita , ina so ta samu tarbiyyar da duka bamu samu ba , Saboda gatan ta mu kawai aka yi , itako tarbiyya zan bata wanda nan gaba itama zata yi alfahari da kan ta” . 


Shiru duka suka yi kana Ibrahim yace “haidar anan ɗin zaka iya ba Ma'eesha tarbiyya kar ka manta karatun soja fa muke yi wannan ce shekaran mu ta farko, dole mu maida hankali Tayaya zaka iya karatu da Raino? . 


Zan iya Ali jarumi ne”! Komai nawa na daban ne , Rainon soja ake faɗa maka yasha ban-ban da sauran rainon da ka sani . Cike da bashi ƙwarin gwiwa Areef ya furta “ Yes of course Ali zaka iya yin fiye da haka , ai mu sojoji ne dole komai namu ya zamana daban dana Mutane,mu fa masu kare al'umma ne , Tayaya tun yanzu ba zamu iya kulawa da wannan yar yarinyar ba ?’. Komawa Aliyu yayi yana ƙwantar da kan sa bisa pillow kana yace“ that why you're always my Best friend ever ” . Ku miyi barci saboda 3:00am muke da fita training.


**

Mami meke damunki tunanin mene kike yi haka? . Muryar Jidderh ya katse Mami wacce take zaune bisa Dinning table ta kasa sarrafa tunanin ta bisa abun da Aliyu ya ɗauko mata a jiya ” . Mamiii”. Jidderh ta kai hannu tana taɓa Mami tare da girgiza ta tana langwaɓe kai tare da ƙara Cewa “ What's up? What are you thinking for...? ” . Humm no..no... Nothing . Mami tayi maganan Muryar ta na rawa , kana ta ɗan kalli jidderh dake sanye cikin shigar Sport wear na makaranta duba ga yau laraba ,ranan saka rigar Sport kenan a school din nasu . Murmushi Mami ta ƙaƙalo don bata son Jidderh tasan da labarin Aliyu da wannan Yarinyar da ya ɗauko , don tasan yanda jidderh ke zafin kishi da son yayan nata bata son taga kowa ya rabe su , to Taji labari bata babu sukuni kuma sai na kuka. 


Sauke Ajiyar zuciya Mami tayi a zuciyar ta tana cewa “ Ai yaga ɓacin raina kuma ya fuskanci horo wurin babban don haka nasan tuni ya maida yarinyar nan , bani da lokacin ma ɓata shi a kan bibiyar wani hali suke ciki , don tuni ya fitar ma kansa da maslaha. Hannun ta takai tana shafa kan Jidderh kana tace “ Are You ready for school now” . Gyaɗa mata kai Jidderh tayi kana ta zauna a bisa kujeran ta inda nan ne wurin zaman ta permanent dama. A h natse mami ta fara bata breakfast ɗin ta , Duk da itama sauri take zata wuce Wurin aikin ta na police amma sai ta sauke jidderh a school sannan zata wuce.  Ganin yanda take feeding ɗin Jidderh da hannun ta tamkar jaririya ya sani cewa“ Lallai Mami anya lamarin ki babu .....🤔to muje dai gaba muji yanda zata ƙare. 


Ture kan ta Jidderh tayi daga ƙoƙarin da Mani take yi na kai mata soyayyar Irish din da take yi . Cikin sauri tasa hannun ta tana Fiddo da Wani white pepper warware shi tayi a bisa jikin ta tana nuna ma Mami zanen ta na jiya da tayi . Wow that's very nice my baby 💃🏻 Wannan zane haka mai kyau? . Yes Mami see daddy here, While Boo mie seating in front of Dad kinga yanda yake haɗe giran nan da ya saba.  Tayi maganan tana sakin dariya tare da nuna fuskar Aliyu Haidar , ta zana shi giran sa a haɗe , Gyefe kuma mami ne sai Yaya Khaleel dake sakin fara'a . Mami have you remembered any little thing about this? . Kin iya tunawa da wani abu ko kaɗan gami da Wannan zanen?. A'a baby na ban tuna da komai ba . 


“Hinmm , wannan fa zanen shekara ɗaya da ta wuce ana gobe birthday din ya Aliyu ne muka zauna a haka yana fushi mara dalili , shi kuma yaya Khaleel na tsokanan sa baki ga dukan mu muna dariya ba ,shine kaɗai fuskar sa babu annuri?. Kallon zanen Mami tayi tana sakin dariya irin na Polisawa😹 don ita komai nata haka zaka ganshi woman like a boss . Haka take bata da wasa.


Girgiza kai tayi cikin sauri tana cewa “ Ohhhh Yes ”.  Na tuna fa haka ya faru . So yau boo mie ɗina yake ranan zagayowar haihuwar sa haka ne mami atleast muyi surprising ɗin shi na yau.  Mami ina so mu zauna a haka mu Biyar,bana son ko wacce baƙuwar fuska ta kutso mana cikin Ahali. Muna jin daɗin rayuwar mu a haka . Ina son Ya Aliyu Sosai,amma shi bai damu dani ba , ya Khaleel yafi shi Sona shi yake kulawa dani Sosai . 


“Shiru ya isa haka babyn Ya Haidar , Wane ya faɗa Miki bai damu dake ba , ko jiya yazo kuma nasan don ya ganki yazo sai dai baku hadu ba.  Mami ya Aliyu yazo? A'a ba don Ni yazo ba koda kuwa ya faɗa Miki hakan, yaushe zai dawo . Hannu Mami tasa tana lankafe takardar kana tace “ ki kwantar da hankalin ki , ai wannan ce shigar su ta farko 4 mount za su yi su dawo gida hutu . Kuma Kinga a yanzu sun yi kusan 3 mount nan ba da jimawa ba. Miƙewa Jidderh tayi tana daukar lunching box ɗin ta tare da cewa " Mami na shirya mu tafi yanzu.....!



Ɓangaren Aliyu kuwa ƙarfe Uku na asuba suka fara shirin fita training exercise da suke yi na awa biyu kullum , Kallon Ma'eesha yayi da take barci yana ƙara rufa mata bargo kana yace dasu Areef mu tafi ko?. Fitowa duka suka yi su kusan shida suke rayuwa a babban Ɗakin kowa da gadon sa da kuma wurin mu'amalar sa . 


Sojoji na hanga birjik dukan su da kayan exercise suna running round tare da ɗaga ƙafafun su , Hango Aliyu Yasa Khaleel saurin isowa inda suke cikin Muryar sauke nishin wahala ya furta “ Haidar ina ka shiga tun jiya? ” . Kallon sa Aliyu yayi yana fara training exercise ɗin ba tare da yaba Khaleel amsan tambayar sa ba sai cewa yayi “ morning ya Khaleel ”. Shafa kan ƙanin nasa yayi yana wuce shi tare da cewa " ka kula yau Please kaji ban son ka sake wani laifi kaji? . Running up and down ya fara yi ba tare da yace da Khaleel komai ba...Kusan 5:30am sannan suka koma Wurin ƙwanan su . Don haka suke yi 7am su shiga class don karatu. Suna komawa Aliyu ya nufi Toilet ɗin su alwala yayo yana sallah kana ya juya yana kallon inda Ma'eesha ke ta barci har a lokacin. Miƙewa yayi yana ɗaura Towel a Kugun shi tare da nufar Toilet don ya watsa ruwa ya fito yayi shirin shiga aji kuma . 


Mintuna Sha biyar ya dauka ya fito hannun sa ɗauke da ƙaramar Towel yana tsane suman kan shi . Areef ya gani da Ibrahim sai Adam suna zagaye da Ma'eesha da ta buɗe idanun ta tana Kallon su duka , Kaman mai tunanin wani abu akan su ,su kuma sai murmushi da wasanni suke yi mata suna kiran sunan ta “Ma'eesha , Areef na wasa da hannayen ta , don kuka ne basa so tayi . Ganin haka yasa Ali sakin Murmushi yana saurin ƙarikowa inda Suke.  Da hannun sa ɗaya ya ɗagota yana Girgiza ta tare da yin wani tambul yana juyata sama zuwa ƙasa kan ta na kallon ƙasa yana dariya tare da cewa “ Kema Bara kiyi naki morning exercise ɗin ”. Innalillahi...Aliyu Meye haka? Bafa ƙashi a jikin ta”. Muryar Su Ibrahim ya katse shi a tare . Kallon su yayi yana kallon Ma'eesha dake ɓaɓɓaka dariyar ta babu alamun Taji tsoro . A'a dole itama zata rinƙa yin morning exercise sannan sai nayi mata wanka.................!





*Wani aiki sai soja😱💃🏻Rainon soja zamu sha kallo🤍🤣 to masu karatu kar ku manta littafin rainon soja na kudi ne masu ɓukatar fara payment ga yanda tsarin yake.  Regular group ₦500 vip group ₦1000 special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne ta wannan number 09061466409 yan Niger zaku turo da katin Airtel na 500f ...kar ku manta wurin yi mun sharing zuwa ga masoya baki daya🙏🏻🕊️.*

No comments